Showing 15001 words to 18000 words out of 121992 words
Chapter 6 - Rayuwar Abdussamad Book Complete Document by Yar Mutan Zazzau .txt
matuƙar birge shi sosai sam basa gajiya da juna sannan babu ruwan su da yaran su kullum cikin bege da ƙaunar juna suke.
Miƙo mishi wayar da tayi shiya katse tunanin da ya tafi, sai da yayi ɗan jim sannan ya amsa, cikin ladabi ya gaishe dashi, shi kuma ya amsa cike da so da kulawa.
"na san Mummyn ka tana ƙoƙari da kai sosai, babu wata matsala ko?", kamar yana gaban shi sai da ya ɗaga kai sannan yace; "eh babu", Dr yace; "to masha Allahu na yi muku order ɗin motocin ku kai da ƴan uwan ku nan da next week zasu iso".
"Daddy yaushe zaka dawo?", tambayar daya jefa mishi kenan, sai da yayi shiru sannan yace; "nan da lokaci kaɗan Insha Allah, kaje Hayin Rigasa?", shima ya jefa mishi tambayar.
" a'a, amma insha Allah zan je zuwa gobe", ya bashi amsa,Dr yayi murmushi yace; "to Allah ya kaimu, ka ƙara kulawa kaji", yace; "to", haka suka yi sallama sannan ya miƙawa Mummyn shi wayar wacce ta zuba mishi idanu.
Kauda kai yayi yana sakin murmushi, can ya kuma ɗagowa idanun nata yana kanshi, ya kwaɓe fuska yace; "First love, me kuma nayi?".
"ina zakaje kake faɗawa Daddyn ku nan da gobe?", ta tambaye shi, ya riƙo hannun ta sannan yace; "Mum muna magana ne akan zuwa na Hayin Rigasa", kauda kai tayi kamar bata ji me yake cewa ba shima kuma yayi murmushi ya kwantar da kanshi saman kujera.
Be san meke tsakanin Mummyn shi da dangin mahaifin nashi ba sai dai ya lura basa wata mu'amala sosai, shine ma me ƙoƙarin zuwa amma sauran basa zuwa sosai kuma itama bata tilasta musu suje kuma shima Daddy haka be wani damu da suje ba sai dai abinda ke bashi mamaki yadda Daddyn ke tilasta mishi shi yaje duk da Mummy bata so, to shi kanshi yaje sai ran shi ya ɓace wani lokacin sai dai duk da haka yana ƙaunar gidan.
🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸
*HAYIN RIGASA, KADUNA.*
Shureim ya kalli Naufal yace; "yauwa kaga wa'incan masu hijab ɗin ruwan toka to ɗaya daga cikin su ce, sannan suna wucewa zamu bisu a baya", Naufal dake ƙunshe dariya ya ɗaga kai duk da suna daga nesa ba zai gane yanayin su ba.
Idanu ya zuba musu har suka matso, duka kyawawa ne, masu haske sannan marasa ƙiba sosai, suna da idanu manya wa'inda suke farare hanci su dogo ne sai bakin su daya kasance ɗan madai-daici duka suna sanye da hijab me ruwan toka wanda ya ƙara fito da ainihin kyawun su, sannan kuma daga gani shine Uniform ɗin islamiyar tasu.
Ɗayar ya kalla, yadda take buɗe ƙananan haƙoran ta farare tas take faman zuba magana yayin da ɗayar ke sakin murmushi inda gefen kumatun ta ke lotsawa duka biyu tana kuma lumshe idanu da har yadda zarazaran gashin idanun ta ke rufe idanun ruf.
Iya kallo na ƙurilla yayi musu amma ya kasa gane makusar su sannan kuma ya kasa banbance su, duka kamar su ɗaya baya jin ko mahaifiyar su zata iya banbance su, ya sauke ajiyar zuciya sannan ya maida kallon shi kan abokin nashi wanda shima su ya zubawa idanu yana kallo.
" to anan waccece tsiwar taka?", ya jefa mishi tambaya, Shureim yayi murmushi yace; "kaima daga gani ai ya kama ta ka bambamce mana, kalle su da kyau ka gani ƙwaƙwalwar ka ta hasaso maka", ya ƙarasa yana kai duba gare su tare da sakin murmushi kamar wani ɗan can haka 🙄.
Naufal ya ƙara kallon su, izuwa yanzu kuwa sun matso sosai kusa dashi kuma yana iya ganin su tarr da suna daf da gifta su, shi dai har yanzu ba zai banbance su ba domin kuwa ko agogon dake maƙale a hannun su me ruwan toka kala ɗaya ne haka zobe dake yatsun su na hannun hagu, sannan atamfar da suka saka me Blue da light yellow duka kala ɗaya ne haka flat ɗin takalmin dake ƙafar su shima kala ɗaya ne wanda ya kasance blue.
Shi dai bashi da wani abu da zai bambamce su, ya maida kallon shi kan abokin nashi daya zuba musu idanu kamar zai cinye abin ban dariyar shine yana ganin sun yi murmushi shima zai, Naufal ya kalle shi ya kuma kalle su ya kwashe da dariya yana faɗin;
"Allah Shureim kana daf da ka zare", Shureim ya kwaɗa mishi harara yace; "so kenan ake faɗa maka malam".
Naufal ya kuma juyawa ya kalle su dan har sun gifta su yace; "nifa bana jin ko mahaifiyar su zata banbance su", Shureim dake tada motar yace; "me zai hana ta bambamce su tunda ita tayi naƙudar su ko kai kayi mata?", ya girgiza kai yana taɓe baki.
Bin su suka yi a baya har zuwa lungun da gidan nasu yake,daga bakin lungun suka yi parking sannan suka fito suna kallon gidan da suka shiga, gida na uku a cikin jerin gidajen dake lungun.
Nusreen da Nusram kuwa suna shiga gida suka tarar da Sahura da uban jibgin kaya a gaba sai kuka take sha, Mama Jummai kuma na gefe tana kallon ta.
Nusram tace; "sannun ku da gida Mama", Mama Jummai tace; "yauwa sannu", sosai hakan ya basu mamaki saboda zagi ne ke biyo baya amma yau ta amsa jiki a sanyaye.
Nusram ta kai dubanta ga ƴar uwar ta tace; "lafiya kuwa ke kuma?", Mama Jumman ta taɓe baki tace; "ina fa lafiya Nusram Nura ne ya sake ta saki ɗaya mahaifiyar shi tace idan be sake ta Allah ya isa shine ya sako ta".
Sosai Nusram ta tsorata, ta tsugunna kusa da Sahurar tana bata haƙuri, Sahura dake zubar da hawaye ta galla mata harara tana jan tsaki.
Nusreen haushi ya cika ta itama kuwa ta ja tsaki tace; "ai ga shi nan garin neman gindin zama kin jawa kanki raini a wajen ƙanwar ƙanwar ki, dama ai duk abinda mutum ya shuka shi zai girba kuma taya zaka kasance mowa a gidan mijin ka ƴaƴan ka ma kace dole sai sun zama wannan ƙaryane yadda kake gasa ƴaƴan wasu haka za'a gasa naka".
Mama Jummai ta miƙe tana wuci tace; "wallahi ki fita hanya ta Shegiyar ƴar Allah bani", Nusreen tayi shewa tace; "ga ƴaƴan Allah bani nan ana korowa gidan Mama, ai duk wanda yace tukunyar wani ba zata tafasa ba nashi ko ɗumi ba zata yi ba".
Mama jummai cikin hayagaga tace; "ai gwara su an shaida dan har aure sun yi kufa babu wacce keda mashinshini,ai ko yanzu kasuwa ta tashi ɗan koli yaci riba", ta ƙarasa tana cewa.
"ai da aure irin na ƴaƴan ki wallahi gwara na zauna har abada babu aure, auren jeka nayi ka ita kanta wannan ɗin da take kamar muciya saki biyu ke akanta, waccan kamar turmin( Sakeena🤣) saki ɗaya ƴar baƙa ma(😂 Habiba) itama saki ɗaya gaskiya ki canza boka wannan inaji batirin shi yayi sanyi😮.
Ba Mama jummai ba har Ummi dake ƙofar ɗaki tana girki sai da ta ɗago ta kalli yarinyar tata balle Nusram da har kusa faɗuwa sai da tayi, duka kallon Nusreen ɗin suke yi ita kuma ta maze kamar babu abinda tayi.
Sahura ta taso cikin rashin kunya tace; "malama ya ishe ki haka, ai naga aiki da bokan ba ita kaɗai ta fara ba wata ma abinda take yi kenan, banza wacce taƙi auruwa".
Mari ta kai mata da sauri Nusram ta tare tace; "kada ki fara ai ke kika janyo ma kanki", Nusreen ta gallawa Nusram harara tace; "ai wallahi sai na mare ta, sai na nuna mata niba sa'ar yin ta bace sa'ar yin uwar ta ce".
Sahurar itama cikin haki da masifa tace; "kamar yadda nake ba sa'ar yin ki ba sa'ar yin taki Uwar ce ba", ai kuwa tana rufe baki Nusreen na sauke mata tafi a fuska.
Jijjiga ta tayi ta wullar ƙasa ta hau kai ta fara duka, Nusram kuwa ta tsaya tana kallon ikon Allah, Mama Jummai ta ɗauki roba ta fara ƙwalawa Nusreen ɗin tana faɗin; "au baƙin ciki yasa zaki kashe mini ƴa ne?",.
Ummi ta kalli Nusram tace; "zo ki wuce ciki", babu musu ta ƙyale su ta wuce ta ɗauki buta domin yin sallar magrib, Nusreen kuwa sai da ta gama kirɓar Sahurar sannan ta ɗaga ta dan kanta tayi ɗaki.
Mama Jumman ta dinga jero mata zagi, yayin da Sahura ke zabga ihu domin ta daku sosai, haka taja jikin ta tayi ɗaki domin dai ta jibgu sosai da sosai.
Nusreen na idar da sallah ta kalli ƴar uwar ta, Nusram taja tsaki tana miƙewa ta bar wajen, Nusreen tayi murmushi tana shafa fuska ta san cewa sai da ta ƙara yin ladabi kafin su shirya da ƴar uwar tata.
Ta kalli Ummi, Ummi kuwa ta zuba mata harara hakan yasa ta saukar da kai tace; "Ummi kiyi haƙuri", shiru ne ya biyo baya domin sallamar wani yaro.
Mama Jummai dake waje ita ta amsa tana faɗin ya akayi me zaka siya?", yace; "yan biyu aka ce na kira", Mama Jummai taja tsaki cike da takaici da kuma mamaki wanda ya bayyana ƙarara a kan fuskar ta.
Nusram dake yanka latas ta ɗago ta saci kallon ƴar uwar tata, ita kuwa Nusreen dama neman hanyar yiwa ƴar uwar tata magana take dan haka tace; "Ram baki ji ba ana kiran ki".
Nusram ta juyar da kai tace; "kada Allah yasa ki tashi kije ki zauna neman magana har Baba ya dawo kinga koda ace kuturu ne ya nemi ɗaura muku aure", ai kan ta ƙarasa ta miƙe ɗauki hijab ɗin ta.
Koda ta fita Mama Jummai ce kawai a waje hakan yasa tayi waje kawai, Mama Jumman tace; "Allah yasa gurgu ne", Nusreen ta saki dariya tana ƙarasa ficewa.
Suna tsaye suna kallon ƙofar gidan, kallon su take ƙasa zuwa sama, ita dai ba zata tuna kosu waye ba domin bata san su ba, amma kuma daga ganin su kaga wa'inda hutu ya samu waje ya zauna a jikin su.
Suna sanye da shadda bugaggiya kalar ruwan madara wacce tasha aikin wuta sosai a jiki, ɗayan kan shi da hula ɗayan kuma babu hula, duka har agogon su kala ɗaya ne haka takalmin su.
Ɗaya baƙi ne ɗayan kuma yana da haske kuma yana da ƴar ƙiba kaɗan yayin da ɗayan yake dogo, dogon baƙin wanda ya zuba mata idanu itama haka ta zuba mishi idanu.
A hankali ta fara takowa zuwa wajen su, Shureim kuwa ji yake kamar ya ɗauke ta su gudu tsabar son da yake mata, Nusreen kuwa sai da ta matso kusa dasu sannan ta gane shi.
Wani irin ɗaure fuska tayi tana mishi kallon uku saura kwata, tana sakin musu harara ganin yadda ya raina mata wayo wato har ma ƙofar gidan su yazo kenan?, da alamu sai ta nuna mishi ita ba sa'ar shi bace.
" marin kazo nayi maka ko kuwa waccan wankin dana yi maka yayi kaɗan ne? Ko dai kazo ƙara zuba mini datti ne? Ko ƴan sanda ka kwaso mini? Ko kazo ganin ni ƴar wacece?", duka ta jero mishi tambayar idanun ta na kanshi.
Shureim da Naufal suka kalli juna cike da mamaki, Naufal kam da ƙyar ya iya riƙe dariyar dake cin shi ganin yadda abokin nashi ke zare idanu, gashi ita kuma ta ɗaure fuska yadda kasan uwa ta titsiye ɗan ta yayi mata laifi, shi kuma sai zare idanu yake kamar yayi wa sarki ƙarya.
#LIKE
#SHARE
#COMMENT
*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.
*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*_daga alƙalamin ✍_*
*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*
*sadaukarwa gare ku*
*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*
*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*
*Heart you so much*
📖📖11-12📖📖
Tsit wajen yayi Shureim dai kallon ta kawai yake yi cike da birgewa yayin da gaban shi ke dukan uku, Nusreen ta kuma balla mishi harara tace; "baka da baki ne?".
Cikin sauri Shureim ya girgiza kai yace; "abinda ya kawo ni daban".
"me kenan? Ko kana bina bashi ne?", ta ƙara jefo mishi tambaya, wacce tasa Naufal ya kasa riƙe dariyar shi.
Ta juya ta kalle shi ta taɓe baki tace; "kai kuma ka sami taɓin hankali ne, ko kuwa sabon wulaƙanci ne da kuka samo ku ƴaƴan masu kuɗi", Naufal ya kauda kai yana mamakin ƙarfin halin yarinyar da kwata-kwata ta hana su maganar.
"ya wani je ya kwaso ka, kai kuma ka wani biyo shi dunƙul-dunƙul, to ko zaka tare mishi, wai yanzu zamani yazo da rashin mutunci ma har ƙofar gidan ku ake zuwa ayi maka, to wallahi ku tattara komatsen ku kubar nan kafin nasa ayi muku rashin mutunci na ƙarshe wanda ko hanyar nan ba zaku kuma kallo ba", tana gama faɗar haka ta shige gida ta bar su a tsaye.
Shureim ya dafe kai da sauri, shi kuwa Naufal banda dariya babu abinda yake yi, lallai wannan yarinyar ta wuce yadda yake tunani, cikin masifa Shureim ya kalle shi yace;
"nifa ba na kira ka nan bane ka ƙara mini matsala, matsala ta nazo ka warware mini amma ji yadda kazo ka lalata komai", Naufal ya kuma tuntsirewa da dariya.
Shureim kamar zai yi kuka yace; "na gode da irin sakamakon da kayi mini", nan ya shige motar ya barshi, shima Naufal ɗin haka ya gaji ya shigo sannan yaja suka bar unguwar.
Nusreen na shiga gida ta nemi waje kusa da Nusram ta zauna, Nusram dake cin abinci ta kalle ta, ta kauda kai.
Nusreen ta janye abincin dake gaban Nusram din ta hau ci, Nusram kuwa bata ce mata komai ba sai tashi da tayi ta wanko hannun ta.
Ummi ta dube ta tace; "wai waye yazo ne?", Nusreen ta taɓe baki tace; "nima ban san shi ba wai ashe kwatancen da akayi mishi ne ba dai-dai ba", Ummi ta bita da kallon tuhuma, ita kuma ta fuske tana me cigaba da cin abincin ta.
Tana gama cin abincin Baban su yayi sallama ya shigo, duka suka amsa mishi, ɗakin Mama Jummai ya nufa suma kuma basu wani damu ba.
Ita kuwa sai dai tayi wata ƴar shewa sannan ta bishi ɗakin nata, Nusreen ta taɓe baki tana jan tsaki.
Ummi ta dube su tace; "tashi ku shiga daga ciki aje a kwanta", babu wanda ya musa haka suka tashi suka shige cikin ɗakin.
Sun kwanta babu jimawa Baban yayi kiran Nusreen, ta amsa tana ƙunƙunai, "shi baban nan ya iya kiran mutane idan tashi ce ta haɗo ku amma hakan nan ba zai tsaya yaji matsalar ku ba", haka ta fice tana mita, ita kuwa Nusram tana jin ta murmushi tayi tana me yiwa ƴar uwar tata fatan shiriya.
Baban ya kalle ta yace; "ance wani yazo wajen ki", ta ɗago ta kalli Baban sannan ta juya ta kalli wacce ke bayan shi Mama Jummai, ta ɗan ja tsaki ƙasa-ƙasa tace; "nifa wallahi gulma ce bana so".
Baba yace; "me kika ce?", ta girgiza kai tana faɗin; "babu komai, ni babu wanda yazo waje na".
Mama Jummai ta sako baki tace; "waye zai miki ƙarya, ina zaune aka aiko kiran naki zaki ce babu wanda yazo ko dadiron naki ne, yara basu son aure sun fi so su zauna suyi ta iskancin su a gidan uban su".
Baba ya ɗaga mata hannu sannan yace; "ya isa haka! Kince babu wanda yazo ko?", Nusreen ta ɗaga kai, yace; "tashi kije zan saka a bincika mini idan na samu akasin abinda kika faɗa sai na ɓata ranki kuma, tashi ki bani waje".
Babu musu ta miƙe kamar mutuniyar arziƙi tayi ɗakin su, Mama Jummai baƙin ciki ya ishe ta hakan yasa ta tashi fuu tayi nata ɗakin.
Baban ya kalli Sahura yace; "ke kuma sai ki faɗa mini lafiya kika dawo gida", cikin sauri tace; "Baba Nura ya sake ni", sai da Baba ya zage Nuran tas sannan yace ta tashi taje zai nemi nuran.
Nusreen na shiga ɗaki ta tuntsire da dariya, jin hakan yasa hankalin Nusram ɗin kwantawa don tayi tunanin ko wani abu ne ya faru.
Nusreen ta zauna gefen katifar su tace; "Ram kinji Mama Jummai da gulma wai har ta kaiwa Baba gulmar wani yazo nema na?", Nusram ta juya kwanciyar ta tana ƙara runtse idanu.
Nusreen taja tsaki tace; "dama na san ba zaki kula ni ba tunda yanzu kin dena ƴar uwar dani", har lokacin Nusram bata motsa ba hakan yasa Nusreen ɗin taɓa ta tace; "Ram ki tashi kiji me nake cewa mana".