Showing 18001 words to 21000 words out of 121992 words

Chapter 7 - Rayuwar Abdussamad Book Complete Document by Yar Mutan Zazzau .txt

28 Dec 2024

16076

Ta turo baki tace; "ai dai nace kiyi haƙuri ba zan kuma ba", saura kadan Nusram da Ummi su kwashe da dariya amma suka dake, Nusram ta tashi ta zauna sannan tace;


"Nusreen kin cika ladabin ƴan Jos 🙄 ne, yanzu zaki tuba anjima ki sake komawa ki aikata kalar wannan aikin, wannan ba hali bane me kyau".


Nusreen tace; "kiyi haƙuri na dena", Nusram ta girgiza kai tace; "ai wannan abin da kike shine ladabin ƴan Jos ɗin, ba dai kince kin dena ba to gobe ma kuma yi zaki yi nafa san halin ki".


Nusreen ta riƙo hannun ƴar uwar ta tace; "Nusram tunda nace na dena na dena ne ba zan kuma ba ki yarda dani", Nusram tace;


"shikenan zamu gani idan da gaske ne, ni nafi so ki fahimci wani abu Mama mahaifiya take a wajen mu dan tana auren mahaifin mu atleast u deserves our respect, amma ke bakya ganewa yanzu kiwon mutum ake ba dabba ba sannan ki sani babu alkhairi a barin wa ƴaƴan ka tarihi ko tabon rashin kunya, ki fahimta wasu abubuwan kauda kai ake yi kada ki manta daba dan haƙurin manzon mu ba da yanzu addinin musulunci be kawo mana ba amma da yayi haƙuri fa ba gashi yayi nasara ba, wallahi haƙuri akwai nasara da dacewa a cikin shi ba komai ake maka kace sai ka rama ba ki dinga sanyawa zuciyar ki haƙuri da salama mana ko zaki dace wajen koyo da ma'aiki".


Kamar da gaske Nusreen tayi shiru tana saurara d most funny part ɗin ma yadda ta maida fuskar ta kai kace da gaske maganar na shigar ta, cikin sanyin murya tace; "nayi nadama sosai ƴar uwata kuma insha Allahu zan yi koyi da Annabin mu(SAW), nasan kina ƙauna ta shi yasa kike faɗa mini gaskiya na gode sosai".


Nusram tace; "yauwa ƴar ƙanwa ta yanzu mu kwanta ko sai da safe", babu musu Nusreen ta zame ta kwanta, Ummi ta girgiza kai tana me yin murmushi.


Sau nawa ana yin irin hakan amma babu abinda ya canza yanzun ma bata jin zata canza zani.


🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸


*UNGUWAR SARKI, KADUNA*.


Brr Farida dake zaune ta zuba tagumi tana kallon gefen ɗaya wanda alamu ya nuna cikin damuwa take, gefen ta Surayya ce ke danna waya sai Adnan dake game a tab dake hannun shi.


Wani irin ƙamshi ne ya ziyarci falon kafin ya sako kai ciki bakin shi ɗauke da sallama, cikin sauri Brr Farida ta ɗago tana kallon shi.


Riga ce a jikin shi kalar Blue sai wando fari, sosai kayan suka yi mishi kyau, dan duk kayan da zai saka to suna amsar shi sosai, Surayya kallo ɗaya tayi mishi ta kauda kai, Adnan kuwa wajen shi ya nufa da gudu.


Abdul ya riƙo hannun shi yace: "yauwa boy", Adnan yayi dariya sannan yace; "Ya Abdul zaka je dani wajen Farha?", Abdul yayi murmushi har kumatun shi ya lotsa sannan yace; "me zai hana kuwa?", Brr Farida ta ɗaure fuska tana me kallon gefe.


Kusa da ita yazo ya tsaya, ta juyo ta kalle shi yana rataye da ƙamar jaka wacce ya zuba kayan amfanin shi a ciki, fuskar ta ɗauke da damuwa tace; "fatan ba zaka jima ba a can ko?".


Riƙo hannun ta yayi yace; "eh bana jin zan wuce sati ɗaya", wani kallo ta wurga mishi sannan tace; "sati ɗaya shine baka jima ba?, ko dai kafi son zaman can ne?", ya girgiza kai yace; "haba first love taya zan so zaman wajen da babu ke".


"to kayi kwana biyu kawai ka dawo", ta faɗa tana kallon shi, yayi murmushi yace; "shikenan First love to amma bakya ganin Daddy zai ce ban cika umarnin daya bani ba munyi dashi one week fa?".


"kaga Allah ya kiyaye hanya", tana gama faɗin haka tana fara ƙoƙarin barin wajen, cikin sauri ya sha gaban ta fuska ɗauke da damuwa yace; "bana so muyi irin wannan rabuwar Mum, dan Allah kada kiyi fushi dani, idan hakan ya ɓata ranki, to kiyi haƙuri", ya ƙarasa muryar shi na rawa.


Ita kanta bata san wane kalar so take wa ɗan nata ba, tana ji dashi sosai kuma bata son ganin shi a damuwa, amma kuma zuwan shi Hayin Rigasa ta san ba wani kula zai samu a can ba.


"shikenan zan haƙura amma da sharaɗi", cikin sauri ya tambaya; "meye sharaɗin?", ta riƙo hannun shi sannan tace; "zaka yarda securities su raka ka har can.


Yayi ajiyar zuciya dama ya san sharaɗin ba zai wuce wannan ba to shi kuma ba wani birge shi hakan yake yi ba balle hakan ya ɗaɗa shi da ƙasa sannan kuma shi baya son hayaniya amma ya zai yi tunda shiri yake nema.


Yace; "shikenan, na yarda", tayi murmushi tana me amsar jakar hannun shi tace; "muje na raka ka", haka suka jera har zuwa inda motocin suke sannan suka shiga a ka jasu, yayin da baya da gaba take cike da motocin securities.


Duk inda suka gifta kallon su ake wanda hakan shine abinda Abdul ɗin baya so amma babu yadda ya iya.


Cikin mintina kaɗan suka iso Unguwar, haka suka fara shiga cikin ta, shi dai ba zai ce ga yanayin da yake ciki ba amma ya san cewa gaban shi yana faɗuwa.


Ya kwantar da kan shi saman kafaɗar Brr Farida yana me lumshe idanu, bakin shi ɗauke da addu'a.


A bakin ƙaton estate ɗin suka dakata, sai da securities ɗin suka duba su sannan suka bar su domin su shiga.


Gida ne me apartment daban-daban gasu nan jere sama da ashirin da biyar kowanne kalar shi ɗaya da ɗan uwan shi, gefe da gefen titin da aka shinfiɗa kuwa flowers ne aka jera wanda suka ƙara ƙawata wajen.


Daga saman get na biyu naga an rubuta *NAGIMI'S ESTATE*, nan ma sai dai aka duba aka ga ko su waye sannan aka basu hanyar wucewa.


Nan fa suka fara wuce gidaje dake jere wa'inda duka kalar su ɗaya, kuma kowanne da get ɗin shi, babu kowa a waje sai masu aiki suma jefi-jefi sun yi tafiya me tsayi kafin su iso ƙarshen wannan titin inda wani get ɗin ke kallon su.


Sai da suka yi horn sannan aka buɗe musu get ɗin suka shiga, gida ne madai-daici me cike da ƙawa da kayan alatu kai daga gani ka san me gidan yana da dukiya sosai.


Haka suka jera parking a harabar wajen, Abdul ya kalli Brr Farida yayi murmushi sannan yace; "First Love muje ko?", wani shegen kallo ta wurga mishi sannan taja tsaki tana kauda kai.


Ɗan langwaɓar da kai yayi sannan yace; "Mum pls ki shiga ki gaida Malama dan na san tana nan ga kuma Hajja itama", cikin haɗe rai tace; "amma ai bance maka ina da buƙatar gaishe dasu ba ko sannan suma basu gaya maka cewa suna buƙatar tawa gaisuwar ba ko?".


"Mum sufa ɗin Ƴan uwan Daddy ne sannan surukai suke a wajen ki dan Allah ki shigo", ba dan ranta yaso ba tace; "sauka muje".


Cikin jin daɗi ya sauko suka fito tare, haka suka jera har cikin gidan, koda suka shiga falon farko babu kowa a ciki dole haka suka shiga falo na biyu wanda wata yar ƙaramar varender ce ta raba tsakani.


Ƙarami ne wannan falon don kujeru set biyu ne kawai a ciki sai wajen dinning a gefe sai ƙofofi guda biyu nan ma babu kowa sai dai hayaniyar su da ake jiyowa daga ciki.


Ya janyo hannun ta yana faɗin; "Mummy mu shiga daka ciki ina jin suna falon ciki", babu musu suka ƙara kutsa kai ƙofar dake ɓangaren daman su.


Shima falon babu tarkace sosai a ciki dan shi be kai falon tsakiya girma ba, suka yi sallama matar dake zaune saman kujera gaban ta ƙaramin table ne tana rubutu a sama ta ɗago tana kallon su.


Da mamaki take bin su da kallo tana me ƙara duba zuwa gare su, wacce ke zaune saman dinning ce ta amsa sallamar tasu tana me cigaba da cin abincin ta.


Sun tsaya sama da minti biyar kafin Brr Farida ta haɗe fuska ta ƙarasa cikin falon ta sami kujera ta zauna, ganin hakan yasa Abdul wucewa ya shiga ƙofar dake can corridor.


Da sallama ya shiga ɗakin, Ƴar tsohuwar dake zaune saman dardumar da alqur'ani gaban ta, ta ɗago tana me kallon shi.


Kusa da ita yaje ya zauna ya ɗora kan shi saman ƙafar ta, ta saki murmushi tana me shafa kanshi, ya lumshe idanu yana ajiyar zuciya.


A hankali yace; "First love na falo tana jiran ki", ya ɗago yana kallon ta, fuskar ta babu yabo babu fallasa don haka ba zai tantance yanayin da take ciki ba.


Sai da tayi jimm sannan tace; "tashi muje", babu musu ya miƙe haka itama ta miƙe, sai lokacin naga irin tsahon da matar take dashi gata fara sosai.


Cikin taƙama da ƙasaita take takun nata, na dafe baki ina faɗin; "Lallai Abdul baka yardar a ƙasa ba ashe abin naku gado ne?".


Yadda ya shiga ya barsu haka ya dawo ya ssme su, baya jin magana ta haɗasu a tsakani, shi kam wannan abu yana bashi mamaki.


Har sai da suka zauna sannan Brr Farida ta ɗago daga danna wayar da take yi ta kuma sauke ƙafar ta ƙasa tace; "Ina wuni?", sai da tsohuwar tayi daƙiƙu kafin ta amsa da ; "fatan kuna lafiya".


Brr Farida tace; "lafiya lau", daga haka babu wanda ya kuma magana a tsakanin su, fin minti biyar sannan aka buɗe ƙofar falon aka shigo da sallama.


Taɓ 🤔! Kallo ya koma sama shaho ya ɗauko giwa 😂😂.


Wata ƴar ƙwalisar tsohuwa ce baƙa ta shigo falon tana taku ɗai-ɗai, ko kayan jikin ta ka kalla kasan cewa ba ƙamar mace bace dan ita mayafi ta yafo saman atamfar da ta saka Holland, ɗinkin doguwar riga wanda ya zauna a jikin ta sosai babu abinda take sai tashin ƙamshi me shegen daɗi.


Kallo ɗaya ta yiwa Brr Farida ta ɗauke kanta, itama kuma Brr Farida bata kalle ta ba, sama da minti biyar shiru sannan Brr Farida tace; "ina wuni".


Taja tsayin lokaci me nisa kafin ta iya cewa; "lafiya lau, ƴar mulki", Brr Farida ta saki wani murmushi na ƙasaita.

Wacce ke saman dinning ɗin ta gama cin abincin ta sannan ta sauko itama kujerar tazo ta zauna ta ɗauki remote ta kunna plasma ɗin dake maƙale a jikin bango.


Ɗan juyowa tayi ba tare da ta kalli ɓangaren Brr Farida ba tace; "ina wuni Brr?", Brr farida ta amsa da ; "lafiya lau Fatima".


Babu wanda ya kuma magana hakan ya bawa Abdul damar gaishe da kakanin nashi guda biyu duka sun amsa babu yabo ba fallasa sai dai wannan ƙasaitar tana nan.


; "Ina wuni Aunty?", Fatimar ta kalle shi tace; "lafiya lau, fatan ka dawo lafiya", ya amsa da lafiya, wacce dai ke rubutu ce har yau bata ɗago ba balle ma naga ya fuskar ta take.

Abdul yace; "Ina wuni Brr", cak ta tsaya da zana biron da take saman takardar sai da taja lokaci kaɗan sannan ta ɗago.

Kyakkyawa ce ajin farko dan sai nace ta kusa kamo Brr Farida a kyau, fara ce sosai wanda farin ta har ɗaukar idanu yake yi kana ganin ta ka san ƴar hutu ce gaba da baya.

Cikin hausa irin ta ƴan boko da kuma zamanin yanzu wacce take cike da ƙaƙale tace; "brr!? Ashe haka kake kiran uwar ka kenan?".


Brr Farida ta saki wata irin dariya me cike da nishaɗi da annashuwa kafin ta janyo ɗaurin ɗankwalin ta ya dawo gaba tace; "wallahi idan kina ƙoƙarin haɗa kanki dani Brr Hauwa dariya kike bani sosai, kema fa cewa ki kayi Uwar shi ai kin san tsakanin mu da bambamci".


Brr Hauwa cikin fushi tace; "ai a juri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe ne Brr Farida", aikuwa babu sanya tace; "nifa na riga da na zama ƙadangaren bakin tulu zama dani ya zama dole".


Brr Hauwa tace; "kada ki manta kayan aro har abada na aro ne, kuma wata rana gaskiya zata yi halin ta".


"ko a yanzu kasuwa ta faɗi ɗan koli yaci riba sannan ki sani ni ɗin ruwan jakara ce idan baki sha ni a kauye ba zaki sha ni a birni".


Cikin sauri kafin Brr Hauwa tayi magana Fatima ta dakatar dasu ta hanyar cewa; "wai meye hakane kuke abu kamar yara ƙanana ku baku haɗuwa waje ɗaya ne sai kun nuna halin ku".


Brr Hauwa tace; "wane kalar hali ai wallahi ko yanzu na san sama tayiwa yaro nisa sai dai ya ɗaga kai ya kalla, domin kuwa idan na raina kasuwa ko sautu bana bayarwa".


Brr Farida ta miƙe tsaye ta taka har gaban Brr Hauwa tace; "nafi ƙarfin ki kira ni da ƙarama domin kuwa ke kanki kin sani hangen dala ba shiga birni bane kuma ba girigirin ba tayi mai, irin ku masu cika baki suna bani mamaki sosai ki sani ni ɗin ce Brr Farida Alƙali har yanzu sunan a haka yake be canza ke in banda ruwa ya daki babban zakara da idan aka ce ki kalle ni ki faɗa mini wata maganar da ba zaki yi ba wallahi koda kuwa kuɗi aka baki kada ki manta nifa itace kabari ce na danne uban kowa dakalin majina a hauni a zame na hau mutum na zauna dai-dai, murucin kan dutse ban fito ba sai da na shirya, kainuwa dashen Allah ba dashe na mutum ba.


"da bamu san asalin ungulu ba sai muce daga misra take, dama dangin ku ai dangin taƙama ne da taka haye", amsar brr Hauwa kenan wacce ke tsaye gaban Brr Farida.


"kada ki manta tunkan a haifi uwar me sabulu balbela take da hasken ta kuma dama ɗawisu ai kowa da zanen ta ya ganta, ke ƙaramar yarinya ce Hauwa ki bini a sannu idan ba haka ba zan koyar dake darasin da ba'a taɓa yi miki ba", daga haka Brr Farida ta ɗauki jakar ta sannan ta juya wajen tsofaffin biyu dake kallon su tace;


"zan tafi Malama, Hajja sai anjiman ku", tana gama faɗin hakan ko Abdul ɗin bata yi zaman jira ba tayi waje kawai.


*tofa abu ya fara fin ƙarfin jin Deeje ƴar gidan Ahmadu jikan inusa, ni kaina a dunƙule suka bani shiyasa nima na baku a haka amma zan ajiye biro na haka har sai naje na tambayo fassarar wa'innan maganganun dan kada inje ko bindige ni suke nufi ayi*.




*kuyi haƙuri da abinda kuke samu daga gare ni kunji na san ina yin delay ɗin posting ɗin amma ku ƙara haƙuri saboda ina da uzururruka a gaba na sosai*.




#LIKE
#SHARE
#COMMENT
#VOTE


*Babyn Abdul, Maman Meenal Elham da Farouk*.




*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.










♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠



https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/




*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*








*~We are bearer's of so golden pen🖊~*


*~we write assidiously perceive no pain~.*


*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*


*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*












*_daga alƙalamin ✍_*



*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*


*sadaukarwa gare ku*



*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*


*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*


*Heart you so much*

*godiya gare ku*.


*Aishatu Babayo*.
*Salamatu( kaka ta)*.
*Hafsat A garkuwa*
*Aunty Ummee*
*Kamal no love*
*Rukayyat Imam (Mama na)*
*Ibanatu*

Na gode sosai da sosai ku ɗin aminan ƙwarai ne kuma mutanen kirki ina ji daku sosai da sosai.


*ina cigayar Khairat aminullah, da Hajjaju dan Allah wanda ya gane mini su ya taimaka yace One Love na neman su*.






📖📖13-14📖📖






Hajja tace; "lallai wuyan ki ya isa yanka Farida har gida kizo ki zage mu tas", ita dai Brr Farida bata san suna yi ba dan tayi nisa da tafiya.


Brr Hauwa tace; "yaushe dama take da wata tarbiya irin tarbiyar gidan su kenan, kuma irin ta take bawa yaran dakta tunda shi yaji ya gani".


Fatima tace; "dan Allah ya isa haka, ku bar naganar mana", Hajja tace; "ba zamu bari ba Uwar mu sai munji duka".


Abdul kuwa a hankali ya sulale ya bar musu ɗakin domin ya san idan sun gama kan shi zasu dawo nan aka barsu da cece kuce ɗin su wanda baya ƙarewa.


Ɗakin ya tura ya shiga a hankali yana nan yadda yake, komai a tsaftace, ya saki murmushi sannan yace: "Fadil kenan akwai tsafta", gefe ya ajiye jakar shi sannan ya faɗa saman gadon.


Ya jima yana tunani wanda shi kanshi be san na meye ba, sannan ya miƙe ya nufi bayi yayi wanka, cikin riga shirt mara nauyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login