Showing 87001 words to 90000 words out of 121992 words
Chapter 30 - Rayuwar Abdussamad Book Complete Document by Yar Mutan Zazzau .txt
aka yiwa fa?, ko Nusreen data ɗebi kwanaki a gidan ta ba zamu ji daɗi ba ace anyi mata wannan, to yadda ba zamu ji daɗi iɗan anyiwa namu ba to muma kada mu yiwa wani, na gode ƙwarai da wannan shawara sai dai nima ku duba nawa magan-ganun dan Allah".
ɗakin yayi shiru, kowa yana tunani daban dana ɗan uwan shi, Nusram ta kuma cewa; "dan Allah kada mu aikata aikin da za muyi dana sani amma idan har kuna ganin abinda kuka yanke shine dai-dai to ni meyi muku biyayya ce".
Abba yace; "tabbas abinda kika faɗa Nusram gaskiya ne, mutane zasu zage mu sannan bamu san wane irin kallon dangin ta za suyi mana ba, dan haka zamu cigaba da taya ki da addu'a kawai".
Nusram tayi ƙasa da kai tace; "na gode Abba, Allah ya ƙara girma", Yace; "Ameen, Allah yayi muku albarka, Sulaiman tashi ka maida ita gida".
Ya amsa da to sannan ya miƙe daga gaban iyayen shi, itama ta miƙe tana yiwa Aunty Sallama, Aunty tace; "Allah ya tashe mu lafiya Nusram Allah kuma ya dube ki, ki gaishe da Maman ki", tace; "to.
Har suka isa ƙofar gidan su Nusram babu wanda yayi magana, kowa kuma abinda yake tunani daban.
Nusram harta yunƙura zata buɗe ƙofa ta koma ta zauna, tace; "Yaya kayi haƙuri da abinda ya faru ba wai ba zan iya auren ka bane a'a zan so ace kaima ka fahimce ni kamar yadda suma suka fahimce ni".
Yaya Sulaiman ya numfasa yace; "kada kice komai, waye zai fahimce ki sama dani, mun rayu tun muna yara tare kallon abu kika yi na san me kike nufi balle har ta kai ga kin furta, kije gida kawai sai da safe nima zan taya ki da addu'a".
Tayi murmushi tace; "na gode sosai sai sa safe", yace; "Allah ya tashe mu lafiya", tana fita ta haɗa ido da Baba wanda ke tsaye yana jiran fitowar Isa da alamu lissafi zasu yi ko wani abin.
Yaya Sulaiman ya danna mata horn ta juya ta ɗaga mishi hannu, ya ɗago mata hannu sannan yayi reverse ya bar wajen.
Cikin natsuwa ta fara tafiya, "barka da dare", abinda ta faɗa kenan lokacin da tazo gifta Mahaifin nata, Baba yace; "waye ya ajiye ki a mota yanzu?".
"Yaya Sulaiman ne", cikin daka tsawa yace; "rufe mini baki gantalalliya ni zaki rainawa wayo, wato Sulaiman ne ya kawo ki ko, kai ni kam banyi sa'ar haihuwa ba, to bari kiji wallahi daga kwanakin dana ɗibar miki babu ƙari, nan da sati ɗaya idan baki fito da miji ba ni da ke ne", Nusram tace; "to Baba", ta wuce gida.
Tana shiga zaure Isa na fitowa daga ɗakin shi, ya kalle ta ya kwashe da dariya yace; "baki da miji da ya wuce ni ɗin nan".
Bata kalle shi ba ta shige cikin gida, Mama Jummai dake gaban murhu tace; "an gama yawon ta zubar ɗin kenan?", itama dai Nusram bata kulata ba.
Ɗaki kawai ta shiga, ta yiwa Ummi sannu da gida, Ummi tace; "ya kika baro su", tace; "suna lafiya sun ce ma a gaishe dake", Ummi tace; "masha Allah".
Har zuwa lokacin da suka kwanta Ummi bata tambaye ta ya suka yi da Aunty ba itama kuma bata faɗa mata ba.
Ta zurfafa kanta cikin tunani ganin cewa gobe fa saura kwana shida kenan, dole tayi wani abu a kai idan ba haka ba tana ji tana kallo matsalolin gidan su zasu fi ƙarfin ta.
Shawarar da taji ta kwanta mata a rai ita ta fara ƙoƙarin bi, dan haka cike da ƙwarin gwiwa tayi barcin ta.
Washe gari da safe duk wasu ayyukan da ta san zata yi duka tayi sannan tayi wanka taci abinci.
Kayan siyarwa da Ummi take siyarwa ta tayata suka ƙulla na ƙullawa sannan ta tashi ta wanko hannun ta.
Tana tsaye a tsakar gida, Atika tayi sallama ta shigo, Nusram ta kalle ta, itama ɗin ita ta kalla fuska ɗauke da murmushin mugunta.
Wani rantsattsen lace ne a jikin, kalar ash da orange, yayi kyau sosai, ita kanta Atikar tayi ƙiba tayi freah, Nusran ta kauda kai daga kallon ta.
Atika tayi shewa tayi juyi sannan ta nufi hanyar ɗakin mahaifiyar ta, bata jima da shiga ba aka fara shigo da buhunan abinci.
Shinkafa buhu biyu, taliya kwali uku, buhun semonvita guda ɗaya, ƙaramin buhun gishiri, sai sugar itama ƙaramin buhu, man ja da man gyaɗa duka galan ɗaya, sai tarkacen maggi.
Nusram kuwa ɗaki ta shige dan wannan dama basu bane a gabanta, ko Ummi bata bawa labari ba, tana daga cikin ɗaki ta jiyo sallamar Habiba, nan suka hau murna suna shewa a tsakar gida.
Ummi ta kalli Nusram, Nusram kuwa hankalin ta naga wayar Abdus-samad tana dubawa kamar wacce ta san kanta, Ummi tace; "bafa kiyi mini bayani akan wayar hannun ki ba".
Nusram tace; "Hajiyar Shureim fa ta bani haɗe da kayan nan", Ummi tace; "aikuwa an gode sosai, amma da kin sani baki amso duka ba, kayan sun yi yawa".
"nima sai da nace mata ba zan amsa ba ta tilasta, shiyasa na amsa ɗin dan kada nayi jayayya da ita", Ummi bata kuma cewa komai ba.
Suna jiyo lokacin da suke ta hidimar su akan kayan da Atikar ta kawo, babu wanda yace wani abu, Nusram ma cikin ɗaki kawai ta shige.
Tun ranar data dawo da kayan ta ajiye a kullum tana son ɗauka amma hakan ya gagara saboda gani take idan ta ɗauka ɓacewa zata yi.
🤣🤣🤣🤣🤣 Nusram baki ɓace ba da kika dauki wayar shi sai kayan daya siya miki a boutique?.
Kwanciya tayi, tana tunanin rayuwar ta har barci ya ɗauke ta, sai lokacin da zata ɗora girkin rana sannan ta farka.
Ta fito ta haɗa wuta inda ta ɗora abinci, Sahura ta fito da sauri, Nusram ta kalle ta tayi murmushi, suka gaisa cikin mutunci.
"ina mijin naki?", tace; "yana gida yace a gaida ke", Nusram tayi ajiyar zuciya tace; "ina amsawa", sun ɗan taɓa fira kaɗan kafin Sahurar ta tafi.
Nusram na gama abinda zata yi ta shige ɗaki, tare da Ummi suka ci abincin, daga nan suna juyo abubuwan dake waka na a tsakar gidan.
Nusram ta taɓe baki kawai tana cigaba da abinda yake gabanta, Ummi ma bata ce komai ba.
"ayyiririririiiiiiiii, gaka inda aka iya haihuwa, ni Jummai waya ganni a saudia", faɗar Mama Jummai kenan kafin kuma suka hau tiƙar rawa ita da Ameera da Habiba, Atika na musu kiɗa.
Sai da suka gama cashewar su sannan Mama Jummai ta kuma cewa; "kai haihuwa me daɗi, ai dama haihuwa suna ta tara mu dai tamu kam sam barka".
Duk da Nusram da Ummi suna jiyo su amma babu wanda ya tanka musu, haka suka gama shewar su da habaice-habaucen su.
Koda yamma da Baba ya dawo, ana nuna mishi kayan da wai Alhajin ya bada a kawo ya hau murna.
"Maimuna ina kike?", ya hau ƙwalawa Ummi kira, ta fito Nusram ma ta biyo bayanta.
"ki kalli inda ake abin arziƙi, kin gani ko wannan shine haihuwar da ake so ba kalar taki ba ƴaƴa sun zama kamar masu farar ƙafa babu ɗaya ƙwakkwara na kamawa".
Ummi tace; "an gode Allah ya saka da alkhairi", Baba da Mama Jummai suka ce Ameen, inda da gaske kike", Ummi tayi murmushi kawai kafin ta juya.
"haba me ake da yaran da basu san su kyautatawa iyayen su ba, ita waccen shegiyar har yanzu ko gidan bata leƙo ba", tsaf Ummi ta san da Nusreen yake amma bata tanka mishi ba.
Sai bayan sun shiga ɗaki sannan ta sami damar share hawayen daya zubo mata, Nusram ita kanta jikinta yayi sanyi, ta miƙe ta shiga ɗaki hijab kawai ta ɗauko kafin tazo ta fice.
Ba tare da sanin inda ta nufa ba, wani lungu tabi sannan ta tsaya tana maida numfashi, lallai ya kamata tayi wani abin kodan ragewa Ummi damuwar da take ciki, to amma yanzu me zata yi?.
Tana nan tana saƙe-saƙe aka fara kiraye-kirayen sallah, ta miƙe sannan ta fara takawa cikin natsuwa.
Masallacin da ta san mahaifinta baya zuwa haka ma Isa nan taje ta laɓe, tana kallon yadda mutane ke hada-hadar su na ƙoƙarin yin alwala.
Wanda ta hango a can gefe idan zata iya canka zai kasance shine liman, tana kallo yana alwala sai da ta tabbatar mutane sun yi alwala sun shige masallaci sannan ta sami damar ƙarasa gaban shi.
Tayi mishi sallama ya amsa, yana cigaba da alwalar shi ta tsaya har sai da ya ƙarasa sannan ta gaishe dashi, ya amsa yana bin ta da kallo.
Tace; "dama.......dama mijin.........dama mijin aure ......nake nema shine ........shine nace bari ......nazo nan masallacin idan dame buƙatar ƙara mata sai yaje ya sami......sami mahaifina", ta ƙarasa muryarta na rawa tana wasa da yatsun hannunta.
Limamin yayi ɗan jimm kan yace; "to shikenan ki jira mu nan waje, amma kamar ƴar gidan Malam Abdullahi", cikin ladabi tace; "eh nice", ya jinjina kai sannan yace; "ki jira bari na shiga muyi sallah tukunna Allah yasa a dace.
Wani gida dake kusa da masallacin nan ta shiga ta rakuɓe, addu'ar da take yi Allah yasa a dace ta sami mijin aure ko ta bar gidan nasu mahahifiyar ta, ta sami kwanciyar hankali.
Tana jiyo lokacin da suka idar da Sallah, liman ɗin yayi sanarwa, bata da tabbacin me suke bada amsa, amma liman ɗin ya sanar musu sannan ya faɗa musu ƴar gidan ko waye yace; "idan dame buƙata sai ya nemi mahaifin nata", daga haka yayi addu'a aka watse.
Daga inda Nusram take tana jiyo wasu samari suna faɗin; "kai haba dai waye zai kai kanshi wajen yarinyar da a ranar da aka kaita gidan miji aka kamata da kwarto".
Ɗayan yace; "kai da ka gane kenan Auwalu, kwananta goma sha biyu fa a gidan kaso", Auwalu yace; "kai Idi a dai wajen ƴan sanda ba gidan kaso ba, shima kuma kwana takwas ne ba goma sha biyu ba".
Ɗayan yace; "ni naji ance ma wai da saurayin suka haɗa baki, suka gudu sai da ya ɗirka mata ciki sannan ya dawo da ita, Mahaifiyar ta itace take goyan bayan duk abinda take aikatawa, sunje zubar da cikin aka sami matsala sai aka kwantar dasu a asibitin kwanan su shida sannan aka sallamo su".
Idi yace; "ai zasu aikata wallahi, kana ganin mahaifiyar nan tasu a haka sumimi kasai, kamar wata mumina da gaske, ta ganku tana wani sunkuyar da kai kamar sabuwar tunkiya, amma ita take tura yaranta karuwanci".
Auwalu yace; "kai raba kanka da irin wa'innan matan yasin, bar ganin ta a haka da zumbulelen hijab waye ya san ita me take aikatawa, shi kanshi mijin nata ai asiri tayi mishi to ance fa ya sake ta amma taƙi barin gidan yanzu haka ma kuɗin da suka yi karuwanci dashi suke ciyar da kansu".
Nusram ta tsugunna a wajen ta fashe da kuka, wato kallon da ake yi musu kenan, lallai rayuwa kenan, sai da gari yayi duhu sosai sannan ta sami damar barin wajen.
Har lokacin kuma basu bar firar su ba, taja hijab ɗin ta rufe rabin fuskar ta sannan ta tafi.
Koda ta isa gida Ummi bata ce mata ina taje ba haka itama bata cewa Ummi ga inda taje ba,
Koda tazo kwanciya sai da tasha kukanta ma'ishi kafin barci ya ɗauke ta
************* *************
Khausar dake kwance saman couch ɗin ɗakin ta wanda yaji kayan more rayuwa.
tana sanye da riga doguwa iya gwiwa, kwananta biyu kenan babu inda taje, Mahaifiyar ta harta gaji da buga mata ƙofa akan ta buɗe amma taƙi.
Yanzun ma Hajiya Salma dake tsaye bakin ƙofar ta kuma bubbugawa tace; "wai Khausar ba zaki buɗe ƙofar nan ba", shiru babu amsa.
Khausar kuwa dake ciki tayi juyi tana jan tsaki, wai me yasa ƴan gidan nan basa ganewa ne itafa Abdus-samad kawai zasu nemo mata shine samun kwanciyar hankalin ta.
Alhaji Mustapha dake zaune saman dinning ya buga uban tagumi, lokaci zuwa lokaci ya kan share zufar da take tsattsafo mishi.
Brr Jabeer yayi sallama ya shigo, cikin sauri Alhaji Mustafa ya miƙe ya isa wajen shi, saman kujera duka suka zauna.
Alhaji Mustapha yayi ƙasa da murya yace; "Brr ina cikin tashin hankali, ƴata Khausar tace babu wanda take so sai ɗan uwan ta Abdus-samad".
Brr Jabeer ya zaro idanu waje yace; "taya suka haɗu a ina kuma ta san shi, shin ko dai ta san sirrin da kake ɓoyewa ne", Alhaji Mustapha yace; "ko Mahaifiyar ta bata sani ba balle ita".
"tun da suka haɗu a wajen siyayya shikenan ta maƙale, yau kwanan ta biyu kenan ta rufe kanta a ɗaki babu ci babu sha wai shi take son gani".
Brr Jabeer yayi shiru tsayin wani lokaci kafin yace; "ni ina ganin kawai abinda za'a yi shine ka nemo shi, kga daga nan zaka sami hanyar da zaka ja sha jikin ka".
Alhaji Mustapha yace; "hakane kuma, amma kai kanka Brr kasan wacece Brr Farida ba sai na faɗa maka komai ba, idan har na sake nayi wani motsi a kai to zata kaini kotu kuma ka san cewa kaini kotu dai-dai yake da tonon asiri na".
Brr Jabeer yace; "kuma hakane tabbas, to amma yin shirun kana ganin shi yafi", Alhaji Mustapha ya jinjina kai yace; "tabbas kuwa shi yafi, idan ta gaji da kanta zata buɗe ƙofar", Brr Jabeer yace; "shikenan".
Tare suka miƙe da Alhaji Mustaphan, inda Hajiya Salma ke tsaye tana fama da Khausar akan ta buɗe ƙofa suka je.
Brr Jabeer yace; "Khausar ki buɗe ƙofar nan ni kuma nayi miki alƙawarin baki number ɗin shi", Khausar jin hakan yasa ta diro daga saman couch ɗin tazo ta buɗe.
Hajiya Salma da Alhaji Mustapha kuwa gaban su ya faɗi, Hajiya Salma abinda take gudu shine alaƙa ta shiga tsakanin su bata fatan abinda zai kawo Abdus-samad ɗin cikin rayuwar su wancan ma tsautsayi ne.
Alhaji Mustapha kuwa tsoron shi shine be san ta yadda zai kare kanshi ba idan har asirin shi ya tonu.
Khausar ta kalli brr, shi kuma yayi mata murmushi sannan yace; "idan kika kashe kanki a ɗaki Khausar taya zaki iya zuwa wajen Abdus-samad ɗin ko kin haƙura dashi ne?", ta girgiza kai.
Ya riƙo hannun ta yace; "idan mutum yana son abu ba wai shiga ɗaki yake yi ya rufe kanshi ba a'a zai iya iyakar yin shi nr ganin wannan abin yazo gare shi, wannan shine abinda ya dace kiyi, kinji ƴar Baba".
Khausar tayi murmushi tana sauke kanta ƙasa, Brr Jabeer kuwa murmushi yayi kafin yayi musu sallama ya fice daga gidan.
Alhaji Mustafa ya kalli ƴar tashi yace da ita; "haba Khausar yanzu kina ganin abinda kika yi kinyi dai-dai kenan".
"kayi haƙuri Daddy ba zan kuma ba", ta faɗa cikin sanyin murya, zai kuma magana Hajiya Salma ta dakatar dashi tace; "Khausar wuce kije kici abinci".
Sai da ta bar wajen sannan Alhaji Mustafa yace; "wai me yasa bakya son na yiwa yaran nan faɗa ne?".
"to Alhaji wane irin faɗa kuma bayan ta riga ta fito daga ɗakin ai shikenan dai ko, ni zan wuce wajen aiki", ta ƙarasa tana tafiya.
Alhaji Mustapha ya bita da kallo har ta fice sannan yayi ajiyar zuciya kafin ya ciro waya ya hau kiran Alhaji Sa'eed.
"Alhaji ina cikin tashin hankali", abinda Alhaji Mustapha ya faɗa kenan bayan Alhaji Sa'eed ya ɗaga wayar.
Alhaji Sa'eed yace; "innalillahi, ka bari anjima mu haɗu a guest house ɗin ka dake by pass", Alhaji Mustapha yayi ajiyar zuciya yace; "to", daga haka suka katse wayar.
Ya nemi waje ya zauna ya dafe kanshi, idan har yayi wasa tofa wanki hula zai kaishi dare, dole ya san abinda ya kamata yayi, be shirya zuwa gidan yari yanzu ba.
******** ***********
Abdus-samad ke gaba yayin da Fadila da Brr Farida suke bayan shi, yana sanye da ƙananan kaya, jar riga da kuma baƙin wando as usual shigar ƙananan kaya.
Brr Farida tace; "yauwa kije insha Allahu nan da sati ɗaya zamu zo kuma za'a yi maganar auren ku, kinji ko".
Fadila ta sunne kai tana murmushi, Brr Farida itama tayi murmushi sannan ta kalli Abdul tace; "Baby ka tafi da ita a hankali banda gudu ka san amarya tsautsayi gare ta".
Sameer da Tameer dake tsaye a wajen parking lot ɗin suka kalli juna suka kwashe da dariya.
Abdus-samad ya shagwaɓe fuska yace; "kai First Love ni na lura yanzu