Showing 45001 words to 48000 words out of 121992 words
Chapter 16 - Rayuwar Abdussamad Book Complete Document by Yar Mutan Zazzau .txt
tara a wajen Auntyn Tudu na san sati me zuwa zata zo dasu a shiga kasuwa sai a siyo koda kayan kitchen ne tunda a ƙalla zai kai dubu ɗari da saba'in sannan akwai wa'inda muke tarawa a gida kinga duk Allah zai rufa asiri dai, ni dai burina yanzu shine na bar gidan kawai".
Nusreen tace; "hakane kuma, kai amma sana'a tana da rufin asiri yanzu fa kinga da bamu yi da shikenan", Nusram ta harare ta tace; "kamar wata gwanar sana'ar ai zan bawa Shureim shawara kawai ya buɗe miki boutique ne kada ya tsaya ɓata kuɗin shi".
Nusreen tace; "nifa gidan radio zan yi aiki na", Nusram tace; "da auren naki ko?", eh mana me za'a fasa", Nusram tace; "Allah ya baki sa'a to", ta amsa da ameen, haka suka cigaba da firar tasu har suka isa makarantar.
Koda suka taso, sauri kawai suke tayi domin su ƙaraso gida dan basa so ayi kiran sallar Magrib suna kan hanya.
A.ƙofar gida suka tarar da Idris, cikin girmamawa ya gaishe dasu, suma suka amsa sannan suka shiga ciki.
"ni Sahura ban isa na faɗa miki magana kiji ba kenan?, Sahura dani kike ja ko, ki koma babu inda zaki je", maganar Mama Jummai kenan wacce ta iso kunnen su.
Su ka kai duba, zuwa inda take ta kama Sahurar ta cukuikuye ita kuma Sahurar tana ƙoƙarin fizgewa, idan kaga yadda suke sai abin ya baka dariya.
Nusreen data kasa riƙe dariyar ta nan ta hau yin ta babu ƙauƙƙautawa, Mama Jummai ta jefo musu harara tace; "shegu mayu, wallahi Allah ya isa tsakani na daku".
Nusreen ta ƙara kwashewa da dariya harda shewa, wanda hakan ba ƙaramumin ƙular da Mama Jummai ɗin yayi ba, itacen dake cikin wuta ta ɗauko ta nufo Nusreen ɗin gadan-gadan sai dai ganin yadda Nusram ta haɗe rai take kuma kallon ta yasa ta kasa ƙarasawa kusa da Nusreen ɗin, tana haki ta nuna Nusreen ɗin tace; "zamu haɗu ne shegu sunƙi aure".
Baba yayi sallama ya shigo, inda ya samu Mama Jumman ta sake cukuikuye Sahurar tana ƙoƙarin tura ta ɗaki, Baba yace; "yanzu dan Allah meye haka?".
Mama Jummai tace; "yauwa gwara daka zo, nice nan nace babu inda zata je, wai amma yarinyar nan sai ƙoƙarin ja dani take yi a gidan nan tana tona mini asiri, kuma wa'incan ƴaƴan mayun sune suke ƙara zugata".
Baba yace; "to ke meye na hana ta tafiya ki barta taje mana, bafa na son rigima", cikin hayagaga tace; "au haka ma zaka ce Abdullahi?, to wallahi ba zai saɓu ba".
Baba yasa hannu ya rabata da Sahurar sannan yace; "ke wuce kibi mijin ki", Sahurar kuwa ta nufi hanyar fita tana murna inda take ɗagawa Nusram hannu, Nusram ta mayar mata sannan ta wuce nasu ɗakin.
Suna idar da sallah Ummi tace; "Nusreen ke ba zaki dena ɗauko mini magana ba a gidan nan ko?", Nusreen ta cuno baki tace; "yanzu me nayi ko dariya ma ta zama rigima a gidan nan kenan bamu da ƴancin muyi dariya kenan?", Ummi ta kai mata duka Nusreen ta fice da gudu.
Nusram kuwa tabarma ta shinfiɗa musu a ƙofar ɗaki sannan ta zubo musu abinci, Nusreen ta ɗauko Kubra ta fito da ita, Nusram kuma ta ɗauko babbar roba sannan ta saka hijab tace; "bari naje na siyo mana ƙanƙara", daga haka ta fice.
Kasancewar gidan babu nisa da nasu yasa bata wani jima ba ta siyo sannan ta nufo hanyar gida, a ɗan lungun kusa da gidan su ta hangi mota, bata kawo komai ba ta shiga lungun.
Ganin shi sai da gaban ta ya faɗi, Babban mutum ne sanye da fararen kaya, hannun shi riƙe da waya yana dannawa, hasken wayar shiya haska mata fuskar shi ina da a take a lokacin ta gane ko waye.
Tana daf da shiga gida ya ɗago sannan yace: "amm ji mana", cak Nusram ta tsaya gabanta na faɗuwa, "idan kin shiga kice ana sallama da Nusram dan Allah", ji tayi kamar ta dawo ta kwaɗa mishi mari amma haka ta daure ta shige gidan kawai.
Koda ta shiga bata kuma bi ta kanshi ba, wajen randar su ta nufa ta ciko jug da ruwa ta buɗe tiyara ta zazzage a ciki ta juya sannan ta sassaka ƙanƙarar ta kawo ta ajiye musu.
Kusa da Nusreen ta je ta zauna amma ta kasa cin abincin har sai da Nusreen tace: "Ramluv, kin ƙi cin abincin?", da sauri ta jefa hannun ta sai dai tana kai lomar bakin ta yaro yana rangaɗa sallama.
Mama jummai dake nata ƙofar ɗakin ta amsa mishi domin yawanci su kan shigo domin yaranta ko kuma siyayya, yaro yace; "wai ana sallama da Nusram", Mama Jummai taja tsaki.
Nusram kuwa abincin da bata kai ga haɗiyewa ba shine ya dawo ya shaƙe ta inda gaba ɗaya ya haddasa mata tari me ƙarfi, Nusreen ta miƙo mata ruwa ta sha.
Yaron ya kuma maimaitawa, Mama Jummai cikin fushi tace; "dallah fita ka bawa mutane waje ai mun ji ko?", Nusreen tace; "kaje kace tana zuwa".
Tana zaune tana ƙoƙarin dai-daita nutsuwar ta taji sallamar Baba inda ya hau surfa mata faɗa akan ta bar mutum a tsaye, dole hakan tasa ta miƙe tayi cikin ɗaki.
"au ɗaki kika shige ba zaki fito ba sai na biyo ki ciki?", Ummi tace; "amma ai ka bari ta shirya ko?", rufe mini baki ɓammbaƙar munafika duk waye ya ɓata yaran idan bake ba", hakan yasa Ummi taja baki tayi shiru.
Nusram dake ɗaki ta fashe da matsanancin kuka, ita tunda take bata taɓa ganin uban da yake yiwa ƴaƴan shi abinda Baban nasu yake yi musu ba, haka bata taɓa ganin mijin da yake yiwa matar shi abinda Baban nasu yake yiwa maman nasu ba.
#LIKE
#SHARE
#COMMENT
*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.
*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*_daga alƙalamin ✍_*
*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*
*sadaukarwa gare ku*
*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*
*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*
*Heart you so much*
*Note:-* masu cewa basu gane rayuwar waye ake so a nuna ba an ce rayuwar Abdus-samad amma kuma ana kawo rayuwar Nusram, kada ku dama idan har kuka ƙara haƙuri zaku fahimci ina littafin ya dosa amma be kamata tun a yanzu ku yanke hukunci ba ya kamata ku haƙura har zuwa lokacin da littafin yayi zurfi sosai kada ku manta fa ko pages talatin ba'a yi ba kuma tun farko na faɗa muku littafin nada tsayi why d eager??.
Sannan ga masu son shiga whatsapp group na Rayuwar Abdus-samad kuyi searching Aishatu Babayo sai ku tura mata da number ɗin ku ta pc zata saka ku a ciki amma dan Allah iya mata kawai banda maza, Na gode sosai ga masu complain suna duba whattpad amma basa gani kuyi haƙuri wallahi ko ƙareenateey na kasa ƙarasa balle na fara saka wannan amma zan dage kan azumi na saka su duka acan ɗin tnxs for ur love😘.
📖📖27-28📖📖
Jiyo muryar Baba yana ƙara wage baki yana ƙwala mata kira yasa Nusram saurin goge hawayen fuskar ta, sai da ta ɗan gyara fuskar dan bata so kowa ya gane halin da take ciki.
Tana fitowa Baba ya kai mata ranƙwashi tsakiyar kai yace; "shegiya me baƙin hali irin na uwar ta, ko kare be taɓa zuwa ƙofar gidan nan da sunan yana son ki ba shine kinyi sa'a yanzu Alhaji Baballe zai rufa mana asiri ya rufa miki kema shine kika tsaya nurƙufanci ko?", Nusram bata iya cewa komai ba ta gifta mahaifin nata cikin baƙin ciki da damuwa.
A inda ta bar shi a nan ta dawo ta same shi, yana hango ta ya hau washe baki, Nusram kuwa cikin mutunci ta gaishe dashi.
Ya amsa yana ƙara washe bakin shi, "kinga dai yadda Allah yake ikon shi ko, wato dalilin da yasa kenan ko Sauro be taɓa zuwa ƙofar gidan nan da sunan yazo wajen ki ba ashe ke ɗin rabona ce".
Nusram ta haɗiye wani abu me ɗaci daya tsaya mata a maƙogoro, wato har labari ma Baba ya bashi kenan, bata iya cewa komai ba banda "Um ko u'um", yayin da shi kuma ya dinga yi mata surutu.
"abu na gaba da ya kamata ki sanu shine mata na guda biyu, yarana Ashirin da ɗaya cif, amarya nada goma uwargida nada sha ɗaya, kinga ke idan kika zo sai kiyo dozin".
Nusram ta kalle shi ta kauda kai, wai dozin lallai ma, suna nan tsaye Isa ya dawo, fuska a murtuke ya kalli Alhajin sannan ya shige gida.
Nusram ta ajiye ɓoyayyiyar ajiyar zuciya, shi kuwa Alhajin da yake be san me take ciki ba be wani damu ba, sai ƙarfe tara da rabi da ƴan mintuna sannan yayi mata sallama ya tafi.
Nusram kuwa har wata iska me daɗi taji tana kaɗata domin dai Allah ya gani ji take da atakure take, tana shiga zaure ta tarar da Isa a tsaye yana jiran shigowar ta.
Yana ganin ta ya nufo ta sannan ya ɗaga hannu hannu ya sharara mata mari, cikin masifa yace; "ni ina can na shanya baki ina jiran ki ashe ke kina nan kina taɗi da wani ƙato ko, to wallahi ko kina sona ko bakya so na baki da miji sai ni", yana ajiye aya Nusram ta raɓa ta wuce.
Ya fizgo ta ya haɗa da jikin bango sannan yace; "wallahi kina wasa dani da yawa ko, matuƙar naga zaki kuɓuce mini sai na raba ki da budurcin naki naga uban me mijin naki zai samu".
Gaban Nusram ya yanke ya faɗi, cikin sanyi tace; "Dan Allah ka sake ni na tafi mana", ya ture ta har sai da ta kusa faɗuwa sannan ya fice ya barta.
Nusram ta tsuguna a wajen ta saka kanta tsakanin ƙafafun ta sannan ta fashe da kuka, ita kaɗai ta san ya take ji a cikin zuciyar ta.
Ta daɗe a wajen dan sai da taji alamun Baba zai shigo sannan ta miƙe cikin sauri ta shige gida, a bakin ƙofa ta tsaya ta gyara kwalliyar ta sannan ta shiga.
Nusreen dake tsaye da hijab a hannu da Ummi dake kan abin sallah suka bita da kallo, Nusram tace; "ke kuma lafiya na ganki tsaye da hijab?", Nusreen tace; "Allah dama naga kin daɗe ne shine wai zan biki naga ina kika tsaya ne ko lafiya", Nusram tayi murmushi sannan ta juya tace da Ummi; "har ya tafi bari naje na kwanta, Rim muje ciki na san dai Shureim ba zai zo ba tunda tara ta wuce", Nusreen kam kai kawai ta ɗaga.
Sai da suka gama shirin barcin su sannan Ummi ta shigo, ta kalli Nusram tace; "Nusram ki faɗa mini tsakanin ki da Allah kina son wannan alhajin?", Nusram babu ko ɗar ta ɗagawa Ummi kai, Ummi tayi ajiyar zuciya sannan tace; "shikenan tunda haka kika ce, ku kwanta kawai amma ki sani matuƙar bakya son shi to ki sanar dani domin rayuwar aure ba ɗaya take data gida ba", tana faɗin haka ta fice.
Nusram ta saki ajiyar zuciya sannan ta kwanta, Nusreen ma haka sai data jima sannan ta sami damar cewa; "wai Ramlove da gaske ne kina son Alhaji Baballe?".
Nusram tace; "sosai ma kuwa, mutumin nan babu ruwan shi gashi da sauƙin hali ga barkwanci baki ga yadda ya dinga saka ni ina dariya ba, ni dai gaskiya yana birge ni sannan ina jin daɗin mu'amalata tare dashi", Nusreen tace; "amma fa kin sani Nusram Alhaji Baballe tsoho ne sannan baya da mutunci akan kuɗi a gaban ki fa Baba yake zagin shi akan baya da mutunci yanzun ma idan kika bibiya kuɗi ne ya haɗa su ake so a saka ki a tsakiya".
Nusram tace; "bana jin abinda Baba yake faɗa akan shi gaskiya ne kin dai san halin baba, sannan maganar kuɗi kuma zato kike yi dan haka kada ki tada hankalin ki akan hakan", Nusreen tace; "amma dai ni ƴar uwar ki ce ko, dan haka ba zan taɓa so wani abu ya cutar dake ba kamar yarda kike ƙoƙari wajen ganin kin bani farin ciki kin kuma kare ni daga duk wani abun cutarwa Nusram kece fa kawai wacce nake da ita, ƴar uwa ta rabin jiki".
Nusram ta balla mata hararar wasa sannan tace; "ina kika bar Kubra, Sahura dasu Ameera kiji mini yarinya".
Nusreen tayi dariya tace; "Allah da gaske basu kai mini ke ba, Nusram tare fa muka kwanta a cikin mahaifiyar mu tsayin wata tara abincin da zamu ci yana haɗe dana juna, muka fito tsayin shekara biyu mahaifiyar mu na ciyar damu da abinci kala ɗaya wanda har kika sha ki saki na kama kema kuma na kan sha na saki ki kama tun lokacin da muka fara wayo har tana Pant kala ɗaya muke sakawa kuma bamu taɓa raba wajen kwana ba, taya zan haɗaki da wasu, ke ɗin *Bloody*😭 na ce".
Ummi ta katse zancen ta hanyar cewa; "tabbas abinda Nusreen ta faɗa gaskiya ne, kunfi kusanci da juna sama da duk sauran ƴan uwanku Kamar yadda bakya son wani abu ya same ta haka itama bata so wani abu ya same ki, dukkanku kuna son junan ku sai dai ba zai taɓa kaiwa koda rabin son da nake yi muku ba, nice mahaifiyar ku na ɗauki wahalar ku tun daga lokacin da kuke ciki na, a cikin abincin da naci a ciki kuke samu kuma kuci, lokacin da cikin ku ya kai wata takwas bana iya barci kwata kwata sai da rana da ranan ma a zaune, nazo naƙudar ku haka nasha wahala kamar zan mutu, bayan na haifo ku nayi tunanin wahala ta ƙare ashe yanzu wata sabuwa zan ɗora domin kuwa da ɗaya ta fara kuka ɗayar zata ɗauka, haka zan ta rarrashin ku, kuyi barci da rana ni kuma da daddare ku hana ni yin barcin amma duk da haka banji a raina cewa wai bana son ku ba, naci fitsarin ku naci kashin ku, naci tunɓuɗin ku amma duk da haka ban gaza, daga baya nauyin kula daku ya dawo kaina haka kuma nake ta haƙuri, ki sani Nusram shekarun dana ɗauka ina wahala dake ba zai saka nace na gaji dake idan ma kina tunanin dan ki kauce mini da wahalar da nake ba to ki sani koda zaki ƙara shekara ashirin ko sama da haka matuƙar ina da rai ba zan taɓa gajiya dake ba", Nusram cikin kuka ta haɗa su duka ta rungume.
"tawa ƙaddarar kenan ba zan taɓa samun farin ciki ba a rayuwa ta, kuma tabbas aure ya zamar mini dole ko dan gudun samun matsala da kuma ɗaukewar farin ciki a rayuwar ku", abinda take faɗa kenan a cikin ranta.
Sun ɗan taɓa fira a tsakanin su kafin su kwanta barci, sai lokacin Nusram ta ɗan sami sauƙin abinda yake ranta don ko babu komai firar da suka ɗan yi ta rage mata damuwa ba kaɗan ba.
******** **********
Jikin shi sanye da Wando jeans fari da kuma rigar polo t shirt kalar blue da ratsin fari, ƴar ƙaramar jakar shi ce riƙe a hannun shi, Fadil kuma yana bayan shi haka suka shigo da sallama.
Kamar koda yaushe suna saman dinning table inda zasu yi breakfast, Sumayya dake cin abinci ta gaishe dashi, ya amsa fuska a sake sannan ya gaishe dasu, kowa ya amsa kamar kowanne lokaci amma banda Brr Hauwa.
"idan kin gama tashi mu tafi", Sumayya tace; "to Yaya", sannan ta miƙe, cikin rawar jiki Husna tace; "Ya Abdul kai ba zaka ci abincin bane?", be kalle ta ba balle ta saka ran samun amsa daga gare shi.
Hajja tace; "baka ji ana yi maka magana bane?, ni ina mamakin halin ka domin iya sani na uban ka ba halin shi ba kenan, anya kuwa kai ɗan shi ne?".
Wata irin ɗagowa Abdul yayi sannan ya kalli Hajja, itama Malama kamar zata zubar da hawaye take bin Hajjan da kallo.
Ganin yadda ranshi ya ɓace yasa Hauwa cewa; "waye ya sani ko a yawon neman shaidu aka samo shi aka zo aka ƙaƙabawa ɗan uwa na, ni dama na jima ina tunanin haka dan ko kama baya yi da ƴaƴan Doctor".
Hajja ta girgiza kai tace; "tabbas hakan zata iya kasancewa bari Abubakar ɗin ya dawo dole azo ayi bincike kada a lalata mana zuria da bara gurbi".
Wannan karan kam da Sumayya da Malama kasa daurewa suka yi dan haka Sumayya ta saki kuka, Malama kuwa hawaye ta hau sharewa, Fadil kan shi na ƙasa sai dai yadda ya tsuke baki zai tabbatar maka da cewa yaji haushin abin.