Showing 30001 words to 33000 words out of 121992 words
Chapter 11 - Rayuwar Abdussamad Book Complete Document by Yar Mutan Zazzau .txt
T345 ta nemo number ɗin shi da ƙyar sannan ta bata, ita kuma Nusram ta kwafe Number ɗin.
Tana miƙawa Sahura wayar ta Mama Jummai na fitowa daga ɗaki, ta kama baki tace; "au yanzu kuma abinda aka koma kenan? Kai ni Jummala ina ganin abu a gidan nan, ke kuma uwar me kike tare da wannan uwar matan?".
Sahura ta zumɓuro baki tace; "kai Mama wannan ai tsakanin mu ne ba sai kinji ba", Mama Jummai tace; "ni kike faɗawa haka wallahi idan baki baro wajen nan ba sai na kusa karya ki".
Ta ƙara zumɓurar baki tace; "ai shiyasa nake so na koma gidan miji na kona huta da matsalar ki, kinji Nusram sai gobe kawai duk yadda kuka yi ki neme ni".
Mama Jummai ta buga salati tana tafa hannu; "Sahura ba dai mijin ki kika bawa wannan ba? Sahura yaushe zakiyi hankali ki fahimci me sanki ne da wanda basu son ki, shikenan ta fitar mini da ƴa ita kuma tana so ta shiga gidan wallahi bari uban ku ya dawo sai na faɗa mishi".
Nusreen dake tsaye a ƙofar ɗaki dan hayaniyar Mama ta fito da ita taja tsaki tana faɗin; "me za'a yi da wannan me zubin ƴan daudun".
Nan Mama Jummai tayi kanta dama kamar jira take yi, ita dai Nusram ɗaki kawai ta shige domin bata da lokacin tsayawa shirmen su dsn yanzu abin ya dena bata tsoro ya koma bata dariya suyi ta abu kamar ƙananan yara.
Ummi dake tsaye bakin ƙofa Nusram tace; "Ummi dan Allah kizo ki zauna ki ƙyale wa'innan da suka koma kamar Annabi da kafiri".
Ummi ta shigo ɗakin ta tsaya kusa da ita tace; "Nusram faɗa mini gaskiya meya haɗa ki da Sahura kuma meta baki a wayar ta".
Nan Nusram ta kwashe komai ta faɗa mata, Ummi ta ɗan yi jim sannan tace; "eh to hakan ma abu ne me kyau amma baki tunanin wata matsalar ta biyo baya?".
"insha Allahu babu abinda zai biyo baya sai alkhairi", abinda Nusram ta faɗa kenan tana maida kallon ta kan Nusreen ɗin data shigo tana faman haki.
Ummi tace; "ke wai yaushe zakiyi hankali ne, wannan fa matsayin mu ɗaya da ita a wajen ku amma ke kullum baki da abokiyar faɗa sai ita".
Waje ta nema ta zauna tana faɗin; "zan dena ne Ummi, Ramluv muga kayan?", Nusram ɗin tayi banza da ita.
Nusreen ta taɓe baki, "nifa na shiga uku na manta nayi alƙawarin denawa yanzu sai na sake ladabi kenan", ta faɗa cikin ranta.
"wallahi Ramluv na manta da munyi alƙawarin na dena kuma ai kinga itace ta fara nema na da faɗa, kiyi haƙuri ba zan sake ba na miki alƙawari".
Nusram ta mata wani kallo sannan tace; "alƙawarin ki na banza Nusreen anjima nan karya shi zaki yi dan haka ki hutar da bakin ki kawai bana buƙata", daga hakan ta juya ta maida kallon ta kan Ummi sannan ta fara bata labarin abinda ya faru amma ce mata tayi kawai tazo tsallaka titi suka bugeta ta kuma ɗauko kuɗin ta nuna ma Ummin.
Ummi tace; "Allah sarki an gode sosai amma kuɗin yafi na kayan da kin sani ma baki amsa ba".
Nusram tace; "wallahi Ummi naso naƙi amsa amma yadda suka bani tasa dole na amsa", Ummi tayi ajiyar zuciya tace; "shikenan ai".
Nusreen tace; "yauwa Rimluv sai mu siyo cooler kawai dashi", Nusram tayi kamar bata ji ta ba, Ummi tace; "eh hakan yayi idan yaso gaba sai ku siyo flask ɗin".
Nusram tace; "shikenan Ummi yadda kika ce haka za'a yi", Ummi tace; "yauwa Allah yayi muku albarka amma cooler ɗin ki siyo ku biyu".
Nusram tayi murmushi tace; "Ummi cooler ta nawa-nawa kenan ki bari dai gaba idan na sami kuɗi na sayi tawa".
Haka Nusram ta ƙara yinin ta tana me share Nusreen ɗin, ita kuma Nusreen ɗin abin duk ya dame ta hakan yasa ta dinga aunawa Mama Jummai harara a ganin ta itace silar ɓatawar ta da ƴar uwar ta.
Da daddare suna zaune suna cin abinci, Baban nasu ya shigo kamar ko wane lokaci be amsa sannu da zuwan da Ummi da Nusram suke mishi ba.
Suna jiyo lokacin da Mama ke faɗa mishi ƙarya da gaskiya akan wai Nusram tana so ta ƙwacewa Sahurar miji.
Nan ya fara bambami tun daga ƙofar ɗakin nasu, yana faɗin; "ba'a nan gidan ba kina babbar banza har yanzu kin kasa fitar da miji yanzu kuma muguntar da zaku koma kenan?".
Nusreen ta cuno baki, yana ƙarasowa kusa dasu ya rarumi itace yayi kansu, Nusreen dai Allah ya taimake ta tayi ɗaki da gudu dan haka dukan akan Nusram aka sauke shi.
Babu wanda yace yayi haƙuri sai Sahura dake ƙoƙarin fahimtar da Baban ba haka bane, amma ina bema bi ta kanta ba, Isa ne daya shigo yayi kan Baban ya samu ya ƙwace itacen yana bashi haƙuri.
Tunda yaga Baban na duka ita kuma bata motsa ba ya tabbatar mishi da Nusreen ce, dan haka yaje ƙwatar ta.
Allah yasa beji mata ciwo ba sai dai duk jikin ta ya tashi, kuma ko ɗigon hawaye domin kuwa idan da sabo yanzu ta saba da dukan baban nasu.
Isa yace; "Baba kayi.mata haƙuri ba zata kuma ba, ke Nusram ki sako hijabi ki same ni a waje", bata amsa ba domin baƙin cikin dake cikin ranta.
Yana fita itama ta miƙe ta shige ɗaki domin zuwa lokacin Nusreen ɗin ta buɗe ƙofar tabbatar da cewa Baban ya fita zuwa lokacin.
Nusreen na ganin Nusram tace; "Ramluv ki dena tsayawa Baba na dukan ki", wata irin tsawa ta daka mata sosai Nusreen ta tsorata dan haka ta ja baya.
"idan ma ya kashe ni ina ruwan ki, ko kina da asara ne?", Nusreen kam ta kasa magana sai dai binta da idanu dan ta san tana misbehave zata iya jibguwa a hannun ta dan idan tayi zuciya babu kyau.
Nusram taja tsaki sannan ta ɗauki hijab ta fice, Mama Jummai na zaune tana guɗa tana kuma sakin habaici.
Nusram ta matsa kusa da Ummi tace; "Ummi zan je kiran Isa ba zan daɗe ba zan dawo", Ummi ta ɗaga mata kai kawai, ita kuma ta juya ta fice.
A saman dakali ta same shi zaune, jiki na rawa ya miƙe yana bata wuri ta zauna, Nusram dai abin har mamaki yake bata.
Sun ɗan jima a haka yana kame-kame kafin yace; "abinda yasa na kira ki shine, kinga wannan dukan da Baba yake miki bana jin daɗin shi kwata-kwata shi yasa na yanke wani hukunci akan mu ni da ke, kinga dama banyi aure ba kema kuma kina zaune bakiyi aure ba shine nace me zai hana mu auri juna kawai".
Wani irin bugawa zuciyar ta tayi bata taɓa kawo haka ba idan tayi la'akari da yadda yake ɗaya daga cikin maƙiyan su na cikin gidan, cikin kiɗima da tashin hankali tace; "me kace Isa ban fahimta ba?".
Yace; "ina nufin mu dai-dai ta kanmu kawai ki amince mini naje da maganar gaban Baba akan cewa mun dai-daita juna a ɗaura mana aure hankali kwance na san Baba ma zai yi farin ciki sosai domin hakan kamar taimakon juna ne".
Wani irin gumi ne ya karyo mata tasa hannu ta share, miyan da zata haɗiya ma.ya gagare ta, gaba ɗaya ƙwaƙwalwar ta bata aiki hakan yasa kawai ta lumshe idanu tana me karanto duk addu'ar da tazo ranta.
Can wata dabara ta faɗo mata rai dan haka ta kalle shi tace; "Isa ka bari naje nayi tunani a kai", ya jinjina kai yace; "shikenan na baki wannan damar amma ki sani idan har kika sake kika ƙi amince mini wallahi sai na faɗawa Baba cewa mun amince da juna sannan kuma in aure ki in gallazawa rayuwar ki sai kin gwammaci zaman ki a nan gidan dan haka kada ki sake ki ƙauracewa magana ta".
Nusram ta girgiza kai hawaye ya zubo mata tace; "dan Allah Isa ka bari na san abinda zan yi akai", Isa ya ɗaga kafaɗa yace; wannan kuma ruwan ki ne?", yana gama faɗin hakan ya wuce ya barta a wajen.
Ta saka hannu ta share hawayen daya zubo mata sannan ta juya domin shiga gida.
Cikin sauri Naufal yace; "Nusreen", jin sunan yasa taja tsaya, juyowa tayi tana kallon su, mutane biyu ne a tsaye kasancewar da hasken farin wata kuma suna cikin hasken yasa ta hango su sai dai basa kusa hakan yasa bata gane ko wasu waye ba.
Jiki a sanyaye ta ƙarasa kusa dasu, ta bisu da kallo Nuafal yace; "sannun ki ko?", ta kalle shi sannan ta kalli wanda ke gefen shi gani take kamar ta taɓa ganin fuskar amma ta manta waye.
"yauwa sannu", Naufal ya kuma cewa; "dama muna neman wanda zai kira ki ne ashe kece ma a nan waje".
Cikin tsananin kisha Shureim yace; "fisabilillahi haka muka yi dake? ni ina can na kasa samun sukuni saboda zullumin amsar da zaki bani amma ke kina nan kina rayuwar ki tare da wani na wai ya kike so nayi ne?".
Naufal ya galla mishi harara domin tunda suka fahimci itace Shureim ɗin yaso yaje ya yiwa saurayin nata rashin mutunci ya hanashi kuma ko yanzu sai da yace; "idan tazo kada yayi mata maganar".
Nusram tayi murmushi domin sai yanzu ta fahimci waye domin kuwa Nusreen ta faɗa mata yadda suka yi, tace; "ya jikin Mama fatan anyi aikin cikin nasara?".
Shureim yace; "kinga ni ba wannan na tambaye ki ba waye wancan daya tafi yanzu?", Nusram ta koma yin dariya sannan tace; "baka gane ni ba ko? To ni ba Nusreen bace ƴar uwar Nusreen ɗin ce dai Nusram".
Wayyo! Ji yayi kamar ƙasa ta tsage ya shige, shifa tsabar kishi ya manta cewa su ƴan biyu ne, ya shafa kai yace; "ayya! Wallahi na ɗauka itace, aikin kam anyi shi sai dai mu jira sakamako kawai".
Tace; "to Allah yasa muji alkhairi bari na kira maka Nusreen ɗin", tana faɗin haka ta juya ta tafi.
Naufal ya kalli Shureim yace; "wallahi yau Allah ya taimake ka amma daba haka ba yau da babu me kwatar ka sai Allah kai da ba'a gama amicewa da kai ba amma har ka sami bakin tuhuma Allah ya soka".
Shureim yayi murmushi yace; "Allah sarki baiwar Allah, me kyawun hali ga hankali", cikin tsokana Naufal yace; "to kodai ita zaka komawa ne?", Shureim ya harare shi.
Nusram kuwa ganin saurayin ƴar uwar nata ya ɗan rage mata damuwa kaɗan don haka da ƴar ƙarfin gwiwar ta ta shiga gidan.
Nusreen na zaune Kubra na saman ƙafar ta yayin da take shafa mata magani Ummi kuma na gefe suna fira.
Da sallama ta shiga kafin ta zauna kusa da ƴar uwar tata cikin farin ciki ta kalle ta tace; "yauwa Rim kawo Kubrar na ƙarasa shafa mata maganin kije waje kina da baƙo".
Nusreen ta washe baki domin kuwa ta san Alƙah ne ya taimake ta har Nusram ɗin ta sauko ta san zuwan mutum ɗaya ne zai dawo da walwalar ƴar uwar tata amma duk da haka cikin salon tsokana tace; "waye kuma?".
Nusram tace; "waye kuwa banda Shureim yana nan a waje dan Allah tashi kije kada ya gaji da jira", Nusreen ta taɓe baki ita ta rasa me yasa ƴar uwar tata ke sonta da Shureim ɗin.
Nusram ta miƙo mata hijab wanda yake a linke tace; "amsa ki saka tashi maza kije", to ya zata yi da naciyar Nusram ɗin gashi tunda ta lura Nusram ɗin na son ta dashi take ganin zata iya amsa mishi.
Amsa tayi ta saka sannan ta yiwa Ummi sallama ta fita, Nusram tace; "yauwa Rim a dawo lafiya", Nusreen ta girgiza kai tana dariya kawai.
Tana fita ta hango su yanzu sun dawo inda su Nusram suka zauna ɗazu domin nan babu hasken wata sai dai ta san su biyu ne kamar koda yaushe dan haka ta hade fuska domin janyowa kanta girma ta fara takawa zuwa inda suke.
Tunda ta fito Shureim ya zuba mata idanu kamar ya maida ta ciki haka yake ji, da sallama ta ƙaraso suka amsa mata sai da suka gaisa sannan Naufal yace; "munzo jin amsar mu ne me aka yanke?".
Nusreen ta dan yi jim sannan tace; "akwai alƙawari da na yiwa ƴar uwata zan jira ta har zuwa ta sami mijin aure dan haka idan kaima zaka iya haƙura zuwa lokacin shikenan".
Naufal yayi murmushi yace; "kafin ayi maganar aure ai za'a yi ta soyayya ko yanzu ita ta kawo mu", Nusreen tace; "tunda ƴar uwata tana sona dashi nima na amince ko dan farin cikin ta".
Naufal yace; "ah lallai mun gode sosai sai ki miƙa mana gaisuwa gare ta, lallai na jinjina mata kuma tayi mana ƙokari", Shureim yayi ajiyar zuciya yace; "Alhamdulillahi na gode sosai".
Naufal yace; "yanzu shikenan zamu sami Baba mu nemi izinin shi dan ya san da zaman mu", Nusreen tace; "shikenan", nan dai suka ɗan taɓa fira.
Suna daf da yin sallama Baban ya iso, da torch light ya haska su, ganin Nusreen yasa yace; "to ƴar banza yau kuma iskancin har ƙofar gida na?", Nusreen ta zumɓuro baki cike da jin haushi.
Su Shureim suka gaishe da Baban ya amsa sannan ya maida kallon shi kan Nusreen yace; "kin wuce kin bani waje ko kuwa?", ba dan ranta yaso ba tayi cikin gida.
Baba ya kalli Shureim yace; "ku kuke lalata mini yara ko?", Shureim ya girgiza kai yace; "a'a Baba", Naufal ya ɗora da cewa; "dama munzo neman amincewar tane kafin muzo neman izini wajen ka".
Baba yace; "su har wani neman izinin ta kuke yi?, waye yake sonta a cikin ku?", Naufal ya nuna Shureim.
Baba ya kalli shureim yace; "yaro ya sunan ka? Kuma wacce kake so a cikin su?", Shureim ya shafa kai yace; "Nusreen nake so kuma sunana Shureim".
Baba yayi murmushi yace; "Shureim in dai Nusreen ce na baka ita kaje ka turo magabanta ka kawai a tsaida rana bana so ta kai wata me zuwa a gida na".
Shureim da Naufal suka kalli juna, su dai tunda suke basu taɓa jin anyi aure haka ba, Naufal yace; "to shikenan Baba mun gode sai dai wani hanzari ba gudu ba, Mahaifin shi ya rasu sai Mahaifiyar shi, Mahaifiyar shi kuma bata ƙasar tana can ƙasar Syria za'a mata aikin ƙafa to muna neman alfarma a bamu dama har zuwa lokacin da zata dawo".
Baba yayi jim sannan yace; "shikenan Allah ya kaimu, kai fa idan har kana so zan iya baka ƴar uwar ta", Naufal ya girgiza kai yana faɗin; "a'a Baba ina da mata".
Baba yace; "to shikenan amma ƙofa a buɗe take idan har da wanda kake ganin zai iya auren ta to kawai ka turo mini shi koda babu akwati sadaki kawai ya isa kaima kuma kada ka takurawa kanka", Shureim ya amsa da to.
Naufal ne ya matsa kusa da motar shi ya ɗauko rafas ɗin ƴan ɗari biyar-biyar ya haɗo da ƴar takarda, biron dake jikin aljihun rigar Shureim ya zara sannan yayi rubutu ya haɗa ya miƙawa Baba yace; "Baba ga wannan a saka mana albarka wannan kuma Number ɗin abokina ne dan Allah a bawa Nusreen ɗin ace ta kira shi dan Allah".
Baba ya washe baki yana faɗin; "ah lallai za'a je daku na gode sosai Allah yayi albarka insha Allahu ina shiga zan bata", ya amshe yana saka musu albarka, nan suka yi sallama ya shige gida su kuma suka tafi.
Ɓangaren Nusram kuwa tana gama shafawa Kubra magani ta ɗauketa ta kaita kan shinfiɗar ta, sannan itama taje tayo alwala tazo ta kwanta.
Abubuwan da suka faru yau su suka dawo mata cikin kai, haka harta gangaro kan zuwan ta kasuwa da bigeta da wannan bawan Allah yayi, dawowar ta gida zuwa ga matsalar Sahura, dukan da Baba yayi mata da magan-ganun da suka yi da Isa.
Tasa hannu ta share hawayen daya zubo mata, yanzu ina zata saka kanta?, gaskiya ko aure zata yi ba zata auri Isa ba sanin cewa ba wai zai iya riƙeta bane.
Ta miƙe ta zauna taja ajiyar zuciya tana ganin kawai gobe zata kai tallan kanta ne masallaci wanda ta yiwa sai yazo ya rufa mata asiri, to kina da tabbacin shi yana da hali me kyau?, abinda zuciyarta ta faɗa nata kenan.
Sai dai duk halin da take ciki bata so Nusreen ta rasa wannan saurayin domin tana ji a jikinta zai zamewa ƴar uwarta alkhairi.
Faɗuwar ƴar uwarta jikin ta ya katse mata tunani, Nusreen ta rungume ta tana dariya, Nusram ma cikin dabara ta goge hawayen fuskar ta.
Ta ɗago Nusreen tace; "Rimluv ban labari na sha meya faru", Nusreen tayi dariya tace; "Ram na amince da Shureim domin shima ya amince da sharadi na".
Nusram tace; "bangane ba? Wane sharaɗi?", Nusreen tayi fari tace; "sharaɗina mana na ba zai nemi aure na ba sai kin sami naki mijin".
Shiru Nusram tayi na ɗan lokaci kafin tace; " haba Rimluv wannan wane irin sharaɗi ne?, gaskiya ki janye", Nusreen ta miƙe tana taɓe baki