Showing 63001 words to 66000 words out of 121992 words

Chapter 22 - Rayuwar Abdussamad Book Complete Document by Yar Mutan Zazzau .txt

28 Dec 2024

16091

tsaye a kaina kan nayi wani motsi ta faɗo jiki na tana faɗin wai sai na biya mata buƙata".


Nusram ta girgiza kai hawaye yana zubo mata jin irin sharrin da Isa yake mata, Baba yace; "ni kam na shiga uku yanzu iskancin naki gida ya dawo kenan?, wallahi idan kika cigaba da ɗauko mini magana zan tsine miki kibi duniya".


Nusram hankali tashe ta rarrafo zuwa gaban Mahaifin nata cikin kuka tace; "dan Allah Baba kayi haƙuri wallahi ba haka bane nazo shigowa gida ne shine ya jani ɗakin shi don yayi mini fyaɗe har ya yaga mini riga amma wallahi bani naje ɗakin ba".


Mama Jummai tayi salati tana tafa hannu tace; "yanzu Nusram waye zai miki ƙarya Isa ko waye", Baba yace; "bar shegiya me baƙin hali".

Baba Sailuba tace; "shegantata zaka yi Abdullahi yanzu ɗan shege yafi ɗan sunna a wajenka, lallai ba banza aka barka ba".


Baba yace; "Yaya ki duba wannan lamarin fa", ta ɗaga mishi hannu tace; "ya isa haka Abdullahi maganar yarinyar nan abin dubawa ne be kamata ka goyi bayan ɗaya daga cikin su ba zaka yi dana sani fa".


Nan dai Baba ya tafi yana bambamin shi, Baba Sailuba ta ɗago Nusram tace; "kinji kiyi ta addu'a Allah yana sane da ke", Nusreen ta amshi Nusram ɗin suka shige ɗaki suna kuka.


Ummi kuwa banda hawaye babu abinda takw gogewa Aunty na ƙara kwantar mata da hankali, to dai magana ta shiga unguwa domin kuwa jama'a duka sun ji, wasu sun yarda da abinda Nusram ta faɗa wasu kuma sun ƙarya ta jin abinda ya faru tsakanin ta da Alhaji Baballe ɗazu.


Ranar dai kam gidan ba kowa yayi barci ba wasu hidimar biki wasu kuma ɓacin rai ya hanasu barci ciki kuwa harda Nusram wacce tasha kuka ta godewa Allah.


Washe gari da safe kuwa da ƙyar take buɗe idanun ta saboda kumbura da yayi, Nusreen ma dai idanun ta yayi ja sosai dan itama kwana tayi tana kuka don taya ƴar uwar ta jimami.


Koda Aunty tazo ta same su a kwance nan ta rufe su da faɗa, haka dole Nusreen ta tashi tayi wanka ta shirya don an kusa ɗaurin aure.


Nusram kuwa magani tasha sannan ta koma ta kwanta, ta ɗaga hannu ta kalli lallen dake zane a hannun ta wanda da ƙyar ta bari akayi mata shi sai da Ummi tayi mata kuka sannan ta bari aka yi shi.

A yanzu kam babu abinda ta tsana kalar auren nan nata, ta ɗaga kai ta kalli yadda jama'a ke hada-hada.

Nusreen ake sheƙawa kwalliya me kyau da kuma ɗaukar hankali, Aunty ta shigo ganin Nusram ɗin a kwance yasa tace; "au yanzu baki tashi ba kenan? haba Nusram tashi dan Allah mana", ta ƙarasa tana kamo Nusram ɗin don ta miƙe.


A haka jikin ta babu wani ƙarfi ta miƙe ta ɗauke sosa da sabulu tayi bayi, ta tarar Aunty ta haɗa mata ruwa me kyau da ƙamshi nan tayi wankan sannan ta fito.


A wajen famfo suka haɗu da Atika wani lace ne me tsada ta saka a jikin ta, sosai taci kwalliya zaka iya tunanin ma itace amaryar.


Nusram ta kauda kai gefe batare da tace mata komai ba, Atika kuwa ta saki murmushi na izgilanci tana sakin shewa.


Tana shiga Aunty ta jata zuwa uwar ɗaka nan suka tarar da Safeena tana zaman jiran su dan haka tana shigowa ta fara aikin ta wato kwalliya.


Sadiya ta buɗe ledar kayan da Yaya Sulaiman ɗin ya bata jiya ta ɗauko mata shaddar, doguwar riga ce wacce taji stone work har zuwa ƙasa tayi kyau sosai.


Babu yadda Safeena bata yi da ita akan ta tsaya ta ɗaura mata ɗan kwalin ba amma taƙi, dan haka gyale fari ta yane kanta dashi zuwa kafaɗar ta kawai.


Tana zaune tana kallon Nusreen yadda take ta sakin murmushi cikin farin ciki da annashuwa.


Nusram ta miƙe tsaye sannan ta ɗauki ɗan ƙaramin memo wanda ke ajiye saman cabinet ɗin su, ta zame ta fice.


Jan gyalen tayi ta rufe rabin fuskar ta hakan yasa har ta gifta Ummi da Aunty wainda ke tsaye suma sanye da shaddar duka kala ɗaya da tasu basu lura da ita ba.


Koda ta fito ƙofar gida babu kowa domin kuwa duk suna masallacin dake gaban gidan kaɗan inda anan ne za'a ɗaura auren.


Haka kawai zuciyar ta ke zafi dan haka ta yanke shawarar fitowa ta dan miƙe ƙafa domin ta ɗan sha iska.


A hankali take tafiya hawaye na zubowa daga idanun ta, yanzu shikenan ta san cewa ba zata taɓa farin ciki a rayuwar ta ba kamar mahaifiyar ta ƙila gwara Ummi ma domin ƙila tana amarya ta ɗan ji daɗi.


Abdus-samad dake sanye da shadda kalar ruwan toka yayi kyau sosai duk da be cika wannan shigar ba, tare suka zo da Fadil domin halartar ɗaurin auren saboda Shureim.


Jin hayaniya tayi yawa yasa ya fito daga masallacin domin ya sha iska, yana tsaye yana danna waya ta bullo hanyar.


Jin ƙamshi me daɗi da sanyi yasa Abdus-samad ɗagowa ya kalle ta, ganin wannan yarinyar ce yasa gaban shi faduwa, ya tsura mata idanu.


Tayi baƙi ta rame yabi ta da kallo tun daga sama har ƙasa tayi kyau sosai sai dai kuka take kuma hankalin ta baya kan inda take tafiya.


Ba lallai ka lura da kukan da take yi ba idan ba ka lura sosai ba, tana zuwa daf dashi ta ɗan bigi hannun shi wayar ta faɗi.


Sai lokacin hankalin ta ya dawo jikin ta, cikin sauri ta tsugunna domin ɗauƙo wayar, a tare suka miƙa hannu domin ɗauƙo wayar. Da sauri ya janye hannun shi ta ɗauka, tana ƙoƙarin miƙewa gyalen kanta ya zame gashin ta ya bayyana wanda yake dogo ga baƙi ga santsi wanda kuma ya sha gyara da mayuka me kyau da ƙamshi.


Saura kaɗan Abdus-samad ya suma a wajen domin Allah yayi shi da son mace me gashi, baya manta lokacin yana yaro haka zai zaunar da First Love ɗin shi ya saka mata rigima akan zai mata tsifa yayi ta wasa da gashin.


Kan ya ankara har Nusram ta miƙe tana ƙoƙarin gyara gashin nata, Abdus-samad ya kai hannu ya ɗauko ribbom ɗin ta ya miƙe domin miƙa mata wanda itama Nusram din sai lokacin ta lura da ko waye.


Zaro idanu tayi jikin ta ya ɗauki rawa, da sauri ta fara ja da baya kafin ta juya da sauri, Abdus-samad yayi saurin binta domin amsar wayar shi ya kuma bata ribbom ɗin ta amma ina ko ƙeyar ta be gani ba.


Cikin sauri yake bin lungunan domin neman ta sai can ƙarshen lungun ya hango ta, tana tafe tana waige-waige kan ya ƙaraso ta fice daga lungun.


Tana isowa ƙofar gida ta samu jama'a cike alamu dai an gama daurin aure, Sahura ta tare ta tace; " Yaya Nusram ina kika shiga", da sauri Nusram ta juya ganin Abdus-samad ya kusa ƙarasowa inda take yasa taja hannun Sahurar suka shige cikin gidan.


Abdus-samad ganin ta shige gidan yasa yayi murmushi yana faɗin; "Nusram! Nice name".


Fadil ya ƙaraso wajen shi da sauri Abdus-samad ya saka ribbom ɗin cikin aljihun shi gudun kada Fadil ya gani.


"ina ka shiga ne ga Shureim.can da abokanan shi suna neman ka", Fadil ya faɗa, Abdul yace; "muje wajen nasu yanzu me zasu yi?".

"zasu shiga a gaisa da ƴan uwan amarya ne", Abdul yace; "ok to.muje wajen nasu", haka suka ɗunguma zuwa cikin gidan su Nusram ɗin.


Sun gaisa da jama'a an kuma ɗauki hotuna inda suka yi al'adar kaduna wato kiɗan ƙwarya nan abokanan ango suka cashe da kakanin amarya akayi wasa da dariya kafin suka bawa kakar su Nusreen ɗin kuɗin cin goro sannan suka fito ana ta sam barka.


Abdus-samad dai duk yadda ya baza idanu Allah be bashi sa'ar hango Nusram ɗin ba haka ya haƙura suka tafi.


Nusram kuwa suna shiga gidan ta saki hannun Sahurar sannan tayi nasu ɗakin, anan ta tarar dasu Ummi ana ta guɗa ana faɗin; "an ɗaura".


Zuciyar Nusram kamar ta faɗo ƙasa tsabar takaici, tana shiga wata cikin abokan wasan su tazo ta turare ta hau fesa mata, Nusram ɗin ta saki kuka sannan tayi cikin ɗaki.


Tana shiga taji ana sanar da shigowar su Shureim ɗin dan haka ta koma gefen katifa ta zauna tana me sauke ajiyar zuciya tana kallon su Nusreen suna leƙe ta window amma ta ita ta kasa leƙawa har suka fita.


Babu jimawa aka sanar da shigowar Alhaji Baballen tare da nashi tawagar, nan suma aka yi wasa da dariya inda ya bawa kakannin Nusram ɗin maƙudan kuɗi na cin goro nan fa waje ya ɗauki shewa da guɗa.


Anan wasu suka ƙara jinjina kuɗin na Alhaji Baballe inda Baba keta washe baki shi a dole ga sirikin me kuɗi.


Abdul dake ƙoƙarin shiga mota yaji an riƙo mishi hannu, da sauri ya kalli wanda ya riƙo shin.


Cikin tsananin mamaki yake kallon shi ya kalli inda Fadil yake yaga hankalin shi yana kan abokan ango.


Cikin mamaki ya nuna shi, da sauri yaja hannun shi ya bar wajen dashi, sai da suka isa inda babu mutane sannan ya sake shi, Abdus-samad yace; "waye kai".


Alhaji Mustapha yayi murmushi yace; "Ka tambayi Brr Farida kace waye Mustapha Tuge a wajen ka?, ka sani koda baka tare dani ni ina tare da kai idan kaje ka tambaye ta", daga haka ya bar wajen.


Abdus-samad ya daɗe be motsa daga wajen ba, ya ja ajiyar zuciya sannan ya koma inda motar shi take har lokacin Fadil yana tare da Angon dan haka ya danna mishi horn cikin sauri ya taho dan ya san kaɗan ga aikin shi ya tafi ya barshi.


Koda yazo sai da yaja tsaki sannan yaja motar suka tafi.


Bayan sallar isha'i aka fara cewa amare su fito nan fa idanun amaren ya fara raina fata, Nusram da Nusreen suka rungume juna suna kuka me tsanani.


Sai da suka saka mutane da yawa a wajen kuka, kafin a samu a raba su, an kaisu wajen Ummi inda suka yi musu nasiha sosai da sosai suna zubar da hawaye suka rabu Ummi tana saka musu albarka da yi musu addu'ar tafiya a sa'a.


An kaisu wajen Mama Jummai wanda babu abinda ta dinga faɗa banda habaici, Baba ma dai cewa yayi idan sun zauna kansu idan basu zauna ba to sai dai su nemi wani uban ba dai shi ba.


Nan aka saka kowacce a mota domin tafiya dasu zuwa gidajen su, nan fa mutane suka rabu gida biyu wasu suka tafi raka Nusreen wasu kuma Nusram.


Aunty tace; "Nusram ki shiga da ƙafar dama", haka ta shiga da kafar dama tana me addu'a, duk da gabanta dake faɗuwa.


Gida fa ya haɗu sosai da sosai dan faɗan kyawun shi ɓata lokaci ne, kowa sai yaba kyawun gidan yake yi.


Amma Nusram ita kyawun gida bashi ya dame ta ba, sai ma zazzaɓi daya rufe ta, babu jimawa ƴan kawo amarya suka gama abinda zasu yi sannan suka tafi, suka bar amarya daga ita sai halin ta.




#LIKE
#SHARE
#COMMENTS


*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.


*ƳAR MUTAN ZAZZAU*




♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠



https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/




*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*








*~We are bearer's of so golden pen🖊~*


*~we write assidiously perceive no pain~.*


*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*


*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*












*_daga alƙalamin ✍_*



*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*


*sadaukarwa gare ku*



*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*


*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*


*Heart you so much*



*yau kam kamar na zubar da hawaye saboda comments ɗin ku naji daɗi sosai Allah ya bar ƙauna.


*godiya gare ku ABDUS-SAMAD FANS CLUB, naji dadin comments ɗin ku, ku sani ina son ku sosai akan san ku zan iya shanye maltina gwangwani biyu😁*.


*Innalillahi wa'inna ilaihirraji'uun, haƙiƙa wannan jarabta ce da Allah ya saukar miki Zulaihat Ubangiji Allah yasa ayi aikin cikin nasara ya bata lafiya yasa ya zama kaffara, ya kuma ƙara muku juriya ya bata lada domin lallai cuta bata da daɗi*.


*ƴan uwa muna barar addu'ar ku za'a yiwa yarinyar ƴar uwarku a musulunci Zulaihat Isma'il aiki yanzu haka suna Asibiti a India dan tana fama da heart attack, dan haka muke roƙon ku taya mu da addu'a Allah yasa ayi a sa'a ameen*.


📖📖35-36📖📖




*HAYIN RIGASA, KADUNA*.


Abdul ya shiga get ɗin Estate ɗin sannan ya sami waje yayi parking motar, cikin sauri Fadil ya kalle shi yace; "me hakan ke nufi?" bece komai ba sai ma kifa kanshi da yayi akan steering motar.


Sanin cewa ba zai tanka mishi bane yasa Fadil buɗe motar ya fice, be jima sosai da fita ba Saleema ta ƙaraso wajen motar ta buɗe ta shiga.


A hankali ta dafa shi sannan tace; "kayi haƙuri, komai yayi zafi maganin shi Allah ka kaiwa Allah kukan ka shi zai share maka hawaye".


Ya ɗago yana kallon ta, tayi murmushi sannan tace; "damuwa da tashin hankali bata yiwa wannan kyakkyawar fuskar kyau, a koda yaushe murmushi da dariya sune suke ƙara ƙawata wannan fuskar me girma da kwarjini, shin ko kasan murmushin ka yana sanyaya zuciya nawa ne a gidan nan?, suna da yawa ciki kuwa harda tawa fatan za'a duba tamu zuciyar a dena shiga damuwa".


Wani sanyi yaji yana ratsa zuciyar tashi, haƙiƙa iya magana ma wani abu ne lallai kam a cikin mata Saleema ta ciri tuta.


Ya saki murmushi sannan yace; "kai Aunty na ke ɗin ta dabance", itama tayi murmushi kan ta riƙo hannun shi tace; "kai ɗin wani ɓangare ne na rayuwata na sani cewa zuciya ta tana girmama abinda duk ya shafe ka".


Kan wani lokaci me tsayi sai ga Abdus-samad harda dariya, sai da Saleema ta tabbatar da bata bar Abdul cikin damuwa ko kaɗan ba sannan ta buɗe motar ta fice.


A hankali ya ja motar ya fice daga gidan, Husna taja tsaki tace; "katuwar banza ta ɓige a wajen ɗan cikin ta", sannan ta juya cikin gida cike da kishi.


Dr Saleema kuwa da batama san Husna nayi ba ganin ya bar gidan yasa ta koma cikin gidan su tana me jin daɗin yadda ta sami nasarar kawar wa da masoyin nata damuwar da yake ciki.


Koda ya isa gida duka ƴan uwan nashi suna falo, Fadila da Sumayya suka hau rige-rigen yi mishi sannu da zuwa, ya amsa musu duka yana ɗaga Adnan sama yana cillashi yayin da shi kuma Adnan ɗin ke yin dariya.

Dr Abubakar da Brr Farida da suke saukowa daga sama suna fira da dariya, Dr Abubakar yace; "kai lallai ma maza sauke mini autana kada ka faɗar dashi".

Brr Farida tayi dariya tace; "aikuwa dai Baby ba zai taɓa faɗar da Autan ka ba, sai dai ya ƙara kula dashi", Abdul yayi dariya har gefen kumatun shi ya lotsa yace; "dat's mah first love".

Dr Abubakar yace; "lallai ma wato shigar mishi kika yi kenan?", tace; "a'a fa ni ban shigar mishi ba", nan suka cigaba da firar su gwanin ban sha'awa.

A hankali Abdul ya zame ya shige nashi ɗakin, wayar Sumayya ya kira akan yana neman ta, babu jimawa ta ƙaraso hannun ta ɗauke da ƙaramin bowl me ɗauke da Fruit salad.

"Ya Abdus-samad gani", ta faɗa tana gyara tsayuwar ta dan ta fara gajiya, ya ƙara gyara ƙafar shi dake saman ƙaramin table din dake tsakiyar ɗakin.

Yana cigaba da danna laptop ɗin dake saman cinyar shi yana yi yana cin fruit salad ɗin, kamar ba zai amsa ba dan har ta cire rai da amsawar tashi sai kuma taji yace; "ranar nan firar me kuke yi ke da Yaya Tameer?".

Sumayya ta zaro idanu tace; "wallahi Yaya yace.....yac......yace kada na faɗ........kada na faɗ", kallon da yayi mata yasa tayi saurin haɗiye wani yawu.

"ki bani amsata kawai", ya faɗa yana cigaba da abinda yake yi, tace; "dama cewa yayi na shawo kan Mummy akan......akan.....aka......akan yarinyar da yake so ya au.....aura", ta ƙarasa tana jan numfashi.

Abdus-samad ya ɗago ya mata wani kallo sannan yace; "ke zaki mata maganar aure ko wato kin girma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login