Showing 42001 words to 45000 words out of 121992 words

Chapter 15 - Rayuwar Abdussamad Book Complete Document by Yar Mutan Zazzau .txt

28 Dec 2024

16098

dafa mini", ya ƙarasa yana ƙoƙarin juyawa.


Cikin sauri ta riƙo hannun shi tana faɗin; "ayya ba za'a yi haka ba gaskiya bari na shiga kitchen ɗin na sama maka abinda zaka ci", tana gama faɗar haka ta nufi downstairs da sauri, Abdul yabi bayan ta yana me jinjina irin soyayyar da take yi mishi.


Saleema ta ƙara washe baki ganin Sumayya a zaune, Sumayyar ma cikin farin ciki ta gaishe da yayar tata, nan Saleemar ta barsu ta wuce kitchen domin sama musu abinci.


Sumayya ta matso kusa da ɗan uwan nata sannan ta miƙa mishi wayar tana faɗin; "Ya Abdul kalli motar da Daddy ya siya muku".


Amsa yayi yana kallo, motoci ne guda uku masu kyau sosai, ɗaya baƙa ɗaya ruwan ƙasa ɗaya ja, ya miƙa mata yana faɗin; "na san dai baƙar suka bar mini ko?".


Sumayya cikin alhini tace; "babu yadda Mummy bata ba akan Ya Tameer ya bar maka wannan amma ƙememe yaƙi bar maka wai ita yake amma naji Mummy tace zata maka order ɗin wasu guda biyu", ya jinjina mata kai kawai ba tare da yace komai ba.


Wato ya san da biyu Ya Tameer ya zaɓi baƙar ya bar mishi ja domin ya san yadda ya tsani mota ja, haka kuma kowa a gidan ya san Tameer ɗin ke son mota ja har ma su kan tsokane shi da kalar mata ce, amma shine ya zaɓi baƙa kawai dan ganin ya ɓata mishi rai.


"Ya amma gobe ba da wuri zamu tafi ba ko?", Sumayya ta katse mishi tunanin da ya tafi, ya ɗaga kai kawai, sun cigaba da fira inda yawanci kawai ɗaga mata kai Abdul ɗin yake yi domin tunanin shi baya kanta yana kan wannan yarinyar ta jiya.


Saleema ta fito hannun ta ɗauke da tray, da sauri Sumayya ta tashi ta amso ta, Sumayya tace; "sannu Aunty Saleema da aiki ai da kin saka Hanne".


Saleema tace; "kada ki damu ƴar ƙanwata kun wuce kuci abincin Hanne a waje na bayan ina gidan", ta ƙarasa tana kallon Abdul ɗin wanda shima idanun shi yana kanta domin ya san akan shi take maganar ba wai dan Sumayya ba.


Yayi murmushi sannan yace; "aikuwa mun gode da wannan karramawar, kuma munji daɗi sosai, abinda zamu ce kuma shine adawo lafiya", ta saki murmushi tana ɗaga musu hannu ta fice.


Tare suka ci abincin kamar suna gida suna yi suna fira wacce bata da hayaniya sosai, a haka Mummyn ta fito ta tarar dasu nan suka gaishe ta, da yake itama da shirin office ta fito hakan yasa ta wuce su kawai.


Ya miƙe tsaye itama Sumayya haka ya kalle ta yace; "ni zan fita kije wajen Nihal na san tana nan", daga haka ya juya ya fice.


Motar Fadil yaje ya ɗauka sannan ya fice daga Estate ɗin gaba ɗaya, wajen Akram yake so yaje wanda zasu haɗu a jiya amma saboda Nusram basu samu damar haɗuwa ba.


Har ya gifta ya hango kamar ita a tsaye a bakin titi, sai fama duba waya take wanda alamu ya nuna sauri take kuma bata samu mota ba, a hankali ya fara dawowa da baya da baya har yazo kusa da inda take.


Yana sauke glass ɗin suka haɗa idanu, Nusreen ta ja ƙaramin tsaki tana me kauda kai, Abdul kuwa abin ya bashi mamaki, a jiya tsoron shi yake gani a idanun ta amma a yau kuma yaga masifa da tsiwa kawai ke cin ta.


Ya jima a haka ita bata waigo ba shi kuma be wuce ba, Abdul ya kuma juyawa ya kalle ta, Atamfa ta saka me ruwan ganye da ratsin ja da fari haka Hijab ɗin jikin ta fari ne, tayi kyau sosai domin kuwa fuskar nan ta ɗauki kwalliya.


Abdul ya taɓe baki domin ganin shi jiya tafi kyau don jiya babu kwalliya a fuskar ta, ya duba agogon hannun shi sannan ya buɗe motar ya fito.


Gaban ta ya je ya tsaya, Nusreen kuwa kamar bata san dashi a wajen ba duk da yadda gaban ta ke faɗuwa dan yana yi mata kwarjini sosai.


Abdul kuwa cikin bada umarni yace; "shiga muje", wani shegen kallo Nusreen ta wulla mishi kan tace; "sannu Malam Abdullahi🙊".


Abdul ya kafe ta da ido yayin da Nusreen ɗin taƙi yarda su haɗa idanu, hannu ya kai zai riƙo nata da sauri taja baya sannan tace; "wallahi ka sake ka ɗora hannun ka saman jiki na sai nayi maka ihun kwarto", sosai hakan ya bashi mamaki kan yace wani abu motar Shureim ta tsaya kusa dasu.


Shureim ya fito cikin sauri yace; "afuwan Sarauniyar mata wallahi na ɗan tsaya amsar saƙo ne", Nusreen ta cilla mishi harara sannan tace; "ka kyauta daka shanye ni a nan har wasu marasa ilimi da hankali suke tunanin ko ni ɗin ina da araha har haka", ta ƙarasa tana kallon inda Abdul ke tsaye wanda tun lokacin da Shureim ya ambaci Sarautar mata yaji wani abu ya daki zuciyar shi.


Shureim ya kai kallon shi inda Abdul yake, cikin sauri ya ƙarasa yana miƙa mishi hannu; "barka da hutawa yallaɓai", Abdul yayi murmushi yace; "Shureim dama kana nan shine ko ziyara babu".


Shureim ya shafa kai yace; "kayi haƙuri yallaɓai wallahi abubuwa ne sun yi yawa sannan ban jima da dawowa najeriyar ba don ina Egypt karatu".


"ina Ammie? Fatan tana lafiya", Abdul ɗin ya tambaya, Shureim yace; "Ammie tana Syria wallahi ciwon ƙafa ne ya matsa mata".


"ayya amma ya ƙafar yanzu", Abdul ɗin ya tambaya, Shureim yace; "eh to wai likitan da ake saka ran zaiyi mata aiki ne sai nan da kwana uku zai dawo Dr John Burlin".


"John Burlin ai na san shi ka bari zan kira shi sai a san yadda za'a yi aikin", nan fa Shureim ya fara godiya.


Nusreen ta baje hanci da baki tana kallon su bata yi tunanin sun san juna ba, ganin abin bana ƙare bane yasa tace; "wai Habibi a waje zaka barni ne ko kuwa zaka wuce muje?", da sauri Shureim yace; "Afuwan Sahiba shiga muje", ya faɗa yana me buɗe mata ƙofa sai da ta harari Abdul ta ƙasan ido sannan ta shige.


Shureim ya kalli Abdul yace; "yallaɓai mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi", babu abinda Abdul ya iya samun dama banda ɗaga mishi kai da yayi, yana kallo Shureim yaja motar ya tafi.


Abdul ya buɗe motar shi ya shiga sannan ya kifa kanshi saman sitiyarin motar, babu abinda ke mishi yawo a idanu banda meye haɗin Shureim da wannan yarinyar?.


"ai amsar a fili take saurayinta ne", zuciyar shi ta bashi amsa, da sauri ya furta; "Impossible!", sai kuma wata zuciyar tace; ina ruwan ka ne?", ya ɗaga kafaɗa alamun babu haka yaja motar shi ya bar wajen.


Nusreen bayan sunyi nisa ta kalli Shureim tace; "meye haɗin ka da wancan?", Shureim yace; "lokacin da mahaifina yake da rai a ƙarƙashin mahaifin shi yake aiki, ke kuma meye haɗin ki dashi", ya dawo mata da tambaya.


Nusreen ta taɓe fuska tace; "babu komai ni ban ma taɓa ganin shi ba sai yau", Shureim yayi murmushi kawai domin sanin halin Nusreen ɗin.


Abdul kuwa koda ya ƙarasa wajen abokin shi Akram ɗin kasa zama yayi dan haka ya miƙe yana faɗin; "ina ji gida zan koma kawai".


Akram ɗin ya miƙe yana faɗin; "haba Abdul yaushe kazo da har zaka koma?, gashi ko maganar da zamu yi ma bamu gama ba", Abdul ya ɗan ja tsaki sannan yace; "kada ka damu idan na dawo next time zamu yi maganar".


Dole haka Akram din ya rako shi har wajen masana'antar, tuƙi kawai yake yi amma hankalin shi naga Shureim da kuma wannan yarinyar ya rasa me yasa abin ya tsaya mishi a rai.


Yana zuwa dai dai layin kamar ance ya kalli hanyar ya hango ta sanye da doguwar riga me ruwan ƙasa da kuma hijab kalar ruwan madara.


Cike da mamaki yake binta da kallo to ko dai aljana ce amma abin da mamaki a yadda yaga tafiyar su ya tabbatar inda zasu je ma da wuya idan sun kai balle har su dawo.


A hankali ya fara bin bayan ta har zuwa ƙofar gidan nasu wato lungun da zaka iya hango gidan su, Nusram da bata san ana bin ta ba ta shige gidan hannun ta riƙe da ledar data siyo kayan lalle wanda ta san zata buƙata wajen yiwa Sahura.




#LIKE
#SHARE
#COMMENT


*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.


*ƳAR MUTAN ZAZZAU*





♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠



https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/




*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*








*~We are bearer's of so golden pen🖊~*


*~we write assidiously perceive no pain~.*


*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*


*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*












*_daga alƙalamin ✍_*



*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*


*sadaukarwa gare ku*



*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*


*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*


*Heart you so much*






📖📖25-26📖📖


Abdul na ganin ta shige gida ya juya da kan motar shi ya fita a layin, lallai akwai wani abu a tattare da yarinyar amma ko meye zai yi ƙoƙari ya gano shi.

Nusram kuwa tana shiga gidan ta tarar Sahurar na jiran ta, dan haka ruwan dake saman murhun su ta juyo, yayin da Nusram ta shiga ɗaki ta ɗauko haɗin man da take wanke kai.

Sai da ta fara shafa mata haɗin Kanumfari da Kaltufah, ta saka leda ta rufe sannan ta ɗauko abin lallen ta fara kwaɓawa, sai da kan yayi tsayin minti goma sha biyar sannan ta buɗe kan, ta ƙara tajewa kafin suka je bakin famfo ta wanke mata.

Kan yayi kyau sosai dan babu laifi Sahurar ta ɗan kwaso dangin mahaifin nasu, Ameera ta Kalli Aziza ganin yadda kan yayi kyau yake kuma sheƙi.

Sai da ta tsane kan gaba ɗaya sannan ta ɗauko haɗin mayukan musulunci, Man zaitun, man hulba, man habbatus-saudaa, man maciji da kuma ɗigon man ayu, ta ware mata kan tana shafawa tana tajewa haka tayi har kan ya saki sannan ta naɗe mata gashin inda take so ko'ina man ya shiga, idan kaga gashin Sahura a lokacin zaka ɗauka taje wajen masu wanke kai ne.

Ita kanta sai da ta kasa yin shiru tace; "Nusram Allah kuwa da zaki buɗe wajen gyaran kai da jiki ko ba ƙaramin ciniki zaki yi ba", Nusram tayi murmushi kawai ba tare da tace komai ba.

Jan lalle ta fara tsantsara mata, sannan ta ɗora mata baƙi a sama, kan wani lokaci ta gama zana mata lallen, sannan ta ɗauko kibiya ta hau yi mata kitson.

Mama Jummai dai sunyi sa'a dan ko kallon inda suke bata yi ba, aikin gaban ta take yi wato ƙoƙarin ɗora abincin siyarwar ta kenan take yi domin rana ta fara yi.

Ƙananan kitso Nusram ɗin ta yarfawa Sahurar wanda yayi kyau sosai, kan wani lokaci sun gama domin kuwa Nusram ɗin tana da sauri akan ayyukan nata.

Tashi tayi taje tayi Alwala sannan ta shige ɗaki inda ta bar Sahura a zaune domin barin ƙunshin nata ya ƙara ja, koda Nusram ta idar da sallah sannan ta ɗebi abinci.

Tana ci tana yiwa Kubra wasa wacce itama kwanon abincin ke gaban ta, duk ta watsa shinkafar a ƙasa.

Ummi ta kalli Nusram sannan tace; "ina so ki faɗa mini gaskiya Nusram shin kina son wannan auren da mahaifinku zai muku?".

Nusram tayi murmushi tace; "Ummi me kika gani?, nifa wannan be dame ni ba kuma ina farin ciki ko babu komai zan bar gidan nan sannan ƴar uwa ta ma Allah ya cika mata burin ta wato zamu yi aure lokaci ɗaya".

Ummi ta kuma cewa; "amma ai ya kamata ki tabbatar da cewa kina son shi kafin auren bana so kiyi abinda zaki yi nadama sannan bana so ki fuskanci matsala a gidan auren ki".

"Insha Allah Ummi ba zan fuskanci wannan matsalar ba, zan yi farin ciki kamar yadda kike mini burin yi", abinda Nusram ɗin ta bawa Ummi amsa kenan.

Ummi tace; "shikenan tunda haka kika ce Allah ya baku zaman lafiya, amma ki sani shi aure ba abin wasa bane idan har kun haɗu kinji bakya son shi to ki sanar dani ni kuma zan yi iya ƙoƙari na wajen ganin ba'a ɗaura wannan auren ba".

Nusram ta riƙo hannun Ummi tace; "kada ki damu kanki Ummi, Insha Allahu zan so shi kamar yadda kowacce mata ke son mijin ta", ba don Ummi ta yarda da abinda Nusram ta faɗa ba ta ƙyale ta.

Sai wajen biyu sannan Nusram ɗin taja ruwa a rijiya inda ita kuma Sahura ta miƙe taje wajen ta, Nusram da kanta ta wankewa Sahurar lallen sannan ta shafa mata muhallabiyya aikuwa yayi kyau sai shinning yake yi.

Sahura sai washe baki take yi ganin yadda tayi kyau sosai ga wani ƙamshi da tafin hannun nata yake yi, domin dai kowa ya san ƙamshin muhallabiyya akwai daɗi sosai.

Koda ta shiga ɗakin su da murnar ta ta nunawa Mama Jummai, Mama Jummai tace; "na fani yayi kyau sai dai ki cirewa ranki komawa gidan Idris".

Sahura ta turo baki gaba kafin tace; "amma ai Baba ya yarda ko?", Mama Jummai taja tsaki tace; "ai ya yarda ne saboda kada ya dinga cefane dake, yau Alhajin da zai auri Nusram zai zo don haka ina so ki san yadda zaki yi ki ɗauke hankalin shi daga kanta".

Sahura ta kalli Mama Jumman sheƙeƙe sannan tace; "Mama ke kina ganin muna da kyawun da zan iya karawa da Nusram ɗin?, to wallahi bana dashi sannan kuma ba zan taɓa aikata mata haka ba kuma ni Mama miji na ya maida ni dan haka ba zan yi aure kan aure ba, gidan miji na zan koma yau ko ki so ko kada kiso".

Mama Jummai cikin hargagi tace; "Sahura ni kike faɗawa haka, to wallahi kinyi kaɗan kuma baki isaba zanga ta yadda zaki fita kibi mijin naki", ba tare da damuwa ba Sahurar tace; "za kuwa ki gani".

Mama Jummai cikin ranta tace; "ina dole na sake dabara idan ba haka ba wanki hula zai kaini dare", tana gama faɗar haka ta ɗauki hijab ta fice.

Nusram tana ƙoƙarin ɗora girki Nusreen tayi sallama ta shigo hannun ta ɗauke da kaya, Nusram ɗin da kanta ta miƙe ta taro ƴar uwar tata.

Ɗaki suka shiga dashi, Nusram cikin farin ciki tace; "wa'innan fa daga ina?", Nusreen tace; "wallahi Auntyn Tudu tace na taho dashi zata zo sati me zuwa kin san bikin Ya Sulaiman wai sati uku suka saka".


Nusram ta ƙara washe baki tana faɗin; "ah lallai kace Yaya Sulaiman ɗin ango yake, ya akayi to?", Nusreen ta tabe baki sannan tace; "ashe ma wai ya san Shureim ɗin baki ga yadda suka dinga fira ba, amma duk da haka yace zai ƙara bincike akan shi, wai daman Maman Shureim ɗin a wajen Ya Sulaiman ɗin ma take siyayya".


Nusram tace; "shikenan ma ashe abin yazo da sauƙi", Nusreen ta cire hijab ɗin jikin ta sannan tace; "na bashi labarin naki angon baki ga yadda ya dinga faɗa ba, yace ma zai zo koda zuwa sati me zuwa ne ko kuma gobe".


Nusram ta harari Nusreen ɗin tace; "to waye yace ki ɗin ki faɗa mishi?", Nusreen tayi dariya sannan ta juya wajen Ummi tace; "gashi nan inji Aunty tace zuwa gobe ko kuma sati me zuwa zata zo wai sai kuyi magana".


Ummi tace; "Allah ya kaimu", suka amsa da ameen, Nusreen ta kwanta yayin da Nusram ta koma wajen girkin ta don so take taci ƙarfin girkin kafin lokacin da zasu tafi makarantar.


Ƙarfe huɗu sun idar da sallah inda suka saka atamfa duka a jikin su riga da zani sannan suka ɗora hijab wanda ya kasance na makaranta sannan suka yiwa Ummi sallama suka tafi.


Nusreen ta kalli ƴar uwar tata sannan tace; "Ramluv kin san me?, yanzu tunani na shine anya kuwa Baba zai yi mana kayan ɗaki masu kyau?".


Nusram tace; "ke kuma abinda ya dame ki kenan kai Rim Allah ya shirye ki, abinda nake so ki gane shine duk abinda Allah ya hore mishi wannan zai yi mana dan haka kada ki damu ga kuma kuɗin da muka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login