Showing 54001 words to 57000 words out of 121992 words
Chapter 19 - Rayuwar Abdussamad Book Complete Document by Yar Mutan Zazzau .txt
Ta goge hawayenta tana mata addu'ar samun sauƙi, can ta ɗago kanta; "ina Sumayya?", kanta rufe baki Fadila ta bude ƙofa ta shigo bayan ta kuma Sumayya ce. Itama Sumayyar wajen ƴar uwarta ta nufa suka rungume juna suna kuka, Surayya ta sake ta sannan ta janyo Fadila itama ta rungume".
Daddy kam ikon Allah yake kallo, babu wanda ya kalli gadon da ɗan nashi yake kwance lallai ya tabbatar da cewa har yanzu Brr Farida bata shirya kan yaran nata ba.
Daddyn Fadila yayi sallama ya shigo tare da mahaifiyar su, cikin sauri Fadilar tayi wajen iyayen nata ana jajantawa juna, Fadil da Salima sune suka shigo daga ƙarshe.
Wajen gadon Abdus-samad ɗin suka nufa su direct, cikin damuwa Fadil yace; "Daddy har yanzu be farka bane?", Daddy ya dafa kanshi yace; "zai farka insha Allahu nan bada jimawa ba kuyi haƙuri tukunna.
Nan suka koma suka zauna jugum domin kuwa daga Brr Faridar har Abdul ɗin babu wanda ya farka har zuwa lokacin kowa kuma a ciki fatan shi shine su tashi lafiya lau.
Salima na riƙe da hannun shi tana zubar da hawaye domin kuwa hankalin ta ya kasa kwanciya, bata so ta rasa abinda take so.
Fadila ta kalle ta sannan ta taɓe baki, ita fa ba wannan bane ya dameta, kuma ta san suna son abinda ba zasu taɓa samu bane daga Husnar har Salimar.
Fadila ta dubi Fadil tace; "ina su Hajja banga sun zo ba?", Fadil ya taɓe baki yace; "kema kin san halin ƙasaitar matar nan waye zai iya zaman jiran ta, Malama tana so ta biyo mu amma matar nan ta hana wai sai dai ta jira ta su taho tare, baki ga yadda hankalin Malama ya tashi ba ina jin har kuka sai da tayi amma wai Hajja taƙi bari a taho da ita......". Daddyn shi ya kai mishi duka a ƙeya yace; "Fadil baka da hankali ko uwar tamu kake faɗawa haka muna wajen", be kuma cewa komai ba sai shafa wajen da yayi yana turo baki.
*********** ************
*UNGUWAR RIMI, KADUNA*
Shureim ya zauna kusa da mahaifiyar shi wacce ke zaune cikin kayayyaki, tunda taji labarin bikin nan hankalin ta ya koma kai.
Tace; "ya akayi fatan an gama komai, ka san bana so azo a sami matsala ga Sharifa har yanzu bata iso ba", Shureim yace; "me kuma Aunty Sharifar zata yi?", Mama tayi mishi daƙuwa tace; "zaku je a ƙaro abubuwan da babu ne, Usman ma munyi waya akan sarƙoƙi da zai ƙaro ya dai ce yana tunanin a satin nan kayan zasu iso".
Shureim ya kwantar da kanshi jikin mahaifiyar tashi yace; "Mama lallai kina ji dani", ta shafa kanshi tace; "wa nake dashi banda kai, Shureim kai nake gani na tuna da mahaifinka, dole na fito na nuna bajinta akan aurenka, ɗana guda ɗaya tilo. Sharifa tayi dariya tana karasa shigowa gidan tace; "Aunty kenan, kullum firar ku kenan".
Mama tace; "to idan bashi ba ɗin da waye zanyi", Sharifa ta zauna kusa ɗa ƴar uwar tata sannan ta tura mata ledar gaban ta tace; "gashi mun riga da mun siyo da naga mun biyo ta wajen Mall ɗin tare da Baban Naufal shine nace mu ƙarasa kawai mu siyo".
Mama ta fara ɓuɗewa tana faɗin; "yauwa gaskiya na gode sun kuma yi kyau sosai", ta ƙarasa tana ɗaga ɗogunayen rigunan".
Aunty Sharifa tace; "nima sun birge ni shi yasa na ɗauko su", Shureim ya miƙe yana faɗin; "bari na tafi wajen aiki".
Mama tace; "yanzu ƴar tawa sai bayan biki zan ganta kenan?", Shureim yace; "Mama kinfa santa ina wacce ranar da zan kai ki Airport.....".
Kafin ya ƙarasa ta miƙe tana washe baki tace; "madallah kamar ka san yarinyar tana cikin raina, saboda hankalin ta nayi maka sha'awar ta gaskiya naji daɗi na san zan ji daɗin zama da ita ba kamar ƴar uwar ta ba, yarinya sai tsiwa". Gaban Shureim ya faɗi kada dai Mama tace bata son Nusreen.
Aunty Sharifa tace; "wai wacece kuke magana akai", nan Mama ta shiga bata labarin ƴan biyun da suka haɗu a hanya da yadda ɗaya tayi musu rashin kunya ɗayar kuma ta basu haƙuri. Sharifa ta washe baki tana faɗin; "lallai kam tana da hankali sosai kuma ta cancanci ta shigo cikin wannan familyn".
Shi dai Shureim a jiki a sanyaye ya bar falon domin kuwa abun yana so ya caɓe masa dole ya san yadda zai yi, ya kira Naufal a waya nan ya shiga faɗa mishi abinda ke faruwa.
Naufal yace; "yanzu meye abin yi tunda dai biki ya matso ni ina ganin kawai ka faɗa mata gaskiya, dan koda baka faɗa mata ba wata rana zata gane idan kayi la'akari da yadda Nusreen take da tsiwa ba iya ɓoyewa zata yi ba".
Shureim yace; "nima abinda nake tsoro kenan kada fa garin son zuciyana na nemo abinda zai zo ya ɓatawa Mama ya kuma janyo matsala tsakani na da ita, banda kowa a yanzu sai ita".
Naufal yace; "hakane amma duk da haka baka sani ba ko meye dalilin da abubuwan suke faruwa a haka ba ta yiwu alkhairi ne auren ku".
Shureim yace; "hakane", Naufal yace; "ni ina ganin ka faɗa mata kawai", Shureim yace; "shikenan zan gwada ɗin", daga nan kuma Naufal ya koma tsokanar Shureim ɗin har sai da Naufal ɗin yaga Shureim ya saki jikin shi sannan suka rabu a wayar.
******** ***********
*HAYIN RIGASA, KADUNA*
Ummi ta zauna kusa da Nusram wacce ta zuba uban tagumi kamar anyi mata mutuwa, ta dafa ta tace; "Nusram na faɗa miki tƴmun farko idan har bakya son wannan auren to ki faɗa mini ni kuma zan saka a hana".
Nusram ta ɗago idanun ta wanda yake cike da hawaye tace; "Ummi kada ki damu da wannan insha Allahu zan yiwa Baba biyayya koda kuwa me zai faru".
Ummi tace; "ban tambaye ki biyayya ga mahaifinki ba ko akasin hakan, tambayar da nayi miki shine kina son shi ko bakya son shi?".
Nusram tayi murmushi me ciwo tana saukar da kai ƙasa, sanin cewa ba zata yi magana ba yasa Ummi miƙewa tana faɗin; "ke kika sani tunda ba zaki iya buɗe baki kiyi magana ba".
Nusreen dake ƙoƙarin shigowa hannun ta riƙe da babbar leda don ta dawo ne daga Tudun Nufawa tace; "Ummi meya faru".
Ummi tace; "meye kuwa be faru ba ni da ƴar uwar ki ne gata can taƙi ta faɗi abinda ke ranta game da auren nan".
"ni wallahi abin na damuna Ummi, Nusram duk tabi ta lalace ta ƙare, gashi wajen gyaran jikin ma ta dena zuwa kana yi mata magana sai kuka Ummi ina tsoron kada damuwar da take ciki ya kaita ga halaka", Nusreen ta ƙarasa cikin damuwa.
Ummi taja tsaki tace; "to ba ita taso ba, Nusreen ta fito ta cewa Baban ku bata son auren ta kasa sai dai ta zauna a cutar da ita".
Nusreen tace; "bari naje wajen ta naji meke faruwa", tana faɗin hakan ta wuce Ummi zuwa cikin ɗakin.
A zaune kamar yadda Ummi ta barta haka ta zo ta same ta, Nusreen tace; "Nusram ki yiwa Allah ki faɗa mana menene damuwar ki".
"auren ne Nusreen bana so, kuma ba zan iya faɗawa Baba ba", wannan shine abinda zuciyar ta ta faɗa amma sai tace; "Nusreen ki taya ni da Addua kawai".
Koda Nusreen ta takura mata kuka ta sakar mata kawai, cike da tausayi Nusreen ɗin ta biye mata suka dinga rera kukan tare sai da Ummi ta shigo tayi musu tatas sannan suka yi shiru.
********* **********
*UNGUWAR SARKI, KADUNA*.
Tameer ya kalli agogo sannan ya kalli Daddy yace; "Daddy har yanzu shiru basu farka ba kome ke faruwa kuwa".
Daddy shima cikin damuwa yace; "ku cigaba da addu'a zasu farka ne", haka suka yarda da shawarar mahaifin nasu.
tana tsugunne tana kuka cikin tashin hankali, taji an dafa kafaɗarta, cikin sauri ta waigo fuskar da ba zata taɓa mantawa bace take kallon ta.
Itama ta tsaya tana kallon ta, waccen matar tace; "Bestyy kin yi sanyi dole ki ƙara gudun tafiyar ki idan ba haka ba Mustafa yana daf da cin miki".
Cikin yanayi na rashin madogara da kuma karyewar zuciya Brr Farida tace; " taya zan aikata hakan bayan ban san inda Abdul yake ba, ji nake kamar ya tafi ya bar ni, Abdus-samad shine ƙarfi na yanzu kuma babu shi".
Matar tayi murmushi tace; "kada ki damu ɗanki na nan be tafi ba, zo muje ki ganshi", ta kama hannun Brr Farida zuwa wani kyakykyawa Lambu ta ɗaga hannu ta nuna mata inda Abdus-samad yake zaune fuskar shi ɗauke da murmushi yana kallon ta.
Cikin jin daɗi ta nufi inda yake sai dai kafin ta kai wani irin jibgegen Shaho da jajayen kaya yazo ya sungume Abdul ɗin yayi sama dashi, nan fa Brr Farida ta fara Kuka tana ƙwalawa Abdul ɗin kira.
Daddy ya riƙo ta yana tofa mata addu'a, ita kuwa da bata san yanayi ba kukan ta kawai take sha tana kiran sunan Abdul ɗin.
A hankali kuma idanun ta ya fara buɗewa har ta buɗe shi tas, shiru tayi tana kallon su ɗai-ɗai sai taji ranta yayi sanyi sanin cewa mafarki take yi.
Tayi murmushi tace: "kaga ashe mafarki ma nake yi, ja ɗauka gaske ne ina Abdul ɗin?", Dr Abubakar yace; "calm down My Brr ɗanki yana lafiya", jin hakan ya tuno mata da mafarkin ta.
Sai tayi murmushi tace; "ina yake My Dr ina son ganin shi, na san duk inda nake zai kasance a wajen?", Sumayya ta ƙaraso kusa da ita tace; "Mummy Abdul barci yake yi yanzu ko kina so a tashe shi ne?".
Ta girgiza kai da sauri tana lumshe idanu sai dai cikin sauri ta buɗe su sannan ta sauke kan Fadila wacce kanta ke manne da plaster, a hankali kuma komai ya fara dawo mata cikin kai.
Cikin sauri Brr Farida ta fara yunƙurin miƙewa amma Dr Abubakar ya hanata, gaba ɗaya ta ruɗe tana faɗin; "shikenan sun kashe mishi shi".
"yanzu meya faru dashi ya mutu ko?, na dena ganin shi?", magan-ganu dai kala-kala, ganin bata hayyacin ta yasa Dr Abubakar riƙo ta jikin shi ya rungume ta saki kuka me ƙarfi.
Kowa yana tausaya mata, Abban Fadil sai da jikin shi yayi sanyi sanin irin ƙaunar da take yiwa ɗan nata, ya kalli gadon da Abdul ɗin ke kwance kamar gawa.
Malama da Saleema kuwa duk idanu ya kumbura tsabar kuka, Hajja ce ma dai ta dai yi hawayen amma ba kamar su ba dan itama yadda tazo ta same su abin ya bata mamaki.
#LIKE
#SHARE
#COMMENT
*babyn abdul maman meenal elham da farouk*
*ƳAR MUTAN ZAZZAU*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*_daga alƙalamin ✍_*
*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*
*sadaukarwa gare ku*
*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*
*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*
*Heart you so much*
*Ga masu cewa ina jan littafin ne dan na samu kuɗi, Wallahi ba haka bane domin kuwa da ina son siyar da littafi da tuni nayi sai dai ina so ku sani kuɗin ku bashi ne a gaba na, duk wanda ya ɗauki wani abu ya bani ya bani dan raɗin kanshi ne ba wai dan na tambaye shi ba, hasalima kyautatawa ce tsakani na dasu, rubutun novel buri na ne dan haka bana fatan ko gaba nayi novel ɗin siyarwa, na gode sosai to ai hikenan😉*.
*Godiya ta musamman ga Zuciya ta, da kuma Matar so ina miki son so sannan ina jin daɗin sharhin ki sosai Shabihaty fans club kuna ƙarƙashin zuciyar One Love*
*Sannan ga masu son shiga whatsapp group na Rayuwar Abdus-samad kuyi searching Aishatu Babayo sai ku tura mata da number ɗin ku ta pc zata saka ku a ciki amma dan Allah iya mata kawai banda maza, Na gode sosai*
📖📖31-32📖📖
*UNGUWAR SARKI,KADUNA*
Cikin sauri ya buɗe idanun shi yana faɗin; "innalillahi wa'inna ilaihir-raji'uun", ƙoƙarin miƙewa yake yi Brr Farida ta riƙo shi cikin sauri.
ya rungumeta yana sakin ajiyar zuciya, Brr Farida kuwa harda ƙara ƙaƙumeshi hawaye yana saukowa daga idanun ta.
Tameer ya shigo tare da likitan da yaje kira, sai a lokacin suka saki juna allurar barci ya kuma yi mishi babu ɓata lokaci barcin ya kuma kwashe shi.
Hajja tace; "tunda yayi barci bari muzo mu tafi Allah ya ƙara sauƙi, Mus'ab(Abban Fadil) ka tashi muje ka sauke mu a gida".
Haka ba dan sun so ba suka miƙe dukkan su, bayan sun tafi Brr Farida ta kalli Surayya tace; "kuma ku wuce gida, na san zuwa anjima zasu sallame mu", haka suma suka tafi cikin jimami Sameer ya tafi kai su.
Ya rage saura Tameer da Brr Farida da Dr Abubakar, hakan yasa wajen yayi shiru, ita dai Brr Farida tana riƙe da hannun Abdul ƙam-ƙam kamar za'a ƙwace mata shi.
Lokaci zuwa lokaci take sauke ajiyar zuciya, kallon shi take cikin tausayawa tabbas da saka hannun wani a wannan lamarin to waye kenan?.
Amsar da ta kasa samu kenan, bata da tabbacin wanda take zargi domin kuwa bata da wata hujja.
Kamar ance ta ɗaga ido ta kalli saitin window idanun ta ya hasko mata dattijon dake tsaye jikin window.
Ƙara zaro idanu tayi gabanta yana dukan uku-uku, shima kuwa ganin ta hango shi yasa yayi saurin barin wajen.
Brr Farida ta miƙe a kiɗime, Dr Abubakar da be san meke faruwa ba yace; "My Brr ina zuwa kuma?", ta bashi amsa yayin da take ficewa daga ɗakin; "ina zuwa".
Sauri take yi kamar ƙafarta zata tsinke ta fice ta zagaya bayan window ɗin, sai dai kash baya wajen nan ta hau jefa idanu tana neman ina zata ganshi.
Har bakin get taje neman shi sai dai Allah be bata sa'ar ganin wanda taje nema ba haka ta gama zagayen asibitin ta dawo.
Tana daf da shiga ɗakin idanun ta ya sauka a kanshi, da sauri ta ƙarasa kusa dashi, shima kuma ita yake kallo fuska gwanin tausayi.
*MUSTAPHA ABUBAKAR TUGE* sunan data ambata kenan a bayan ta iso kusa dashi, ya kalli mutanen wajen sannan ya maida idanun shi kanta itama ta kalle shi ta ɗaga gira ɗaya.
"ko nace Mustapha Sulaiman harɗo, wanne yafi dai-dai? Yadda kake da fuska biyu hakama sunan ka yake".
Alhaji Mustapha ya kalli kanshi ya ƙara kallon jama'ar wajen yana da tabbacin dan basu gane ko waye shi bane da yanzu sun cika wajen dan kowa ya san shi a faɗin garin kaduna kai kaf Nigeria yana ɗaya daga cikin masu kuɗi na farko-farko, gashi kuma da taimakon jama'a sosai wannan ya ƙara mishi farin jini.
Cikin kwantar da murya yace; "Brr dan Allah kizo muje garden ina so muyi magana dake".
Brr Farida tace; "babu magana tsakani na da kai domin babu abinda ya haɗa ni da kai", ta ƙarasa cikin ɓacin rai.
Ya sauke ajiyar zuciya sannan yace; "naji ance Murad yayi hatsari ne shine nazo duba shi, naga jikin nashi ma da sauƙi hankali na ya tashi sosai ina ƙasar Mali labarin yazo mini", ya ƙarasa fuskar shi ɗauke da damuwa.
Brr Farida ta taɓe baki sannan tace; "kamar da gaske yadda ka maida fuskarka sai kace na Allah, to bari kaji kana ɗaya daga cikin prime suspect ɗina kuma zan yi bincike matuƙar da saka hannun ka akan abinda ya sami Abdul bar ganin kana da kuɗi zan tarwatsa farin cikin ka ne".
"haba Farida ya kike magana haka, kada ki manta nine mahaifin Murad ba zan taɓa iya cutar dashi ba, waccen ma baki fahimta bane kuma Fiddausi ma..........".
"dakata ya ishe ni haka! Ka tabbatar ka bar wajen nan domin dai ka sani koda wasa ba zan taɓa bari kaje kusa da ɗana ba ko?, Sannan nayi maka gargaɗi ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba akan ka fita harkata nida ɗana kaƙi ji ko? To wallahi zan ɗauki babban mataki akan ka", tana gama faɗar haka ta shige ta barshi a tsaye.
Alhaji Mustapha ya tsaya cike da takaici gashi yana so ya ga lafiyar ɗan shi amma babu dama, ya kalli kayan dake jikin shi riga daban wando daban sai hula irin taɓani kaji hadisin nan, wannan duk yayi ne dan yazo yaga lafiyar yaron