Showing 114001 words to 117000 words out of 121992 words
Chapter 39 - Rayuwar Abdussamad Book Complete Document by Yar Mutan Zazzau .txt
yace; "na san nayi laifi dan Allah ki yafe mini, idan baki yafe mini ba ban san inda zan saka raina ba", zata ture shi Dr Abubakar ya girgiza mata kai.
Cikin dauriya tace; "naji zan yafe maka amma da sharaɗin ba zaka kuma aikata wannan kuskuren ba, matuƙar ka kuma gigin zuwa inda Alhaji Mustapha yake to sai dai ka nemi wata uwar bani ba".
Ya ɗan yi jim yana kallon ta, a matuƙar tsorace yace; "First Love naji na amince amma dan Allah kada kiyi mini baki", ta ɗan yi murmushi tace; "ba zan yi maka baki ba Abdul ko dan soyayyar da nake yi maka, amma matuƙar ka cigaba da bibiyar Alhaji Mustapha tofa zamu raba hanya dan mutum ne dana tsane shi na tsani wanda ke son shi".
"to ki faɗa mini abinda ya shiga tsakanin ku har kike mishi wannan ƙiyayyar", kamar ya watsa mata wuta haka ta miƙe, idanun ta ya kaɗa yayi jajir, da hannu ta nuna shi tace; "ba sai kaji ba, na sha gargaɗin ka da cewa ka fita tsakani na da Alhaji Mustapha ba abinda ya shafe ka bane amma kana neman ka zama mara jin magana ko".
Ganin abin zai yi tsayi ne yasa Dr Abubakar jan hannun Abdul zuwa waje, "Abdul ka rufawa kanka asiri ka dena tambayar mahaifiyar ku menene tsakanin ta da Alhaji Mustapha idan ba haka ba zaka nemowa kanka bacin rai ne kawai".
Kan shi a ƙasa yace; "in Allah ya yarda Daddy ba zan kuma ba dan na lura abinda ke tsakanin su be shafe ni ba", Dr Abubakar ya jinjina mishi kai.
Abdus-samad cikin sanyin jiki ya juya ya bar wajen, Dr Abubakar ya bishi da kallo cikin tausayawa, rayuwar yaron tana cikin hatsari me girma gashi shi kanshi yaron be san menene takamaimai ainihin abinda ya janyo hakan ba, tun ba yanzu ba yake fama da matar tashi akan ta fito ta faɗawa yaron gaskiya amma hakan ya gagara.
kuka ya same ta tana ta faman yi, Dr Abubakar ya zauna kusa da ita ya riƙo hannun ta kana yace; "Brr Farida ya kamata ace zuwa yanzu kin zama jarumar da zaki dena zubar da hawayen ki akan Alhaji Mustapha, ki dinga daurewa idan ba haka ba zaki saka shakku a zuciyar yaran ki musamman Abdus-samad".
Brr Farida ta girgiza kai cikin kuka tace; "Alhaji Mustapha ya cuce ni, cutar da bazan taɓa yafe mishk ba, kuka kuma dole ne inyi ko dan rage raɗaɗin da zuciyata take yi mini".
Cikin tausayawa ya janyota zuwa jikin shi, yace; "Brr Farida ki zama jaruma sannan ki daure ki bari a sanar da Abdus-samad abinda ya shafi rayuwar shi idan ba haka ba zai cigaba da zama da maƙiyan shi kana kuma yana musu kallon masoyan shi".
Cikin kuka tace; "tsoro nake ji dakta, kada Abdul ya guje ni, kada hakan yayi sanadiyar rushewar farin cikin shi, kada na shiga jerin wa'inda zai dinga zargi, ba zan iya ba, a kullum idan naga farin ciki da ƙaunata a idanun shi ina jin farin ciki sosai bana so wa'innan abin so kuma ƙiyayya da kuma damuwa ba zan so abinda zai nisanta ni da ɗana ba".
#LIKE
#SHARE
#COMMENT
*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.
*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*_daga alƙalamin ✍_*
*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*
*sadaukarwa gare ku*
*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*
*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*
*Heart you so much*
📖📖61-62📖📖
tunda ya bar ɗakin, part ɗinshi ya wuce kai tsaye, saman gadon shi ya faɗa, ya saki ajiyar zuciya me ƙarfi, be san meyasa ba sai yake jin kamar akwai wani abu da Mahaifiyar tashi bata so ya sani.
"zan barta har zuwa lokacin data faɗa mini da kanta", wannan shine abinda zuciyar shi take faɗa mishi.
Runtse idanu yayi ga gaban shi dake faɗuwa, gobe ne zasu tafi Hayin Rigasa be san me zai faru ba wajen taron.
Tashi yayi ya faɗa bayi, yayi wanka sannan yazo ya kwanta, ya san cewa rayuwar shi yanzu ta fara zama abin tausayi.
Brr Farida ta turo ƙofar a hankali ta shigo, ja tayi ta tsaya tana kallon shi, ɗakin babu haske sosai sai dai dim light daya kunna wacce ke gefen gado, da wannan ta sami damar ganin fuskar tashi.
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke kana ta matsa kusa dashi, tun daga saman kanshi ta shafa har zuwa fuskar shi, hawayen dake kwance gefen idanun ta suka zubo.
Ta haɗiye wani abu me ɗaci a maƙogoronta, bata so ta bata da kanta, bata so ace Alhaji Mustapha yaci nasara akanta, amma babu yadda zata yi tausayin abar ƙaunar nata ya hana ta nuna jarumta.
A nutse ta fara jero addu'o'i haka hawayen dake fuskarta be dena zuba ba, ta shafe mishi jiki dashi.
Hannun shi ta riƙe gam tana sakin kuka me ban tausayi, "ya zanyi Abdus-samad, tausayi da ƙaunar da nake yi maka tana neman ta zamar dani raguwa", hannun ta sumbata kana ta miƙe ta fice daga ɗakin tana sharar hawaye.
Washe gari da safe kowa ya kama shiri domin tafiya Hayin Rigasa, shi dai Abdus-samad ba wani daɗin tafiyar yake ji ba, dan gaba ɗaya gaban shi faɗuwa yake yi.
Brr Farida dake shirya abubuwan da zasu buƙata ta kalle shi sannan tace; "meya faru ne?", ya shagwaɓe fuska yace; "First Love bana son wannan tafiyar".
Brr Farida tayi mishi hararar wasa tace; "so kake yi kenan ka ɗauko mini magana, daman nice kullum me laifi".
Sameer yaja tsaki yace; "nifa wallahi wannan gidan ba ɗaɗa ni da ƙasa yayi ba, haka kawai duk sun bi sun ishi mutane, dan dai baka da yadda zaka yi ne".
"to idan baka je ba waye kake gani zai yi maganar auren ku, ni dan Allah tashi ka bani waje", abinda Brr Farida ta faɗa kenan.
Sameer ya tashi yana ƙunƙunai ya fice, duk wannan abin dake faruwa idanun Abdul a lumshe suke, har wannan lokacin baya jin tafiyar a cikin ran shi.
******* *********
Fadila ta tuntsire da dariya, Muhibba ta harare ta kana tace; "ai wallahi gadkiya na faɗa, kuma zaki gani gobe ko kwalliyar da zan yi sai tafi ta kowa kyau".
Fadila ta kuma dariya kana tace; "hakane sarauniyar gidan mu, amma dai kin san a kwalliya akwai Nihal ko sannan akwai kuma akwai Abdus-samad, dan haka kema kin san ba zasu bari ki kada su gobe ba amma Allah ya kaimu goben ban san wane tanadi kika yi ba".
Muhibba taja tsaki tace; "sai anyi magana ki wani kawo maganar waccen banzar nifa bata dame ni ba, kowa ma ai ɗan gatan iyayen shi ne".
Nusram dai kawai da idanu take bin su, ita kanta zuwa yanzu ta fara shan jinin jikin ta domin baƙin da suke zuwa da kuma yadda estate ɗin ke cika.
Dr Saleema ta shigo ɗakin hannun ta riƙe da foil paper, "ku baku san kuyi shiru bane duk kun damu mutane da hayaniya", duka suka ja bakin su suka yi gum.
Hannun Nusram ta riƙo tace; "taso muje ki rakani wani waje", Nusram ta miƙe yayinda Fadila da Muhibba suka turo baki gaba.
"dan Allah ke Aunty Saleemar nan sai muna cikin farin ciki zaki zo ki wani ɗauke ta", faɗar Fadila kenan.
Dr Saleema tace; "ni dan Allah ku ƙyale ni, Saloon zamu tafi tare da ita", da sauri duka suka miƙe suna faɗin muma zamu je.
Dr Saleema tayi murmushi tana faɗin; "ai sai kuyi sauri ku shirya, bari naje na kaiwa Abba wannan saƙon", ta ƙarasa tana jan hannun Nusram ɗin.
Wata ƙofa taga ta buɗe sai wani siririn corridor da suka bi, sun ɗan yi tafi me tsayi kafin suka iso matattakala, nan suka hau suna buɗe ƙofa wani haɗaɗɗen falo suka shigo.
Nusram ta saki baki tana kallo, koda wasa ba zaka ce gidan ya kai girman haka ba, shiru falon sai tibin dake magana.
Wani mutumi suka samu zaune wanda Nusram ke kyautata zaton shine mahaifin nasu dan ita basu taɓa haɗuwa ba tunda yazo.
Ya ajiye jaridar dake hannun shi yana kallon su, Dr Saleema ta ƙaraso da sauri kusa dashi, ɗan sunkuyawa tayi ta sumbaci goshin shi sannan tace; "barka da hutawa ga sandwitch ɗin", ta ƙarasa tana ajiyae foil paper ɗin hannun ta.
Bece komai ba sai ɗaga kai da yayi, ta juya kenan aka buɗe wata ƙofa aka shigo, wata mata ce me kauri gajeruwa sai dai tana haske sosai koda ba'a faɗawa Nusram ba ta san cewa wannan itace kishiyar maman su Dr Saleemar.
"barka da hutawa Aunty", bata ma kalle ta ba ballantana ta amsa mata, Dr Saleema ta juya ta kama hannun Nusram.
"wacece wannan?", tambayar da Mahaifin nasu yayi mata kenan wanda yasa suka tsaya, ba tare da shakka ko fargaba ba tace; "ƙawata ce".
Bece komai ba sai dai kallo daya bi Nusram ɗin dashi, har taji kamar ta harɗe ta faɗi, suna fita tayi ajiyar zuciya.
Dr Saleema ta kalle ta tace; "ya dai?", Nusram tayi murmushi tace; "babu komai", babu wanda ya kuma cewa komai har suka ƙarasa harabar gidan.
A wajen suka sami Fadila da Muhibba da kuma Fadil, mukullin ta miƙawa Fadil ya amsa.
Duka suka buɗe suka shiga, Nusram, Muhibba da Fadila suna baya, yayin da Dr Saleema ke gefen Fadil ɗin a gaba.
Nusram taba hanyar da kallo, sai hada-hadar shigowa ake yi ga manya manyan motoci da suke shigowa cikin Estate ɗin wannan yake tabbatar mata da gaskiyar yanayin gidan wato gidane na ƴan boko.
suna daf da shiga motar su ta sako kai,, Fadil yayi murmushi yace; "gafa manya nan sun iso, Familyn Alƙali", ya ƙarasa yana dariya.
Fadila tace; "da gaske?", ya nuna mata motar yace; "gasu nan kina gani", tayi ihu tana faɗin; "ashe yau akwai show kenan?".
Ita dai Nusram bata fahimci me suke magana akai ba dan haka ta ja bakin ta tayi shiru, haka har suka isa wajen saloon ɗin.
Ko kallon wajen kayi ka san cewa waje ne na manya, abin mamakin suna zuwa aka tare su cikin sakin fuska hakan ya tabbatarwa Nusram da cewa an san Dr Saleema sosai.
Duka suka zauna, Dr Saleema aka fara yiwa kana Muhibba da Fadila, Nusram itace a ƙarshe.
Kasancewar duk ta fisu gashi yasa nata yafi kyau, Dr Saleema ta kalleta ta gefen ido tayi ajiyar zuciya, babu abinda zata ce ta ɗari Nusram ɗin dashi.
Muhibba da Fadila kuwa sai santi suke ita kuwa Nusram ɗin banda murmushi babu abinda take yi, gyaran fuska ƙafa da hannu akayi musu.
Kowacce a cikin su masha Allah domin dama ance idan kana da kyau ka ƙara da wanka, lalle aka fara yarfa musu me kyau.
Ɓangaren su Abdul kuwa, koda suka iso can wajen su Hajja suka sauka, ko'ina a cike yake dan haka babu tsayawa ɓata lokaci wajen ƙananan magan-ganu kowa gaisawa ake yi dashi cikin sakin fuska.
Ɗakin Malama Abdus-samad ya wuce, sai dai babu wasu mutane a ciki, banda Ummin su Fadil da kuma ƴaƴan ta, cikin girmamawa ya gaishe ta, ta amsa itama cikin sakin fuska.
Ita dai yaron yana birge ta sosai, Malama dake saman kujera hannun ta riƙe da littafin hisnul muslim ya sauke littafin.
Abdus-samad ya matsa kusa da ita ya gaishe ta, tayi murmushi ta amsa har tana ɗan tsokanar shi.
Wayar shi ya ciro kafin yace; "ina Fadil ne?", Malama tace; "ina jin ya tafi kai su Fadila gyaran kai", Abdus-samad ya taɓe baki.
Shifa baya jin zau iya wannan aikin, wai su mata basa gajiya da wannan ƙyale-ƙyalen kenan?.
Tashi yayi ya fito daga ɗakin, karo suka kusa yi da Surayya, ta turo baki tace; "kai Yaya Abdul, daga zuwa kuma sai ka gudu, Fadila na ciki ne?", bece mata komai ba ya raɓa ta gefen ta ya wuce.
Har ya fito Husna ta biyo shi da gudu tana ƙwala mishi kira, Abdus-samad ya ɗan ja tsaki shifa wannan takurar ce baya so.
"haba Yaya na sai kuma ka zo amma ko nema na baka yi ba", ya kalle ta sama zuwa ƙasa, riga da wando ne a jikin ta pakistan, tasha gyaran jiki ga wata ƙumba da aka saka mata zaƙo-zaƙo, haka an mata ƙarin gashin gira sai ƙifta ido take kamar ƴar baby.
Tayi fari da idanu tace; "Yaya na nayi kyau ko?", ya ɗan yi murmushi yana kauda kai gefe, shi dariya ta bashi ma, tafiya ya fara yi yayin da ta biyo shi a baya.
Shifa ta kasa fahimtar wani abu ne wannan shirmen da haukar basa wani birge shi yafi son natural beuty, Husna ganin hanyar da suka ɗauka yasa ta haɗe rai.
Ko kallon ta Abdus-samad beyi ba, ta ɗan ja tsaki ƙasa ƙasa, bata da yadda zata yi haka dole suka shiga appartment ɗin tare.
Da Kabeer da Hafeeza ke zaune saman kujerun dake balcony sai Aunty Maryam dake tsaye tana waya.
Sai da ya jira ta kammala ya gaishe ta sannan ya shiga ciki, Kamal da Aunty Muhsina ke zaune suma suna fira.
Ya gaishe da Muhsina ɗin ya kalli Kamal yace; "ina Saleema?", Kamal yace; "gaskiya ban sani ba sai dai ɗazu naga sun fita tare da Fadil amma ban san inda suka je ba".
Be kuma cewa komai ba sai kwanciya da yayi saman kujerar, har wajen ƙarfe shidan yamma basu dawo ba, kasa haƙuri yayi ya fara kiran Dr Saleemar.
"Hello Abdul, ya akayi?", abinda ta faɗa kenan bayan ta ɗaga, ya ɗan yi jim kafin yace; "kuna ina ne?".
Ta kalli gefen ta, "muna wajen gyaran gashi ne dake Sardauna crescent,an ma kusa gama mana ba jimawa zamu yi ba", bece komai ba ya kashe wayar.
Kiran sallar magrib aka fara wadda shine silar da ya saka ya tashi, Husna ta kuma miƙewa ta bishi suka fice, ganin yayi hanyar waje yasa tace; "Yaya na ina kuma zaka je".
"masallaci", abinda ya faɗa kenan a taƙaice, Husna taja ta tsaya tana kallon shi har ya ɓace daga ganin ta, tayi ajiyar zuciya kafin ta juya domin komawa appartment ɗin su.
Koda aka idar da sallah kiran Dr Saleema ya kuma yi amma ta sanar dashi basu taho ba tukunna.
Tana ajiye wayar ta maida kallon ta kan Nusram wacce gaba ɗaya hankalin ta ma baya kansu, take taji wani irin kishin ta, domin ita a ganin ta Abdus-samad ya damu su dawo ne saboda ita.
Koda ya isa gidan har sun fara shirye-shiryen cin abinci, dan haka shima saman dinning ɗin ya hau domin cin abinci.
Gaba ɗaya suka ci abinci cikin ƙaunar juna, kuma abin birgewar shine rashin samun matsala tsakanin Hajja da Brr Farida dan Brr Hauwa ma bata gidan kwata-kwata.
Shi dak Abdul kallon su kawai yake yi, suna gamawa ya riƙo hannun Brr