Showing 102001 words to 105000 words out of 121992 words
Chapter 35 - Rayuwar Abdussamad Book Complete Document by Yar Mutan Zazzau .txt
zauna cikin damuwa ba, Abdus-samad nada mahimmaci a rayuwata saboda haka duk wani abu daya dangance shi ina mahimmanta shi kin fahimta".
Nusram ta kuma ɗaga kai, Dr Saleema ta ɗan kishingiɗa jikin couch tace; "yanzu ki bani labarin rayuwar ki", Nusram tayi murmushi me ciwo kafin ta fara bata labari.
Dr Saleema har da hawaye sai da ta yi, cikin shesheƙar kuka tace; "lallai duk wanda kuka haɗu dashi akwai dalilin haɗuwar ku, kuma ko a jima ko a daɗe zaka ga akwai wani abu wanda kuke kamanceceniya dashi, kin ganni Nusram shekaruna talatin da huɗu na kusa shiga talatin da biyar amma babu aure".
Nusram tace; "babu wanda ya taɓa cewa yana son ki ne kamar ni", Dr Saleema ta girgiza kai tace; " na samu samari lokacin da nake tashen ƴan matanci amma sanin halin gidan mu yasa dole na ɗauke kaina, a cikin su akwai wanda ya nace sosai har gidan nan sai da ya turo amma iyayena suka ci mishi mutunci dalilin haka mahaifan sa suka yi fushi suka ce ko a hanya ya kuma kulani basu yafe ba, na damu sosai amma haka na haƙura yanzu gashi da zama na likita shekara takwas kenan, Nusram kuɗi iya kuɗi ina dashi babu abinda nake nema, duk wani abu da kika sani ina da kuɗin siyan shi sai dai aure kawai".
Nusram ta kuma cewa; "toke yanzu baki da wanda kike so ne", Dr Saleema ta share hawaye tace; "ina dashi mana sai dai na sani cewa ba zai taɓa maido mini da soyayya ba, ni kaɗai kawai nake son shi, a da dai ina saka ran koda da idanun rahama zai kalle ni amma zuwa yau na tabbatar da yayi mini nisa Nusram ba zan taɓa samun shi ba".
Kafin Nusram tace wani abu Dr Saleema ta ƙwalawa Sakina ne aikin su kira, ta shigo cikin sauri.
"ki kawo mini abinci", abinda ta faɗa kena, Sakina ta amsa da to sannan ta fita, Dr Saleema ta miƙe ta fara cire kaya, ita dai Nusram tana ta binta da kallo har ta shige bayi.
Nusram tayi shiru tana mamakin rayuwar wannan baiwar Allah, ta sake ɗaga kai ta kalli ɗakin nata komai yaji dangane da alatu na rayuwar duniya, ta shafa gadon da take zaune a kai shi kanshi royal bed ne me tsada, ƙaton wardrobe wacce ta cike bango ɗaya, change room da kuma dressing mirror, wasu irin manya-manyan glass masu shape ɗin duniya sai me heart a tsakiya, cikin su wasu irin ruwa ne me ƙalƙali, ƙasa kuwa italian carpet ne me taushi da kyau, sai flower vase dake kusa da window guda biyu manya-manya, duka kuma ash and milk ne,
Tana nan zaune Sakina ta shigo da ƙaton tray a hannun ta, ƙaramin teburin dake jingine ta janyo ta ɗora tray ɗin sannan ta juya ta fice bayan ta yiwa Nusram sannu.
Dr Saleema ta fito ta kalli Nusram tace; "ya baki ci abincin ba", Nusram tayi murmushi tace; "jira nake ki fito sai muci tare", bata kuma cewa komai ba sai ma nufar madubi da tayi.
Nan fa ta hau ƙalƙale jiki, itama ba wata kwalliya tayi sosai ba, powder ne sai jan baki light pink da kwalli shikenan.
Ta buɗe wardrobe ta ciro rigar bacci me shegen kyau pink colour ta saka, nan ta hau feshe jiki da turare, kan kace me ɗakin ya hau ƙamshi.
Sai da ta dawo ta zauna sannan tace; "komai ma zai zo da sauƙi tunda dama kina karatun ki kinga da an koma makaranta sati biyu masu zuwa sai ki cigaba da karatun ki kawai, zuwa ƙarshen satin nan zamu je muyi registration", Nusram cikin farin ciki ta amsa da to, abinda ta cire rai akai.
Lafiyayyen tuwun shinkafa ne da biyar taushe, ba me yawa ba ta zuba musu suka hau ci, babu sabo a tsakanin su hakan ya haifar da yin shiru, suna gamawa suka wanke hannu.
Dr Saleema ta janyo laptop ta fara dannawa ganin hakan yasa Nusram zama ta zuba mata idanu.
Sun jima a haka kafin Dr Saleema tace; "kiyi shirin barci mana", cikin sauri Nusram ta miƙe, kayan barci ta ciro cikin jakar ta sannan ta hau sakawa.
Dr Saleema tayi mata kallo ɗaya ta kauda kai, wani abu ta danna sai ga plasma yana fitowa, Nusram ta ƙwalalo idanu, Dr Saleema ta miƙa mata remote ɗin tace; "gashi idan zaki rage dare", Nusram ta saka hannu ta amsa sannan ta koma ta zauna.
Tana zaune tana kallon kamar dole don ita ba wai ya dame ta bane, haka har barci ya ɗauke ta wanda bata san lokacin da hakan ya faru ba.
Dr Saleema ta kalleta tayi murmushi, ta ajiye Laptop ɗin ta matso gare ta, kallonta tayi sosai tana jinjina kyawunta waye za'a bawa mace kamar wannan yaƙi amsa tabbas Abdus-samad ta tabbatar yanzu yafi ƙarfinta, ta share hawayen da ya zubo mata kafin itama ta fara canza kaya zuwa na barci.
Kan couch ta kwanta har lokacin ranta a cunkushe yake, a yanzu kam tana jin cewa wata kila harta koma ga ubangijinta bata da rabon yin aure.
******** ************
koda ya bar gidan babu abinda yake yi banda tunani, Allah ne ya taimake shi har ya kai gida lafiya, yana yin parking suka haɗu da Sameer.
"kai kam zaka tashi office da wuri amma duk zamu riga ka isowa gida", cewar Sameer ɗin kenan, Abdus-samad yayi murmushi kawai.
Part ɗin shi ya fara wucewa, sai da ya shiga bayi yayi wanka kafin ya fito ya hau shiryawa, gaban madubi yaja ya tsaya hannun shi riƙe da comb, wai yau shine da mata!?, shi Abdus-samad Abubakar Nagimi?, ya sauke nannauyar ajiyar zuciya.
Turo ƙofar da akayi itace tasa ya kalli wajen, duk da sanin wacece ta shigo, kamar yadda ta zuba mishi idanu haka shima ya zuba mata idanu, tsoron shi ɗaya kada ace ta gane cewa an ɗaura mishi aure.
Dr Farida ta kauda kai tace; "idan ka gama shiryawa kazo kaci abinci", be amsa ba itama kuma bata tsaya jiran amsar tashi ba.
Tana daf da fita sai kuma ta juyo tace; "wai baka kuma magana akan yarinyar da aka harba ba a shopping mall?".
Ya ajiye comb ɗin hannun shi ya ɗauki kwalbar turare ya hau fesawa, har ta cire rai da zai yi magana sai kuma taji yace; "First Love komai yana faruwa saboda ɓoye mini abubuwa da yawa da kuke yi".
Cikin sauri ta kalle shi ya kauda kai yama cigaba da abinda yake yi, ta jima tsaye ko zai kuma cewa wani abu amma be kuma magana ba hakan yasa ta ɗaga ƙafa ta fara tafiya, wannan murɗaɗɗen hali irin na uban shi ne", abinda ke ranta kenan ita kanta duk da take lauya wani lokacin idan yayi magana a murɗe ta kan jima bata fahimta ba.
"ita ɗin ƴa ce ga Alhaji Mustapha Tuge", abinda ya faɗa kenan tana dafa da fita, Brr Farida gabanta ya yanke ya faɗi, cikin sauri ta juyo ta sake kallon shi kamar ma bashi yayi maganar ba.
Taja ajiyar numfashi tace; "Baby ita ɗin ta faɗa maka haka?, taya akayi ka sani ko ka sake binta asibitin ne?, kun haɗu dashi Alhaji Mustaphan?", duka ta jero mishi tambayar babu amsa ɗaya da ya bata hakan yasa ta fice kawai.
Abdus-samad ya bi bayanta da kallo tana ficewa ya saki ajiyar zuciya, ƙarar wayar shi itace ta dawo dashi daga duniyar tunanin daya faɗa.
Number ce babu suna hakan yasa be ɗaga ba, tana yankewa wata ta shigo itama tana yankewa wani kiran ya sake shigowa, ya saka hannu ya ɗauka ya kai kunne.
"Hi!", shine abinda ta faɗa, a gajarce shima yace; "barka", ta ɗan yi gyaran murya sannan tace; "ka gane me maganar".
Cikin ƙagara yace; "a'a wacece?", jin abinda ya faɗa yasa jikin ta yin sanyi, "Khausar ce", ta faɗa cikin sauri.
"oh ya gida?, fatan komai lafiya", ya tambaye ta, murmushi tayi kana tace; "lafiya lau, dama cewa nayi bari na kira mu gaisa", ya ɗan shafa gefen fuskar shi yace; "na gode" kan ta kuma magana ya yanke kiran.
Sororo ta tsaya hannun ta riƙe da wayar, Hajiya Salma data ji duk abinda ya fara ta taɓe baki tace; "wai ke qace irin wahalalliya ce?, bafa shi kaɗai bane namiji".
Khausar ta saki murmushi tace; "ni fa Mommy ina son shi kodan kama da yake yi da Daddy", ta ƙarasa tana me juyawa ta kalli Mahaifin nata.
Alhaji Mustapha kuwa banda zufa da take karyo mishi babu abinda yake yi. be iya cewa komai ba.
"Daddy ai ka ganshi kwanaki ko?, kana nan yazo gaishe dani a asibiti, wallahi da badan na san cewa nida Khalee kawai Mummy ta haifa ba da sai nace ɗan kane".
"Umm", shine abinda Alhaji Mustafan ya faɗa, Hajiya Salma ta ƙunshe dariya, Khausar zata kuma magana Hajiya Salma ta dakatar da ita.
"wai ke baki ga Mahaifin naki baya son surutu bane, gobe ƴar uwar ki zata dawo dan haka kije ki kwanta kin san dai isowar wuri zata yi", Khausar ta miƙe tana zumɓurar baki tayi ɗaki.
Hajiya Salma ta miƙe itama ta shige nata ɗakin, Alhaji Mustafa ya dafa kanshi da hannu biyu yana sauke ajiyar zuciya.
"wannan wane irin masifa ce take tunkaro shi, ƴar shi ta cikin shi ke son ɗan shi na cikin shi?, taya zai fito ya shaidawa duniya cewa Abdus-samad ɗin ɗan shi ne na cikin shi?, akwai babban al'amarin da ko tunawa baya son yi".
Wayar shi ya zaro ya fara kiran Alhaji Sa'eed, sai dai kash ana amfani da layin, miƙewa yayi cikin sauri kana ya fara zagaye ɗakin.
Daidai lokacin kuwa Hajiya Salma ce da Alhaji Sa'eed suke waya, "Alhaji wallahi ban san yadda zan yi da yarinyar nan ta fahimci halin da ake ciki ba, bana ƙaunar ganin yaron nan a raye gashi na rasa yaya zan yi".
Alhaji Sa'eed yace; "kada ki damu Hajiya Salma, zamu iya amfani da ita wajen tunowar asirin mijin ki, na san cewa idan har abinda yake ɓoyewa ya fito fili to tabbas yaran nashi zasu tsane shi tsana me tsanani, sannan shi kan shi Abdus-samad ɗin zai tsane shi tsana mafi muni sannan kinsan Nagimi's Family dole zasu ɗauki mataki, zasu maka shi kotu kuma kin san hukuncin da za'a yanke mishi ɗaurin rai da rai ne".
Hajiya Salma tayi ajiyar zuciya tace; "Alhaji Sa'eed har yanzu baka san waye abokin ka ba, ko tafiyar nan da yayi hannun jari yaje ya zuba a wani company dake Hong Kong ƙimanin dala billion sha biyar, sannan yana ɗaukar kaso mafi tsoka a babban companyn dake ƙera gwalagwalai a Dubai, dan haka bana jin kuɗin Familyn nan zai iya da nashi, ba zasu taɓa iyawa ba ka chanza shawara".
Jim yayi yana tunani, yayin da Hajiya Salma take tunanin mafita yake nemo musu, shi kuma a nashi ɓangaren kuɗaɗen ne suka fara girgiza shi, lallai wato Alhaji Mustaphan ashe yana ɓoye mishi wasu abubuwan, shi dai kawai ya san cewa yana da Companyn ƙera motoci a Dubai da kuma lagos, sai Company biyu da yake da hannun jari a India da kuma Bangkok ashe likafa ta cigaba kuɗin nashi ya fara wuce tunanin shi kenan?.
"Me zai hana kawai idan Khausar ta gayyace shi gidan nan mu saka mishi guba a abinci sai ya mutu, idan yaso Baban shima daga baya sai muji dashi?".
Abinda ta faɗa ya katsewa Alhaji Sa'eed duniyar tunanin daya fara kenan, ya girgiza kai kamar tana gaban shi yace; "hakan bame yiwuwa bane Brr Farida a sanin da nayi mata ba zata taɓa ƙyale abin a haka ba, bana so muyi abinda zamu shiga ciki".
Hajiya Salma taja tsaki tace; "yanzu meye abin yi?", Alhaji Sa'eed yace; "watan gobe Brr Farida zata tafi Korea yin wani case ina ganin zamu yi amfani da wannan damar ne kawai".
Hajiya Salma tayi murmushi tace; "shikenan Allah ya kaimu da rai da lafiya, amma wallahi na ƙosa komai ya dawo hannu na, nima na zama ɗaya daga cikin matan da ake lissafawa masu kuɗi a duniya".
Alhaji Sa'eed yayi wani munafikin murmushi sannan yace; "nima na ƙosa wannan lokacin yazo ke dai kome ke akwai ki dinga sanar dani", ta amsa da to.
A haka suka rabu, Alhaji Sa'eed na katse wayar ya miƙe tsaye cikin sauri, Brr Hauwa dake kwance jikin shi tayi saurin miƙewa tana tambayar shi lafiya.
"babu komai, dan Allah ina buƙatar yin tunani yanzu bana son damuwa ko zaki tafi ne?", Brr Hauwa ta ɗaga gira ɗaya tace; "kuɗin da Hajiya Salma ta faɗa maka Alhaji Mustafa na dashi shine ya tsorata ka ko me".
Jin abinda ta faɗa yasa ya ɗan saki rai yace; "ba haka bane, mafita nake nema dole Abdus-samad da Alhaji Mustapha su mutu, kuɗi Hauwa dole ya dawo gare mu, ni dake".
Brr Hauwa tayi murmushi tace; "ka kwantar da hankalin ka, har yanzu fa Brr Farida bata faɗawa Abdus-samad komai ba, suna ganin sannan sirrine tsakanin ta da Alhaji Mustafa banda su biyu babu wanda ya sani".
Alhaji Sa'eed yace; "amma shi Alhaji Mustaphan ai ya san na sani ko", ta shafa fuskar shi tace; "amma kuma ai ya yarda da kai sosai ko".
Ya koma ya zauna kana ya girgiza kai yace; "bana tunanin hakan Brr a da Alhaji Mustapha baya yin komai sai da sani na amma a yanzu ya canza sosai", miƙewa yayi ya ɗauki wayar shi kana yace; "bari naje wajen Oregbu zamu haɗu gobe kawai dan yau till down zamu yi".
Brr Hauwa ta figi jakar ta sannan tace; "muje ka ajiye ni a gida ko?", daga haka suka fice daga gidan.
#LIKE
#COMMENT
#SHARE
*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.
*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*_daga alƙalamin ✍_*
*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*
*sadaukarwa gare ku*
*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*
*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*
*Heart you so much*
📖📖55-56📖📖
Alhaji Mustafa ke tsugunne jikin shi sanye da jan ƙyalle iya gwiwa, tsaye a saman shi Appu ne shima sanye da jan ƙyalle a kwankwason shi sai dai shi ya yafa wani saman kafaɗar shi.
Wani abu dogo ne riƙe a hannun shi, wani ƙaton mutum me ƙaton tumbi ke gefe tsaye da ƙwarya ƙatuwa a hannun shi, Appu ke saka wannan abin cikin ƙwaryar yana yayyafawa Alhaji Mustapha yana zagaye shi yana wasu irin surutai.
Sauran kuwa kansu na ƙasa duka a tsaye suke sanye da jan kaya riga da wando, wajen yayi tsit sai tashin muryar Appu dake wannan surutan.
Sun jima a haka kafin wani hayaƙi ya fara cika wajen, basu motsa ba kai daga gani kasan sun saba da yanayin, sai dai wasu ƙalilan da suke zubar da hawaye kasancewar hayaƙin akwai zafi sosai amma babu halin rufe idanu.
Sun jima a haka wajen awa ɗaya kafin komai na wajen ya ɗauki rawa, wutar dake kunne koda yaushe wacce take saman wata ƴar ƙaramar ƙwarya ta ɗauke, nana fa ko'ina a wajen ya ɗauki duhu.
Minti talatin da faruwar hakan sannan hasken ya dawo, Alhaji Mustafa ya kalli inda yake tsugunne jini ne a gaban shi malala wanda har ya gangaro ya tarar dashi, sai yara guda biyu da suke kwance a wajen cikin su a fafe wanda yake nuna alamun tana nan ne aka sha jinin nasu.
Appu ya fashe da dariya kafin ya matsa, wajen wata giggimemiyar kujera yaja ya tsaya sannan ya nuno Alhaji Mustapha yace; "haƙurin Oregbu ya kusa ƙarewa Tuge, dole ka kawo jinin ɗanka na cikin ka idan ba haka ba fushin sa zai sauka a kanka, shekara talatin kenan da yi mishi alƙawari amma har yau ka gaza cikawa, tun ana rarrashin shi yana amsar jinin wasu wata rana fa ba zai aminta ba", ya juya ga sauran mutanen ya nuna mutum biyu a cikin su yace; "Oregbu yace a gaya muku ya ji daɗin sadaukarwa da kuka yi mishi, dan haka yayi matuƙar murna shi kuma zai canza muku da abinda kuke so".
Ya nuna wani dogo fari a cikin su yace; "yadda ka bashi ɗan ka yace a gaya maka kaine zaka dinga juya shugaban ƙasa wanda za'a rantsar hasalima ma ƴan majalisu kai zaka yi list ɗin