Showing 1 words to 3000 words out of 67328 words
Chapter 1 - Diya Mace Book Complete by khadija sidi .txt
Skip to content
ummu-abdoul
MENU
Diya mace by khadija sidi
Posted by UMMU-ABDOUL on OCTOBER 17, 2016
[16/10 21:43] .: 7/24, 11:46 PM] Salmah Ateeku: [11:40pm, 4/30/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
1⃣
Jin an idda sallar isha’i,ga jama’a na ta fitowa daga masallaci ya sanya Hajara wacce ake kira da hajjo kara sauri,ji ka ke kululu! Karar kugin yunwa da cikin ta ke ma ta kenan,silifas din ta hadin bauta,daya ya tsinke saboda haka sai cire shi ta yi,ta ruke a hannu. Dauke ta ke da katuwar kwaryar dawa wanda ta je aka niko domin Innar su ta samu ta tuka mu su na dare,hajjo ta dada sauri,cikin ranta fadi take yau dai Inna za ta yi tuwan dare,wata kila ma sai goman dare za mu ci,ko da yake mu ma godewa Allah baba yau ya kamana dawa mai tarin yawa,ma huta da shan garin rogo kwana biyu.
Titi ta tsallaka,ta wuto ta wajan mai shayi,kamshin tuyen wainar kwai ya daki hancin ta,ba ta san san da ta mayar da mugun yawu ba,ba ta da buri da ya wuce ta gifta ta wajan,dan har dan tsayawa a wajan ta ke,taitahura hanci,ita a lalle sai ta shaki kamshin wainar kwai ko Allah ya sa ta ji shi har cikin ta kamar ta ci ta koshi. Wannan karan ma tsayawa ta yi ta na baza hanci,ga wata bakar yunwa da ta addabe ta,tini ta shagala ta ma manta da dawar da ke kanta,ba ta ankara ba sai ga mahaifin ta zaune cikin rumfar mai shayi,gaban sa katan buredi ne,ga kuma wainar kwai manya manya cikin faranti,ya na yagar buredin ya na hadawa da wai nar kwai,ga kuma shayin sa a gefe ya na korawa. Da sauri Hajjo ta matsa ta na fadin laa Baba,Baba ne wlh,Baba! A fusace ya waigo ya dube ta,ganin Hajjon ce ba kunnen sa ke zagi ba,ya daka ma ta tsawa,ke uwarki! uwarki na ce! Hajjo ta sha jinin jikin ta,sauran jama’a da ke zaune cikin rumfar su ka zubo mu su na mujiya. Na ce Uwarki! Ya ma ta dakuwa,shegiyar kaya! Ki kai ma ta dawar ba za ki kai ma ta ba kin tsaya gantali! Tafi gida dan uwarki! Ya daka ma ta tsawa,jiki na bari ta juya,har da tuntume Allah ya sa ta ruko dawar ba ta zube ba,Baba ya ce assha,kun ga dai shashasha,maza zubar da dawar kwa yi kwanan yunwa dan uwar ki!! Ita dai Hajjo ta ti maza ta kama hanyar ta,jiki na bari,ta ma manta da wani kamshin wainar kwai da ta ke bala’in so,shi ko Baba buredin shi ya ci gaba da yanka ya na hadawa da wainar kwansa ya kaiwa baki,sai gunguni ya ke kamar kuturu!!
Tin da ta dau hanya,ba ta zame ko ina ba sai cikin gida gaban Inna ta dire kwaryar har lokacin jikin ta be daina rawa ba,Inna ta dube ta tace sai yanzu Hajjo? Layi ki ka tadda a wajan ne? Lfy ya na ganki ba nutsuwa jiki na bari haka? Hajjo ta zauna ta na maida numfashi ta ce Inna wai fa dan na ga Baba ya na cin buredi da wainar kwai wajan mai shayi,ba fa emmin zance ya yi ba,kawai dama magana dai kawai na ma sa shi ne ya fatattako ni,kamar na ce ya emmin!Inna ta dafa kafadar ta kema Hajjoo me ya kai ki yi ma sa magana tin da kin san ba ya so,yanzu haka sai ya time ki idan ya dawo. Tsigar jikin Hajjo ya tashi tuno dukan mahaifin ta,kana ta ce wlh Inna rai na ne ya biya ban san sanda ma na ma sa magana ba,ni dama ya emmin da yayyai ta bugu na bazan damu ba ma,yunwa na ke ji kamar na ci babu. Inna ta ce inbe emmiki ba ai ya emmiki bugu,yunwa kuma ga danwake cen dazu da fitar ki yayar ki Indo ta aiko ma na da shi sai…. ba ta jira Inna ta gama magana ba ta tashi da gudu ta nufi inda danwaken ya ke ta ja kwanan ba tare da ta wanke hannu ba ta afka ma sa,hannu baka,hannu kwarya,Inna ta bita da kallo ta ce oh Hujja kamar kin shekara ba ki ci komai ba? Allah dai ya yanke ma na wannan bakar wahalar da mu ke ciki,amen.
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[11:49pm, 4/30/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
2⃣
Hajjo kenan,Hajara Mamman Mansur,diyar Mallam Mamman Mansur,wanda suke zaune a kauyen Kumurya,na yankin birnin kano. Wato Mallam Mamman wanda su Hajjo ke kira da Baba mutum ne mai rufin asiri matuka,ya na daya daga cikin ma su kudin yankin,amma kash mako gare shi,be san ya wadatar da iyalan sa ba,gidan sa kullum cikin faci-faci ake,mafi munin halin Baba shi ne kyamar haihuwan ‘ya’ya mata,ya ki jinin ‘ya’ya mata dan a nashi wahala ne kawai babu wata riba,a wannan dalili ya sa ya auri mata shida ya na saka a dalilin sun haifar ma sa diyoyi mata,duk wacce ta haifi diya mace da sai ta bar ma sa gida ita da diyar da ta haifa,wacce ta ci sa’a Allah ya zaunar da ita ita ce Inna,uwar gidan sa wato mahaifiyar su Hajjo,ita ma din dan Allah ya nufe ta da haifar da namiji a haihuwar ta na fari wanda aka radawa Mahmud,ake kira Mudi,da wannan dalili ne ya sa ya saki cikin sa ya zauna da ita,bayan shekara biyu ta dada haifa ma sa wani jinjirin Namiji mai suna Ayuba,murna gun Baba ba a magana,ita kanta Inna sai da ta zama yar gata dan cikin matan da ya aura ita kadai ce ke haihuwar maza,ko da Allah ya sake ba ta ciki a karo na uku,sai fa Inna ta haifo diyar ta mace,bakin ciki gun Baba kamar ya zaune diyar ya huta,yayyai ta masifa da bala’i wai an haifo masa jidali,wacce ba za ta amfana komai ba sai dai kai ka amfana ma ta,ai ta dawainiya ana jidali a karan banza a karan hofi,haka dai ba dadi aka sanyawa yarinya suna Indo. Tin daga nan Inna ta fara ganin sauyi,abunda ta ke gani Baba ya na wa matan da ya aura na shirin afkuwa kan ta.
A haka zaman ba dadi,sam be san rayuwar Indo ba,sai dai na Mudi da Ayuba,su ka ci gaba da zama,Baba na auran mata ya na saki,gashi kuma kudira na Ubangiji har ya yau babu wacce ta haifa ma sa da namiji in ban da dai Innar.
A haka ba dadi har shekara goma ya shude,an fidda rai da sake haihuwar Inna,kwatsam sai Allah ya ba ta wani cikin,tin ya na karami Baba ke ma ta kashedi kar fa ta haifo diya mace,ya dai fada ma ta,da ke abun na Allah ne bayan wata tara Inna ta sillibo diyar ta mace,Baba ranar har da zage zage,ai fa Inna ta kwashe kayanta ta bar ma sa gida,da kyar yan uwan sa suka sa baki ya bar ta,a fadar sa ta ci darajar yaran ta maza. Ranar suna aka radawa yarinya suna Hajara,shekara biyar da haihuwar Hajara aka aurar da yayar Indo wacce ta ke da shekara goma shabiyar.
Kwanci tashi,yanzu Hajjo ta kai shekara goma shabiyu cif a duniya,amma daidai da rana daya Baba be taba fada ma ta magana ta arziki ba sai kyara da tsangwama. Hajjo yarinya ce da ba ta fiya jiki ba,yar fiyot ta ke kamar ka hure,kuma ba ta da wani tsayin azo a gani. Ba wani sifar kyau gare ta ba,amma kuma ba laifi tana da wani irin boyeyyen kyau wanda har ka kare zama da ita ba dai ka ga munin Hajjo ba,sai dai ma ka ga tana kara ma ka kyau. Hajjo ba fara ba ce,ba kuma baka ba,an fi danganta ta da wankan tarwada,idanun ta ba manya ba ba kuma kanana ba,haka zalika hancin ta be da wani tsini,ba ba’a ba hancin na ta ya so yayi gajarta sai Allah ya taimaka be yi ba,ba ta da gashi,amma kuma gaban kan ta rufe ya ke ruf da gashi .dan ko ta daura dankwali gashin be buya kamar ta sa hula ka ganshi lub lub a kwance kai ka yi zaton irin mai gashin nan mai yawa na gaske ce. Ba a kira ta mai karamin baki ba,amma girman leben na ta ba me muni ba ne,shi ne wanda turawa ke kira full lips,abubuwa biyu da ke karawa Hajjo kyau shi ne lotsewar da kumatun ta keyi duk sanda ya yi magana bare kuma uwa uba fara’a,dama ga ta gwanar murmushi,ga kuma yar wushiryar wanda ke dada bayyana kyanta cikin nutsuwa
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[12:01am, 5/1/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
3⃣
Washagari da safe Inna ta na wanki Hajjo ta shigo a guje ta na waka..
“Wata tafi wata a gashi ko
Ni na fi a gashi,wata ta
Fi wata a hanci ko ni na
Fi a hannci…”
Ta fada bayan Inna ta na dariya,Inna ta ce Hajjo hankali!za ki karasa min bayan nawa,yau kuma wannan wakar aka yi a dandalin kenan!Hajjo kyalkyale da dariya ta ce wlh Inna shi aka yi,amma kin se me Inna? Inna ta ce sai kin fada auta,Hajjo ta ce da ance wata ta fi wata,sai ki ga wata ta fito ta ce ko ita tafi,Mairo ta ce ta fi a gashi,Bintu a Ido,Hanse a hanci,ni kuwa ban fito a kowani baiti ba,da aka gama na ce ni me ya sa ba a bani nawa fitowar ba sai Mairo ta ce wai ai ban da abun fitowar dan babu abunda na fi su da shi,wai gani kwakwido,kuma komai nawa kadan ne!
Inna ta murmusa,kyale su Hajjo,ai shi ya sa ki ka fisu kyawu saboda komai na ki daidai ne ba kuma kadan ba,dan haka ne ki kin fi kowa a kyawu! Hajjo ta saki Inna ta zura a guje..ke ke ke Hajjo! Ya ki nan! Inna ta kwalla ma ta kira,Hajjo ta dawo ta na haki,cike da mamaki Inna ta ce ina kuma za ki? Cikin haki Hajjo ta ce zuwa zan yi na fada mu su na fi su a kyauwu! Inna ta girgiza kai auta hankali! Ki yi hakuri idan kun sake haduwa anjima kya fada mu su,ko fa karyawa ba ki yi ba,ga kokon ki da dumame can maza ki dauka ki karya. Ba dai haka ta so ba,ta ce toh,ta karasa ta dauko koko da kwanan numame ta ya haye kan tabarmar da ke shimfile karkashin bishiyar mangaro ya yayi rumfa a tsakiyar gidan. Babban gida ne mai dauke da dakuna shida a jere,sai kuma guda daya mai ciki da falo,shi ne wanda Baba ke kwana ciki,sai daya na Inna da Hajjo,na biyu na Mudi da Ayuba,daya dakin girki,daya kuma dakin aje kayan abunci duk da ba aje mu su kayan abuncin ya ke ba,sai kuma dayan dakin da ke kulle cike da kayan takarce har da wani tsohon gado mai rumfa. Da ke Inna mace ce mai tsaftar gaske kullum gidan tsaf sa shi.
Sai da ta fara kai loma sannan ta daga ido ta kalli Inna ta ce laa Inna wankin ki ke ashe,ni da na ce zan na taya ki. Inna ta dara,Hajjo hankali,ke tin shigowar ki ba ki lura da wankin ba sai yanzu? Baki cike ta ce eh wlh Inna,bara na gama sai na sa mi ki hannu,Inna ta ce a gama lfy auta.
Inna! Hajjo ta kwada ma ta kira,na’am auta,menene kuma? Hajjo ta ce ni ma dan Allah ki ce da Baba ya sani makarantar gaba da firamari kamar yanda ya sa su Mudi da Ayuba…..ba za a saki din ba! Baba ya fito a fusace,ya ci ado da babbar rigarsa aska shida,ashe ya na daga daka ba ta sani ba.
A fusace ya ke duban Hajjo da tini ta sha ruwan jikin ta,ta yi tsumu tsumu. Shegiyar kaya,ke dubanni nan!ke wacece da za a saki makarantar gaba da firamari? Inna ta dauke kai ta ci gaba da wankin ta,ba da ke na ke magana ba! Ido na shirin kawo ruwa ta ce ni Hajjo ce… Baba ya ce Hajjo me? Hajjo ta ce diyar ka mutum! Ungu nan! Ya ma ta daguwa! Hajjo diya mace ba diya ta ba za ki ce! Ke diya mace ce,su Ayuba da Mudi maza ne shiya na sanya su makaranta koba komai idan su ka gama ma amfana da su,ke kuwa fa? Ita diya mace jidali ce,a haifo uban ku yayi dawainiya da ku,mu aurar da ku mazajen ku su yi dawainiya da ku,ku tsufa ‘yayan ku su yi dawainiya da ku,shegiyar kaya na ki na yi asara,bazan sa ki a makarantar ba! Da ma ki ka samu na.sanya ki firamari din?Har kina sa bakin magana dan kin ga ban buge ki jiya ba ko? Ya kama kunnen ta sai da Hajjo ta dan yi kara dan zafi,in kara gani kin maimaita abunda ki ka min jiya sai na lahira ya fi ki jin dadi! Ya saki kunnan,Hajjo ta durkushe ta na kuka,ko a jikin sa,hannu ya sa a aljihu ya fiddo da damin kudi,ya zaro naira hamsin ya karasa wajen Inna ya na fadin ke Amenatu ungo nan kudin cefane,sai Allah ya dawo da ni,na tafi daurin auren Garbati dan Alhaji Baso,ta dago ta karba tare da ma sa fatan dawowa lfy,ya fice ya na baza babbar riga. Inna ta dubi Inda Hajjo ta ke durkushe ta na kuka,tace maza tashi diyar albarka ka karasa cin tuwan ki,kar su Mairo su shigo su cinye mi ki fa!
Hajjo fuskarta cike da hawaye ta ce Inna dama ni ma namiji ce kamar su Mudi da Baba ya soni ko da dan gutsire ne! Inna ta baro wajan wankin ta zauna kusa da Hajjo,ta ce kul Hajjo,na godewa Allah da yaiyo ki diya mace,kin san darajar ‘ya’ya mata kuwa? Ai darajar diya mace da yawa take Hajjo,yanzu in tambaye ki,da ki zama kamar Inna da ki zama kamar Baba wanne ki ka so? Hajjo ta ce caf! Gwara na zama kamar Inna ta wlh,Inna ta rungumo ta yauwa diya ta,shi ya sa na ke san ku,Baban ma fa ya na son ki,har ya fi gutsire,kawai baya nunawa ne. Hajjo ta dara Allah Inna? Shi ya sa ma jiya da ya dawo ya ga na yi bacci be buge ni ba ko? .Inna ta gyada kai kwarai da gaske,maza ci tuwan ki toh sai ki zo mu yi wankin,ko kin fasa taya ni ne? Hajjo ta ja kwanan tuwan ta, zan taya ki mana Inna,bara na yi sauri na zunzunduma loma! Inna ta tashi ta na dariya,ta ce a dai ci a hankali,ta koma kan wankin ta,ta bar Hajjo ta na zunduma lomar kamar dai yanda ta ce
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[12:11am, 5/1/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
4⃣
Babban Masallacin Kumurya,jama’a an taru,Baba tare da aminin sa Alhaji Baso baban ango zaune cikin masallaci suna jiran waliyan amarya su karaso,shiru ba su karaso ba,har rana na shirin takewa,Baba ya dubi Alhaji Baso ya ce anya kuwa lfy? Ka ga fa yanda aka shanya mu kamar kayan wanki? Alhaji Baso cikin damuwa ya ce ni ma dai jiran ya fara damuna Alhaji Mamman! Daga can gefe su ka hangi Garbati,yaci babbariga tare da abokansa. Garbati kato ne mai girman gabobin jiki,gashi dai yaro ne mai kimanin shekara ishirin da biyu a duniya,amma sai kayi zatan ya haura haka,fari ne mai zubin gwabaye. Kai Garbati,ya ka nan! Alhaji Baso ne yayi kiran sa,Garbati ya karasa da sauri ya durkusa gaban su,gani Baba,Alhaji Baso ya ce ya haka ne? Ya da girman mu a gari ana shirin maishe mu kanana mutum ne? Mun tara Jama’a amma ba waliye na amarya? Cikin maganar sa irin ta gwabaye,da karfi ya ke ya ce yo ni ma Baba hakan na gani!har raina ya fara baci! Aw Baba ka ga yayan Jummalan ma ya karaso! Ya yi nuni da wani matashi da ya shigo,Illo ga mu nan! Ya kwalla ma sa kira,Illo ya karaso ya gaida su Baba,Baba ya ce ya haka ku ka makara kuma? Illo ya durkusar da kai ya ce ai an sami matsala ne daga wajan amarya,ta ce maganar aure ba ta san shi ba,ta fasa auren Garbati…..lahailahaillallahu Mahammada Rasulillahi Sallallahu alaihi wasallam! Su duka su ka doka salati!Garbati ya fara muzurai! Alhaji Baso ya ce wannan ai yashashshen zance ne! Mu za a maida kanana mutane! Tintini ba ku san ku fasa auren ba sai da mu ka tara jama’a! Dan Allah Mallam Mamman taya ni jin maganar kananan mutanen nan! Shi de Illo ya yi kasa da kai kawai,Baba ya ce to a wani dalilo yarinya ta fasa aure? Illo ya ce a dalilin kin ware ma ta gida ita kadai ba tare da ya hada ta iyayen sa ba! Zancen banza zancen hofi! Alhaji Basu ya dakatar da shi ya na kumfar baki,an ki a ware ma ta gidan! An ki din! Ta fasa auren dan iyayenta! Mu nan mu mu ka hana shi ware ma ta gidan,tashi ka bamu waje! Illo ya ce na bar ku lfy,ya tashi yayi gaba ya bar su cikin takaici,ga Jama’a an tara.
Baba ya dafa kafadar Alhaji Baso ya ce kar ka damu,ba dai yau aka sa za a aura auran Garbati ba? Aure kam kamar an daura an gama,kai Jama’a a saurara za a fara abunda ya kawo mu,Garbati dai sarautar Allah ya zubawa ido kawai.
Can gida kuwa Inna ta aiki Hajjo siyo daddawa,dake Hajjo akwai san gudu,ta taho a guje ga daddadawar ta a hannu,ba ta ankara ba ta gwabje Idi dan makota ya dauko tallar manja,tini farantin manjar ta yi kasa,manjar ta zube malale a kasa,Idi ya bi manjar da kallo ya ce kan uba! Wlh sai an biya ni ko na daki kudina!mahaukaciya wacce ba ta san tafiya a hankali ba! Jin haka Hajjo ta dada zurawa a guje ta na fadin ba sai ka biyo ni ka daki kudin na ka ba in za ka iya kama ni! Ai kuwa shi ma bin na ta yayi,tsabar gudu ba ta hango Baba tafe ba,da gudu ta shige gida. Baba ya shigo ya na fadin komai aka yi shegiyar kayan nan wani masifar ta jangwalo ma na ya sa take gudun fanfalaki haka!