Showing 15001 words to 18000 words out of 67328 words
Chapter 6 - Diya Mace Book Complete by khadija sidi .txt
su ka sami Garbati,da ke juma’ar Allah ce sai ga Garbati an yi fes an sami wanka kenan,wata kodaddiyar babbar rigar sa ce a jikin sa,ya kafa wata hular shi irin ta mutan da har goshi. Ganin su Mudi yayi saurin ba su hannu su ka gaisa,sannan su ka yi sallama da Hajjo,ko ta kula su,ita dai rera kukan ta take,Garbati ya tisa ta a gaba ya na fadin da ba ki tashi zuwa gidan ba sai da ki ka ga kina da ciki dan ki min asara,toh wlh ba ki isa ba. Cikan ka ba tace ma sa ba,suna tafe jama’a na kallan su har su ka shige gida…
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[7/25, 9:35 AM] Salmah Ateeku: [6:18pm, 5/15/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
2⃣1⃣
Wasa wasa cikin Hajjo ya girma ya fito sosai,ta sha laulayi,ga jarabar Garbati da ya karu ba dare ba rana. Yanda Allah ya so ta da rahama sai warin Garbati ya dai na damun ta,sanadiyyar cikin da take dauke da shi. Duk dare sai dai ya zo ya ce Hajjo gyara,da ya sami abunda ya ke so ya zube ya na munshari,ita ko baiwar Allah har ta ma soma sabawa.
Sanda cikin na ta ya kai wata tara sai fa jikin Inna yayi tsanani sosai,gashi Mudi da Indo ne masu kula da ita,dan Ayuba dai ya shiga layin yan shaye shaye. Ko da Indo ta fada ma Hajjo halin da ake ciki,ita take kula da ita da rana,saboda yara sai ta ke komawa gida da magrib ta barwa Mudi kula da Innar. Hajjo ta ce ai jinyar mace sai mace,bari Baban Garbati ya dawo za ta tambaye shi in ya so ita take kwana da Innar,Indo ta ce da wannan tsohon ciki Hajjo za ki iya? Hajjo ta murmusa kwarai ma kuwa,ina iya komai fa. Da haka su ka rabu.
Baban Garbati Alhaji Basu be yiwa Hajjo mu su ba,dama ya san halin da Innar ke ciki,dan haka da Hajjo ta fada ma sa bukatar ta sai ya sa Mairo ta yi kiran Garbati. Ko da gogan na ta ya ji zancen sai ya ce sam ba da shi ba,ya ce Baba ni wlh ban iya kwana ba Hajjo,caf wannan ba ma maganar dauka ba ne Baba! Gaban Hajjo ya fadi,ta fara karanto addu’oi cikin ranta,ba ta da buri da ya wuce dai na kwana rumfa daya da Garbati.
Garbati ya dube ta ya ce yo Baba idan ta tafi bukatata kanwa zan na sauke ta eh Baba? Alhaji Baso dai da ya gane in da Garbati ya dosa sai cewa yayi toh toh na gane,toh ke Hajjo kin ji daga bakin mijin ki. Hajjo ta ce wlh Baba Inna ta na bukatar taimako!! Garbati ya ce wlh nima ina bukatar mata ta!!! Hajjo ta watsa ma sa harara,ji take kamar ta kurma ihu.
Alhaji ba so ya nisa,ya ce ina ke Hajjo,yanda za a yi ki na zuwa wajan Innar ta ki da safe ma na,in ya so da magariba ta yi yar uwar ta ki ta karbe ki ki dawo dakin mijin ki,ko kuwa? Hajjo ta san idan ta yi wasa wannan damar zai wuce ta,dan haka ta amsa da toh Baba,na gode,da ga gobe zan fara zuwa. Alhaji Baso ya ce Allah ya sauwake.
Bayan tafiyar Hajjo Garbati yay ta mi ta,wai fa ana ma sa katsalandan fa,Allah ya bashi kudi ya tashi ya bar gidan ya huta,Alhaji Baso ya ma sa banza,Mairo ce ma ta taya sa da ameen,mu ma ma huta da masifar ka,ya bita zai daka,Iyalle ta hana,kawai sai ya fice ya na ta bala’i,wai ana so a kar shi a gidan.
Jikin Inna dai ba dadi,kurji ya zame mata ciwo mai cin jiki. Yan da Alhaji Baso ya ce hakan Hajjo da Indo su ke,suna ba ta kulawa matuka,duk da kuwa ta so hana Hajjo amma ta dage,dan haka ta kyale ta tana ta ci musu albarka,fadi ta ke in ban da diya mace wai zai ma ka wannan gatar? Wanda ba su da shi Allah ya ba su. Alhaji Garbati kuwa da Magariba ta yi za ka gan shi kofar gidan su Hajjo,gudun kar ma ya ji shiru ta ce za ta kwana,kullum ta na mita ta ke bin shi zuwa gida,wata rana ta ki fitowa da wuri amma sai ya jira ta ya tisa kyeyar ta zuwa gida.
Bayan an idar da sallah magariba Hajjo zaune tsakar gida tare da Inna,Inna ta sa ta dauko wata fanteka,kayan jarirai ne,riguna uku da wandunan su,sai kuma atamfa da sabulun wanka da na salo,dai kuma kayan yaji da ga can kasa. Inna ta ce Hajjo wannan kayan uwa ne,gashi nan na mi ki na fita hakkin ki na baki tin yanzu kar ki haihu ba na nan. Ido cike da kwalla Hajjo ta ce dan Allah Inna ki dai na magana haka,ki nan mana,ina za ki kuma? Indo da tuni ta zo ta fito daga daki ta na fadin Inna kuwa,ai kin san zancen ta kenan Hajjo. Inna ta murmusa kawai,ta ce da Indo ta dai aje kayan gun ta,hankalin ta zai fi kwanciya. Ana haka sai ga yaro wai Hajjo ta fito in ji Garbati. Hajjo ta ja tsaki. Indo ta ce sai ki tashi ki tafi kafin ya ta jero aike,Inna ta ce aifa! Cikin sirniki kamar ba za ta fita ba take shiryawa,Garbati ya yi aike har yara biyar,sannan Hajjo ta mu su sallama,za ta fita kenan Inna ta ce ya ki nan Hajjo,Hajjo ta dawo ta zauna gaban Inna,Inna ta ruko hannun ta cikin musabaha ta ce diya ta Hajjo,Allah ya mi ki albarka,Allah ya azurta ki da ‘ya’yaye na gari,ya ba ki diya mace mai kamar ki wacce za ta tausaya ta ji kanki kamar yanda ki ke min. Idanun Hajjo cike da kwalla ta ce amen Inna,ameen Allah ya baki lfy. Cikin zolaya Indo ta ce Inna yau kuma har da musabaha..yaro ya kara shigowa wai Hajjo….gani nan dallah! Hajjo ta katse shi kafin ma ya karasa. Inna ta murmusa,ta ce Allah ya sadu mu da alkhairin sa Hajjo,tashi ki bi mijin ki. Hajjo ta saki hannun Inna ta ce amen,sai da safe Inna,ta yiwa Indo sallama ta tafi.
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[6:34pm, 5/15/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
2⃣2⃣
Garbati na ma ta mitar ta jirga shi ta ki fitowa ta ma sa shiru,gaba daya ji ta ke ba ta jin dadi,ta rasa me ke damunta. Washagari da asubar fari Mudi ya buga musu gida,ya zo yayi kiran Alhaji Baso,Hajjo na bacci ba ta ma san an yi hakan ba. Da tashi sallah ta ga Garbati ba ya nan tai ta mamaki,yau wata rana Garbati an tashi sallar asuba.
Gari yayi dan haske ta fara aikace aikacen ta sai ga Garbati ya dawo,biye da shi Mudi ne,gaba daya a rikice ya ke,ganin sa gaban Hajjo ya fadi,ta daure ta ce maraba da Mudi,fuska cike da damuwa ya ce Hajjo shirya mu je gida jikin Inna yayi tsanani…..wayyo Allah Inna ta na shiga uku na lalace!!!!! Ihun da ta sa kenan! Ihun na ta ne ya fito da su Iyalle da Kande daga daki dake da ma su sun san halin da ake ciki,Hajjon ce dai ba a fadawa ba.
Ke dallah ba na san shashanci! Wani abu na ce ya sami Innar? Za ki sa fa na fasa tafiya da ke idan hauka za ki min!!! Hajjo ta ruke bakin ta tana fadin na yi shiru,wlh na yi shiru dan Allah kai ni wajan Inna ta! Garbati ne ya dauko ma ta mayafin ta,su Iyalle ma sai ba ta baki suke,su ka kama hanyar gidan su Hajjo.
Ko da su ka Isa Hajjo ta ga Jama’a a kofar gida,wasu suna alwala,sai ta kara fasa kuka,Mudi ya ja hannun ta ya na fadin kar fa ki yiwa kan ki illa,ki yiwa mutane shiru Hajjo,shigar su gidan ta kara ganin mata a tsakar gida,ta ns shirin faduwa Mudi ya ruko ta,dakin Inna ya shige da ita.
An yi mata sutura dama Hajjon ake jira su yi sallama a tafi da ita,tsakar dakin ta ke kwance,Indo zaune gaban ta,hawaye na kwaranya. Mudi ya karaso da Hajjo gaban gawar Inna ya ce ga Inna nan ki ma ta addua ba kuka ba….Hajjo ta yanki jiki za ta fadi,Mudi ya ruko ta,nan jikin shi ta zube sumammiya.
Sai bayan da aka kai Inna aka dawo Hajjo ta farfado,gaba daya idanun ta sun kafe ta ma kasa kuka,sai dai surutai kamar wacce ta fara zarewa. Gidan na su tai ta kwana,randa Inna ta yi uku Garbati ya ce ta dawo gida,su Mudi su ka ba shi hakuri,su ka ce ya bari a yi bakwai tin da aka yi rasuwa Hajjo ba ta sami cikakkiyar lfy ba. Bayan da zai yi ya hakura,amma dan an fi karfin shi ba dan ya na so ba.
Ranar da aka yi bakwai Hajjo ta tashi da naguda,ta sha wahala matuka har sai da aka fara shirin kai ta asibitin gwamnati da ke gari sai kuma Allah ya sauke ta,ta silbo diyar ta mace,sai dai ta karu sosai sanadiyyar girman yarinyar,Fara ce ga tsayi ga jiki kamar dai Garbati,amma kuma fuskar ta Hajjo ce sak,kamar ta yi kaki ta tofar….
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[7
[16/10 21:46] .: 7:11pm, 5/15/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
2⃣3⃣
Unguwar zoma ta ce da su Indo da Hajjo ta sami kanta sosai sai su kai ta asibiti a ma ta dinki,suka ce toh,ga koshi ga kwanan yunwa,an rasa Inna an kuma sami karuwa. Hajjo zaune,ta na ta kuka dan tin da Inna ta rasu ba ta yi kukan ba sai yanzu,dan haka sai su ka barta ta yi mai isar ta,dama dai sun damu da rashin kukan na ta. Ta yi ta koshi,sai ajiyar zuciya ta ke,kanwar Inna ta fara ma ta nasiha na da ta dangana,Allah da ya bada Inna shi ya karbe ta,ya kuma ba ta wata diyar mace. Da haka Hajjo ta yi shiru,jaririyar ta na ta tsala ihu,aka ce ta ba ta nono mana,Hajjo ta ki saboda da yarinyar ta kama sha cikin ta ke ma ta ciwo,sai da aka sa ta gaba,ta na kuka haka ta ke shayar da diyar ta ta. Duk wannan abun da ake Garbati be tako kafa ya zo ba,kayan da ke jikin jinjirar ma kayan da Inna ta bawa Hajjo ana gobe za ta rasu ne. Shiru shiru an aika be zo ba,da Mudi ya ga haka ya ce da Hajjo wani suna su Hajjon su ka yanke za a sawa diyar ta su ne? Dan ya kamata a yi ma ta huduba Hajjo ta ce ba su taba zancen ba,amma dan Allah ya ma ta da sunan Inna,Ameena ta san shi ma ba zai ki ba,Mudi ya ce toh a kawo masa yarinyar,ya ma ta huduba da Ameenatu,Inna ta tafi Inna ta dawo.
Washagari bayan Hajjo ta yi wanka ta shirya,ta yi tsaf da ita,ta ciko sosai kamar ba Hajjo ba. Indo ce ke wa jariyar wanka,ta ce Hajjo? Hajjo ta ce ummm kin san kuwa jiya ki ka cika shekara gomasha uku? Hajjo ta gyada kai kawai ba tare da ta ce komai ba. Har aka gamawa yarinyar wanka sai cilla ihu take,dake yarinyar akwai kuka. Indo ta daura ta kan cinyar Hajjo,ta ce ki daure ki ba ta tasha Hajjo,Hajjo ta yamutsa fuska ta ce wlh da ta fara cikina ciwo ya ke,gashi ba ta koshi,Indo ta ce ki yi hakuri Hajjo,ya za ki yi tin da kin haifa dole ki shayar ai,daure ki ba ta. Hajjo ta turo baki ta sa ma ta nonan a baki,caraf diyar Garbati ta karbe ta fara sha kamar wacce aka koya ma ta.
Sai da yamma su Iyalle su ka zo,sun zo da sakon Garbati na a yiwa yarinya huduba da suna Katime,sunan Iyalle. Indo ce ta mu su bayani cikin ba da hakuri akan yarinya da aka ji shiru an ma ta huduba da suna Ameena,an yi tunanin hakan zai yi daidai da ra’ayin Garbati. Toh ai ba komai,Allah ya jikan Ameenatun,amsar da Iyalle ta bayar kenan,amma sai da fuskar ta ta nuna ba a mu su daidai ba,dan haka ba su jima ba su ka tafi.
Har suna ya zagayo ba Garbati ba alamarsa,ko ragon suna be aiko ba. Mudi da Indo da Ayuba sun yi cirko cirko a tsakar gida,ana tunanin ko bin sawun Garbati Baba ya shigo ya ce ya aka yi cirko cirko haka?lfy?
Mudi ne mai bayanin,ya ce Baba muna tattaunawa ne akan lamarin Hajjo,Allah ya waye mu suna amma mai gidan na ta shiru haka yan uwansa,ko rago ba su turo ba bare kuma ayi batun abincin da za a bawa yan suna. Baba yace yo ba ku ku ka jawo ba,ai na zuba mu ku ido ne kawai,yaro tin da aka yi uku da rasuwar Ameenatu ya ce mai dakin sa ta koma,ku ka kiya,ta haihu ku ka ma ta huduba da sunan da kuka so ba tare da kun jira shi ba,yanzu ga irin ta nan,sai kusan yanda za ku yi dan na sadu da Alhaji Baso dazu ya ke fada min an yiwa Garbati ba daidai ba dan haka ya ce tin da ku ka rada sunan ku siyi ragon suna,kuma kwayar shinkafa tawa ban yarda a dafa dan sunan asara ba,kun dai ji na fada mu ku! Kuma gobe goben nan Hajjo za ta koma dakin mijin ta,na gaji da hidama da ita da diyar ta ai ta cinye ma hatsi!Ya shige ciki ya barsu suna kallan kallo,Indo ta ce toh kun ji fa,yaya kenan? Ko dai cikin ragunan da maigida na ya ke kiwo za mu ranci guda a yanka? Ayuba ya ce zai ba mu ne? Indo ta ce mai zai hana,ai Sani be da matsala. Mudi ya ce ai Indo Mijin na ki ne balalle a same shi ba. Ta ce ya na gida,be tafi kanan ba tukun,ku yi azama ku riske shi. Su ka ce toh su ka tafi,ita kuma Indo ta koma daki wajan Hajjon da tun safe ta ke kuka,ga Ameena da take kira Inna sam ba ta barin ta ta sami bacci da daddare. Ta ce Hajjo ki rufa min asiri dan Allah ki bar kukan nan haka. Mu fatan mu a samu a yi yankar nan,na so ace an mi ki wannan dinkin kafin ki koma gidan ki amma Baba ya ce gobe za ki koma,saboda haka bayan kin koma din ma samu mu je asibiti a mi ki kin ji ko? Komai zai wuce,yanzu Ina Inna? Gaba shi yau mun wayi gari ba ita ba,haka duk za mu wuce komai mai wucewa ne ai.
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[7:16pm, 5/15/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
2⃣4⃣
Hajjo uhum kawai take iya cewa,ita kadai ta san abunda ta ke ji. Ba a jima ba sai ga Mudi da rago,har da shinkafa kwana biyar Sani mijin Indo ya hada su da shi. Ba bata lokaci aka yi yanka,Yan uwa sun ka fara zuwa,da taimakon dangi aka sarrafa shinkafar zuwa dafa duka,aka hada kunun zaki…a haka da faci faci aka yi suna aka gama da ke ba wani taro aka yi ba,dama ga babu ga kuma rasuwar Inna.
Washagari Hajjo ta koma gidan ta,Mairo da Kande kadai ke hidima da ita,su kan daukar ma ta Innar na ta sosai,ita kuma Iyalle bakin cikin ta na an ki a sa sunan ta,an sa na Inna. Shiko Garbati bakin cikin sa da yawa,gashi Hajjo ta tafi ta ki dawowa sai da ta haihu,gashi an sa sunan da ba shi ya ce a sa ba,gashi diyar ta Hajjo kukan dare gare ta,ta hana sa bacci,dan haka ko kallan inda ta ke be taba yi ba bare ya dauke ta,ko tsinke be taba siyawa yarinyar ba kayan barka na yan uwa da abokan arziki ake sa ma ta. A haka Hajjo ta yi arba’in.
Da la’asar ta na sallah,Mairo ta goya ma ta Inna, kwatsam sai ga Garbati ya shigo,ganin Hajjon ta na sallah sai ya fara bala’i,kut! Ke Hajjo da ma munafunta ta ki ke kin fara sallah ba ki fada min ba? Munafukar aure! Sallah ta ke amma sai da gaban ta ya fadi,ta dade da fara sallah,amma kiyayyar da ta kewa Garbati ya sa tai ta buye ma sa,da ke shi din ma ba zama ya ke ba,yanzun ma dubun ta ne ya cika. Ta tsora kwarai,ji take kamar tai ta sallah har illa mashaAllah. Garbati ya sami waje ya zauna ya ce toh sai ki idar ki bani hakki na,dan wlh bazan jira dare yayi ba,munafuka kawai!!
Badan gaban Allah ta ke ba da taki sallma,amma bayanda za ta yi dole ta yi sallamar. Ta ce yau fa na fara sallar,dama zan fada ma…ya ce na ji toh gyara! Hajjo ta ce ka jira mana dare yayi,ya ce ban jira,ya tashi ya sakace kofa,yayi wulgi da babbar riga ya ce maza ki gyara na ce Hajjo! Yanda ya ke so haka aka yi,amma fa ko da ya gama biyan bukatar sa,sai labari ya canza.
Rai bace ya ke kallan ta,murya a sama ya ce Hajjo! Wai ya na ji haka kamar kofar gari? Yaya haka ne? Hajjo ta mayar da hijabin ta,ta takure gefe guda. Ya ce ke Hajjo ba da ke na ke magana ba! Ya na ji haka ne! Murya kasa kasa Hajjo ta ce dama da na haifi Inna ne aka ce na karu sai an min din ki….kin karu? Ana nufin kin yage za a dinke ki? Kai diya mace ta na yagewa ana dinke ta kamar tsumma! Wai wannan yar mitsilar abar da ki ka haifa ita ta maida ki sai ka ce kofar gari? Caf da sake kuwa! Wannan ai ba zan iya ba,wlh bazan iya zama da mace wankakekiya haka ba!!! Sauki zan yi! Ke wlh na ma sauki,ki hade kayan ki na sauki saki daya……!
DEDICATED to The WOmen Of Virtur💁👰🙋
[7/25, 9:36 AM] Salmah Ateeku: [7:17pm, 5/18/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
2⃣5⃣
Hajjo ta daga ido ta kalli Garbati,maganar ta sa ce ta ma ta ba za ta. Ta ce kunne na ke zagi ko kuwa dai sakin na ji? Garbati ya na hura hanci ya ce eh sauki na yi kofar gari! Hada na ki ya na naki,ki hada har