Showing 60001 words to 63000 words out of 67328 words
Chapter 21 - Diya Mace Book Complete by khadija sidi .txt
ga ya sake salo sai ta koma shirin kwacewa,gaba daya tsoran abunda ya ke so take,ba ta ji dadin rayuwar ta na da ba gani take kamar maimaitawa za a yi duk da kuwa salon Garbati da na Khalid akwai bambamci,kamar duhu da haske ne. Shi kuwa Khalid ba ya ji ya ba ya gani,yayi lallami yayi lallami amma Hajjo ta ki amince ma sa,sai kawai ya bi san ransa amma ta lallami da lumana,cike da so da kulawa,a daren Hajjo ta tabbata matar Khalid. Manne da shi ta yi bacci,ba ita tashi ba sai da asuba,dan ta ma so ta makara. Ta duba gefanta ba Khalid,sai kuma abunda ya faru jiya ya dawo ma ta,yanda yay ta lallaba ta sannu a hankali,ba shakka shi dai kam Garbati ya tabbata bagidaje,ashe dai ita ba aure ta yi ba. Bayan ta yi wanka,ta idar da sallah sai ga Khalid ya dawo,ta yi saurin kasa da idon ta dan bala’in kunyar sa take ji. Ganin haka sai ma ya dauko ta cak ya aje bisa gado,ta ce ni fa ban komawa bacci,ya ce ni ina komawa,ai yau asabar ba aiki,pls ko ba za ki yi ba ki kwanta,ina son ki a kusa,I jst want to hold you,kan Hajjo ta tanka tuni ya janyo ta jikin sa,ya cire hijab din ta ya aje gefe. Kamar yanda ya ce din,he jst kissed nd hold her,kan kace me tuni bacci ya sake sace su. Sai wajen 8 Hajjo ta tashi,a hankali dan kar ta tada shi ta zame jikin ta. Ta shige toilet ta yiwo wanka,sauri sauri amma kuma a hankali ta shirya cikin kananan kaya rigar ruwan hoda da wando da ya bi jikin ta amma ba sosai ba shi kuma blue. Ta sanya wata yar hular ta,kafar ta sanye da takalmin ta flat ruwan hoda ta fito ta shiga kitchen. Nan ta tsaya tunanin abun dafawa dan ta makara,ba ta so ta bar Neena da yunwa. Dankali ta dauko Irish ta na barewa,kusan minti goma sha biyar kan aikin tana yi tana tunanin rayuwar da ta shiga jiya,saban rayuwa mai dadi,ta na yankawa ta ji anyi hugn din ta ta baya,har sai da ta dan tsorata.
Fuskarshi ya kwantar bisa kafadar ta ya ce ni ne Suuuger,duk duniya ma wa ya isa ya tabaki in ba Khalid ba,yayi kissing wuyan ta,I love you suger…murmushi kawai ta yi,tare da fadin aiki na ke,pls ka kyale ni. Ya ba za ki ce you love me to ba? Thou na san you do. Murmushi Hajjo ta yi,dax Khalid for her. Ta ce toh tin da ka sani ba sai na fada ba,dan Allah ka sake ni kar fa Neena ko mamanta su shigo mu ji kunya…ya ce ba zan sake ki ba sai kin ce you love me too. Hajjo ta ce i love you tooo..kamar daga sama su ka ji muryar Hauwa na fadin amma dai kun san ba ku kadai ba ne? Akwai yarinya a gidan A rikece cikin jin kunya Hajjo ta cire jikan ta da ga jikin Khalid,shi kuwa Khalid ko a jikin sa ya juyo ya na kallan Hauwa da idanun ta tuni su ka kada,kishi kararara ya bayyana a idanun ta,ya ce ina manners din ki su ke Hauwa?ba kya iya sallama or atlest ki juya mana kawai ki tafi abun ki! Hauwa ta ce no kai zan tambaya ina manners din ka ya ke? Na zaci nan kitchen ne ba dakin ku ba da zan fara labewa ina sallama,dan kitchen is meant for everyone,har da diyar ku Neeena da ta zo neman brkfast ta gan ku yanda na ganku,ta zo ta fada min,am sure itama ba ta saba ganin haka cikin kitchen ba may b dax y ba ta mu ku sallamar ba,ta zo ta fita ba ku sani ba,musammam ma ni da kai ta tashi ta saba gani,d presence of a co-wife,b it her mother or watever is still unsual to her,be kamata ba,pls ake yin sara ana duban bakin gatari…ta juya ta fice,kunya da takaicin ya rufe Hajjo jin Neena ce ma ashe ta kai maganar..a fusace Khalid ya bi yanta,ba ta kai ga kaiwa falo ba ya janyo ta tare da fadin hw dare you za ki kunya ta ‘yar mutane haka,God Hauwa she is her daughter for crying out loud!ke zai mi ki dadi aka mi ki haka? Toh menene dan na yi hugn din ta? Ba mata ta bace!!
Hawaye na zuba daga idanun ta,ba ta taba tunanin rana irin ta yau za ta tsirga cikin tarihin rayuwar ta ba,ta ga Khalid din ta da idanun ta jikin wata,kuma da bakin sa ya na tuna ma ta Neena ba diyar ta bace,gashi ya na jaddada mata cewa uwar Neenan is his wife. Ta ce yes ba diya ta bace,kuma matar ta ka ce Khalid dan Allah ka kyale ni na wuce. Sakin ta yayi,ta shige ciki da gudu,har zai bita sai kuma ya dakata ya buga hannun a iska tare da fadin ya salam! Hauwa za ta iya zarar da ni!
Ita ko Hajjo kasa cigabawa ta yi da girkin gaba daya,sai da Khalid ya dawo ya ce da ita kar ta damu ya yi magana da Neena,so ba wai wani abu bane. Duk da haka da kyar ta gama brkfast din,amma ranar ba dadi zaman cin abunci,kowa yayi shiri,Khalid ne ya saki jikin sa ya na ta musu hira. Ita Hajjo kunyar Hauwa da diyar ta ce damuwan ta,ta san Hauwa dole ta san yanzu ita da Khalid ar intimate. Ita kuma Hauwa kishi ne damuwan ta,gaba daya ta tsani Hajjo,haka kuma ta fara jin dacin Neena cikin ranta. Ita ko Neena ta manta da komai,brkfst din ta kawai ta ke ci ta gama ta hau kan game,fargaban ta daya Hajjo za ta iya hana ta,ta ce sai dai ta taya ta aiki a kitchen,dax y sam ba ta san zaman Hajjo a gida,takura ne da ita,tai ta sa ta aiki.
Soyayya tsakanin Hajjo da Khalid tai karfi,idan ba ya dakin ta Allah Allah ta ke ya dawo,idan kuma ya dawo ba ta san kwanakin ya kare. Haka shi ma Khalid,ya na jin ta har ransa ko dan kwanciyar hankalin da ya ke samu wajan ta,gaba daya Hauwa ta fara sauya hali,wanda haka ya ke taba daga Khalid din har Neena,hakan kuma ya sa ya ke kwalafacin Hajjo.
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[1
[16/10 22:01] .: 12:54pm, 6/14/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
6⃣6⃣
Mota Khalid ya siyowa Hajjo,ya kuma ware lokacin da ya ke koya mata,nan da nan ta iya da ke Hajjo komai idan za ta koya da gaske ta ke tsayawa ta koya.San da Hajjo ta cika wata hudu sai ga ta da tsintuwa,ta fara laulayi sosai. Ko da Khalid ya lura da hakan,ya kuma tabbatar da burin sa ne ya ciki tuni duniyar sa ta zama sabuwa,Hajiyar sa ya fara fadawa sannan su Jabir da Nabeela. Har gida su ka zo taya sa murna duk da dai suna taka tsantsan saboda Hauwa,shi ya sa ma Nabeela ba ta yawan zuwa wajan Hajjo sai dai Hajjon ta je. Tin da Hauwa ta san da cikin Hajjo gaba daya ta susuce,duniya ta mata zafi,duk da sam Hajjo na gudun duk abunda za ta yi wanda ta san zai motsa zuciyar Hauwa. Zama inda Hauwa ta ke ma dainawa ta yi saboda ta na yawan laulayi ba dadi kar Hauwa ta ga kamar da gangan ta ke,gashi ba ta iya girki,ba ta kuma ta san warin gas ko zaman dining area gagarar ta ya ke,sai dai ta yi zaman ta bangaran ta abun ta. Da fari Hauwa na jurar yi ma ta girki,daga bisani ta dai na,haka kawai ta na yiwa mace girki,ita kuma ta na kwana da miji! Nan ko nima na taya Hauwa kokawa,ba zai sabu ba bindiga a ruwa,ba za a maisheta yar aiki ba. Dan haka ranar girkin Hajjo sai dai a samo abunci gidan Hajiya da ke Hajiyar ba suruka ta ke da Hajjo ba,diya ta ke da ita,ran da ba aiki gidan Hajiyar ta ke zuwa ta wuni,musammam idan ranar girkin ta ne. Khalid na kaffa kaffa da Hajjo,ta sha kwararo ma sa amai a jiki,sai dai ya wanke,hakan kuma be hana shi sake kwantar da ita jikin sa ba,Hajjo dai ta zama yar gata.
Wasa wasa,kuma kwanci tashi,da dadi ba dadi cikin Hajjo ya kai wata tara,yayi girma sosai wane na Neena,gashi ta kumbura kamar wacce aka hura,ya sake ma ta kamanni gaba daya,dama ba tsayi gare ta ba sosai sai ta zama kamar za ta kife idan tana tafiya saboda cikin rinjayar ta yake,Khalid yay ta tsokanar ta wai ta yi muni kamar a yanka a boye wukar. Hauwa kuwa tuni ta bata rawan ta da tsalla,gaba daya Khalid be jin dadin zama da ita,ta dau kishi da bakin ciki ta ji zugan ma su ziga hatta diyar ta ta Neena ta watsar,sam ta dai na nuna ma ta kulawa irin na uwa,hakan na damun yarinyar da Khalid da ma ita kan ta Hajjo,duk da haka Hajjo ba ta janye Neenan ba,ta barta tana addua Allah ya sa Hauwa ta farga ta san abunda ta ke,haka kuma ba ta ga laifin Hauwa ba,after ol ko wace diya mace ta shiga halin da Hauwa ke ciki sai abunda Allah ya yi. Sau dayawa sai ta ki zuwa dauko Neena,mussammam idan Khalid na Abuja,sai dai principal din su Neena ta kira shi ta ce ba a zo daukan ta ba,idan ya kira Hauwa sai ta ce ba ta jin dadi,sai ya kira Hajjo,ta bar aikin da ta ke ta dauko ta,sannan ta koma bakin aikin na ta.
Hajjo na sane ta ki daukan hutu,tafi so sai daf da za ta haihu saboda ta samu ta na motsa jikin na ta sosai. Ranar da ta ke san zuwa aiki na karshe kafin ta fara hutun haihuwar na ta ranar Khalid shi ma ke shiring tafiya Abuja saboda wani meeting da za su yi. Tare su ka shirya da sassafe,ya sanya suit baki,yayi kyau sosai kamar dai bakin baturen na Hajjo,ita kan ta Hajjo ta na alfahari duk sanda ta tuna mijin ta ne. Team din su Hajjo na da wani discussion mai matukar muhimmanci,dan haka a gurguje ta shirya,by 8 za su fara.
Tare su ka fito,su ka tadda Neena zaune a babban falo,Ta gaishe su,Khalid ya ce ya dai? Ina maman ta ki ba ta kai ki makaranta ba har yanzu? Za ki makara ai,ko ma na ce kin makara. Neena ta ce Momma ba ta tashi ba. Ba ta tashi ba?ba ki karya ba ma kenan!,aje briefcase din da ya ruko,kai tsaye bangaran Hauwa ya shiga,a daki zaune kan gadon ta ya tadda ta. Ta ce da shi barka da asuba. Da ga bakin kofa Ya ce yauwa Baby-luv,diyar ki fa ta dade da shiryawa,ke ta ke jira. Ta ce wata diyar tawa kenan?tambayar tata ta bashi mamaki,ya ji kamar an tsaya a baya san,da ya dan waigo sai ga Neena,ashe biyo shi ta yi. Wata diyar ta wa? Kamin shiru? Dawo da kallan sa yayi gare ta,sannan ya ce kina da wata diyar ne da ya wuce Neena? Juya ma sa baya ta yi ta fara ninke mayafi,ita sam ba ta lura tare ya ke da Neenan ba,ta ce no ban da wata diya,ko Neenan ma ba diya ta bace,ga uwar ta can Hajjo ta kai ta,ko na haife ta da zan na dawainiya da ita……? Ta juyo,sai a sannan ta yi ido biyu da Neena da ta karasa shigowa ta tsaya kusa da Khalid,idanun ta cike da hawaye. Baki bude cike da dana sani ta ce Khalid ba ka fada min ba…ban san tare ku ke ba…idanun sa jajur,ya murmusa ya ce no ba sai na fada mi ki ba,abunda ki ka yi kan ki kikayiwa Hauwa. Juyawa yayi ya fice a fusace. Hajjo da ke zaune falo sai ganin shi ta yi ya fito cikin bacin ran da ba ta taba ganin sa ciki ba,ko kallan in da ta ke be yi ba ya nufi bangaran sa. Tashi ta yi da kyar da niyar bin sa,sai ta jiyo muryar Hauwa na kira Neena! Neena! Ga mamakin ta sai ga Neenan ta fito a guje ta na kuka,za ta shige Hajjo,Hajjo ta janyo ta baya,hakan yayi daidai da fitowar Hauwa,ta yi turus ta tsaya,ita ma hawaye ne fal fuskar ta. Cike da bacin rai Hajjo ta tsawatarwa Neena,ta ce ina za ki? Ba ki jin Mahaifiyar ki na kiran ki!! Jikin Hauwa ya dada sanyi. Neena na kuka ta ce ki yi hakuri,amma ba mahaifiya ta ba ce,ke da ban dauka a matsayin uwa ba sai gashi ke ce uwa ta,ta fada ita ta fada da bakin ta…..a gajiye Hajjo ta saki Neena,maganar Neena ta gajiyar da ita kwarai.
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[7/25, 6:15 PM] Salmah Ateeku: [1:14pm, 6/14/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
6⃣7⃣
Da gudu Neena ta shige bangaran Hajjo. Hajjo ta juya za ta bi ta,sai kuma ta tsaya,ta ma rasa ya za ta yi,Khalid za ta bi ko Neena? Gashi sai dada makara ta ke,ta juyo ta ce da Hauwa,Hauwa zan mi ki magana a matsayi na na diya mace,zan baki shawara a matsayin diya mace. Na san halin da ki ke ciki,amma karya ne na ce na san yanda ki ke ji,i undstnd ur situation,amma you pushing dem away,kina pushing mijin da ke son ki matuka,you pushing him to the wall,tura idan ta kai bango ba ta bullewa,you ar letn him go,d more u push him,d more he get close to me,nd am sorry to say dis the more i get to knw him well,d more i get to love him. Yanda ya ke san ki duk da kuntata mi shi da ki ke ya sa na san waye mijin ki,kuma na kara respectn din shi! Haka diyar ki,duk duniya ba wacce ta ke kira Momma,ta ke kira uwa sai ke,ba kuma wai dan ba na nan ba ne,ko ba na san ta,ina nan da rai na,ina kuma san ta,amma saboda compassion irin na diya mace,na runtse ido na,na danne zuciya ta,i let u guys b,ba ma sharing din ta na ke da ke ba,i overly let her b urs,ta na san ki wit oll passion na diya ga mahaifiyar ta,amma me u jst pushed her away. Wake up nd hold urslf,ko wani dan adam da kaddarar rayuwar sa Hauwa,bare kuma kina diya mace,it is part of ur destiny,jst take lyf d way it is,Allah be cutar da bawan sa,sai dai bawa ya cuci kansa…dan takaici Hauwa kasa magana ta yi,har Hajjo ta juya ta nufi bangaran ta,kai tsaye dakin ta ta nufa,jin shi a rufe ya tabbatar ma ta Neena na ciki,tai tai ta bude,amma ta ki,kukan ta kawai ta ke ji,sai kawai ta juyo,ta haye sama bangaran Khalid. Hauwa ma juyawa ta yi ta shige na ta bangaran cike da da na sani.
Ya na tsaye hannu cikin aljuhu gaban window,idanun sa na kallan waje,gaba daya hankalin sa be wajan,ya ji an taba shi,ya saki ajiyar zuciya,duk da be juya ba ya san wacece. Ta ce am sorry,ka yi hakuri,undstnd her,try to undstnd,thou ba lalle ka fahimta sosai ba,diya mace ce kawai za ta gane,amma itama ba haka ta ke so ba,ba san ran ta bane,shez tyt,shez emotionally disturbed,Khalid ya ce ban taba canza ma ta ba,Allah shi ne sheda ta. Hajjo ta ce na sani,itama ba a san ranta ta canza ba,she need you! Juyowa yayi ya ruko hannun Hajjo,tare da fadin no i need you,i need you Hajara more dan ever….Hajjo ta girgiza kai,ta ce nd we need ur wife more,we need each other to survive,i need her Khalid,ita ce mahaifiyar diya ta,you need her,am a busy woman,dole za ta zama part of ur children’s lyf,nd she need us,we ar fmly. Khalid ya girgiza kai,ya ce na so Hauwa,ina san Hauwa ta kasa ganewa. Wani irin kishi ne ya tasowa Hajjo,ta yi saurin kauda shi,amma duk da haka Khalid sai da ga gani,ya saurin cewa don’t get me wrong Suger. Dariya Hajjo ta yi,ta ce haba worry nt,na fahimce ka,u ar tryn to make a point,bare kuma idan ba ka so Hauwa ba ai sai Allah ya tambaye ka. Hugn din ta yayi tare da fadin u ar ao diffrnt,ya ba zan so ki ba Hajara? Ta na murmushi ta ce nd i u. Maza ka je wajan diyar ka,ta rufe kanta a daki sai ka fito mu tafi na aje ka kar ka yi missing flight na samu ni ma na wuce hosptal. Hannun ta cikin na sa su ka fito,ya na fadin ya fasa zuwa Abujan yau,zai daga meetn din dan ya kula da Neena,tai tafiyar ta kawai.
Hauwa kuwa gida ta tafi,ta na kuka ta fadawa Mahaifiyar ta abunda ya faru. Mahaifiyar ta ta ta ce ai ga irin ta,za ki yi biyu babu,kishiyar ta ki da ki ke tinkaho kin fita komai gashi ta zo ta fiki komai ai yanzu tsabar rashin hakuri,ita ki ka san menene na ta kaddarar rayuwar,kawai ganin ta ki ke amma ki ka san yanda rayuwar ta take? Ke kuma ga uwa ga uba,ga gata ga arziki,ga miji mai san ki so na gaske,ba ki haihu ba amma Allah ya baki soyayyar diyar wata,ki ka yi watsi damar ki. Ta na kuka ta ce yanzu ya zan yi? Ta ce ya za ki yi kuwa,ki je ki nemi yafiyar mijin ki,ku samu ku sasan ta. Da wannan kudirin Ta koma gidan ta.
Da dadare Hajjo ta fito da niyar zuwa wajan Khalid,sai ga Hauwa ta ci ado mai kayatarwa,wasu irin kaya ta sa wanda su ka kama ta ma su jan hankalin mai kallo,ta yi kyau kamar yar tsana,itama din wajan Khalid din za ta,ganin Hajjo sai ta tsaya. Ganin yanda ta yi kyau sai da zuciyar Hajjo ta motsa,amma a zahiri murmushi ta yi,ta gyada ma ta kai alamar go ahead,ni bara na koma. Ita ma Hauwa murmushi ta sakar ma ta sannan ta haye bangaran Khalid. Zuciyar ta na bugawa Hajjo ta koma na ta bangaran. Dakin ta ta shiga ta na ambaton sunan Allah dan