Showing 48001 words to 51000 words out of 67328 words

Chapter 17 - Diya Mace Book Complete by khadija sidi .txt

ya iya zama da ita tsahon shekarunnan ba haihuwa,dan ya ce zai kara sai ta tada hankalin ta,ita ba mai ba shi shawarar ya kara ba ne! Yayyar Hauwa mai suna Zeena wacce bayan iyayen Hauwa sun gama ma ta fada ta zo,tare da kanan ta ne su ka ta zuga Hauwa,wai wlh ta bari ya auri yar aikin gidan su ta fado,duk matan da ke garin nan in ma kishi za su yi auro ma ta class din ta mana! Hauwa ta ce da ta ke mai aiki,yanzu fa doctor ce. Zeena ta ce sai me? Kowa dai ya san asalin ta,turan gini ran zane! Ke ce ma kin dau diya kin manne kamar ta ki! Yanzu kya gane kuran ki! Daya daga cikin kannan ta su ka ta ce Hajjon mummana ma da ita! Dayar ta ce ai kamar ta daya da Neena! Wlh kar ki kara kawo ma na yarinyar gidan nan. Ita kuwa Hauwa har lokacin jin Neena ta ke har ranta,dan haka ta ce ah ah fa,ba ruwan yarinya,ku dai taya ni bakin ciki amma kar ku kyarar min Neena! Hada baki su ka yi su ka ja tsaki. Mahaifiyar Hauwa ta shigo,da ke ta dan cinci maganar,ta ce maza ki biye mu su ki yi biyu babu,su zuga ki Neenan ma ki rasa,kin dai ji shawarar da mu ka baki! Hauwa ta ce uhum.
Khalid da ya tashi ya ga Hauwa ba ta nan ya san za a yi haka. Sai cewa yayi da Neena maman na ta ta je gida ta yiwa dady sallama dan ba ya so ta gane ta yi abunda ba ta taba yi ba,wato yaji,shi zai kai ta makaranta,da ke Hauwa ke kai ta kulli yaumin,ko ya ce zai kai ta hanawa ta ke. Duk da hakan ya yiwa Neena wani iri,sai ta amsa da toh. Da ya sauke ta makarantar ya biya ta gidan su Hauwa. Iyayen ta su ka ce ta fito ta bi mijin ta,har da bashi hakuri,tare da mu su dan nasiha. A hanyar komawan su gida ba wanda ya ce da dan uwan sa kala. Sai da su ka shiga gida,Hauwa ta ce da Khalid me ya sa Hajjo? Me ya sa za ka zabi Hajjo maimakon wacce ta isa,na san yes isasshiya ce zan iya kira da sunan kishiya?yayi mamakin maganar na ta,dan shi zaman sa da Hauwa ya san mace ce wacce ba ruwanta da arziki ko rashin arzikin mutum,mace ce mai saukin kai,amma kishi na neman sauya ma ta hanya. Murmushi kawai yayi ya ce ki yi hakuri Hauwa. Zai wuce ta shagaban sa,ta ce me ya sa ita? San ta ka ke? Ya girgiza kai,alamar ah ah,ya ce ke kadai na ke so. Ta ce toh ka sake wata! Ya ce ba zan iya ba! Ta ce y her? Ya ce ita zuciya ta ta zaba,ki yi hakuri Hauwa. Yayi saurin shige ta ya shiga bangaran sa gudun ganin saukar hawayen ta. Nan ta zube ta na kuka,ta na fadin wlh san ta ya ke! Mayaudari! Makaryaci! Santa ya ke wlh!!!nan ta karaci kukan ta ta koshi. Jin Khalid shiru ta san ya bi ta kofar baya ya fice,ita ma ta lallaba ta shige dakin ta ta kwanta,tuni ta fita da ga hayyacin ta.
Da azahar ta na tunanin Neena a makaranta dan ba ta ji za ta iya fita,sai ga ta ta shigo dakin sanye da kayan makarantar ta,da alama dawowar ta kenan. Ta ce Momma sannu da gida,ya ba ki zo dauka na ba sai dady? Ba ki da lfy? Ta zauna gaban ta kamar za ta shige cikin ta. Hauwa ta kau da kai ta na ban da lfy,Neena ta yi saurin ruko hannun ta,Dady ya kai ki asibiti? Cikin ranta cewa ta yi ai shi ne asibitin tinda shi ya daura min,azahiri kuma hawaye ne su ka fara zuba daga idanun ta,ganin haka Neena ta rude,tuni ta fara kuka ita ma,ta na pls Momma ki yi shiru na kira Dady mu je hosptal,bara na kira Uncle Jabir. Hauwa na hawaye ta ce rashin lfy na ba na hosptal ba ne Neena,ki min addua kawai dan na kusa zaucewa,aure Dadyn ki zai kara… a razane ta ce aure? Me ya sa? Ya dai na san mu? Hauwa ta ce ki tambaye shi da kan ki. Ai kuwa sai ta tashi fuuuuu ta fice,a falon sa ta tadda shi,ganin yanda ta shigo ga fuska shabe shabe da hawaye sai ya tsuke fuska,ya ce ya dai? Ta dan yi kasa da murya ta ce Dady wai za ka kara aure? Ya ce haka ne. Ta ce Dady saboda me ya sa? Ya ce kin yi kankanta,ba za ki fahimce ni ba yanzu. Ta ce ka dai na san mu ne? Ya ce na fi san ku akan kowa…ta ce plss Dady idan ka na san mu kar ka yi. Ba ta taba rokansa abu ya ki ba,amma wannan karan ta zo da maganar da ba wacce ta isa fadan ta ya amince idan ba Hajiyar sa ba. Ya ce ki yi hakuri Neena,it is for your own gud,dukkan ku,ina san ku,amma dole sai na yi. Idanun ta cike da kwalla,yayi mamakin yanda yar yarinya wai itama ta san ta ya wacce ta dauka mahaifiyar ta kishi,kai kishin mata daban ya ke. Juyawa ta yi za ta koma,sai kuma ta dawo ta ce wa za ka aura Dady? Ba tare da ya ji komai cikin ran sa ya ce Hajara ce wacce ake kira Hajjo,ta ce Anty Hajjo ta gidan Hajiya? Ya ce eh. Ta ce Momma ba ta so,Allah ya sa ka fasa Dady. Kallan ta ya ke kawai,Hajjo kawai a tsaye,da ta san matsayin Hajjo a rayuwar ta,da ta fi kowa farin ciki,amma a sannu za ta fahimta,har yanzu yarinya ce. Sai da ta fice,sannan ya koma ya kishingida.
Ya shedawa Hajiya,har ta fadawa yayye da kannen Baban maza,su za su yi komai har sa rana da kai lefe,lokaci ya canja,ya fi san mazan su kai dan a rage bidi’a.
Sati biyu su ka dauka kafin Sani ya mu su jagora zuwa wajan Baba,da ke dama Baban ya san Khalid sosai,sai gashi har da gayyato yayan sa da kuma Alhaji Baso baban Garbati,duk da kuwa ba wai warkewa yayi garau ba,jikin na sa na tashi lokaci lokaci,karfin hali ya ke kawai. Lokaci guda su ka bada kudin na gani ina so,ga kuma kayan sa rana da lefe,su ka ce wata uku su ke so a sa,ba mu su su Baba su ka amince,musamman yayan Baba da ya gaji da surutan jama’a wai kanin sa ya bar yarinya ta lalace ta zama yar boko ta ki aure. Lefe ma na gani na fada da Khalid ya hada cikin gaggawa su ka sauke su gaban su Baba. Su Baba sun yi mamakin yawan akwaitinan,ko da bakin su ka tafi bayan an basu tukwicin su daga kudin da su ka kawo bisa al’ada tuni magana ya fara zagaye gari,an kawo laifen birni gidan Alhaji Mamman,an sauke arziki gidan Alhaji Mamaman. Shiko Baba da ya san wacece Hajjo da irin rayuwar da ta yi a baya ya san kadan ma ya gani daga sakayyar alkhairi da Allah ke yiwa Hajjo.
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[7/25, 6:05 PM] Salmah Ateeku: [12:17am, 6/11/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
5⃣5⃣
Hajjo ta na zaune tsakar gida,ta cika ta yi fam,fashewa ne kawai ba ta yi ba. Sai ga Indo ta shigo ta na guda,wato ta gano kayan Hajjo kenan,har da takawa,ta na rai dai,rai dai,rai dai! Ina ma Inna ta na raye ta ga arzikin autar ta,Hajjo? Tin da na ke ban taba ganin kaya,kaya dai irin na akwatin lefan ki ba!anjiman nan ma Baba ya ce a zo a kwasa a kawo mi ki idan Sani ya sami lokaci. Ko a jikin ta,Hajjo ta ce hmmm. Indo ta kara da wata uku aka sanya ranar ma…..nan Hajjo ta fusata,ta ce na fasa auren na shi! Indo ta ce iyye? Hajjo ta ce eh na fasa! Indo ta na tafa hannu ta ce ku ga wacce ba a yiwa abun arziki dangin gidan maza! Akan wani dalili? Dan an sa rana wata uku? Hajjo ta ce haba Indo,ki na fa gani tun da na amince da auren mutumin nan be sa kafa ya tako ya zo gidan nan ba,ko waya ma be min ba,ba shawara ta ba komai an tashi an samin aure wata uku,na san Baba zai iya sa awa uku ma ba wata uku ba tinda dama ba kauna ta ya ke ba,amma shi ba sai ya tambayi shawara ta ba!!
Indo ta ce gaskiya be kyauta ba,ai na zaci kun yi shawara ne,amma ki ma sa uziri be kai ga a fasa aure ba,ki yi kiran sa mana….Allah ya sauwake! Hajjo ta katse ta,wlh ba zan kira shi ba Indo! Indo ta ce toh sai ki yi hakuri tin da ke ma na ki jin kan ya hana ki neme shi,maganar fasa aure babu…ta na magana ta shige ciki ta bar Hajjo na ta faman kwafa.
Khalid kuwa Hauwa ce ta ke gasa ma sa gurasa danya a hannu,gaba daya ta birkita shi,ta hana shi kwanciyar hankali,tashin hankalin yau da ban na gobe da ban. Har ya gwammaci zaman Abuja akan kano,ba dan ya na so ba sai dan ya ba ta lokaci ya yi nesa da ita ko ta huce. Idan ya zo kano shirye shiryen auren sa ya kai shi ko kuma ya leka site din sa ne,inda ake dankara ma sa hadadden gidan sa da ya yi designing da kwakwalwar sa dan zaman mata biyu. Hajjo na ransa kwarai,ya na son zuwa ya ganta,amma ba dama saboda abubuwa sun cude ma sa,gashi ya daga waya yay ta kiran ta,amma ba a dagawa,ashe wayar ta ta faduwa ta yi. Har ya yi fushi ya ce shi ma ya dai na kiran na ta,ta zo gidan sa sa na gaisawa gaba daya. In dan zai aika ma ta da sako Sani kawai ya ke bawa,idan aka kai ma ta ta ki karba,sai Sani da Indo sun ma ta ca ta ke hakura.
Ana saura wata guda biki,su Doc Hussaina da yan uwanta likitoci aka kawowa Hajjo kayan gyara,su cikwaidi,zuman mata,tsumi har da turarukan tsugunno. Doc Hussaina ta ce matso nan ki ji diya ta,dan ni fa Hajara diya na ke da ke ba abokiyar aiki ba. Cikin jin kunya ta matsa kusa da ita,sauran matan ma matsowa su ka yi dan sun san Doc Hussaina ba da ga nan ba. Ta gyara murya ta ce Hajara kin shirya yin aure kin shirya zaman aure? Hajjo ta yi shiru,Doc Hussaina ta ce amsa min mana. Hajjo ta gyada kai alamar eh. Ta ce toh saurare ni da kyau,auren dai kin taba yi,amma ki sani wanda ki ka yi da da na yanzu ba daya ba ne,da bambamci,da ba ki san ciwan kan ki ba,yanzu kuwa kin san wacece ke,kuma kin san wa za ki aura,toh fa Hajara sai kin yi hakuri,dan hakuri shi ke zaunar da ko wace diya mace gidan mijin ta,Hajara da ba hakuri da aure dayawa tuni ya mutu,ki yi hakuri,ki toshe kunnuwan ki,ki kuma runtse idanun ki,ki sai ta harshen ki,ki ji ki ji,Hajara ki gani ki ki gani,kar ya hau ki hau,idan ya hau,shafawa zuciyar ki salama ta hanyar ambaton ubangiji,ki tuna Allah ki ke bautawa,ba wai dan shi wanda ya aje ki gidan na sa za ki yi ba,sai ki ga ke kin sauko,da iyaye ma sai an yi hakurin zama bare wani can da ya ganki da hakoran ki ras da wayan ki. Sauran su ka ce ba shakka. Doc Hussaina ta ce kin ga watannin farko na aure,nan su ke fara nuna isa,su a lalle sai sun gwada wannan ikon da Allah ya ba su kan mace tin da ta zama mallakin su,ke kuma daure ki gwada wannan sallamawar da Allah ya yassare mi ki,kwantar da kai,ba komai ba shi girman sa,girmama shi,yi ma sa ladabi da biyayya muddin be wuce gona da iri ba,kar ki yarda ki yi abunda zai rai na ki,duk da ba ke bace matar sa ta farko,dole da tambiyar uwar gida zai tafiyar da ke,da kin ga abunda be dace ba a musulunce da dabi’ance gyara ma sa a dabarance. Kar ki taba yarda wai kin zama daya da miji ki saki jiki,ki na zama anyhw,idan an yi abun dariya ki saki baki ki ta dariya kamar shashasha! Ah ah Hajara raini ya ke kawowa,wlh ba ko wani irin sakin jiki za ki yi da shi ba,kar ki yarda idea din an zama daya ta shiga ran ki,idan ki ka bari ya rai na ki kin shiga uku,ki yi yanda zai yi respectn din ki,ja girman ki ki ja ajin ki,yan da za ki yi reapectn din sa yayi respectn din ki,reapect beget respect. Uwar gidan sa gaba ta ke da ke,ko da kuwa kin girme ta,ita ma ba ta girmanta, tare ki ganta da mijin ta,kar ki yarda daidai da rana daya tunanin ki fitar da ita ya tsurga cikin zuciyar ki,ke ma diya mace,kuma ki na da diya diya mace,ki na da yan uwa,ba za ki so a yi mi ki ko na ki haka ba,ke ma ki yi adalci kar ki yiwa wata,amma fa kar ki yarda ta raina ki. Haka dangin miji,zama da su sai da dabara,zama da su iyawa ne,ki saki jiki a raina ki,ki ja jiki a ce kin ki su,toh sai dai ki ti kaffa kaffa da su,ko uwa tushe daya ku ke sai kin iya takun ki,bare ke zama ki ka taba yi sa su,da kin auri na su toh sun zama dangin miji,tsakanin ki da su kyautatawa,ki bude hannu,ba su,ke dai ba su,kyauta ta na raba ki da su,kar ki zura jiki,kar kuma ki janye jikin ki gaba daya,sama sama,sai wa kanki mutunci kar ki yarda a rai na ki. Tsakanin ki da facalolin ki mutunci,wacce ta ku ta zo daya sai ku yi,wacce ta ku ba ta zo daya ba ruwan ki da ita,kowa ya tsaya matsayin sa,I keep repeatn dis,kar ki yarda a raina ki,kar ki raina kowa. Ki zama mai tsafta,mai kula,mai tattali,mai boye sirri,Hajjo ki rufa sirrin mijin ki,ban da tona sirri,kin san duk abunda ya fita daga bakin ki zuwa kunnan wata ya tashi daga sirri,sirrin ma iri iri ne,akwai na dakin mijin ki,akwai na aljuhun shi,akwai kuma na tsakanin ku,akwai kuma na zamantakewa. Na zamantakewa ne mai wuyan boyewa,yau da gobe dole akwai randa za ki bukaci ki yi sharing abunda ke damun ki akan yanayin zaman auren na ku,ko da kuwa ba solution za a baki ba,ke dai ki fada ki sami sauki,wannan ba laifi idan kin sami wacce za ki yi sharing da ita,toh amma me? Ba kowa za ki fadawa ba,ban da ma iyaye,ke za ki manta,su ba sa mantawa,rukewa su ke a ransu,kawaye ba ko wacce kawa ba ce mai ruke sirri,wasu rashin ruke sirri ma a hilittar su ya ke musammam wacce ta fiya surutu,dan ko gawa za a wanka ba a yi a gaban mai surutu ko wanda ba na ka ba saboda kar ta ga wani abu suruta ya sa ta furta,dan uwa sai kin sami wacce ta ke very close da ke kuma kun saba sharing problems dinki,san samu ki sami mace wacce ta ke ta manyanta,cikin yan uwa ne kawayen mamanki ne,aunties ko ma maman kawar ki,idan kuma kawayen na ki ma akwai ta sirri wacce ki ka aminta da ita shi ma din ba laifi,dan ba a rasa na kwarai,kafin a same su ne aikin,inshaAllahu sai ki ga kin sami mafita asirin ki a rufe…
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[16/10 22:03] .: 2:36am, 6/11/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
5⃣6⃣
Waje yayi shiru,Doc Hussaina ta kara da batun gyara,kin san dai ganyen magarya ko? Hajjo ta gyada kai. Doc Hussaina ta ce toh ki ruke shi,ya na da amfani matuka,musammam da aka hana amfani da soaps da kuma antibacteria,saboda any thing antibacteria is powerful,kuma ur private part is the most delicate part of ur body a matsayin ki na diya mace,wajan akwai flora wanda su ke da amfani,shi kuma antibacteria idan ki ka yi using ba ya iya bambamce tsakanin flora da bacteria,duka ya ke hadawa ya kashe,kin ga anyi ba a yi ba,haka kuma ya na sane mace yawan amfani da su,plus soap wari ma ya ke sawa. Shi ko ganyen magarya na tsaftace jiki kwarai,ya na hana warin gaba,ya na matsi,ya na maganin toilet infections, ya na kuma kara ni’ima,tin daga yanzu ki same she danye ko busasshe, ki fara daurayewa,sannan ki tafasa ki ta ce ki na tsarki da shi da dumin sa ba da sanyi ba. Haka farin almiski,dan kin ga shi ana ma kiransa miski Aisha,wanda ya samo asali daga wajan Nana Aysha Allah ya kara yarda da ita,duk san da ta gama period ta ke amfani da shi,ya na matsi kuma ya dauke wannan karni da gaifi na period. Kin ga ni duk juma’ar duniya na kan yi amfani da shi. Ni yara na da sun fara period na ke koya mu su amfani da ganyen magarya da miski badan komai ba sai dan period kadai kara budurwa ya ke,musamma idan ya na fita da yawan nan,tashi guda ka ji bulum ya sauka,gasu yawancin su suna shiga toilet na makaranta,akwai every possibility na kwasar toilet infection,so da sun gama sai na ba su ganyan magarya su kama ruwa sannan na ba su miski su shafa,ba wai sai sun zo aure ko sun yi ba. Daya daga cikin Docs din ta ce Anty Hussaina tin da kin ce period kadai ya na bude budurwa,ba laifi kenan budurwa ta yi amfani da abun matsai idan ta tashi aure? Doc Hussaina ta ce eh ba wai ba laifi ba ne,kamata ya yi ayi daidai ruwa daidai tsaki,kin ga lokacin mu dake at our tender age ake ma na aure,da yawa dakin mijin mu mu ke fara period,so idan aka tashi mana aure ba wani maganin matsi da mu ke bukata,amma yan matan mu na yanzu an yi period na kusan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login