Showing 63001 words to 66000 words out of 67328 words
Chapter 22 - Diya Mace Book Complete by khadija sidi .txt
kishi ne ya tashi,raban shedan da ke zuciyar ta ya motsa.
Khalid na zaune ya na Allah Allah ya gama hade papers din gaban sa ya je wajan Suger. Jin an bude kofa yayi zatan ita ce ya ce Suger Allah Allah na ke fa na gama na zo gare ki. Jin an yi shiru be kuma ji kamshin turaren na Hajjo ba sai ma na Hauwa ya sa shi dagowa,Hauwar ce gaban sa,God shez beautiful! Abunda ya fada kenan cikin ransa,ita kuwa karasowa gaban sa ta yi cikin yanga da kissa ganin yanda ya tsaya cak. Ta durkusa gaban sa tare da fadin dan Allah kamin afuwa,na kasance mace mara godiyar Allah,duk soyyayar da ka ke min amma nai ta saba ma ka,ka yafe min Khalid. Ganin be motsa ba,ta dago su ka hada ido,ta ga ya na murmushi,ya ce da gaske kike? Ta ce cross my hrt! Cikin jin dadi ya aje papers,ya ce come here baby-luv. Da sauri ta tashi ta shige jikin sa ta na kuka,ya ce shhhhhh is owk.
Hajjo kwance bisa gadon ta,Ta ji an bude kofa,daga idon da za ta yi,ta ga Neena tsaye kofar dakin,ta ce zan iya shigowa? Hajjo ta tashi zaune tare da fadin shigo mana. Ga mamakin Hajjo sai ga ta ta shigo ta durkusa gaban ta,ta ce Mama,dan Allah zan iya kiran ki mama a matsayi na na diyar ki? Tashi Hajjo ta yi,ta tada ita su ka zauna bakin gado kamar yaya da kanwa,ta ce Ameena? Neena ta ce na’am,ta ce ko ba ki kirani mama ba ni mahaifiyar ki ce,wannan ba zai taba canzawa ba,zan fi so ki cigaba da kira na Antyn da ki ka saba,ki kuma kira dayar maman taki da Momma da ki ka saba,kar ki canza ma ta,ita ma maman ki ce,ta na san ki kwarai kamar yanda ni ma na ke san ki. Neena ta gyada kai tare da fadin na gode. Hajjo ta shafa kanta,nan fa hira ta bige,ta ma manta da Hauwa na wajan Khalid,hira har da dariya,ta na bata lbryn mai sunan ta,a haka har bacci ya dauke Neena,Hajjo ta gyra ma ta kwanciya,ta san Khalid na tare da Hauwa ana ta soyayya,sai kawai ta yi kwanciyar ta da diyar ta,a karo na farko kenan tin bayan da aka dauke ta ta na shekara biyu.
DEDICA to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[16/10 22:05] .: [2:25pm, 6/14/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
6⃣8⃣
Washagari cikin jin dadi aka karya,Khalid ya tafi Abuja,Hauwa ta kai diyar ta makaranta,Hajjo da ta daina fita ta yi kwanciyar ta a gida,rayuwa ta fada dadi. Da yamma bayan Hajjo ta gama waya da Indo,ta na tambayar yaya dai? Ba a motsa ba? Hajjo ta ce tukunna,ko yau ko gobe ta ke sa rai dan ta jin kab ta ba daidai ba,su ka kare da fatan alkahilairi,Indo ta ce suna nan suna jiran abun arziki dai. Aje wayar ta ke da wuya wani kiran ya shigo,kawar su ce Yusrah. Ta daga ta na Yusrah ashe ana tunawa da mu. Daga dayan bangaran ta ce haba ai kuna nan rai na,ni fa ance da ni an sake venue din walimar Aysuh da ke jiya ban sami daman zuwa ba,dan Allah taimaka ki fada min….cike da Mamaki Hajjo ta ce walima? Walimar me kuma Ayush ta ke? Kai Hajara! Yusrah ta fada daga dayan bangaran,ki na nufin ba ki san bikin Ayush ake ba? Ina amintar ta ku? Duniya da alkawari kuwa….? Ganin yanda Yusrah ta yi reactn Hajjo ta yi saurin yin kwana,ta ce no ban san da walimar bane,amma ma na san da biki,da ke na yi nauyi shi ya sa ta ke boye min. Yusrah ta ce yanzu na ji batu,bari na kira wata kawar ta mu na ji toh. Su ka yi sallama ta aje wayar. Hajjo ta dade ta na jinjina maganar,Ayush? Ayush kuwa? Ayush din ta? Ta dai san Ayush ta ja baya da ita,amma ba ta san abun ya kai ga haka ba. Kasa hakuri ta yi,tai ta gwada numbar Khalid ba ya shiga,kawai sai ta shirya,ta ce da Hauwa bari ta dan je ta dawo. Hauwa na be kamata ta fita ba a yanayin da ta ke ciki,ga kuma hadari na ta haduwa. Hajjo ta ce ba nisa za ta yi ba,kar ta damu garau ta ke.
Kai tsaye gidan su Ayush ta je,ganin mutane a waje,ga motoci ya tabbatar ma ta amarya ake jira a tafi wajan walima. Gidan ta shiga tana tambayar Aysuh,wata kanwar ta ce ta gano Hajjo,ta ce laaa Anty Hajjo,ai ban gane ki ba da. Ita ta kai ta inda akewa Ayush make up,an gama ma ta kenan sai ga Hajjo gaban ta. Ta yi kyau sosai, Ganin ta Ayush ta ji wani iri,kunya ta rufe ta,ta ce da jama’ar wajan su dan ba ta wuri,kawayen su sai yiwa Hajjo biki su ke,wai bikin Ayush guda sai yau ta ke zuwa.
Bayan kowa ya watse daga Hajjo sai Ayush,Hajjo ta ce Ayush,ina zumunci? Lefin me na mi ki haka? Bikin ki Ayush ki kasa fada min? Abun ya kai haka? Idanun ta sun yi rau,ta ce ban san da wani baki zan baki hakuri ba Hajara,ban san da wani ido zan kalle ki ba,ba yanda zan yi ne. Hajjon ma kwalla ne ya cika idanun ta,ta ce y? Saboda me ya sa? Kin fitar da ni daga cikin yan uwa da abokan arziki? Is dat y? Ayush ta girgiza kai. Hajjo ta ce den y? A sanyaye ta ce saboda mijin da na aura ne….Hajjo ta kasa fahimtar ta,ta ce kamar yaya mijin da ki ka aura? What bussiness do i hav wit him? Shi ya ce kar ki yi zumunci da kawar ki Hajara? Ta yi saurin cewa no ba haka bane! Wata yar budurwa ce ta leko ta ce Ayush tin dazu fa Su Ya Suraj su ka zo,ya ce ki fito! Ayush ta gyada ma ta kai. Kamar blow haka abun ya bugi Hajjo. Sai a sannan ta gane komai,hw can she blind? Ta kasa ganewa tintuni! Ta na murmushi ta ce Suraj? Suraj ki ka aura Aysuh? Dama shi ne Crush din na ki? Shi ne cousn din na ki da ki ke matukar so? Ayush ta gyada kai hawaye na zuba daga idanun ta. Hajjo ta ce oh my God!! Da na yi making mistake of my lfy! Ashe soyayyar Khalid ba karamar alkhairi bace a gareni!ta yi hugn din ta,tana mumu me ya sa baki fada min ba Ayush! Me ya sa. Ayush ta ce saboda ke kawata ce Hajjo,kuma ke ya ke so ba ni ba tym din,i can’t jst hurt you! Hajjo ta ce gwara kin yi hurtn kan ki Ayush? For you information,wallahi ban taba jin soyayyar Suraj cikin rai na ba,I was doing it for u mumu! It was all for ur sake!Duka su ka sa dariya,budurwar ce ta kara dawowa,kafin ta yi magana Hajjo ta ce gata nan,pls a yi hakuri. Ta ce da Ayush ina ne wajan bikin? Ayush ya ce ta yafe ma ta wlh ga hadari ga tsohon ciki! Hajjo ta ce wlh babu abunda ya isa ya hana ta zuwa auren Ayush da crush,so kawai ta fada ma ta,ta na fada ma ta,Hajjo ta taya ta share hawayen fuskarta,su ka fito.
👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
6⃣9⃣
Tin shigar ta mota Aysuh ke kokarin gayawa angon na ta suna da babbar bakuwa,amma ina mitar ta ki fitowa da wuri ga hadari da ya ke ta ma ta ya ki bari ma ya ji,dan haka sai ta yi fushi ta ma sa banza. Sai da su ka shiga su ka zauna a dakin taron sannan Hajjo ta sami damar karasawa a na ta motar. Har ta fito sai ta tuno alkawarin da ta tabawa yiwa Suraj,ta ga lalle tin da Allah ya nuna ma ta ranar,dole ta cika,dan haka sai ta dauko ajiyayyar lapcoat din ta da ke cikin mota,ta sanya.
Tin da ta shigo ya ke kallanta,ba komai ne ya ja hankalin sa ba sai lapcoat din da ya gani sanye jikin ta,haka ma dayawa daga cikin jama’ar wajan kallan ta su ke,mace mai tsohon cikin da ke rinjayar ta dan girma,ta na taku da kyar ga lapcoat ta daura,likitocin da su ka gane ta kuwa dariya kawai su ke,dax Doc Hajara for them,komai na ta da gaske ta ke yi. Suraj was lyk wacece wannan? Maganar sa da Hajjo ce ta fado ran sa,lapcoat? Sanya lapcoat ranar bikin sa? Mutum daya ce da wannan aiki! Ya juya ya kalli amaryar sa da alamar tambaya,murmushin da ke fuskar ta ya gasgata ma sa Hajjon ce ba kowa. Kai tsaye wajan ango da amarya ta nufa,ta isa gaban su Suraj ya dara tare da Fadin dax Hajjo for us! kin dai sa hankalin ki ya kwanta! Duka dariya su ka sa,da ke ya taba bawa Ayush lbryn sanda suna shawarar irin shigar da za su yi. Hajjo ta ce ana bikin Doctors ai ban yi adalci ba idan na kasa cika alkawari. Suraj ya gyada kai,ya ce yes,thank you for dat,amma you tooo heavy,ya kamata ki koma gida kar ki haihu wajan bikin doctors! Ayush ta ce menene ciki? Gwaggaro za mu aje mu karbi dam bebyn mu. Duka dariya suke,Hajjo ta tsaya tsakiyar su da tambatsatsen cikin ta aka mu su hoto,sannan ta mu su sallama da fatan alkhairi,zuciyar ta fari fat da annuri ta baro wajan.
Tana shiga gida gaban ta ya fara faduwa,Khalid jingine jikin motar Hauwa,kallo daya za ka ma sa ka tabbatar da bacin ran da ke tattatare da shi,ya cika yayi fam dawowar Hajjo ya ke jira,tin dawowar sa da ya ga ba ta nan gaba daya hankalin sa ya gama tashi,gashi ba ta daga waya. Gefe ta faka,ta fito da fa’ar ta ta ce sannu da zuwa…bin ta yayi da kallo ya tabbatar da lfyn ta lau,fuska tsuke ya ce ke ce da sannu ke da ki ka fita bayan kin san na hana tsabar ba ki san ciwan kan ki ba! Nxt tym idan za ki fita ki aje min ciki na a gida sai ki je duk inda za ki! Ban mukullin motar! Rai ba dadi ta mi ka ma sa,tare da fadin ka yi hakuri! Banza ya ma ta,ya shige ciki ta na biye da shi,sai shunan sa ta ke da baki,ta na fadin masifaffe kawai! Da su ka shiga ciki ya juyo ya ce mekika ce? Ta ce ah ah ba magana na ke ba! Cikin takaici ya ce ina ma ki je? Ta ce wlh bikin Ayush ake,yace wacece Ayush? Ta ce kai Khalid kawar tawa ka man ta? Aysha? Ya ce cousn din tsohon saurayin ki? Ta ce yauwa Suraj din ma ta aura…WHAT bikin tsohon saurayin ki ka je! Hajjo ta ce Khalid! Ina ya hau ta inda ya ke shiga ba tanan ya ke fita ba,gaba daya ya masife ta tsaf! Kafin ya haye bangaran sa,sai ga Hauwa ta fito ganin Hajjo tsaye ta kuma jiyo masifar Khalid din ta ce lfy kuwa Hajjo? Hajjo ta ce wannan masifaffan mijin na ki ne ke masifar rashin gaskiya. Hauwa ta ce ahh ran maza ya baci,aje a lallabo shi. Hajjo ta tabe baki ta ce caf bar ni na ji da kai na kin ji,can ma sa,sai dai ke ki lallabo shi din ba dai ni ba. Hauwa ta ce ah ah wane ni,ban shiga wannan fadan Hajjo. Hajjo ta ce toh ya je can ya karata,ina jin dan ciwo kadan,bari na je na kwanta ko zai lafa.
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[7/25, 6:15 PM] Salmah Ateeku: [2:35pm, 6/14/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
7⃣0⃣
Hauwa ta ce ko dai abun ne? Tana tafiya Hajjo ta ce ah ah,da saura dai,kawai ban jin dadi ne. Ta shige ciki Hauwa na ma ta sannu. Da aka zo cin dinner Hajjo ba ta fito ba,haka ma Khalid da ke fushi. Da ke Hauwa ta san haka sai su ka ci abuncin su ita da Neena. Sai da ta gama ta leka Hajjo,sai ta ga ta na bacci,ta kyale ta ba tare da ta tashe ta ba. Garin yayi baki matuka,hadari ya hadu sai walkiya,dan haka Hauwa da Neena ma da wuri su ka yi kwanciyar su.
Cikin bacci ta ke jin ciwan na tsikarar ta sama sama,tin tana iya jurewa kamar a mafarki,abu ya zama unbearable har sai da ta farka,ta tashi zaune cikin zufa,sai da ciwan ya lafa sannan ,ta duba agogo ta ga karfe tara na dare. Tashi ta yi ta watsa ruwa,ta sanya wata rigar ta iyaka gwiwa,ta koma ta kwanta. Ciwan be kara motsa ma ta ba sai kusan wajan goma,one hour interval kenan,da ta ga haka ta tabbatar naguda ta ke,amma ta san da saura,za ta iya kaiwa ma zuwa asuba. Sai ta saki jikin ta ba ta kira Khalid ba,shi da ma ya ke fushi da ita ta ma kashe wutar dakin dan ta san ba shigowa zai yi ba. Haka ta yi zaman ta,tin tana kan gado sai ga ta ta sauko kasa,wato ya kara motsa ma ta kenan.
Khalid kwance bisa gadan sa,ya na so ya kaurace Hajjo yau dai daya,amma abu na so ya gagare shi. Kamar wanda aka kira ya tashi da sauri,ya sauko sai gashi bakin kofar dakin Hajjo. Ya bude kofar a hankali,ganin wutar dakin a kashe ya san ta yi bacci,amma idanun sa na matukar san ganin ta duk da ita mai laifi ce. Dan haka sai ya shiga dakin,makunnin wuta ya danna,haske ya gauraya a dakin,ga mamakin sa gadan na ta ba kowa,ya na tunanin ko ta shiga bandaki,ya nufi bandaki da niyar kwankwasawa,sai ya hange ta can gefe,zaune dai dai bisa carpet,da sauri ya karasa wajan ta yana Suger ya dai? Ta na murmushi ta ce labour na fara. Ya ce ya salam! Ya ba ki kira ni ba! Bari na kira Hauwa mu tafi hsptal! Ta yi saurin ruko hannun shi ta ce da saura,pls ka dan barta tukunna,ina ga sai ma zuwa asuba zan haihu. Kallan ta yake kamar ma neman gaskiya daga fuskar ta,daga bisani ya ce tun yaushe ki ka fara jin ciwan? Ta ce tin dawowa ta gida. Ya ce da hadari Hajara,tin kafin ruwa ya sauka mu je asibiti. Ta ce blv me da saura Khalid. Sai da ya dan yi tunani,sannan shi ma ya zauna kusa da ita,ya janyo ta jikin sa. Bini bini sai yayi kissing kumatun ta,ko hannu ko wuyan ta. Can ya ce Hajara? Ta ce ummm ta yaya za mu gane kin kusa ne mu tafi? Ba ana gwadawa ba?ya ake yi?da me ake yi?
Da ke ciwan ya lafa sosai,kamar ba ita ke yi ba,sai ta murmusa ce ita diya mace in tana labour abin da ake fara dubawa shine wannan hanyar da dan yake futowa aga yana budewa to in ya na budewa,budewar shine Cervical dilation ko Dilatation of cervix,sai a gwada hw many Cm ta ke,yatsa daya shine 2cm,biyu 4cm,uku 6cm,hudu 8cm, biyar kuma 10cm. Idan diya mace tana 2cm xata iya kaiwa 6hrs bata haihu ba, Idan taje 5 still she is on the way xata Iya taking 3hrs kafin ta haihu, It depends on multip ce ko primid, In primid ce xata dade saboda itace haihuwarta ta farko, In multipce baxa takai hrs din primid ba saboda tataba haihuwa,kamar ni kenan, Buh duk inda akaje 8 haihuwa taxo kusa xata iya haihuwa within 30mint, In kuma akace fully dilated dax 10cm tofa yanxu xa aga kan da.
Khalid ya ce yaya kenan ke da ba wanda zai iya dubawa? Ta ce kar ka damu,na riga na kintati lokaci base on yanda ciwan ya ke tashi. Shiru su ka yi,daga bisani ya ce yaushe raban ki da abunci? Ta ce kafin na fita na ci. Ya ce kin dade,bari na samo mi ki,ta ce noo i can’t eat,bazan iya ba,ka dai bani black tea,shi zai iya keeping dina strong,ya ce owk ina zuwa ya fita jiki na rawa,sai gashi ya dawo dauke da flask din ruwan zafi,ya hada ma ta tea din,ya dawo ya dada jawo ta jikin sa,ta na sha suna dan hira. Tin suna jin saukar yayyafi sama sama,tuni ruwa ya tsuge kamar daga bakin kwarya,Khalid ya ce Allah ya taimake mu ruwan nan ya tsagaita san da za mu fita. Ta ce amen amen. Sai da ma ta manta shaf sannan ciwo ya dawo,mara ta fara juyawa,ta damki hannu Khalid, gaba daya ya kideme sai sannu Hajara,sannu sannu Hajara,me zan yi? Me zan mi ki na rage mi ki ciwo? Baki cize ta dafa bayan ta,ganin haka sai ya fara shafa ma ta bayan,sai sannu da surutai ya ke kamar shi ke jin ciwan ma. Can kuma kamar abun iska sai ciwo ya lafa,yayi hugn din ta gam daga zaune,ya na da ana daukewa da na dauke mi ki suger,I love you soo much! Ita dai uhum kawai ta ke cewa,ita ta san abunda ta ke ji. Haka su ka kusan raba dare,ciwo ya tashi ya lafa,tin yana after one hour,ya dawo 40mnts,30,25,20…..wajan uku da rabi sai fa abu yazo gangaganga,gashi ruwa ake sosai,ba karamin tashin hankali Khalid ya shiga ba. Da gudu ya taso Hauwa,tare su ka dawo kan Hajjo,gwara Hauwa atlest yayar ta Zeena ta taba haihuwa a gida dan haka ta na dan san kadan daga yanda za ta yi. Khalid ya kira wayar Jabir ba adadi amma saboda ruwa wayan be shiga,haka na matar sa. Gani ya ke laifin sa ne da yarda da maganar Hajjo,da sun tafi asibiti tuntuni da tuni hankalin su kwance.
Carpet mai kamar leda Hauwa ta shimida gaban Hajjo,Khilid ya ce me ki ke yi haka? Asibiti fa za mu kai ta! Hauwa ta ce cikin ruwan nan? Kan mu karasa ta haihu,dubi kafar ta ka ga! Wani farin ruwa ne mai jini jini ya ga na bin kafar Hajjo,ta ce wannan zaki ne ke fita,daga shi sai faya,sai kuma kan da fa! Khalid ya ruko hannun Hajjo da ta ke ta nishi,ta na wayyo,wayyo,Hauwa ta ce addua Hajjo,summas sabila yassara! Summas sabila yassara! Caraf kuwa sai ta kama,tin tana fada a hankali,har ta fara fada da karfi.