Showing 6001 words to 9000 words out of 67328 words

Chapter 3 - Diya Mace Book Complete by khadija sidi .txt

bacci ya sace ta.
Washagari sai karfe takwas rana ta fito Garbati ya tashi,ko sallar asubahi dama ba ya tashi,sai gari ya waye tangaradau ya ke yi,ko da ya Hajjo kwance a kasa bakin kofa sai ya tsallake ta abun shi cikin nuna ko in kula yay ficewar sa.
Bayan kusan minti talatin cikin bacci ta jiyo muryar Mairo ta na fadin Iyalle na. tafi dandali sai na dawo!!! A firgice Hajjo ta tashi,ta ma manta inda ta ke,ita ma ta fito a guje ta na fadin ke Mairo tsaya ni mana dallah!Mairo tace tsaya ta na fadin toh ki yi saurk ki wanke bakin ki da ido mu tafi dan wlh Garbati ya na ciki ya na shan koko,cikin sauri Hajjo ta dau buta tana fadin toh Mairo….gidan ubanwa za ku?muryar Garbati suka ji kamar daga sama,Hajjo ta saki buta ya fadi kasa hannu na rawa. Ya nuna Mairo da yatsa ke zan ci uban ki Mairo,ba ki san Baba ya aura min ita ba? Iyalle! Ke Iyalle! Sai ga mahaifiyar su Iyalle biye da ita Kande ce sun fito daga daki da sauri dake tsakar gidan daya ce,ba wani girma kuma gare ta ba.
Iyalle ta bi su da kallo ta ce kaka an kayi Garbati? Garbati ya ce wlh Iyalle ki shiga tsakani na da mairo,yo ban da rashin mutunci Hajjo fa ta gayyata su ke dandali,har da ta yo sauri ina ciki! Iyalle ta ce ke Mairo ba ki san ita Hajjo matar aure ce ba? Cikin gunguni tace yo ni na ce ta biyo ni? Ba ita ta ce in jira ta ba! Karya ta ke,makaryaciya!Garbati ya katseta,Mairo ta murguda baki tace ba dai ni ba! Hajjo kuwa tini ido ya kawo ruwa. Garbati ya yunkura zai bugi Mairo Iyalle ta hana shi,ta ce Mairo je ki abunki,haka kawai akan wata ba za ka dakar min diya ba Garbati!Garbati ya ce wlh Iyalle ke ki sa yarinyar nan ta na dada rai na ni,Mairo ta juya za ta fita,Hajjo ta bi ta,ina za ki? Ya daka ma ta tsawa sai kuwa ta sa kuka. Iyyalle ta ce ni dai ba za ka bugi diya ta ba,je ki abunki. Hajjo ta na ji ta na gani Mairo ta fice,Garbati ya fizgo hannun ta ya wulga ta daki ya ja ya rufe ya na fadin za ta dawo ita ma ta sa me ni ne. Iyyale ta ce in ka taba Mairo sai na bata ma ran ka! Ta dubi Kande shige mu tafi kin ji! Su ka shigewar su ciki. Garbati ya fice shima ya huci,ita ko Hajjo inda ya jefa ta nan ta durkushe ta na ihu,fadi take na shiga uku na lalace!wayyo na shiga uku wayyo Inna!
Su Iyalle da kande suna ji su ka mata banza,har ta gaji ta yi shiru,sai ga Kande ta shigo dauke da kwanan sha ta aje gaban Hajjo,ta ce ga Koko da kusai inji Iyalle. Hajjo ta ture ta ce ba na so,ni gidan mu zani,ni wajan Inna zani! Kande ta dube ta ta ce yarinya zancen ki ke so,ta juyo tai fitowar ta.
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[12:38am, 5/1/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
9⃣
Hajjo tana nan kwance ta jiyo sallamar Indo,da.sauri ta tashi ta na fadin yauwa Indo sai yanzu ki ka dawo wlh sai na hada ki da Inna! Ta bude kofa ta fito,sai ta hangi Indo cikin dakin Iyalle suna gaisawa,ai kuwa ita ma Hajjon kofar dakin ta nufa,ta tsaya hannu a kugu ta na fadin ku gama gaisawa ki fito mu tafi dan Allah! Iyalle ta ce ina ruwan Hajjo,har yanzu ba ta fahimci ta girma ba,ki dai ma ta fada Indo,Indo murmusawa ta yi ta na duban Hajjo,cikin ranta kuwa sanyi ta ji dan daga ganin Hajjo Garbati be ma ta komai ba,ashe dai ya na da tunani. Indo ta nisa ta ce zan ma ta Iyalle,za ta gane inshaAllahu. Iyalle ta ce toh amen dai.
Ta fito hannun ta dauke da jakar buhu,ta ja hannun Hajjo,ko da Hajjo ta ga Indo na shirin shigar da su dakin ta sai ta ce Indo wlh ni ba na so na kara ko minti biyar ne a gidan nan,dan Allah kawai mu tafi kafin Garbati ya dawo wlh shi ya hana ni zuwa dandali,kuma dan iska ne wlh,jiya fa da daddare cewa ya yi na tube….shhhh! Indo ta toshe mata baki,dan Allah Hajjo ki rufa min baki,muje dakin ki bani labarin kafin mu tafi din. Hajjo ta ce ina gama baki lbry za mu tafi yasin! Indo ta ja ta suka shige dakin. A tsakar daki Indo ta ce yanzu Hajjo dubi dakin nan da kyau,ki ga yanda aka jera langa tuwo da miya,jibi akwatin karfen can,dubi sif din can fa,dubi gadan can mai rumfa ga kuma na ki an hado mi ki da shi,duka na ki ne Hajjo,ke ma kin zama ‘yar gata an mi ki aure kamar yanda ni ma aka min..Hajjo ta zumbura baki ta ce yo ni ban ce a min auren ba ai! Indo ta ja hannun ta suka zauna bakin gado,ta ce ki na nufin duk damin kayan nan ba kya so Hajjo? Hajjo ta ce ina so mana,amma ni Garbati ne ba na so,wlh jiya sai da ya yay ta min fada,ce min yayi na tube riga ta…nan ta kwashe yanda su ka yi da Garbati ta fada ma ta,Indo ta saki ajiyar zuciya jin yanda ta kasance tsakanin su,ta kuma kwabeta da kar ta fadawa kowa ko da kuwa su Mairo ne za su yi ma ta dariya da ihu da gori,ta ga dai su ba a musu aure ba,komai ya faru kar ta bari kowa ya ji,batun komawa gida kuma babu,nan ne saban gidan ta shi ya sa ma Inna ta ce ta kawo ma ta sauran kayan ta,ga su cikin buhu. Hajjo ta dubi kayan ta kalli Indo ta ce wai shikenan an min aure ni ma zan ta haihuwa kamar yanda ki ke yi? Indo ta ce eh idan lokaci yayi za ki haihu,ke ma ki sami katuwar bebin ki da ta fi ta roba. Hajjo ta daka tsalle ta ce wayyo farin ciki,wlh da ko sai na yiwa su Mairo kambo,ba zan na ba su dani ba yasin!
Indo ta ce dama mana,da ke sai abun ki babu mai taba mi ki,har fa kudin cefane za a na baki,da kan ki za ki na girki abun ki,idan kin so ma sai ki na toya wainar kwai. Hajjo ta mayar da mugun yawu ta ce Allah Indo? Indo ta ce sosai ma kuwa,can ba kwanan abuncin ki bane? Hajjo ta dubi kwanan da Kande ta ce eh wai ni kande ta kawowa,Indo ta tashi ta dauko ta tisa Hajjo a gaba,ta na ci ta na mata dan nasihohi cikin dabara dan a samu dai ta zauna dakin mijin ta Garbati…
DEDICATED to The Women OF Virtue💁👰🙋(group)
[12:43am, 5/1/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
1⃣0⃣
Shi ko ango Garbati kai tsaye wajan abokin sa Nuhu ya wuce,ya tadda shi cikin dakin sa kaca kaca kamar ba mutum ke kwana ciki ba. Nuhu na ganin sa ya fara ango ango ango ka sha kamshi….! Garbati ya zube kan katifa ya na fadin yo wani kamshi na sha Baba ya aura min kwaila! Ai wlh an bata min rai na! Jummala ta cuce ni,wlh kwaila Baba ya aura min,kai da ta tube jiya ko ni na fita awk yasin ni da na ke na namiji….hahahahahaaha! Nuhu ya sheke da dariyar mugunta,yo in ban da abun ka Garbati me za ka gani jikin Hajjo? Kasan yarinya ce danya sharaf! Garbati ya buga kafa! Ni wlh Nuhu Jummala ce ta cuce ni! Ta bata min rai na! Nuhu ya ce ka ce dai kai ma ba ka gama lalube yan matan tasha ba!hahaha ashe da saura! Garbati ya ce indai Hajjo ce mata ta yanzu na fara lalube yan matan tasha! Ta shi ma muje dan Allah! Bazan iya jira gari yayi duhu ba! Nuhu ya tashi har yanzu be dai na dariyar ba,ya dau wata rigar sa,dan dauda har annakiya datti da jirwaye ta yi,ya zura,su ka fito ya ja kufar shago ya rufe,kai tsaye tasha su ka nufa….
Gidan su Garbati kuwa wuni Indo ta mata,sai da ta tabbatar Hajjo za ta iya zama sannan ta saki ranta,dama Inna ce ta turo ta saboda hakan,kafin Indo ta tafi yan uwa sun dan lekowa Hajjo,ita ko Hajjo tin da Indo ta ce za ta haihu ta saki ranta,dama yarinya ce mai san yara,gashi za ta na girki,kuma komai na dakin na ta,ai sai kuma lamari ya fara ma ta dadi. Indo ta sa ta yo wanka aka cancada ma ta ado,ta ce haka za ta na yi kullum tin da ita matar aure ce. Hajjo ta ce toooh,abun nema ya samu! Iyalle ce ta kawowa bakin Hajjo abunci,sai yaban ta su ke kuwa ta karrama su. Da la’asar sakaliya kowa ya kama hanyar gida,ko da Indo za ta tafi sai Hajjo ta fara shirin yin tsiya,da kyar ta lallaba ta,ta yarda ta zauna a daki shiru ita kadai. Da abun ya ma ta yawa sai ta zari mayafi ta ci dammara,ta yi sa’a ba kowa a tsakar gidan sai ko ta yi ficewar ta.
A waje ta tadda su Mairo suna enter,ta ce ku da Allah zan yi,kun ji? Mairo ta ce yarinya idan Garbati ya kamaki ba ruwana! Hajjo ta murguda baki ni ina ruwa da shi,za ku yi da ni ko kuwa? Hanse ta ce za mu yi da ke mana,ai sai a fara daga fari,ta yi saurin daga hannu ta ce fess! Mairo ta ce sakan! Hajjo da Habi suka hada baki su ka ce los! Da kyar aka raba gardama Hajjo ta zama los din Habi ta biyo ta a baya,sai kuma sauran wasan suka zabi na su,ya dai danganta da wanda ya riga fada,sun kai su bakwai. Kan ka ce me,enter yayi enter,amma sai aka cinye Hajjo ta zama kariya,ai kuwa nan aka shiga ma ta waka….
“Wacece wacece?wacece
Kariya,Hajjo ce Kariya!
Ta yi cikin dan tsako ta
Buye a gajeran wando
Kariya!ku fada mana
Ko kuna tsoran ta ne
Yar ficika ta Alhaji
Baba ta ci tuwo ta
Na mana yanga….”
Suna ma ta wakar ta na bin su za ta kama dan ta shafa kan su ta tsira amma ta kasa,gaba daya ta hada zufa,ko da Mairo ta gifta ta gaban ta sai ta yi kanta da gudu,idanu rufe ba ta ankara ba sai ji ta yi ta yi gware da jikin mutum,azatan ta Mairo ce,fadi ta ke yarinya na kama ki,ko da ta ga kafar namijj sai fa ta sha jinin jikin ta,ta daga kai a hankali,yayinda ta yi ido biyu da jajayen idon angon na ta Garbati…..
DEDICATED to The Women OF Virtue💁👰🙋(group)
[16/10 21:44] .: /25, 12:39 AM] Salmah Ateeku: [11:03am, 5/5/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
1⃣1⃣
Gaba daya rudewa ta yi,su Mairo ma su waka tini suka yi shiru babu wanda be tsorata da ganin Garbati ba. Cikin tsawa da daga muryar nan ta sa da ya saba ya ce ke Hajjo!Hajjo ta daura hannun ta biyu bisa kanta,ta cure gu daya a durkushe,tana jiran saukan duka,ya ci gaba da fadin uban me ki ke a waje sai ka ce shashasha! Kai ni wlh an cuceni! Yau sai kin gane kuranki yarinya! Ya fizgi hannun ta,Hajjo ta sa kara wayyo Allah Inna zai kashe ni! Cikin takaici ya saki hannun,a fusace yace wlh Hajjo kar ki bata min rai na,ki wuce mu tafi na ce! Hajjo ta ki ta motsa,shi ko Garbati ya gama kulewa,sai ya sunkume ta ya aza a kafada ta na ihu da bori,gaba daya warin dadti da gumi da ya ke ma kadai ya isa sata ihu,sai Mairo su ka sa ihu,wooooyiii an dauke ta,ya nufuso da sauri kowa yayi ta kansa,Mairo ta shige gida a guje,Garbati biye da ita,a tsakar gida su ka tadda Iyalle ta na tuka tuwan dare,dan ko dakin girki ba su da shi. Saura kiris Mairo ta sa ta bari ta tsallake ta a guje ta shige dakin Iyalle ta banko kofa garam! Iyalle na fadin wakika tsokano ke ko Mairo za ki lalata min kyaure…sai ga Garbati ya shigo,ya na huci ya saki Hajjo ta fadi gaban Iyyale sharaf kamar kayan wanki fuska cike da hawaye ta dada curewa. Kai Garbati ina ka samo wannan fitinanniyar diyar da aka aura ma ka? Cikin daga murya ya ce Iyalle! Iyalle ki bar ni na jibgi Mairo! Mairo daga daki ta ce yo ni ina ruwana! Ni na ce ta fito? Iyalle ta ce gaskiya Mairo ita daya ta fita abunta,ita wannan mata taka ita ya kamata ka jibga ba diya ta ba! Ina ruwan Mairo? Kande ta fito daga bayan gida dauke da buta,ta gifta gaban Garbati ta ce kwarai ko ni ma na ga fitar ta,sannan ta aje buta ta shige dakin Iyalle. Cikin takaici ya ke duban Hajjo,ya ce Iyalle,wai ya zan yi da yarinyar nan ne dan Allah? Ya zan yi ta daina fita kar fa watarana kuma uban ta ya zo ya ga abun da na gani yau?
Iyalle ta ce aiki za mu ta jibga ma ta,duka aikin gidan nan ita za ta ke yi,ka ga ba ma za ta sami damar fita ba. Garbati ya ce Iyalle ita fa wannan babu abunda ta iya sai fitina,za ta iya aiki kuwa? Iyalle ta ce ba dai diya mace ba ce? An gama magana,koya ma ta za’a yi. Garbati ya saki ajiyar zuciya ya ce indai zan sami sauki a tula ma ta aikin,dan wannan ko dukan ta zan yi sai dai na daki kashi! Iyalle ta ce daga gobe ma kuwa. Ya dubi Hajjo cikin zafin nama ya dada cincincibar ta yay daki da ita,kan gado ya aza ta,tini warin sa ya game daki,Hajjo ta na so ta toshe hanci ta na tsoro,ya nuna ta da dan yatsa ya ce ki ka sake fita sai na jibgeki,shashasha kawai. Ya ja tsaki ya fito ya rufo kofar dakin,dama gashi tagar dakin yar karama,ga Garbati ya gume daki da wari,ga shi kuma ya ja kofa ya rufe. Ai ko da gudu Hajjo ta biyo bayan shi,ta ja kofa ta ki buduwa,tayi kuka,tayi kuka har da birgima kamar za ta shide. Sai bayan isha’i ya shigo,ya tadda har ta yi bacci wahala,be damu ya tada ita ta yi sallah ba ko ta ci abunci,ya tsallake ta nan inda take kwance a kasa bakin kofa ya dauko tuwan sa miyar kuka da ta ji daddawa,ya ci ya koshi,ya wanko hannu ba tare da kuskure baki ba,bare sauya kaya,tin babbar rigar jiya ce jikin sa,ya haye gado ya saki gabba da su labba ya fara munshari..
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[11:04am, 5/5/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
1⃣2⃣
Washagari da sassafe,kafin ma Garbati ya tashi Iyalle ta zo ta buga mu su kofa,tini Hajjo ta tasha ta na murje ido,shi ko Garbati da ko sallar asuba be tashi yayi ba da kyar ya tashi ya na gunguni,ganin ya nufo kofa Hajjo ta matsa da saurin ta,be ma lura da ita ba ya bude kofa ya na fadin wai menene Iyalle! Ita kanta Iyalle sai da ta ja baya jin yanda Garbati ke tashi,gashi da yayi magana sai ka ji kamar za ka sume. Iyalle daga baya baya dai ta ce Hajjo na zo tashi ta fara shirin hada mana karin kumallo ai ba kai ba. Ya fara ware ido,ke Hajjo,ya ki ki bita dallah! Dama ita Hajjo burin ta ta fita,da saurin ta ta fito,Garbati ya ja kofa ya rufe ya haura gado ya ci gaba da bacci. Iyalle ta dubi Hajjo maza wanko ido ki zo ki sa min hannu wata rana ma ke zan sakarwa,Hajjo da ke yarinya ce me san aiki,sam ba ta sa kiwa,bare kuma an ceto ta daga warin Garbati,ta ce toh,bara na yi sallah,banyi magariba da isha’i da asuba ba. Iyalle ta ce maza je ki dungura ina jira. Hajjo ta ce toh. Ta dau buta ta yi bandaki.
A dakin Iyalle ta yi sallah wai gudun kar ta tada Garbati,wato Iyalle mace ce mai shegen san lallaba yaran ta,amma na wani ko oho. Ta na Sallah Alhaji Baso ya fara wai ina kokon ne? Iyalle ta leko ta ce ke ki fa yi sauri dallah,Mallam ina zuwa be sauka ba tukun. Da sauri Hajjo ta idar,ta na ganin Mairo da kande sai baccin su su ke,haka ta fita ta fara tular aiki ba kakkautawa,duk da ba ta iya ba,amma Hajjo akwai saurin dauka,wuyar ta a koya ma ta,shikenan. Ranar dai Hajjo ba ta sami hutu ba,hatta wanki ita ta yiwa Iyalle,ta na ta zuba ido ko Indo za ta zo shiru,tin tana kuka har ta fara sabawa da rayuwar da ta tsinci kanta,kullum cikin aiki,ta zame mu su kamar baiwa,ta ma fara tunanin Innarta ma ta yada ita,ga Warin Garbati na bata wuya duk da kowa da gadan sa amma daki daya su ke. Wasa wasa haka rayuwar ta ta kasance,gashi har ta cika wata dakin mijin ta. Iyalle ta tura Garbati wajan wani malamin sauro ya na karbar ruwan rubutu,wai dan ya kafe Hajjo,ya kuma mallake ta dan ta na jin maganar sa,duk daren Allah sai Garbati ya tisa ta gaba ya bata ruwan rubutu ta sha,idan ta ki sha ya nuna zai buge ta,haka dai sai ta karba ta sha,idan ta yi karfin hali ta tambaye shi na menene sai ya ce maganin dangana da hana yawo ne,tin abun ya na damun ta har ya zame ma ta jiki.
Rannan ta hada zufa da tsakar rana ta na ta wanke wanke,ba kowa a gidan sai ita kadai,an tula ma ta aiki,kamar daga sama ta ji sallamar Indo,ta daga ido ta ga Indon ce,sai ta saki kwanan da ta ke wankewa ta zuru wajan ta a guje,tana fadin wayyo Indo sai yau za ki dawo! Ganin yanda Hajjo ta rame

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login