Showing 54001 words to 57000 words out of 67328 words

Chapter 19 - Diya Mace Book Complete by khadija sidi .txt

ce toh ai shikenan,ta cigaba da aikin ta. Har Hajjo za ta sa baki,sai kuma ta yi shiru,amma har ranta ba ta ji dadin abun ba. Ana kiran sallar la’asar,Hajjo ta tashi ta yi na ta,ta na zaune kan dadduma Hauwa ta sake shigowa ta ce da Neena a tashi a yi Sallah ma na. Idanun ta kan game ta ce sai an min game over Momma,Hauwa ta ce toh ai sai ki ta yi,ta shige kitchen. Ran Hajjo ya baci,ta ce ke aje game din nan ki je ki yi sallah. Ko kallan Hajjo ba ta yi ba bare ta aje game din,ta ce ai na ce sai an ce game over…..a fusace Hajjo ta tashi ta fizge handle din,tashi maza ki je ki yi sallah ko na sabar mi ki! Ta daka ma ta tsawa,a kideme Neena ta tashi,ta fashe da kuka da ke ba a saba ma ta tsawa ba,ko a jikin Hajjo dan ji take kamar ta make ka ta huta,ta ce dan iskanci ana mi ki magana ki na jin mutane sai kin gama game za ki yi sallah! Ki je islamiya kin ce kin gaji! Wlh ba zan juri wannan saken ba! Sai ga Hauwa ta shigo da sauri,ganin ta Neena ta karasa wajan ta da gudu ta na kuka,sai tambayar ta take lfy? Dukan ki ta yi? Kuka ya ci karfin Neena ta ka sa magana,sai Hauwa ta ce je ki dakin ki ina zuwa,sai kuwa ta shige bangaran Hauwa da gudu,ta na jiyo Hajjo na fadin ki tabbata kin yi sallah! Hauwa ta kalli Hajjo ta ce me ki ka ma ta? Kar dai dukan ta ki ka yi. Hajjo ta ce ban dake ta ba,amma kiris ya rage na dake ta,yarinyar is too spoiled,ya kamata a fara handling din ta wit iron hands. Hauwa ta ce ke kar ki nemi ki fada min magana! Me ki ke nufi? Ki na nufin ban iya tarbiya ba? Hajjo ta girgiza kai,ta ce ba haka na ke nufi ba,Hauwa ta ce haka ne mana,wato iko za ki nuna min,ban iya tarbiya ba muna sangantar mi ki da diya. Hajjo ta ce ba ki fahimce ni ba,gyara kayan ka ai ba zai zama sauke mu raba ba…ke tsaya matsayin ki! Hauwa ta daka ma ta tsawa,ta ce har ke kin isa ki fada min magana dan mijina ya auro ki,ki na ganin ba na haihuwa shi ki ke tunanin za ki iya min gori kan diyar ki……Hajjo dai tura ta kai bango,ita ma ta fusata ta ce eh an mi ki gorin,karya ne? Ba diyar tawa ba ce? Ko ke ki ka haifa min……karaf sai a kunnan Khalid da shigowar sa kenan ya tsinci maganar Hajjo,ran sa ya baci matuka. Ganin sa tsaye Hauwa ta juya ta shige bangaranta da gudu. Hajjo ta yi kasa da idanun ta,yanda ta ga idanun Khalid sun kada sun yi ja ya sa ta kokarin ma sa bayani….ya dakatar da ita ta hanyar fadin dama haka ki ke? Na zaci ke me rufa min asiri ce,amma ji yanda ki ke gorantawa mata ta? Ki da ki ke haihuwar ba Allah ne ya baki ba? Ko dabarar ki ce aka ce mi ki? Idanun Hajjo cike da kwalla ta ce ba haka ba ne,she pushed me to d extrem wall ne,dole na yi magana,ba zan iya jure ganin yanda Ameena ke tashi ba kwaba ba! Ba zan iya jure ganin ta na tashi kamar Baban ta ba,God shez becoming d personication of her biological father! Khalid ya cize lebe,ni ma gorin za a min? Na ji ba ni ne baban ta ba am so what? Hajjo ta ce me zan yi ku gane? Menene laifi dan na gyarwa diya ta tarbiya? Karya ne ba diyar tawa ba ce?yanda na san ciwan ta wlh ba zan sa ido ta tashi yanda ta ke yanzu ba,ba gata ba ne wannan,diya mace ce,uwa kuma za ta zama nan gaba…Hajara! Ya daka ma ta tsawa,enough of ur insult! Ita din da ki kewa gori ba taimaka mi ki ta ke ba?ki na da lokacin diyar ta ki ne?idan ki ka sa kafa ki ka bar gidan nan tin 8 ba ki dawowa sai 4,ina ki ke da lokacin kan ki bare na tarbiyar yara? Murya kasa kasa Hajjo ta ce no you ar mistaking,ku bani diya ta mana kuga ko zan gaza tarbiyartar da ita,ko bani ita ku ka ko za ta gaza samin lokaci na! Never underestimate d power of mother! Zan iya zama both! A responsible mother as well as a dedicating Doctor!Khalid ya daga kafada,Wuce ki bawa mata ta hakuri! Hajjo ta ce Khalid dan me ya sa? Dan me ya sa zan ba ta hakuri? Dan ni ba mutum ba ce ko dan ni ba a sona? Dan me ya sa? Me na mata da zan ba ta hakuri? Fuska murtuke ya ce a matsayi na na mijin ki na ce ki ba ta hakuri,it is an order! Rai bace,kwalla na shirin sauka ta makale,da sauri ta nufi bangaran Hauwa,ko da ta shiga dakin ta,ta ganta kwance,sai ta sake shawara,ta juyo za ta fita ashe Khalid na biye da ita,ya ce juya ki ba ta hakuri! Hajjo ta juya ta ce Hauwa Allah ya baki hakuri. Ta juyo tana kallan Khalid ido na spark din kwalla da bacin rai ta ce na bawa matar ta ka hakuri,ta fice da sauri. Shigewa dakin yayi,ya jawo Hauwan jikin shi ya na kara ba ta hakuri.
Hajjo na shiga dakin ta sai ta fashe da kuka,sam ba za ta iya zaman gidan ba,dama ta san wulakanta ta Khalid ke da niyar yi shi ya sa ya auro ta. Tuni ta hada yan kayanta cikin karamar jaka,ta dau kudin mota,ta fito ba tare da kowa ya sani ba sai hanyar Kumurya. Sai da ya tabbatar Hauwa ta saki ranta,sai kuma hankalin sa ya koma ga Hajjo,ya fara ji kamar be kyauta ma ta ba tunda be ma ta uziri ba ya ji kanun zance,kawai tsintar ta yayi ta na gorantawa uwar gidan sa rashin haihuwa. Dakin Neena ya je,ya tambaye ta me ya faru ta yi kuka? Da ke yaro be fiya karya ba sai ta bashi lbrn yanda aka yi har kin zuwan ta islamiya da ma kin yin sallah. Jikin shi ya yi sanyi,ya tashi da sauri ya nufo bangaran Hajjo,amma me zai gani? Wayam babu Hajjo babu alamar ta,ya bi daki daki na bangaranta,har bandaki ya duba amma shiru,tuni ya rude,hankalin sa ya tashi. Da sauri ko takalmi be iya sawa ba ya fito wajan maigadi ya na tambayar ko ya ga fitowar amaryar sa? Maigadi ya ce kai be gani ba,in ma ta fita watakila sanda ya zaga bawali ta fita din…..
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[16/10 21:48] .: :55am, 6/14/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
6⃣0⃣
A kidime ya koma ciki,takalmin da ya sako ma hadin bauta ne be sani ba,tashin hankalin sa ina Hajjo za ta da yamma likis haka? Ko sallama be yiwa Hauwa ba ya figi motar sa dan bin sawun Hajjo. Ko da ta isa kumurya,idanun ta sun kumbura da kuka,sai tadda Indo ba ta nan sai yara,su ke fada ma ta wai Indo ta na gida dazu aka zo aka ce Baba ya kone. Nan tsakar gida ta saki jakar ta,bayan shekaru da dama sai ga ta ta dau hanyar gidan su,dan idan ba ta ga halin da Baba ya ke ciki ba hankalinta ba zai kwanta ba. Ganin yanda kofar gidan ya kwarabe sai da gaban ta ya fadi,bare da ta shiga gidan,kamar ba nan ne Innar ta ke rayuwa ciki ba da,gidan ya lalace,ya kazance. Muryar Indo ta ji ta na musayan magana da matan su Mudi,Indo na fadin wlh sam ba ku kyau ta ma na ba,amma ba laifin ku ba ne,laifin mazajen ku ne,idan ku be haife ku ba ai su ya haife su. Tare su ka ce eh mun ji din,yo ba shi ya ce a bashi garwashin ba,sai mu hana shi?ace mun yiwa siriki rowa? Muna fama da yara muna fama da tsoho,ai idan ba a gode mana ba ba a zage mu ba. Baba kwance gaba daya hannun sa na dama ya kone,yatsun duk sun durkushe,sai nishi ya ke dan azaba,bakin sa karkace daga alama barin jikin sa ya shanye. Hajjo ta yi sallama jiki sanyaye. Indo ta amsa ta na yauwa Hajjo gwara da Allah ya kawo ki,ji yanda Baba ya sanya hannun shi cikin garwashi ya kone dan Allah! Sai ta sa kuka…Matan Su Mudi su ka rude ganin Hajjo,dake sun santa tin kafin ta auri Garbati,tare su ka yi wasa,amma zaman kauye sun tsufe sun tsomare kamar ba sa’annin Hajjo ba. Su ka fara laha’ila Hajjo,Hajjon ce kuwa! Ko ta kan su ba ta yi ba,ta karasa wajan Baba da tin randa ya ce ta zauna wajan Indo ba ta kara sa shi a ido ba,gaba daya ya tsufe ya tsomare saboda cuta da rashin gata. Gaban shi ta zauna ta na hawaye. Jin ana Hajjo Hajjo! Idanun sa runtse sai yayi sauri ya bude ya na ina Hajjo? Ina diya ta Hajjo,ku hada ni da Hajjo na nemi gafarar ta! Indo ta ce yi magana Hajjo,taba shi ya jiyo ki! Hajjo ta sanya hannun ta cikin na Baba,ta kasa magana sai kuku. Tana kuka Indo na kuka. Su kuwa matan su Ayuba sai abun ya zama mu su na kallo.
Sani Hajjo ta nema,su ka yi sa’a shigowar sa kumurya kenan,ya ce gashi nan tafe. kafin su iso Indo ke ba ta lbryn yanda aka yi Baba ya kone,wai cewa yayi a bashi garwashi zai yi turare,da ke Baban ba lfy gare shi ba,ya na cikin turaren ya yanki jiki ya fadi,sai hannu ya fada garwashi,gashi bangaran jikin sa ya shanye,ba daman ihu,baki ya karkace ko ya yi ihu ba mai ji bare a ka masa dauki,matan ‘ya’yan sa ba sa iya kula da shi,sai da babban dan Mudi ya gifta ta dakin ya ga Baban ya fasa ihu,shi ne fa aka zo aka cire hannun. Mudi da Ayuba sun dawo,sai mita su ke wai laifin Baba ne,shegen rigima na tsoho,ina shi ina turare! Abun mamaki da kudirar ubangiji a nan shine diyoyin matan na sa da ya guja ya ke kyama,ya ke kira da jidali su ke jin kan shi su ke tausayin shi,su kuma ‘ya’yan na sa maza da ya nunawa gata sam ba su damu da shi ba,shi ne ma ya zame mu su jidali su da matan su,sun ma daina kiran sa Baba sai rikitaccan tsoho. Jin yanda su ke wa Baban ran Hajjo ya baci,ta ce da Sani ya sa Baba a mota,su fara tsayawa a gida ta dan wanke konuwar in ya so sai wuce kano. Hakan ko aka yi,gidan Indo a tsakar gida aka yiwa Baba shimfida,Hajjo ta wanke konuwa ta ma sa dressing. Zaune gaban sa ta na ma sa fifita Sani ya ce bara ya samo mai ya kara a mota sai a tafi. Fitar shi ba da dadewa ba sai gashi ya dawo tare da Khalid.
Jin muryar Khalid cikin gidan gaban Hajjo ya fadi,ta tashi da sauri ta shige ciki ba tare da ta ko daga ido ta kalle shi ba bare ma ta ga yanda ya ke a birkice. Daga ciki ita da Hajjo su ke jiwo maganar su,ya na ta jajanta jikin Baba,gashi ganin Hajjon kan sa ya ji dadi kwarai. Sani ne ya kwallawa Indo kira,ta fito su ka gaisa da Khalid,ba dan ta na fama da ciwan Baba ba da babu abunda zai hana ta dariya ganin Khalid ba yanda ta saba ganin sa ba,yau takalmin ma hadin bauta aka sako,lalle kanwar ta ta ruda shi,dake ta ba ta lbryn abun da ya faru. Khalid ya ma ta ya mai jiki,tare da fatan samin lfyar sa. Sani ya ce da Indo ta kawowa Khalid dadduma bara ya je ya karo mai. Khalid ya ce ka bari mana a tafi a tawa motar? Sani ya ce da ke har da su Mudi za a tafi,wajan ba isar mu zai yi ba. Khalid ya ce eh haka ne,toh a dawo lfy.
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[7/25, 6:13 PM] Salmah Ateeku: [12:01pm, 6/14/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
6⃣1⃣
Daga can gefe ya na fuskantar inda Baba ke kwance ya zauna bisa dadduma. Indo ta zauna ita ma daga gefe,su na dan tattaunawa,Khalid ya kawo maganar Hajjo,ya ce wato Yaya ta(sunan da ya ke kiran Indo tin da ya auri Hajjo)na ji dadi kwarai da na ga Hajjo na kula da Baba,da har ina zargin ta da kin kula da lamarin sa da ma lfyar sa,ki ga sanda ya kwanta dinnan ko duba shi kin zuwa ta yi. Indo ta murmusa tare da fadin ai ina ga duk cikin mu babu wanda ke kula da Baba kamar ita,ka ga kwanciyar ta shi da ka ke magana a kai,eh kwanciyar da yayi ba ta je ta duba shi din ba,amma ita ta biya duka kudin asibitin,ina sanda ka zo ka ke tambaya ta wa ya biya kudi ka je biya aka ce an biya? Ai ita din ce ta biya. Khalid ya ruke baki tare da fadin ikon Allah,wani abun sai Hajara,a haka sai ka yi zatan ba ta damu ba! Indo ta ce ai haka take,ba mai gane halayyar Hajjo,ita dai kam wuyar sha’ani gare ta yanda ka san hawainiya haka ta ke rikida. Toh amma duk cikin mu babu wanda Baba ya yiwa ba daidai ba kamar Hajjo. Ta ba shi lbryn Hajjo tsaf,ba ta boye ma sa komai ba,gaba daya jikewa yayi da zufa,idanun sa sun yi jajur kwalla fal ciki,wani irin abu ya ke ji game da Hajjo,tausayi ga kuma abun da ya ke ji na game da ita da shi kan sa ya kasa ganewa. Shiru ya yi,ya ka sa magana dan ya rasa me zai ce yanda ya ke jin kan sa.
Baba ne ya fara tari mai karfi,fitowar Hajjo da gudu da kuma tashin Indo da sauri lokaci guda ne,su ka yi kan sa,Hajjo ta tallafo kan sa hannun ta ruke da hannun sa mai konuwa,ita kuma Indo hannu bisa kirjin sa ta ke dan masa luf luf. Sha’awa su ka bawa Khalid,yanda su ka damu da mahaifin na su da yanda su ke ma sa sai dai diyoyin mata,ga mazan na shi can majalisa suna hirar su,wai suna jira Sani ya zo su tafi. Duk kiyayyar ta shi na diya mace gashi diyoyin na sa mata ne ke ji da shi,su ke ta hidama da shi,gaba daya soyayyar diya mace ta shiga zuciyar Khalid,gaskiya duk wanda be haihu ba abin tausayi ne,haka kuma duk wanda ya haihu din amma be sami diya mace ba toh be gama morewa. Idanun sa bisa Hajjo,sun samu tarin na Baba ya lafa,ta dauko ruwa ta na bashi da cokali saboda yanda bakin yayi. Hasken farin wata da na fitilar tsakar gidan ya haske fuskar ta,sai ta kara kyau da annuri,ji ya ke kamar ya tashi ya je yayi hugn din ta,kamar ya ruke ta gam ta shige har tsokar sa,kamar ya yi kissing din ta fiye da wanda yayi rannan…kamar kamar kamar…God i love dis woman! Abunda ya fada cikin ransa kenan ba tare da ya san ya fada ba a lokaci guda kuma ya ankare,ya fara tunanin so yace? Yes so ne,ya na san Hajara,ya kuma dade da fara san ta,soyayya da sabon da yayi da Hauwa ya sa ya kasa ganewa! Shi kadai ya ke murmushi idanun sa kan Hajjo,ta kwantar da Baba za ta koma ciki Indo ta ce kin ko gaisa da mijin ki? Wani irin kallo a marairaice na nuna rashin jin dadin maganar Indon ta yi ma ta. Shi kuwa Khalid cewa ya yi bar ta ta huta Yaya ta,ma gaisa anjima. Da amsar ta sa ta yi shigewar ta ta ciki. Sani ya dawo aka shirya tsaf aka sa Baba cikin motar Sani,Mudi ya zauna da shi a baya kan Baba bisa cinyar sa,Hajjo ta yi saurin shiga gaba. Khalid ya ce ta sauko a tashi za su tafi,ta ce wlh ba za ta shiga ta sa ba,aka yi aka yi ta fito ta bawa Indo wuri ta ki,da dai suka ga su ka biye ta Hajjo bata ma su lokaci za ta yi,sai aka hakura,Indon ta shiga bayan motar Khalid,Ayuba a gaba,Khalid sai kwafa ya ke bini bini. Su ka dau hanyar kano.
Sai wajan goman dare su ka isa kano. Asibitin nasarawa su ka kai Baba da ke AKTH suna yajin aikin,ita ko Hajjo haka daidai ya ma ta,ga ta ga Baba ta fi kula da shi. Aka ba su daki V.I.P.,da ke baban Doc Hajara ne har riga rigan duba shi da kula da shi doctors din su ke,hakan ya burge Indo,cewa ta ke hmmmm ilimi dadi,kai ilimi yayi. Su kuwa Mudi da Ayuba sai kallo,wai Hajjo ce ke da matsayi haka har mutane ke dawainiya da Baba dan darajar ta? Shi ko gogan na Hajjo wato Khalid cikin takama ya ke jin kan sa,yes shine fa mijin Doc Hajarar nan,gwara kowa ya sani,kamar cingum ya like ma ta,ko ina ta yi biye da ita ya ke. .
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[12
[16/10 21:48] .: 13pm, 6/14/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
6⃣2⃣
Kan kace mai har an duba Baba an daura shi kan medication. Sai fa rigimar kwana ta tashi tsakanin Indo da Hajjo,Indo ta ce Hajjo ta bi mijin ta ta tafi gida ita za ta kwana da Baba,Hajjo ta ce ba inda za ta sai dai Indo ta tafi,Mudi da Sani su ka sa baki,a dole su ka ce Hajjo ta tafi ta bar Indo tinda ita ce babba. Shi dai Khalid ya na gefe be tanka ba,amma har ga Allah ba zai so Hajjon ta kwana ba,zai fi so ya tafi da matar sa. Shi kuwa Ayuba cewa yayi toh kai Mudi kai za ka kwana ko? Dan ni ina da abun yi. Mudi ya ce sai na kwana din.
Hajjo ta yiwa Indo da Mudi sallama rai bace baki zunbure Khalid ya tisa ta su ka tafi. Sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login