Showing 66001 words to 67328 words out of 67328 words
Chapter 23 - Diya Mace Book Complete by khadija sidi .txt
Idanun Khalid cike da kwalla,ya ce Hauwa ki taimaka min! I can’t bear this! Hauwa ta ce ka fita kawai Khalid,ya tashi zai fita,wani ihun da Hajjo ta yi sai gashi ya dawo da sauri ya na sannu! Sannu Hajara ra! Haka mata ke yi! Haka Hajiya ta ta yi? Hauwa Hajara ta jigata! Wanda be daraja uwar sa ba yayi asara!
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
5pm, 6/14/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
7⃣1⃣
Hauwa ta ce taimaka mu sa ta on her kneels,ga faya ta fashe,na kuma ji kan da, Ko da ya ga yanda Hajjo ke zufa,tana cize lebe kamar za ta gatsa,sai ya tashi a gigice ya na fadan i can’t take it,I can’t take dis! A guje ya fice ko takalmi be sanya ba,haka ya fita cikin ruwa ya tada mai gadi ya bude ma sa gate,sai gidan Jabir.
Da fitar shi,Hauwa ta ce da Hajjo yi nishi,yi nishi Hajjo da yardar ubangiji! Hajjo ta ce dallah kyaleni! Ba zan yi ba! Ba zan iya ba! Wayyo Inna! Allah ka ji kan Inna ta! Wayyo Inna! Allah ka gafartawa Inna…wayyo summassabilayassara! Innalillahi! Wayyo Allah! Hauwa ta ce ga kan dan ki,yi nishi! Ai kuwa da yardar ubangiji wani karfi ya zowa Hajjo,ta nisa da karfi sai ga katan dan ta ya sullubo mai kama da Khalid sak,har tsayin! Tuni ya fara callara ihu Hauwa ta yi saurin riko shi,Allahu akbar Khalid ya yi da. dan murna hawaye wiwi ke zuba daga idanun Hauwa,ji take kamar ita ta haihu,ta aje yaro a gefe ta ce saura mabiyiya,sa hannu mai za ta ji? Cike da mamaki ta ce Hajjo..Hajara…wani kan ne! Ai kuwa sai Hajjo ta fashe da kuka,ta ce kumamawa?na baki wlh,dan Allah na baki,wlh bazan iya ba,bazan iya haifo shi ba! wayyo Inna ta!. Hauwa ta ce na gode,amma sai dai kimin addua ni ma na haihu dan bazan iya haifo na cikin ki ba,ke kadai za ki iya,yi nishi ya fito. Hajjo ta ce na mi ki,Allah ka sa Hauwa ta haihu,Allah ka sa ta haihu,Allah ka sa ta haifo har na ciki na! Hauwa ta murmusa,cikin lallabi ta ce Allah ya amsa,amma sai kinyi nishi,Hajjo ban yi nishin ba! Ke ki yi nishin mana! Dallah ki barni na ji da abunda ke damu n! Wayyo Inna,karfi na ya kare,Hauwa ta ce daure….da karfi duk da dai be kai wanda ta yi na fari ba,ta nisa,sai kuwa subul na biyun ya fito wanda be da bambamci da na farko! Ya na fitowa shi ma ya callara na shi kukan,tuni mabiyiyi ta biyo sa,ba kari sam ba ta karu ba,nan ta kwanta ta na mayar da numfashi,Hajjo mai kuka sai gashi ta na murmushi. Hauwa ta ce Khalid sak mu ka samu har su biyu,ya zan yi na yanke cibiyar? Daga kwance murya shake tana mayar da mumfashi Hajjo ta ce duba cikin waccan drawer akwai saban reza da zare,ki dauko. Jarirai na kuka Hauwa ta dauko,Hajjo ta ce awna da danyatsan ki na tsakiya,daidai tsayin za ki yanke,sai ki daure karshen da kyau,in be dauruba jini zai zo yana zuba tawajan.
Yanda ta gwada ma ta,hakan ko Hauwa ta yi,ta nade su cikin shalw,ta ba ta daya ta bashi nono,sannan ta fara gyaran wajan. Kafin Hajjo ta shiga wanka sai da ta ba su nono dukkan su,sai dai wannan karan ma tana wannan ciwan cikin kamar na haihuwar Neena.
Ruwa ya tsagaita sai yayyafi,da ke asuba ta yi ,an fara kiraye kirayen sallah,tana wanka Hauwa zaune da babies sai ga Khalid jike jagab,Jabir biye da shi,shi ma din ya jige amma ba sosai ba. Ganin jarire har biyu Khalid ya rikice,gashi jike ya ke ba damar dauka,hugn din Hauwa yayi, fadi ya ke dukwannan nawa ne? Alhamdulillah ka ga kyautar Allah,da ya tashi bani sai ya bani biyu!!! Jabir ya ce dama yanda cikin nan kamar tulu ya kumbura sis dina ai sai dai biyun!Ya Hajaran ta ke? Hauwa ta ce lfy lau,sai dai ciwan ciki,Jabir ya ce yea dama wasu na yi,PCM ya kamata a mata,da an yi mata allurar za ta sami sauki inshaAllahu,idan gari yayi haske sai kawai ku kai ta hosptal dan duba su da kyau,haihuwan gidan nan ban fiya san shi ba,gaskiya ka yi sakaci,Allah kuma ya kawo da sauki. Toh toh toh Doctor!ahhh ai bazan sake ba! Khalid ya fada cikin murna. Hauwa da Jabir dai uziri kawai su ka ma sa,Gaba daya a rude ya ke,ya kalli wannan sai ya dawo ya kalli wannan,ya daga waya ya kira Hajiya,ita ma Hajiya murnar gun ta kamar ta fito ta wayar,cewa ta yi gari na haske za su ganta. Masallaci su ka tafi,kafin su dawo Hajjo ta fito ta shirya tsaf. Hauwa ke ba ta lbryn kyautar da ta ma ta tin kan ya fito duniya,har da gwada maganar ta Hajjo. Dariya su ke sosai,har Khalid ya shigo,ya na mata murmushi cike da kauna,ya ma manta Hauwa na wajan ya jawo ta jikin sa,Hauwar ta shige bandaki ta wayance da wanke hannu,shikuwa Khalid hugn matar sa yayi gam,sannan ya bi fuskarta da kiss ta koina,ya na na gode maman yan biyu,na gode na gode. Jabir zai iya shigowa ya gan ki? Ta ce eh bissimillah. Sai da ya shigo da Jabir Hauwa ta fito. Cikin nuna kulawa su ka gaisa. Khalid ya dau babban dan sa,ya zauna kusa da Hajjo ya ce Suger da wani suna zan ma sa huduba? Ta kalli Jabir sannan ta ce sunan yaya na,ka ma sa da suna JABIR! Farin ciki da alfahari su ka bayyana fuskar Jabir,sai gyada kai ya ke. Khalid ya ce toh Khalid ya haifi Jabir kenan! Sai a yi din. Duka su ka sa dariya,yayiwa yaran huduba da Jabir,Jabir ya karbi takwarar sa,Khalid ya karbi na biyun,ya ce wannan fa? Sabir ne? Hajjo na dariya ta ce wannan kuma sai dai ka tambayi maman sa,baki bude Khalid ya ce wata maman ta sa kuma? Hajjo ta ce ga ta kusa da kai. Ya juya ya kalli Hauwa,sai murmushi ta ke,ya ce ta yaya ki ka zama maman shi? Hauwa ta ce tin kafin ya fito aka min kyautar sa ai,kai amma Hajjo daban ki ke,da gaske ni zan zaba ma sa suna? Hajjo ta gyada kai,Hauwa ta ce toh a sa sunan Baba na,Abbakar. Khalid ya gyada kai,ya ce madallah da Baba,ya ma sa huduba da sunan Baban Hauwa,shi ma ya ce da ya sani ya tsaya da kila ta haifi uku,shi ma ya sami na shi. Da wasa da dariya ya raka Jabir. Ya dawo ya tadda Hauwa da Neena wajan Hajjo,murna ya cika Neena,atlast! Ita ma ta na da kanne. Hauwa ce ta janye ta,su ka fita suna jin ta ta kira baban ta tana Baba an sami karuwa fa,na haifo takwarar ka! Sai murna ta ke!
Khalid ya janyo Hajjo jikan sa,ya ce ba fa ko dayaushe za ki na ba su nono su ta tsotsa ba,daga ganin yaran nan tsotso za su yi! Hajjo ta ce toh idan ban ba su ba me zan yi da shi? Kayya! Me za ki yi da su? Ai nawa ne! Bazan barai su lalata min mata ba! Hajjo ta ce Ah wannan ai child abuse ne!! Ya ce eh na yarda,in kin ga dama ma kira ni Child abuse in dai kan wannan ne zan amsa! Duka dariya su ke,ya ce kara kara dai in dai kara ce sai DIYA MACE! Ya bazan so ki ba? I love you big. Ta ce hw big? Ya ce bigger nd larger than lyf. Ya fara kissing din ta,babies su ka callar kuka a tare,ya dago da sauri ya na nifa ba za a matsa min ba!kar fa a bata min rai na!! Hajjo na dariya ta ce me aka ce da maza?? Takura indai irin wannan yanzu ka fara gani! Ba dai ka zama Baba ba? Wlcm to d system……….!!!!
“Every female is an angel
Don’t west tym in selecting
Unique,instead spend tym in
Undstanding them……..”
ALHAMDULILLAH
Ta ku KHADIJA SIDI
RAMADAN KAREEM:)
For your comment nd correction txt me
07018583783
Advertisements
SHARE THIS:
TwitterFacebookGoogle
RELATED