Showing 42001 words to 45000 words out of 67328 words

Chapter 15 - Diya Mace Book Complete by khadija sidi .txt

well cikin dogayen maza irina gajere ne,cikin mata irin ku Suger ina ga shi ne za a kira shi dogo,kai kamar ma tsayin ku daya ma fa,shi dogo ke kuma doguwa! Hajjo ta watsa ma sa harara. Ya kara da kina da elegant man kamar Khalid ina mamakin me za ki yi da mutum laba laba kamar mace! Hajjo ta katse shi da fadin ban san cin fuska! He is my husby to be! Khalid ya dara,ya ce ba ku dace ba,you deserve someone lyk me. Hajjo ta ce no,u ar nt my type,plus ban san ka!! Dariya yayi mai kayatarwa,ya ce Suger Suger my dear innocent Suger! Ban da ke da abun ki ai ba maganar so mu ke ba,maganar making family mu ke,you don’t luv me nd i u,equation balanced,u love ur daughter nd i her,ina so na haihu nd u need a fmly,in dat case we both need each oda Suger… Hajjo ta murtuke fuska tare da fadin no ni ban bukatar fmly,in ma ina bukata din ba dai da kai ba,sai dai da Suraj…sun shigo kumurya,sun kama hanyar unguwar su Hajjo.
Shiru Khalid yayi,daga bisani ya ce d more u try to push me away,d more find you interesting,you ar such an adventure in my lyf dat i can’t resist Suger,so get use to it. Banza ta ma sa,cikin ranta kuwa tafasa ta ke,ya maishe ta kamar toy da zai na having fun da,burin shi ya takura ta a kullum yaumin ya ji dadi,gashi Allah sai hada su ya ke. Ganin mota fake kofar gidan Indo ya sa ta sake kallan wajen da sauri. Ya salam! Suraj,motar Suraj ne,ai kuwa sai ta hango shi jin gine jikin motar. Ya dade yana jiran ta,ya kira ta ba ta daga ba,gashi waje da da nisa bare ya ce zai je ya dawo. Allah Allah ya ke ya sa ta a idan sa,tin bayan rabuwar su da Ayush ya ke shiraya abunda zai fada ma ta,son ta yake ji ya na ma sa ambaliya cikin ran sa,tin da ya ji lbryn ta ya ke tausayin ta,idan be auri Hajjo ba gani ya ke ya yi asara babba.
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(gro


























.
Skip to content
ummu-abdoul
MENU
Diya mace 3rd
Posted by UMMU-ABDOUL on OCTOBER 17, 2016
​[16/10 21:48] .: /25, 5:20 PM] Salmah Ateeku: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
5⃣0⃣
Ganin abun da ya dauke ma ta hankali zuciyar Khalid ta kada,ran sa ya fara baci,wato wannan be hakura ba kenan. Ya ja mota ya faka daga gefe,sai a sannan ta ji karar wayar ta,kafin ta dauka ta katse,ta dubu ashe Suraj ne,ya jima ya na kiranta ba ta ji ba,ya ma ta miss calls ba adadi. Daga ido ta yi ta kalli inda ya ke tsaye,wayar ruke a hannun sa. Ba shakka ya gane motar,motar jiya ce,kuma ya gane wanda ke zaune cikin motar tare da Hajjo,mutumin jiya da ta kira autan Hajiya ne,wato Khalid,dama dan tana tare da shi ne ta ki daga wayar sa?kishi da bakin ciki su ka taru su ka ma sa malulu kasan makogaro.
Da sauri ta yunkura za ta bude mota ta na Suraj! Khalid ya sa lock tare da fadin idan ki na san kanki da arziki kar ki fita Hajara!ta juyo a fusace ta ce Khalid kar fa ka kai ni bango! Ka kusa kai ni bango! Idanun sa sun fara kadawa suna ja,lalle fadan rashin gaskiya. Rai bace ya ce ni dama a bangon na ke,ga shawara ta kar ki fita,idan kuma ki ka fita zaki sa na yi abunda daga ni har ke za mu yi danasani,i tell you! Rai bace ta ce zan fita,ka yi duk abunda ka ga dama,idan har abunda ka yi jiya be hana Suraj kara zuwa waje na ba,to babu abunda za ka yi ya hana shi,no way! Ya saki murmushi tare da fadin way! Yayinda ya bude motar,ya ce as u wish. Ai kuwa sai ta fita. Khalid ya girgiza kai tare da fadin dax it! Da ba ki fita ba Hajjo,wit d feelings am having ryt now,I don’t knw wat am capable of.
Fitar ta ta karasa wajan Suraj ta na dan Allah ka yi hakuri,ban san za ka zo ba. Rai bace ya ce wayar ki fa? Me ya sa ba ki dagawa? Ta ce wlh ya na jaka ban san….ganin Khalid gefen ta,ya sanya hannun shi cikin na ta ya sa ta daskarewa,za ta fincike da karfi sai ta yi tuntube,da sauri ya dago ta ba tare da bari Suraj ya gane tuntuben ta yi ba,ya hada ta da jikin sa,ya yi hugn din ta kam a jikin shi. Daga ita Har Suraj ba wanda be yi mutuwar tsaye ba! Kwakwalwar ta daskare,ji ta yi kamar zuciyar ta ta daina bugawa…ta yunkura da niyar kwacewa,Khalid ya ruke ta kam,ya kalli Suraj ya ce she mine,stay away! Suraj ya gyada kai tare da fadin na gane,kar ka damu,ya juya zai shige motar shi,Khalid ya saki Hajjo ta daga hannu ta sauke kan kuncin shi,ji ka ke tas ko motsawa be yi ba. idanun ta na spark sanna ta bi bayan Suraj da tuni ya shige motar sa,ta ce Suraj dan Allah,dan Allah fito ka saurare ni! Duk da idanun sa sun yi jajur,sam ba ya gane komai sai ya murmusa,ya ce bazan iya ba Hajjo,idan har zai iya mi ki haka a gaba na,Allah ya kadai ya san me zai yi a bayan ido na,ni namiji ne mai kishin kan sa da abunda ya ke so,na barki lfy,wish you d best in lyf! Ya tada motar sa,ta na Suraj! Suraj! Suraj!! Ina hankalin ya yi gaba,ba ko waiwaye ta na ji na gani ya fita daga rayuwar ta. Ta juyo ga Khalid da ke jingine jikin ta sa motar,ta ce Khalid na tsane ka fiye da tunanin ka,na gode da gudunmawar da ka bani a matsayi na na diya mace! Ta juya za ta shige cike,ya biyo bayan ya da niyar dakatar da ita,amma ina ta shige da sauri. Ya yi aiken yara har ya gaji,gashi wayar Sani na wajan sa bare ya kira shi,dan ya san tabbas Sanin ba ya nan ne,da ya na nan aiken da ya ke ta mu su da tuni ya fito. Da wannan ya juya ya koma kano,ran sa shi ma ba dadi ganin halin da Hajjo ta shiga.
Wata daya ba Suraj,duk yanda za ta yi ta ji daga gare shi ya yanke. Ta yi kokan har ta gaji,ita bakin cikin ta zubar ma ta da mutunci da Khalid ya yi a gaban Suraj,ya ma zai yi ya ma ta haka,Khalid da ko hannun ta be taba kokarin rukewa ba yayi hugn din ta gaban wanda ya ke san ta,ya ke so ya aure ta tsabar shi bai da adalci! Kamar Suraj din shi ma Khalid raban ta da shi wata daya kenan,ya raba ta da me san ta ba dole ya dauke wuta ba! Abunda Hajjo ke fadi kenan duk sanda ya zo ranta,gashi kuma ya na yawan zuwa din. Ta yanke shawarar yin aure da gaggawa ta karbe diyar ta ko Allah ya raba ta da Khalid ta huta.
Bangaran Khalid kuwa karfin hali kawai ya ke,so dayawa ya kan dauki mota yayo hanyar kumurya sai ya kai rabi sai kuma ya sake shawara ya dawo. Ko hanya ba ta hada sa da asibiti ba sai ya san yanda yayi ya yi zagaye ya biyo ko Allah zai sa ya sa ya hadu da Hajjo. Har cikin ransa missing din ta ya ke,missing din kallan ta,kamshin ta da uwa uba fadan su. Wani sa’in shi kadai sai a ganshi ya ma murmushi har dariya ma,toh ya tuno wata rigimar ta sa da Hajjo,hatta randa ya fara ganin ta tana fada da dan adaidaita akan naira hamsin ya tuna dariya ya ke sosai,it appears dat Hajjo ta shiga rayuwar sa. Ba kuma mai yawan tado ma sa da Hajjo kamar Neena,da ta yi wani abu ko be yi niyar tuno Hajjo ba sai ya tuno ta,kan ka ce mai sai ga Khalid ya fara fita hayyacin sa,hankalin Hauwa ya fara tashi dan ta kasa gane me ke damun mijin na ta,har ta fara zargin ko rashin haihuwan ta ne,ita ma ta fara daga hankalin ta,ta zaunar da shi tai ta ma sa kuka,ya ce kar ta damu,ba komai amma ta ki ji,sai kawai ma ta kai korafi wajan Hajiya. Hajiya ta yi kiran sa,su ka sa shi a gaba ita da Jabir a lalle sai ya fada mu su damuwan shi,Hajiya ta ce ji fa har ya fada,ko wani abu Hauwan ta yi ma ne? Khalid ya girgiza kai ya ce lfy lau fa,ita dai ta damu kan ta,na fada ma ta ba damuwan ta ba ne! Jabir ya ce ya za ka ce damuwan ka ba zai zama na ta ba? Shez ur wife bro.
Hajiya ta ce Khalid,na san da akwai da abun da ke da mun ka,hakan nan ba za ka fada ka ramr haka ba,let d cat out of d bag!ya kalli Jabir,ya ce Hajiya ya dan ba mu wuri…Jabir ya ce ku ji mara kunya,ba in da zani,Hajiya ta ce ka dan ba mu wurin ma na Jabir,Jabir ya ki motsawa,ya ce ai damuwar Khalid shi ma damuwar sa ce. Da dai su ka ga da gaske be motsawan,Hajiya ta ce Khalid ya yi hakuri ya kyale sa,ya fadi damuwar sa. Khalid ya dan sunkuyar da kai saboda nauyin abunda zai fita da ga bakin sa,ya ce Hajiya wlh kan maganar Hajara ne……wato wani irin dariya Jabir ya sheke da,har da mingirowa daga kan kujera!,ita kan ta Hajiyar daurewa ta yi ba ta yi na ta dariyar ba,ta fara yiwa Jabir fada ka ga yayan banza,menene abun dariya?.dole ya ce ka bashi wuri. Khalid ya murtuke fuska,dan ya san za a yi haka. Jabir na kwalla tsabar dariya ya ce Khalid yau kuma ina tunkaho da ji da kan na ka? Ina kuma takamar? Nan fa ce min kayi da ka fada ma ta murna za ta hau,ai ni da na ji shiru na zaci an gama magana,ashe kanina na nan ya na garuwa! Khalid ya ta shi a fusace zai fita,Hajiya ta dakatar da shi,ta ce dawo ka zauna,shi ya kamata ya fita,idan ba za ka bashi shawara ba ka tashi a sauka lfy. Da kyar ya iya daina dariyar. Hajiya ta ce ba na so na sa baki zancen nan na ku da Hajjo,shi ya sa ka ji na mu ku shiru,amma yanda za a yi yau ka sake komawa,ka gwada shawo kan ta,idan ba ta yarda ba,sai mu sa baki,ko Jabir? Ya na murmushin mugunta ya ce haka Hajiya,ka je ka lallabo child abuse din ka,ka kwantar da kai,ba wai ka je da gadara da jiji da kai yanda ka saba ba,kila ka shawo kan ta. Duk da dai ta shakiyanci ya ke maganar,shawarar ta yiwa Khalid,ya tashi da sauri ya na fadin yanzu hudu na san ta na kan hanyar komawa,bara na yi sauri na shirya na tafi,ya fita da sauri,ya na jiyo dariyar Jabir,shi abun ya ma sa dadi.
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
5⃣1⃣
Har in da za ta sami mota Ayush ta sauke ta,ta na dada ba ta baki akan halin da ta ke ciki. Hajjo ta ce ba komai,ta so dai in ma rabuwa za ta yi da Suraj suyi na girma da arziki,ba irin wanda su ka yi yanzu ba. Ayush ta ce kar ta damu,a hankali zai gane. Su ka yi sallama,ta hau motar da zai kai ta kumurya. Da ke a tasha ta sauka sai da ta kara hawa wata motar,ta sauke ta a titi,ta tako dumin karasawa gidan Indo. Ta wuto ta wata majilasar yan zaman banza,suna ganin ta su ka fara maganar ta kamar yanda su ka saba duk sanda ta gifta ta wajan,wani ya ce ummmm ga fa iyayen boko,wa zai ce wannan diyar garin nan ce! Gaba daya sai saura su ka sa baki a ka sa Hajjo a faifai,cikin su har da Nuhu abokin Garbati,sam ba ta lura da shi ba. Takalmi ya sa bi bayan ta,ya ga gidan da ta shiga ya tabbatar Hajjon ce da gaske sannan ya juya da sauri sai gidan su Garbati. A kofar gida ya tadda shi,ya yi dakal dakal da shi,ga kazanta ga talauci,ga rashin haihuwa,ya yi aure auren har ya gaji amma shiru be sake samun haihuwa ba,sai ma mata da ya ke aure mai nakada ma sa na jaki duk sanda be kawo na cefane ba,Iyalle da Baba kadai ke iya cetan sa. Yanzun ma tunanin inda zai samu na dare ya ke Nuhu ya zo ya tadda shi.
Bayan Hajjo ta yi wanka ta na cin abunci sai ga yaro ya zo ya ce wai ana sallama da Hajjo,ni kuma? Kai ka ce ba ta nan. Indo ta ce ba a haka Hajjo,ko lekawa ne ki yi mana ki ga wake sallamar,je ka ce ta na zuwa. Rai bace ta cire hannu daga abunci,tuwo ne miyar yauki,ta wanke hannu,ta yafa mayafi ta fito. Lekowar ta ta yi arba da Garbati da Nuhu. Cikin mamaki dan ta gane su sarai ta ke kallan su,shi kuwa Garbati sam be gane ta ba,zubewa kasa yayi ya na Hajiya ina wuni? Nuhu ya dan bige shi tare da fadin kai dallah tashi Hajjon ce fa,dallah Hajjo ce,gane ta ne ba ka yi ba! Garbati ya tashi da sauri ya na aw aw ashe!ya kalli Hajjo da kyau ya ce yasin ita ce,Hajjo ai kin zama kamar diyar yan birni shiya sa ban gane ki ba! Murmushin ta kaici ta saki,ta ce lfy? Garbati me ya kawo ka guna? Garbati ya ce eh na’am? Nuhu ya zingure shi. Sannan ya ce dama dai kin san saki daya na mi ki,na zo ne mu sasanta mu gyara auren mu ko kuwa ki bani diya ta……dariya Hajjo ta sa,har ta kusa kwarewa,Garbati ya ce yo menene abun dariyar? Kar fa ki bata min rai na! Ta na dariya ta ce ko ba ran ka ba? In yayi dubu toh zai dauwama a bace Garbati! Tin dosowar Khalid layin ya hangi Hajjo tsaye tare da wasu,har zai fara kunar rai sai ya ga wasu almajirai ne ma,ba shakka sadaka su ka zo nema,sai ya saki ran sa ya faka motar ya fito. Tin da Hajjo ta ke ba ta taba farin ciki da ganin Khalid ba sai yau,ya fito tas da shi cikin farar shadda ta sha bugu da guga,dinki boda an masa aikin sama da shudin zare,ga wani shudin hula da ta sha kari ya sanya ta a karkace,ga takalmin sa shudi,hunnun ruke da mukullin mota ya karaso wajan su Hajjo,tuni kamshin sa ya maye su,su kan su su Garbati sun kiyaya. Ta kasa dauke ido da ga kallan shi,ya ce Suger yanda ki ke kallo na…. kar ki damu i miss you more!ya kashe ma ta ido. Ta dauke kai ta na fadin in ba ka yi fariya ba ba sunan ka Khalid ba. Murmushi yayi tare da fadin na zo mi ki da magana mai muhimmanci yi sauri ki sallame su,taimako su ka zo nema gurin ki ko? Ya sa hannu a aljihu ya fito da dubunne farare kal ya ce nawa ku ke bukata bayin Allah? Ganin kudi makudai hannun Khalid tuni hankalin su ya tashi,Garbati ya ce eh na’am diya ta na zo karba,diyar ka? Khalid ya maimaita,ya kalli Hajjo ya ce Suger kin kuma fara ruke diyar mutane? Turo ma sa diyar ta sa ma na ya kama gaban sa,if u realy need a daughter dat much da kin fada min na kawo mi ki Neena. Hajjo ta murmusa tare da fadin ai Neena ya ke nufi! Khalid ya kalli Garbati ya ce kina nufin wannan local champion din is ur…..ex- husband ta karasa ma sa. Sai da yayi dariya mai isar sa,sannan ya ce amma Allah ya isan ki Suger. Ya mayarda kudin sa cikin aljihu,Nuhu ya hadiyi yawan bakin ciki ganin komwar kudin,Khalid ya ce kun ga wannan? Mata ta ce! Karo na farko da ya kira ta mata ta ba tare da ta musa ba. Ya kuma ce diyar da ka ke magana akai,tin shekara gomashabiyu da su ka shude ta zama diya ta. Ran da na sake ganin ku anan sai na sa an kama mun ku,an kulle am batar mun da ku! Abun ku da yan kauye tuni su ka tsorata,dama ga damin kudi sun gama gani hannun Khalid ba mamaki ma su ne masu kasar. Garbati ya ce ba ma sai an kai ga haka ba,bara mu tafi,ya ja Nuhu,su na dan yin gaba Nuhu ya fara sirfa ma sa masifa,wai ai gashi ya mu su asara,mai makon ya hakura su zauna a almajiran da Khalid ya yi zato,ko ya ce a ba shi wani abu ko a bashi diyar sa,yanda su ka yi za su fada. Shi ko Garbati ganin yanda Hajjo ta koma,ga kuma wanda ke kiran kansa mijin ta ne ya kashe ma sa jiki,wai yar Hajjon sa da ya sani a matsayin matar sa,Allah kenan! Allah kenan! Allah kenan! Abunda ya ke ta maimaitawa kenan.
Bayan tafiyar su Hajjo ta ce me ya kawo ka mallam? Khalid ya murmusa ya ce is dat a way of sayin thank you? Ta ce thank you for wat? For saving u from dat local champoin u ar callin an ex-husby!Hajjo ta ce ko ba ka zo ba dama zai tafi,ya ce u ar glad am came Suger,admit it. Ta yi shiru. Da ya ga ba ta niyar magana ya ce magana za mu yi,za mu iya zama a soro? Kafin ta ba shi amsa ma har ya shiga,ta ce dan ma su gida! Ya ce na’am biyo shi ta yi ta ce no ba magana na yi ba. Murmushi kawai ya ma ta dan ya ji abunda ta ce saraj. Ta shige ciki dauko abun zama,ta ke fada ma Indo Khalid ne fa ya zo. Indo ta ce shi ne za ki zaunar da shi a soro? Cikin awaki,ki shigo da shi tsakar gida mana. Ta ce toh,ko dan darajar korar ma ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login