Showing 9001 words to 12000 words out of 67328 words
Chapter 4 - Diya Mace Book Complete by khadija sidi .txt
ta yi baki ya dagawa Indo gankali,har ta rungumeta Indo kallan ta ta ke,ta ce Hajjo sai ka ce da ke ake miya wannan rama taki? Ina mutan gidan? Hajjo ta ce sun fita,daga ni sai baban su Garbati,kuma sun hana ni fita,Garbati ya ce duk randa na sake fita sai ya kusan kashe ni. Kashe ki? Indo ta kama baki,ta ja hannun Hajjo su ka yi daki,ga dai dakin tsaf da shi Hajjo ta gyara ko ina,sai dai kuma dakin gum ya ke da warin Garbati,Indo ta zauna tare Hajjo bakin gado,ta ce Hajjo ya dakin na ki wari haka? Hajjo ta ce kayan wankin Garbati ne,idan ya sa kaya ranar juma’a baya sauya su sai wata Juma’ar in yayyi wanka dama juma’a juma’a ya ke wanka,toh kayan na sa can bisa kyaure su ke warin….
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[11:04am, 5/5/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
1⃣3⃣
Indo ta dafe kai ta ce hoo Hajjo zama da kazamin miji sai hakuri,Hajjo ta ce wlh ba na san shi Indo,na fi san zama da Inna ta,dan Allah ki mu su magana su bar ni na koma gida. Indo ta ce ki yi hakuri Hajjo,ki yi hakuri,sai da na biya ta wajan Inna kafin na zo,ta fito da kayan kamshi,su kananfari,jitta da dai sauran su,ta mikawa Hajjo ta ce ga tsarabar Inna. Hajjo ta ki karba,ta ce Inna ba ta so na,ta ki cewa a mayar da ni ta kuma ki zuwa. Hankalin Indo ya dada tashi,nan ta ci gaba da ma ta bayanin Baba ne ya hana Inna zuwa,ita din ta na kewar ta,sannan ta hakura ta karba. Indo ta tambaye ta ya zaman ta a gidan,ta na jin dadi kuwa? Nan ta kwashe komai da take ciki,har da ruwan rubutun da Garbati ya ke bata,Indo ta ce oh ya Allahu,Allah sarki Hajjo shi ya sa na ga kin zama shiru shiru haka,asirce ki ya ke,so ya ke ya maisheki baiwar sa nan gaba,kai wannan akwai azzalumai,nan gaba ya baki kar ki sha,ki faki idon sa ki zubar,kin ji ko? Hajjo ta gyada kai alamar eh. Indo ta ce wannan duk aikin ke kadai ki ke yi Hajjo? Wlh da sake,da gida zani amma na fasa wajan Inna zan koma dole a kwatar mi ki hakkin ki! Tashi mu je na taya ki aikin! Hajjo ta ce laaa zan iya,ai har na fara sabawa,har fa girki na ke,da na sa hannu na ke gama komai. Cikin tausayawa Indo ta ce Hajjo Allah ya zama gatan ki,mu je na taya ki dan Allah. Hajjo ta wuce Indo biye da ita. Ta sa ma ta hannu su ka gama aikin gidan tas.
Kamar yanda Indo ta fada,wajan Innar ta koma,jin halin da Hajjo ta ke ciki ran Inna be so ba,amma sai ta buye ta ce in banda abun ki dan an sakarwa Hajjo aiki wani abu ne? Hajjo diya mace ce,aiki ga diya mace ai taimako ne,kin ga za ta tashi a kwararriyar mace mai himma,kuma zancen asirce ta Indo ba su isa su yi ma ta abunda Allah be kaddara ba,wannan shiru shirun da ki ka ga Hajjo ta zama wlh adduar uwa ce,nutsuwa ta ke kasencewar adduar da na ke ma ta na Allah ya nutsar min da diya ta gidan mijin ta,adduar iyaye ga ‘ya’yan su karbabbiya ce,dan ko asirin Garbati ya ci Hajjo,to kadan zai yi tasiri kanta,zan kuma ci gaba da ma ta addua,kuma ki na yawan zuwa ki na duba ta dan Allah,ba komai ai diya mace dama da aiki aka san ta. Jiki a sanyaye ta ce toh Inna,Allah ya sa mu dace,Inna ta ce ameen,Allah ya ci albarka. Indo ta ce amen,gami da mikewa ta ce Inna bara na koma toh. Inna ta ce a sauka lfy,Allah ya tsare,ta ce amen amen.
Washagari da wani irin matsanan cin ciwan mara Hajjo ta tashi,haka a daddafe ta dinga yin aiki,duk da Iyalle ta lura da haka,sai ta yi kamar ba ta gani ba,sai Mairo ce ma ta zo fita dandali ta ga Hajjo durkushe gaban murhu ta ce ke Hajjo mene wai? Baki da lfy ne? Ta dago idanun ta sun kada ta ce Mairo kasan ciki na ciwo,Mairo ta ce sannu toh!ta kama hanyar ta ta fice. A haka tai ta fama da hura wuta ta na gyarawa Iyalle har Iyalle ta gama girkin ta,Hajjo ta yi shara ta yi wanke wanke…
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[1
[16/10 21:44] .: 05am, 5/5/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
1⃣4⃣
Ta na gamawa ta koma daki ta kwanta,ciwo ya ki ya barta,daga bisani kuma ta ji kamar wani abu na fita daga jikin ta,ta nan kwance ta ki motsawa sai ga Kande ta shigo ta na fadin Hajjo wai me ke damun ki ne? Hajjo ta ce kasan ciki na ke min ciwo,yanzu na ji kamar wani abu na fita daga jikina,kande ta ce mugani? Dan matsa na gani,ko da ta matsa Kande ta ga halin da Hajjo ta ke ciki,ita ma Hajjo sai a sannan ta gani,sai ta sa kuka. Kande ta ce menene na kukan? Ai al’ada ce,kowace cikakkiyar diya mace ta na yi,ke ma yau kin zama cikakkiyar diya ma ce,hukunci ya hau kan ki,ki bar kuka,ita dai Hajjo ta ki ta yi shiru,gani ta ke mutuwa za ta yi,da kyar Kande ta shawo kanta,ta ce auduga ake siya ake sawa,ko kuma kyalle,itama ba ta da audugar,Hajjo ta kawo kyalle mai kyau sai ta koya ma ta,cikin kayan Hajjo ta sami wani dankwalin ta,ta yanka,sai da ta kai ma ta ruwa bandaki,sannan ta gwada ma ta yanda za ta sa kyalle,dake ciwan diya mace aka ce na diya mace ne,Kande ba ta nuna kyama ba,taiwa Hajjo kara kafin ta fito ta cire zanin gadon da Hajjo ta bata ta wanke ta shimfida ma ta wani,sai da ta tabbatar Hajjo ta yi tsaf,ta ba ta Panadol sanan ta ce da Hajjo ta kwanta kafin Garbati ya dawo sai ta tambaye shi ya bada kudin auduga ta siyo mata,Hajjo ta na fama da ciwan mara,ta ce ma ta toh kawai,idanu runtse.
Ko da Garbati ya dawo Kande ta fada ma sa halin da Hajjo ke ciki,ya ba da kudi ta siyo ma ta auduga,sai ya kalle ta yace yo wani kudi zan ba ki? Ina na gan sa? An fada mi ki tsintar su ake a kasa? Ta yi kunzugu in za ta yi,idan kuma ba za ta yi ba tai ta zama haka,kar fa ki matsa min Kande,dallah bace min da gani. Cikin takaici Kande ta tafi,ta na Allah ya sauwakewa matsolo. Ya ce kar ki nemi ki zage ni sai na kwade ki wlh! Kande ta yi tafiyar ta abunta. Da Hajjo ta tashi,sai Kande ta ce da ita idan akwai zani ta kawo ta yayyanka ma ta,sai ta ke amfani da shi tin da audugar ba ta samu ba. Duk da ba ta wani sitirar arziki,wani zanin ta ta bayar,Kande ta yayyan ka,ta ce da ta ji ya jike ta sake wani,Hajjo ta ce toh,ta yi godiya. Ranar dai a takure ta wuni,Allah ya so Iyalle ta daga ma ta kafa ba ta kara ma ta wani aikin ba,shi ko Garbati bin ta ya ke da kallo kawai,ashe wannan yarinyar ma ta cika diya mace,lalle ya kusa dai na kawar da kai ya na shuka dusa kullum ba riba.
Kwana biyu Hajjo ta daina ciwan mara,ta dan fara samin nutsuwa,kuma yanda Kande ta koya ma ta hakan ta ke yi,gaba daya wasa da su Mairo ya fita da ga kanta,ita yanzu kullum lissafin ta shi ne wani aiki za ta fara,wanne zai fi ma ta saukin yi. Ga tsafta sosai,ba za ka taba ganin kazantar Hajjo ba. Rana na hudu sai ta ga ya dauke,ko da ta fadawa Kande sai ta ce ta dan jirkin ta ta tabbatar ya dauke sai ta yi wanka,ta dai san yanda ake ko? Hajjo ta ce waye be iya wanka ba?ba dai a dirje jiki da soso da sabulu ba? Kande ta ce ba wannan na ke nufi ba,irin wanda addini ya koyar fa,wankan tsarki,Hajjo ta ce ayyo,dama akwai shi?ita ba ta taba ji ba ai,Kande ta yi mamaki,ko a islamiyar ku ma ba a koya mu ku ba?Hajjo ta ce ta allo na ke zuwa da ai,kuma aramma be taba koya mana ba. Kande ta ce toh,bari na koya mi ki,ba wuya ai. Nanan ta gwada ma ta,tare da ma ta bayanin hukunce hukuncen wankan.
A ranar da ta cika kwana biyar,da daddare Ayuba da Garbati tage tafe,sun dawo ne daga gun matan matan tashan da su ka saba lalubewa,Garbati ya ce da Ayuba kai aboki na na fa yi hakuri alkura’an,dan haka wannan yarinyar Hajjo ta cika diya mace,tinda har ta fara jini…kai ta fara? Ayuba ya katse shi da tambaya. Garbati ya ce yasin. Ayuba ya kame baki cike da mamaki,ya ce caf Garbati na ga kokarin ka,ai da ni ne da tuni na afka ma ta! Ya da aure na zan je ina samin faci faci wajan yan tasha? Garbati ya ce kai dai bari ayuba,yau din nan kuwa,a daren yau za a yi ya ta kare,afka ma ta zan yi yasin! Ayuba ya ce atoh ko kai fa,haka su ka ci gaba da tafiya suna hirar su da karfi murya a sama,ko da su ka zo kofar gidan su Garbati sai Ayuba ya bashi hannu su ka tafa,kana ya ce kar fa ka bani kunya mutumi na,na san ka da himma,Garbati ya washe baki,ka dai jira lbry gobe,suna dariyar shakiyanci su ka yi sallama su ka rabu,Garbati ya shige gidan su,Ayuba ya kama hanyar shagon sa
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[11:05am, 5/5/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
1⃣5⃣
Hajjo na idda Sallar ta na isha’i ta yi baccin ta,da ke tin a jiyan da daddare ta samu ta yi wanka. Garbati ya shigo ya ja kofa ya sakace,ya jima a kanta ya na kallan ta,ya cire babbar rigar da ta yi kusan sati jikin sa ya wulgar a kasa,tini warin zufa ya gume dakin,ba wani nafila bare neman yardar ubangiji,ba lallami da lumana,ba tausayi bare soyayya,kamar yanda ya ce zai afka ma ta din,haka ko ya afka ma ta kamar dabba. Tini Hajjo ta fara neman ceto,tana kokarin kwacar kanta,tana ihu da kuka,Garbati ya sa hannu ya toshe ma ta baki,sai fa inda karfin sa ya kare………
Hajjo tinda Garbati ya tashe ta ta hanya mafi muni,har ya gama biyawa kansa bukata ya mingina ya fara munshari kamar rago ba ta rintsaba,ta ma kasa kuka da baki sai hawaye da ajiyar zuciya kawai,ga warin Garbati da ya addabe ta da ke gefen ta ya ke kwance,yanda ka san ya sami sa’ar sa haka ya gwada ma ta karfi,dan haka ta ma ka sa kwakkwarar motsi,dan ita kam jira ta ke kawai ta Allah ta kasance a kan ta,ta mutu ta huta.
Idanun ta biyu,ba ta samu ta runtsaba har asuba ta yi Iyalle ta zo tashin ta yanda ta saba yi da an idda sallar asuba. Ta fara buga kofar ta na Hajjo! Ke Hajjo Allah ya yi dare gari ya waye,a fito aiki!Hajjo ta na fama da kanta ko motsawa ba ta yi,Garbati ne ya amsa ma ta cikin bacci,ya ce Iyalle Hajjo fa ba za ta iya ko motsawa ba,yau dai a barta ta huta. Iyalle ta ce a barta ta huta? Zancen banza zancen hofi! Wani hutu kuma Allah ya wayi gari? Yau ga saban salo! Ta ci gaba da buga kofa,Hajjo,kai Garbati tashe ta mana!!!!
Iyalle! Na fa fada mi ki Hajjo ba ta iya tashi ba. Iyalle ta ce a wani dalili wai? Garbati ya ce Iyalle kin fa dame ni,tam! Na ce ka tada min matar ka kace ba za ta iya motsawa ba,dole na dame ka! Da ke Garbati gabo ne,da karfi ya ce Iyalle! Afka ma ta na yi jiya da dare,kuma na ma ta tilis! Aradu ko motsawa ba ta iya yi in kina musu shigo ki ganta!!!!! Shiru ake ji,Iyalle ba ta kara tankawa ba ta juya ta koma dakin ta,maganar Garbati ta rufe ma ta baki,shi ko Garbati ko ajikin sa ya ce Iyalle? Iyalle? Dama ai sai da na ki fada mi ki ki ka dage sai kin ji,kuma na fada kin min kunne uwar shego! Yo ai shikenan! Ya juya ya ci gaba da baccin sa,ba batun wanka bare kuma sallar asubahi. Iyalle ko ba ta sake waiwayen su ba.
Sai da rana ta take sannan Garbati ya tashi,ya dubi Hajjo da ke kwance kamar ba kashi a jikin ta,ya ce ke Hajjo! Kin fiya raki wallahi,dallah tashi,kar ki bata min rai na!!Hajjo ta sa kuka,dama kukan kwance ya ke kasan makogoranta,maimakon ya tausaya ma ta,sai ma ya ja tsaki,mtsw yo kukan na menene? Kan ki aka fara? Idan kin yi mai isar ki kya tashi,ya kwashi kayan sa masu datti ya mayar ya fita ya na mika,Iyalle da Kande da ke zaune tsakar gida su ka kalle shi su ka kau da kai,cikin ko in kula ya dau buta,ya shiga yayi wanka dan sami tsarki ba tare da yayi na soso da sabulu ba,kayan nan na sa mai taddi dai ya mayar,ya fita abun sa ya na taku dai dai,gani ya ke daidai ya ke da kowa,sallar asubahi ma wa ya sani ko da azahar zai hada.
Da fitar sa,Iyalle ta ce da Kande,Kande je ki gano yar mutane,Allah ya sa bai karta ba. Jiki na rawa Kande ta ce toh,ta shiga dakin da Hajjo ke kwance,duk da Garbati ba ya nan dakin be daina warin sa ba. Ta na yi tana dauke numfashi ta karasa gadon da Hajjo ke kwance sai kuka ta ke,ganin Kande kan ta,sai ta fara dan Allah Kande kira Indo,dan Allah kirawo Inna ta da Indo,cikin tausayawa da ke Kande bazawara ce,ta san halin da Hajjo ke ciki,bare kuma Garbati kan fanka ne mijin ta,da sauri ta ce toh. Ta fito ta fadawa Iyalle,Iyalle ta ce ai sai ki maza ki yi kiran Indon,Kande ta ja mayafi ta fice,ta bar Iyalle cikin zulumi,can sai ga Kande da Indo,sama sama su ka gaisa sannan ta shige wajan Hajjo,ganin halin da Hajjo ke ciki Indo ta rabka salati,ta na fadin sannu Hajjo,ki yi hakuri,girman kenan,diya macen kenan,ita dai Hajjo sai kuka. Da taimakon Kande aka hada ruwan zafi a daki aka dan gasawa Hajjo jiki,da ta dan ware sai aka kai ma ta ruwa bayi,da kyar ta ke iya tafiya,kamar mai koyan tafiya sai da Indo ta dan dafa ma ta,ta kai ta bayi,sannan ta barta ta yi wanka,Kande ta ce har da wanda na koya mi ki jiya za ki yi,niyar za ki banban ta kamar dai yanda na ce kin ji ko? Hajjo ta ma ta banza,Indo ce ta tsaya ma ta,sai da ta tabbata ta yi,ta kamo ta su ka dawo daki,ta taimaka ta shirya,da kyar ta yarda ta sha kokon da Kande ta kawo ma ta,ita wallahi gidan Inna za ta koma,Garbati zai kashe ta….
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[11:06am, 5/5/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭CIWAN DIYA MACE👭👭👭
1⃣6⃣
Indo ta barta ta na shan kokon ta je ta wanke zanin gado,ko da ta dawo sai ta tadda Hajjo ta sami bacci,ta gyara ma ta kwanciya,sannan ta yiwa su Iyalle sallama,ta ce ta bar yara gida.
Hajjo ba ta tashi ba sai da la’asar ta yi,ko da ta ga Indo ta tafi sai ta sa kuka,gaba daya tsoran gidan ma ta ke,har abun ma ya fara kullar da su Iyalle,tin suna ba ta baki su ka ma ta banza,da ta ga dai ba mai rarrashin ta sai ta yi shiru. Ta fito ta na takawa da kyar za ta yi alwala,Mairo da ke zaune a tsakar gidan ta kwashe da dariya har da mirginawa,ta ce ke Hajjo! Kin ga yanda ki ke tafiya kuwa kamar yar kaciya yasin! Hajjo ta kalle ta ta daka ma ta harara,ta ce yarinya ke ma Allah ya sa a mi ki aure! Mairo ta tafa ta ce ai min din mana,sai mai? Ji ta da Allah! Ta dada kwashewa da dariya,Hajjo ta cije lebe,Kande ta fito ta na ke Mairo wlh idan ba ki dai na tsokanar ta ba sai na hada ki da Iyalle,kyale ta Hajjo,ba ta da hankali. Mairo ta fara gunguni,Hajjo ta gyada kai ta yi shigewar ta bandaki,ta na jiyo dariyar Mairo,Kande na kwabarta amma ta kasa shiru.
Shiko Garbati tin fitar shi be dawo ba sai bayan isha’i,Hajjo na jin shigowar shi ta suri filonta ta fito duk da da kyar ta ke takawa sai ga ta tana sauri sauri,har karo ta yi da Garbati,ya na ke bakya gani ne? Ta ma sa banza,dakin Iyalle ta shige,kamar daga sama su ka ganta a kan su hannun ta ruke da filo,lfy Hajjo? Iyalle ce ta tambaya,Hajjo ta ce Garbati ne ya dawo,kuma wlh bazan sake kwana a dakin ba….sai ta sa kuka har da shassheka. Iyalle ta tashi tsaye yayinda ita ma Kande ta bi sahun ta,ita ko Mairo tini ta yi baccin ta. Iyalle ta ce ah ah ba a yi haka ba Hajjo,yi hakuri ki koma…..ke Hajjo! Tahooo, muryar Garbati ce ta katse Iyalle,labulai ya daga hannun sa ruke da aci balbal. Ganin sa Hajjo ta kara ciki da sauri ta buya bayan Kande. Garbati ya ce Hajjo ki taho na ce! Kar ki bata min rai na! Hajjo ta ce na ki na taho din,na ki,wayyo wlh kashe ni zai yi!!! Ta kamkame Kande! Iyalle ta ce da Garbati kai kuwa Garbati yarinyar nan ta tsorata,ka dan bar ta ta kwana a nan din mana. Garbati ya ce Iyalle! Wlh sai na hado ki da Baba! Ina aka ce mace ta na gudun mijin ta! Yo ina ya dace ta kwana idan ba dakin ta na sunnah ba! Ke Hajjo taho mu tafi na ce! Iyalle ta kame baki,ta ce Hajjo zo ki bi mijin ki…Hajjo ta kurma ihu ni wlh bazan bi shi ba,wayyo na shiga uku na lalace! Wayyo yau mutuwa zan yi!!!!
Garbati ya na huci ya ce wlh sai kin kwana dakin ki!!! Yo toh menene amfanin aura min ita da aka yi! Hajjo ta ce bazan kwana din ba,ni ban ce a aura min kai