Showing 3001 words to 6000 words out of 67328 words

Chapter 2 - Diya Mace Book Complete by khadija sidi .txt

Amenatu ki na ina ne! Inna ta fito daga dakin ta yayinda shi ma Idi ya shigo a guje,ya tsaya gaban Baba ya na haki. Baba ya ce kai lfy? Menene? Idi da kyar ya ke magana dan haki ya ce Hajjo ce ta baran min da manja ta ta gudu,wlh sai ta biya ni! Ko na daki kudi na! Inna ta ce Hajjo kuwa? Daddawa fa na aike ta ta siyo min!
Baba ya murmusa,ya ce ni na ga abunda ba ki gani ba,kai yaro nawa ne manjar ta ka ga sadakin ta na biya ka a ciki! Inna ta dafe kirji SADAKI kuma! Baba ya ma ta banza,yayinda ya fito da kudi daga aljihun sa,Idi ya ce dari uku ne,Baba ya dirga dari uku ya mi ka ma Idi,ka ci sa’a yanzun nan na karbi sadakin ta,da wlh sai dai ka daki kudin na ka dan da kudi na dai ba zan cira na biya ba. Idi ya karbi kudi ya kama hanyar fita ya na fadin Allah ya so ki yarinya! Inna ta ce Mallam magana na ke fa,na ce wani sadaki ka ke magana akai ne? Baba ya ce sadakin Hajjo mana,Allah ya yanke min wahala ai,yarinyar da Garbati zai aura ta ce ta fasa auren,sai ni kuma na samawa kai na sauki na Hajjo dan na fitar da abokina kunya! Inna ta fara salati ta na sallallami,ta ce Mallam aure fa ka ce? Hajjon nawa ta ke Mallam!kwanan nan fa ta cika shekara goma shabiyu Mallam,Kai kuji wani yashashhsen zance,Hajjon nawa ta ke? Zama zan yi da ita in ta dawainiya da ita?kin manta motsin gado ce ba yarinya ba,ina ma ta ke ne? A gaban ido na ta shigo a guje kamar walkiya! Ke Hajjo ki na ina ne wai! Za ki fito ko sai na sabar mi ki! Inna ta ce Mallam na ce da kai na aike ta siyan daddawa…Baba ya ma ta banza,ya cigaba da fadin Hajjo wlh na dirga uku ba ki fito ba sai na mi ki dukan kawo wuka,ya fara dirge daya,biyu….
Tim!kamar daga sama sai ga Hajjo ta diro daga kan bishiyar mangaro,Baba ya ce shegiyar kaya! Ki ganta nan bishiya ta haye kamar birinya,Inna kallan Hajjo da ta yi tsumtsumu da ido ta ke cike da mamaki da tausayi. Ke tashi! Baba ya daka ma ta tsawan da ba ta san sanda ta saki daddawar Inna ba ya zube kasa,jiki na bari ta tashi,Baba yace daga yau dawainiyar ki ta tashi daga kai na kuma ya koma ga mijin ki,ya mikawa Inna kudin hannun sa,ta ma kasa karba sai da ya ce ke karbi mana! Kun ga shashanci,jiki ba laka Inna ta karba,Baba ya ce dubu biyar ne ba dari uku,dari ukun na biya kudin barnan da ta yi kin dai gani,sai ki siyo ma ta langa tuwo da miya da kuma dai abunda ki ka san za ta bukata,kudin sadakin ta kenan,na ce da Alhaji Baso ba sai sun kawo lefe ba dan ni ma ba gara zan yi ba,zan kira kafinta ya ma tsohon gadon da ke dakin can fanti,dan gobe za a yi jere akai Hajjo dakin ta…..
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[12:16am, 5/1/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭 DIYA MACE👭👭👭
5⃣
Yauwa Allah ya sa na yar da kwallan mangwaro zan huta da kuda! Ya na ware babbar riga ya shige ciki,Inna sakin jiki ta yi ta na kallan sa,wannan abu da me ya yi kama? Ganin Baba ya shige Hajjo ta kwaso daddawar da ya zube,ta tashi da sauri ta mi kawa Inna ba tare da ta san abunda ake ciki ba,dan dama ta saba da ganin bala’in Baba dan haka ba ta kawo komai a ram ta ba,fadi take Inna ungo daddawar ai wannan dan rainin wayon ne ya biyo wai dan ban sani ba na buge shi manjan sa ya bare! Maimakon Inna ta karba kawai sai ta fashe da kuka,hakan ba karamin dagawa Hajjo hankali ya yi ba dan ba ta taba ganin Innar tata ba a cikin wannan hali,ita ma kukan ta sa tana fadin wayyo Inna ta me ya same ki ki ke kuka,ni Hajjo na shiga uku na lalace!Baba dukan ki yayi Inna? Baba ya na jiyo su ya musu banza,Mudi da Ayuba su ka shigo,sun dawo daga makaranta.
Gani uwa da ‘ya na kuka tini hankalin su ya tashi,da kyar su ka shawo kan Inna ta yi shiru ta fada mu su dalilin da ya sa su kuka,Mudi da ke ya mallaki hankalin kansa shi ya shiga bawa Inna baki,ya tura Ayuba gidajen yan uwa domin sheda mu su abunda ke faruwa,kan ka ce me? Kafin la’asar tini gida ya fara cika da yan uwa,ita dai Inna ta zubawa sarautar Allah ido,bare ita amaryar da ba ta ma san ana yi ba,tin da ta samu Inna ta dai na kuka ta shiga sabgarta irin na yara,Baba kuwa tin da ya sa kafa ya fita be sake waiwayan su ba.
Yanda Baban yace haka ko aka yi,gado mai rumfa ke aje shekara da shekaru aka fidda aka shiga ma sa fenti,haka kuma Inna tace a hada da gadon Hajjo mai spring,sai a hada ma ta har shi,tinda dai amare ma su gata gado biyu ake hada mu su. Indo yayar Hajjo ta karaso,gaba daya ranta yayi matukar sosawa,daka su ka zauna ita da Inna suna jin jina al’amarin.
Hajjo ta ci danmara,fuskar ta cike da kwalliya an zane da gazar,ta faki idon jama’a,ta fito sim sim,ba ta ankara ba ta ci karo da Ayuba dauke da su langa tuwo da miya da Inna ta aike shi ya siyo. Wayyo dan Allah yi hakuri Ayuba,yasin ban san ka taho ba!Ayuba ya ce Hajjo hankali! Dama ina za ki san na taho? Sai a sannan ya lura da dammaran da ta ci,ga fuskar an bi an zane,ya ce ke ina za ki wai? Cikin yanga tana tafa hannu ta ce ai Mairo ce ta gayyace ni fatin yayan ta Garbati,ta ce ma ba sai na kawo kudin fatin ba ma! A fusace ya ce ku ji shasha,fatin kaniyar ki,ba ki san yanzu ke matar aure ba ce? Ai kece amaryar Garbatin! Hajjo ta murguda baki caf Allah ya sauwake! Ya ma samo amaryar sa kafin dare ya masa,ta yi gatsine. Wuce ciki kafin na bata mi ki rai! Sakarya kawai! Hajjo ta cije ta ki motsawa,ya ce ba da ke na ke magana ba Hajjo? Ta na buga kafa bakin nan cure ta shige ciki Ayuba na biye da ita,suna shiga Jama’a su ka fara waya taba amarya? Ta mu su banza,kai tsaye gun Inna ta shige,ta tadda ta tare da Indo,kan ciyar Inna ta zube ta na ihu an hana ta zuwa fati! Ayuba ya biyo ta ya na fadin kiyi kukan jini ma ba inda za ki je! Indo ta ce ayya mana Ayuba ka bi ta a hankali dan Allah! Ayuba ya ce anki a bita din,yarinya ace har aure an daura ma ta amma ta gaza hankali,ba dan Allah ya hada mu ba ai da an tafka abun kunya,ganin ta fa na yi za ta gidan sun Garbati wai Mairo ta gayyace ta fati.
Inna ta kama baki,ai kuriciyar kenan Ayuba,kuruci dangin hauka,shi ya sa gaba daya hankali na ya gaza kwanciya kan lamarin auren nan wlh,yi shiru auta,Allah zai zama gatan ki. Indo ta ce amen,amma ba a kyautawa Hajjo ba gaskiya,ko nima sai da na kai shabiyar aka min aure,bare kuma Hajjo da ta ke shabiyu. Ayuba ya aje langar a gaban su,ya ce da Indo kar dai ki bari Baba ya ji ki yarinya,za ki yi bayani. Ya sa kai ya fita Indo ta na fadin ya ji ni din,ba gaskiya na fada ba!Inna ta ce kul Indo,ban san tsaurin ido. Indo ta ce na yi shiru Inna,Inna ta duba fuskar Hajjo sai gani ta yi ta yi bacci,ta gyara ma ta kwanciya zuciyar ta cike da tausayin ta.
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[16/10 21:44] .: [7/24, 11:57 PM] Salmah Ateeku: [12:22am, 5/1/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
6⃣
Biki dai gadan gadan yin shi ake,da daddare aka yiwa amarya kunshi. washagari aka yi jere da wuni,da magrib aka fara shirin kai amarya sai aka nemi Hajjo aka rasa,da kyar Ayuba ya gano ta cikin duhun bishiya ta na ta shan mangaro,ya daka ma ta tsawa ta sauko. Da gudu ta shige dakin Inna,jama’ar biki sai dariya su ke. Ta na shiga ta ga an aje kayan sallan ta bisa gadan Inna,Indo ta ce maza ta sanya. Hajjo ta daka tsalle ta na fadin Indo yau sallah ne? Ashe ban sani ba! Ita dai Indo banza ta ma ta,jiki na rawa sai da ta yi tik sannan ta sanya kayan sallan na ta,ta bazama za ta fita Indo ta ruko ta ta na fadin ina kuma zaki amara? Baki washe ta ce su Mairo zan je na nunawa dama Inna ta ce na fi su a kyawu!Indo ta ce ba sai kin je ba,dama mu ma gidan zamu. Hajjo ta ce Allah? Za ku da ni? Indo ta ce eh dole mu je da ke,ungo mayafin ki sanya,Hajjo ta karba za ta ci dammara,Indo ta dakatar da ita,ah ah Hajjo ba haka ba,a ka za ki rufa,ta karba ta rufa ma ta ruf,Hajjo ta yi saurin yayewa,ta ce wayyo Allah,alquran tsoro na ke ji! Indo ta ce ke fa shasha ce Hajjo,Allah ki ka ci gaba da kullar ni buge ki zan yi! Inna ta shigo ta na fadin yi ma ta a hankali Indo,auta yi hakuri ki yafa,Hajjo ta ce toh Inna,ke ma da ke za a gidan su Mairo? Inna ta kwauda kai ta ce ah ah. Hajjo ta ce saboda me ya sa? In ce ba iyalle ta aiko mi ki da cingam ba….?
Kafin Inna ta ba ta amsa sai guda ya fara tashi,da alama dai masu daukan amarya sun zo,yayye da kannan Inna su ka shigo suna fadi toh Hajjo Allah yayi lokaci yayi,maza Innar ki ta karasa mi ki fada ku yi sallama kuma sai watarana! Inna ta kwauda kai da alama kuka ne ya ciyo ta,Hajjo ta ce fada? Toh me na yi da za ta min fada? Daya daga cikin yayyen Inna ta ce nasiha za ta miki,maza karasa gefan ta ta mi ki.
Hajjo ta karasa wajan Inna ta ce Inna yi min nisihan toh za mu tafi…..Inna ta fashe da kuka! Hajjo ta ce laaaa toh menene eh? Ke ma so ki ke ki bi mu? Yo ki biyo mu mana ko Baba zai yi fada? Da Allah ki bar kuka Inna wlh zan rago mi ki kwili da kunun zaki! Gaba daya dakin ba wanda be tausaya mu su ba,ita ko Indo tini itama ta sa na ta kukan. Yayar Baba ce ta kamo hannun Hajjo ganin Innar ba ta da niyar yiwa Hajjon nasiha,har sun kai kofa Hajjo ta fizge ta dawo da gudu ta fada jikin Inna ta na fadin ni ma na fasa zuwa alqur’an na fasa!nan fa ana jan Hajjo Hajjo na dada kamkame Inna da kyar aka samu aka bambare ta,Inna na fadin Allah ya mi ki albarka,Allah ya zama gatan ki,Allah ya sa ki je a sa’a Hajara.
Hankalin Hajjo ya tashi,ko by h da su ka kai kofar gida sai ta cije,aka yi aka yi ta saki kofa ta fito ta ki,ana haka sai ga Mudi,ko da ya ga halin da a ke ciki,ya kuma san halin Hajjo,idan ta kafe ko Baba be iya tankwasa ta,sai kuwa ya cincibi Hajjo,ta na buri ta na ihu,mata su ka sa su tsakiya,aka nufi gidan su Garbati,gaba daya ta cika kunnan jama’a da ihu.
A haka aka shigar da Hajjo har kuryar dakin mijin ta. Mudi na dire ta ya daka ma ta tsawa,amma ko a jikin ta,ita dai ya mai da ta gidan Innar ta! Da dai ya ga jan ido ba zai kai shi ko ina ba sai ya shiga rarrashin Hajjo tare da alkawarin zai mai da ta gun Innar sannan ta yi shiru,su Yayyen Inna da Baba su ka sami damar damkata amana gun uwar mijin ta wato Iyalle,shi ko Mudi gida ya dawo abun sa.
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[12:29am, 5/1/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
7⃣
Tafiyar su Indo ma fa sai da dabara,sai da su ka mata wayo wato su ka ce bari su leka makota suna zuwa,ganin yayar Mairo tare da Mairon sun shigo dakin na ta sai ta yarda su ka tafi,ta saki jiki suna ta hirar su kamar ba ita ce mai kukan dazu ba. Kande wacce ta ke sa’ar Indo amma ita bazawara ce ta ce da mairo ta taya Hajjo hira ta na zuwa. Da fitar ta Hajjo ta ce yarinya kin ga kayan salla na!ai Inna ta ce na fi kuwa a kyawu,wai ina amaryar Garbatin na? Mairo ta ce lalle ma ke Hajjon nan! Ga ba ki nan ba! Ba ki da wayo da ki ka yarda aka aura mi ki yaya na Garbati! Hajjo ta harare ta,waya ce mi ki aurar Garbati na yi? Allah ya sitiri bukwi! Mairo ta ce yarinya an sha ki ai,ni ce fa na sa Jummala ta fasa auren Garbati,wlh shekaran jiya da safe dan ban sani ba na dan tankwabar ma sa da kokan safe ya kamani yay ta jibga,ni kuwa da dare yayi na je wajan Jummala na fada ma ta gaskiya. Cikin kaguwa ta ji Hajjo ta ce wani gaskiya? Mairo ta ce aw kema ba ki sani ba ki ka yarda aka aura mi ki shi? Hajjo ta ce wlh Mairo za mu yi fada idan ki ka kuma cewa an daura min shi! Ni ki fada min dallah! Mairo ta ce hmmm ai Garbati mugu ne,wlh mugun ma na gaske,dan ya sibirbide ki ba wani aiki ba ne,gashi ba ya wanka da buroshi sai ranar juma’a,warin Garbati sai ya kar mutum har lahira…Hajjo ta toshe hanci ta na fadin Allah da gaske Mairo? Mairo ta ce kwarankwatsa da gaske na ke,idan karya na ke ki kwace yar babyn roba na,ke ki ma tambayi Kande ki ji! Kande ta shigo,Mairo ta ce yauwa dan Allah Kande Garbati ba mugu ba ne? Ai har kema bugu ya ke ko? Dan Allah ba baya wanka ba ba…..ke Mairo! Kande ta katse ta,ba ki da hankali ko? Na kuma ji sai na hada ki da iyalle,kai wannan diya akwai surutu,karya ta ke mi ki Hajjo kin ji ko?
Hajjo ta dubi Mairo,Mairo ta kifta ma ta ido tare da kada ma ta kunne alamar dai Kande karya ta ke. Muryar Garbati su ka jiyo daga waje,Kande ta ce ga angon nan ke Mairo ta shi mu tafi,Mairo ta tashi da sauri Hajjo ma tashi ta yi za ta biyo su,Kande ta ce ah ah ai ke Hajjo nan dakin ki ne,ba ki san Garbati mijin ki ba ne?
Hajjo ta yi zuru zuru da ido,ta ce wallahi karya ne,ba miji na ba ne! Kun ga na ce ba na so…ni gun Inna zan tafi….kai su waye cikin dakin nan? Muryar Garbati suka ji ya na maganar nan na shi kamar ya na yi da sama,tini jikin Hajjo da Mairo ya fara bari! Labule ya daga ya ce ke kande azo a wuce daki ko? Su ka kama hanya sim sim za su fita Hajjo ta ruke Mairo,Garbati ya dube su ya ce ke Hajjo! Sau ta! Ki sau ta na ce! Kar ki bata min rai na! Jiki na rawa ta sake ta,Mairo ta fice da sauri,Hajjo ta gama tsorata da Garbati,ta bi bayan Mairo ya daka ma ta tsawa,ke wai ke ina za ki? Koma ciki dallah! Jiki na rawa ta yi baya ta na wayyo Inna,ni gida zani! Ta daga ido ta dubi Garbati,ya kusan yin biyun ta ma,ga tsayi ga jiki! Garbati ya ja kofa karaf ya rufe,ya daga fitar acibulbul da ke ci tsakar dakin ya haska fuskar Hajjo,murya a sama ya ce kan uba! Ku ga kwailar da Baba ya aura min dan Allah!
Hajjo dai gaba daya ta gama tsorata,dan jikin ta har bari ya ke,gani take Garbati rufe ta zai yi da bugu tinda dai Mairo ta ce halin sa kenan! Kamar daga sama ta ji ya ce tube! Ta yi zaton kunnan ta ke zagi dan haka ta ce iye? Ya ce ki tube rigar ki na ce Hajjo! Kar ki bata min rai na!!!!!!!! Jiki na rawa a gigice Hajjo ta ce wayyo Allah wayyo Inna wai fa na tube! Wlh ba zan tube ba! Ke Hajjo! Wlh zan buge ki! Kar ki bata min rai na!!! Ya dada ma ta tsawa,ya yiwa Hajjo kwarjini,ba shiri sai ga Hajjo ta cire rigar ta.
Garbati ya dada haske ta,ya ce ahaf! Dama wlh na san kwailace Baba ya aura min! Ku duba ku ga ko nawa ya fi nata! Dirgan dangin ma yanzu ta fara! Dallah mai da rigar ki! Yo ni me zan yi da ke yanzu! Wlh Baba ya bata min rai na,ki sa rigar na ce!!! Jiki na rawa ta mayar da rigar,ta fara shirin fita,ya ce yo ke ina zaki? Ta na kuka ta ce gun Inna zani!! Ya ce Innalo ba Inna ba! Haye can ki kwanta! Ya ma ta nuni da karamin gado,ta ki hawa,ya ce kar ki bata min rai na!!!!! Ya daka ma ta tsawa,jiki na rawa ta haye gadon ta na kuka,ya dada ma ta wani tsawar ki min shiru kwaila!!!ko tarin ki ba na son ji!!!Hajjo ta sa hannu ta toshe bakin ta tana ta ajiyar zuciya,shi ko Garbati gado mai rumfa ya haye,ba tare da ya cire babbar rigar jikin sa ba,ko min ti biyar be yi ba ya shiga numfashi kamar ba mutum ba,bacci yayi gaba da shi…
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[12:33am, 5/1/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
8⃣
Jin munsharin sa ya sa Hajjo saukowa,cikin sanda ta nufi kofa,ko da ta ja sai ta ki kam ko motsawa kofar ta ki yi,Garbati ya sakace,gashi sakatar can sama ne ko ta taka kujera tsayin ta ba zai kai ba. Nan ta durkushe ta na kuka amma a hankali gudin kar Garbati ya ji ya jibgeta,a haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login