Showing 45001 words to 48000 words out of 67328 words
Chapter 16 - Diya Mace Book Complete by khadija sidi .txt
da Garbati da ya yi. Sai ta dauko tabarma duk da ta san ba ya zama kan tabar ma ta shimfila,sannan ta ce ya shigo ciki. Ya shigo sai ya ga tabarma,ta na jira ya ce ba zai zauna ba sai kuma ya ba ta mamaki ya zauna. Indo ta fito suna gaisawa sai ga Hajjo nan ta kawo ma sa ruwa a kofin roba,bayan ta san baya sha ko cin abunci a roba. Indo ta ce ya za ki kawo ma sa kofin roba ga na karfe Hajjo,ta na murmushin mugunta ta ke kallan sa,ta ce ya fi san na roba,ko Khalid? Shi ma murmushin yayi,ya san abunda ta ke yi,dan haka sai ma ya daga sha ya koshi ya aje sannan ya ce kwarai kuwa. Cike da mamaki Hajjon ta ke kallan sa. Sai ta kara da bara na kamasa abunci,na san shi da san miyar yauki. Ihu ne kawai Khalid be kurma ba,ba shakka Hajjo niyar ta ta kashe shi,duk abun da ta san ba yayi shi ta ke ma sa,wa ya sani ma ko guba za ta sa ma sa a abacin ya mutu ta huta,duk duniya idan akwai abuncin da ya tsana ya bi bayan miyar yauki. Ciki Indo ta koma ta na fadin saka ma sa mana,ki hado da yajin daddawa ma. Toh ta amsa cike da farin ciki. Ta kawo ma sa tuwon. Ga mamakin ta sai ya wanke hannu,ya dan ci kadan,dandai ya kunya ta ta,amma da kyar ya ke hadiya,har ya dan bata ma sa gaban riga. Bayan ya wanke hannu ya zauna ya ji zuciyar sa na tashi,ya ce dan Allah suger taimaka min da leman tsami,da har za ta hana shi,sai ta tausaya ma sa,ta dauko ta yanka ma sa,sai da ya dan sha kadan sannan ya samu nutsuwa,ya dago ya kalle ta,ya ce come here Suger,ya nuna kusa da shi. Ta harare shi ta ce Hajara ce ba diyar ka ba da za ka min irin kiran yara. Tashi yayi ya na murmushi,ya zo gaban ta,ya durkusa gwiwowi biyu a kasa,ya ce Hajara yau ga Maighty Khalid gaban ki,ya zo da kokan baran sa……baki bude ta tsaya ta na kallan sa.
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[7/25, 5:22 PM] Salmah Ateeku: [11:38pm, 6/10/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
5⃣2⃣
Hajara ki yi duba da soyayyar da mu kewa diya daya,diyar ki,kuma diya ta,ki amince na zama miji a gare ki dan cigaba da gina zuri’ar da za su kasance tsatso daya,idan ki ka ki aure na,za ki raba ni da diyar ki,ta riga ta shiga rayuwa ta,haihuwan ta ne kawai ban yi ba. Kuma za ki iya auren wanda kuma zai hana ki rukon ta,tin da uba aka sani da alhakin riko ‘yaya ba uwa ba,kin ga kenan mun yi biyu babu. Hajjo ta ce dan Allah ka tashi,kar wani ya gan ka haka na banu. Ya ce answer me first sai na tashi. Ta ce ba zan iya auren ka ba Khalid…saboda me ya sa? Saboda am nt ur type? I wil try to adjust to ur type,kawai ki fada min ya type din na ki ya ke. I promise to b good,zan yi respectn din ki untill my last breath,zan kuma so ‘ya’yan mu na ba su kulawa kamar uba na kwarai. Hajjo ta ce ba soyayya,ka san ba na san ka,ta ya za mu zauna?
Khalid ya murmusa,ba soyayya,amma akwai respect,ba kya so na,i can do wit dat,ni ma wai san na ki na ke ba,amma ina san diyar ki Ameena zan kuma so yaran da za mu samu a gaba inshaAllah..duk da dai ita ta fara furta zancen rashin soyayyar sai da amsar ta shi ta ma ta daci,ita ta fada ne dan ta na san ji ya yake ji game da ita,ashe it is ol abt haihuwa da kuma diyar ta da ya ke so. Gashi ita har ran ta ta na jin sa,wanda kuma ke san na ta ya raba ta da shi. Yawun takaici ta hadiya dan jika makogaranta da ya bushe,ta ce ba ni kadai ba ce mace mai haihuwa a duniya,ka ne mi wata mana! Ya murmusa,ai nan gizon ke saka,ke zuciya ta ta zaba,ke ce zabin rai na,ba dan haka ba da ina tuni ma na yi watsi da zancen,i don’t go after gurls,gurls come after me,nd olryt u ar an exceptional. Babu yanda zan yi. Hajjo ta ce ka raba ni da mai sona,Khalid ya amsa da ba zai so diyar ki ba Hajara,dan haka be dace da ke ba! Ajiyar zuciya ta yi,sannan ta ce zan yi tunani a kai. Tunani akai? Kamar ni Khalid na zube gwiwowi na kasa na rokeki amma ki ce sai kin yi tunani?gaba daya kin taba tsarin rayuwa ta,har kin min gibi. Hajjo ta daga kafada ta sauke tare da fadin dax in za ka iya jira,idan kuma sauri ka ke sai ka sake saban lale. Tashi yayi ya na murmushi,ya ce ba sauri,amma ki sani da ga yau bazan sake bibiyan ki ba,da fatan za ki yi tunani da kyau,dan Allah ki yiwa sirika ta sallama,sai na zo maganar auren mu,ya zira takalmi,ya na murmushi ya fice,Hajjo ta bi bayan shi da kallo,kamar ta ce ya dawo ta yarda,dan ba wai yardan ne ba ta yi ba,ta na jin tsananin tsoran kishi da Hauwa,dan ta fita komai,bare uwa uba mai san auren na ta ba ma san ta ya ke ba.nan ta yi zaman ta sai da Indo ta fito ta same ta,ta yi nisa cikin tunani. Da ta matsa sai Hajjo ta fada ma ta damuwar ta ne sai ta fada ma ta yanda su ka yi da Khalid. Indo ta ce to menene na ki na kin yarda? Menene laifin Khalid,Hajjo kar fa ki yiwa kan ki asara! Mutum mai asali ga ilimi da komai na rayuwu? Ya na san ya aure ki,ya na kuma san diyar ki,ba kowani namiji za ki aura ba ya yarda ki zauna ma sa da agola ba,shi gashi saboda ita din ma ya dage ki aure shi,wani zancen ba ya san ki ki aje,ki ka iya zama da Garbati ma bare mutum kamar Khalid? Hajjo ta nisa tare da fadin ni fa kishi da matar shi ne bazan iya ba,ta fini komai,ni da ita ba gami. Indo ta ce Hajjo,ya fa san da matar ta shi ya dage sai ya aure ki,saboda kina da abunda ya ke bukata matar shi ba ta da shi,yar ki da kuma ‘ya’ya tsatson ki ya so,kin ga kuwa ba ta fi ki komai ba din kenan. Hajjo ta ce wulakanci ne ban so Indo. Indo ta ce ai kin fi karfin wulakanci Hajjo,bare ma Khalid ba zai wulakanta ki ba,a de bar shi da jin kai,amma ba wulakanci….Hajjo ta dara,ta ce aw ashe ke ma kin san halin nan na shi. Indon ma dariyar ta yi,ta ce waye be sani ba. Allah dai ya tabbatar da alkhairi,ki dai kara nazari Hajjo,ki kuma cire san zuciya ki zabi hanyar da zai fisshe ki. Hajjo ta ce amen amen,inshaAllahu,Allah ya sa mu dace. Ta amsa da amen.
Da tunanin Hajjo khalid ya isa kano,shi kan shi ya kasa gane dalilin da ya sa ta mamaye zuciyar sa,gaba daya ta mamaye zuciyar sa,ji ya ke kamar ya kusa fara numfasa sunan ta tsabar yawan yanda ya ke tunanin ta a rana. Duk da haka ya ki yarda wai san Hajjon ya ke,shi a na shi daga Hauwa ba zai iya kara san kowace diya mace ba. Shigar shi gida be ga Hauwa da Neena a falo ba,kai tsaye bankaran Hauwa ya nufa,ya jiyo su a daki. Da shigar sa dakin kamshi da ya sani,ya ke balain so ya shaka,ya bi ta hanci ya shige har cikin zuciyar sa,be san sanda ya yi subul da baka ba ya ce ya na ke jin kamshi Suger? Hauwa da ke zaune kan gado ta na yiwa Neena kalaba,da tuni ta ankare da shigowar sa,ta amsa ma sa zuciya daya ta ce ba Suger ba ne,Humrah ne fa ya dade ajiye a kan dressing mirrow na Neena ta zubar garin tabe taben ta. A sannan ya gane kwaban da ya kusa tafkawa,yayi saurin bin ta ta hanyar yin kwana shi ma ya ce aw Humrah sunan turare? Kai amma yayi dadi,ki na da shi amma ba ki amfani da shi? Hauwa ta ce wlh be dame ni ba ne. Khalid ya karaso kusa da su,ya zauna tare da fadin ni ya dame ni,ki na amfani da shi daga yau. Hauwa ta dara,toh zan sa a kawo min wani,ina kasan kamshin humrah? Tambayar ta sa gaban sa ya fadi,ya na tuninin amsar da zai ba ta da gaggawa Neena ta ceto shi, Daga yanda ta ke a durkushe,ta ce sannu da zuwa Dady. Da sauri tare da maraba da gaisuwar ta ta ya amsa da yauwa sannu my beloved one. Ya kiriniya? Hauwa ta ce kasan ba kiriniya sai shagwaba. Ya na murmushi ya tashi gudun kar a koma maganar humrah,ya ce ki yi san ranki indai shagwaba ba ce,diyar Khalid ki ke. Neena ta ce yauwa Dady. Hauwa na dariya ta ce dama kai ka ke kara shagwaba ta. Ya ce ita diya tilo ya bazan shagwaba ta ba? Hauwa ta ce gaskiya fa. Ya ce in kun gama kwasame ni a bangare na. Hauwa ta amsa da toh. Ya fice ya na dirga sa’ar shi na yau,amma lokaci yayi da zai sanar da Hauwa kudirin sa akan Hajjo.
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[11:50pm, 6/10/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
5⃣3⃣
Kusan sati daya kenan raban Hajjo da Khalid,kamar yanda ya ce ma ta din ya daina bibiyan ta,amsar ta ya ke jira. Da ya sanar da Hajiya da Jabir yanda ya yi da Hajjon amma be fada mu su har tsugunna ma ta ya yi ba gudun sharrin Jabir. Jabir ya ce ahaf,dama na fada mi ki Hajiya,jin kai irin na Khalid ba zai bari ya iya shawo kan ta ba,gashi kullum rama ya ke kamar kudin guzuri. Hajiya ta ce Jabir ai sai ka sa baki. Jabir ya ce toh Hajiya,gobe zan je na same ta inshaAllahu. Hajiya ta ce toh Allah ya kai mu. Ba karamin dadi ya ji ba jin Jabir zai sa baki,ya san Hajjo ta kusa shiga hannu kenan. Tattaunawar Hajjo da Jabir a asibiti Hajjo ta nuna amincewar ta kan auren Khalid. Jabir ya ji dadi matuka da yanda Hajjo ta ke ma sa,komai ya ke so ta yi,wuyan ta ya yi magana kamar yanka wuka haka ta ke aiwatar da shi. Ya ma ta alqawarin tsaya ma ta a komai kan auren,sannan kuma ta ba su sati biyu za su zo su nemi iyayen ta dan yanke maganar auren. Da kamar za ta fada ma sa tsakanin ta da Baba,sai ta ga ai kamar tonawa kan ta asiri ta ke,gwara su je da kan su,su ganewa idan su. Da wannan maganar su ka yi sallama.
Cikin dalleliyar motar shi da ya sake ya nufi gidan Khalid. Bayan ya gama ma sa tsiya da Allah ya san ya alkhairi,Jabir ya ce albishirin ka? Khalid ya ce goro,bayan motar ka siyi private jet ko? Jabir ya make shi tare da fadin shegen maza,sai na siya ai,ka san da kudin. Khalid ya ce ni ko na san da su,ci ne dai kawai ba a yi. Jabir ya murmusa tare da fadin da kasan albishirin da zan ma ka da ba ka tsaya jan wannan shirmen da ka ke fada min ba…Khalid ya gyara tsayuwa,ya ce toh fadi na ji. Jabir ya ce na ga Hajjo yau. Cikin kaguwa ya ce dan Allah,ya ku ka yi? Jabir ya ce sai ka biya. Khalid ya ce kaiya! Dan Allah ka fada min mana,ban san wasa da irin wannan maganar,haba yaya na na kai na! Jabir na dariya ya ce na ji wannan social bribe din,toh ka shirya nan da sati biyu za mu kai gaisuwa da kuma sa ranar auren ka da Hajjo….baki Khalid ya bude kamar zai yi magana,sai kuma ya rufe,ya kara budewa ya na rufewa kusan sau uku,Jabir ya ce fadi ma na,Khalid ya ce Alhamdulillahi rabbi alamin!Jabir ya ce ko kai fa! Murna ce ta lullube Khalid,fiye da tunanin kuwa,gani ya ke ya haihu ma ya gama dan daga ganin Hajjo za ta yi kwayaye,baze bari ta yi fmly planing ba,yara za ta jero ma sa kamar bene. Ya ce Jabir wlh da na isa na ma ka kyauta da na ma ka,maganar da ka fada min ta yaye min rabin matsala ta. Jabir ya ce ka min mana,girman ka ne. Khalid ya ce ni din banza,me na isa na baka. Jabir na murmushi ya shige motar shi ya na fadin sauran mtsalar ta ka,ka yi saurin kau da shi,ka kuma tuna ma ta Allah ne ya bamu damar mu yi,kar ta yi jayayya da fadar Allah. Darawa Khalid ya yi,ba shakka Jabir ya san sa kwarai ya na iya karantar sa,ya ce madallah da wannan yaya nawa,na gode,Allah ya bar zumunci. Ya tada motar shi ya ce ameen dan rasulillahi,kar fa ka fara ma ta jiji da kan sosai,ka bari a daura kar ta ce ta fasa! Ya na dariya ya figi motar sa,Khalid na daga ma sa hannu,sannan ya juyu gida,ya fara tsara wasikar da zai karantowa uwar gida Hauwa.
Kwance jikin shi,bayan ya gama nuna ma ta duk duniya ba diya mace kamar ita. Ya kira sunan ta,Hauwa?Jin ya kira ta ba tare da ya ce baby-luv din da ya saba fada ba musammam lokaci irin yanzu ta san da wani abu. Ta amsa da na’am. Ya ce kin san shekaran mu nawa da aure? Ta ce sha daya. Ya murmusa tare da fadin,ol those years da san ki ke kadai na ke kwana na ke tashi,haka ma har tsawan shekarun da Allah ya kindaya ma na,you ar d love of my lyf. Maganar ta sa tai ma ta dadi,ta dada kwanciya jikin sa,tare da fadin tell me more,ba ta san more din ba mai dadi ba ne. Sai da yayi shiru,sannan ya ce kin san dai Allah ba ya cutar da bayin sa,sai dai bawa ya cutar da kan sa,Hauwa ta ce haka ne. Ya ce kin san kuma kowa akwai kaddarar rayuwar sa..gaban ta ya fara faduwa,ta ce haka. Ya kara da kin san Allah na jin kunyar macen da be bawa haihuwa ba? Hauwa ta gyada kai,ta ce eh,ki tabbatar Allah na tare da ku,ya kuma san da ku,ku din ma mata masu daraja ne. Ya sake yin shiru,Hauwa ta ce ina jin ka. Ya ce Hauwa ki saurare ni da kyau dan Allah,wlh ban taba san kowace diya mace ba sai ke…zuciyar Hauwa ya fara kaduwa,ta ce dan Allah fada min,menene wai. Khalid ya nisa,ya ce aure n ke son na kara…….a razane ta dago daga jikin sa ta na kallan sa kamar wanda ya yi sabo,ta ce aure? Wasa ka ke ki Khalid! Aure fa? Kai ba da gaske ba ne! Yi shiru kawai mu kwanta mu yi bacci. Shi ma tashi yayi zaune gami da ruko hannun ta,ya ce ba wasa na ke ba,ba kuma ba dan ba na san ki ba ne….idanu cike da kwalla ta ce Khalid,me ka ke fada haka,ba ka san abunda ka ke fada ba! Ta ficge hannun ta,ya ce Hauwa ki saurare ni! Ta ce me za ka ce min? Ina jin ka! Ya ce Hauwa ki tausaya min,tsufa na ke,wlh duk yanda na so na hakura na kasa,ina san yara……sai ta fashe da kuka,ta na fadin dama na sani,dama na sani. Ka kasa hakuri? Dole ka kasa mana tunda ba kai ba ne da ralural ba! Bambamcin diya mace da namiji kenan,da kai ne da matsalar ka san haka zan hakura na zauna da kai ba ma me ji,amma yau dan ni ce gashi za ka tuzar ta ni….ya yi saurin rufe ma ta baki,ya ce haba Hauwa,kar ki manta bambamcin diya mace da namijin har da umarnin ubangiji da ya ce mu auri hudu,ko uku ko biyu har zuwa daya,manzo sallallahu alaihiwasallam be zauna da daya ba Hauwa,ya ce mu auri fiye da daya har zuwa hudu in har za mu iya adalci. Hauwa manzo sallallahu’alaihiwasallam ya ce mu hayayyafa dan mu zamo abun alfahari a gare shi ranar gobe kiyama,shin da wannan damar Hauwa na cigaba da ruyuwa yanda mu ke ki na gani na yiwa kai na adalci kenan? ‘Ya ‘ya na ai na ki ne Hauwa…ta na hawaye ta ce ni da ban haifa ba,ta yaya za su zamo nawa? Sanin kan ka ne Neenan da na ke gani kamar tawa ma an kusa raba ni da ita. Ya ruko hannun ta tare da fadin babu mai raba ki da ita,saboda na tabbatar da hakan ya sa na zabi na auri mahaifiyar ta…..dif Hauwa ta ji ta dai na ji,ta daga ido ta kalli fuskar Khalid da ke ma ta haske duk sanda ta daura idanun ta akai,yau sai gashi ya ma ta duhu dulum. Hauwa ba ta ji ba ta gani ta cire hannun ta daga na Khalid. Ta tashi za ta fita,shi ma din tashi yayi da sauri ya na Hauwa,Hauwa! Ina ba ta tsaya ba,ya bi bayan ta da sauri,ganin haka sai ma ta sa gudu,ya na biye da ita,ta yi saurin shiga bankaranta ta kulle. Sai ta zube kasa ta na kuka mai ban tausayi. Khalid yayi yayi ta bude ta ki,dan haka shi ma sai ya sami waje ya zauna daga jikin kofar,ya na jiyo kukan ta,ya rasa me ke ma sa dadi nan duniya.
DEDICATED to The Women Of Virtue🙋👰💁(group)
[16/10 21:54] .: :02am, 6/11/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
5⃣4⃣
Hajjo ma a na ta bangaran bacci nan ba ta yi ba. Tin da ta amince da auran Khalid ta kasa nutsuwa. Sai da ta dage da karatun alqur’ani,da kuma nafilfilu Allah ya sa hakan alkhairi ne. sannan ta samu idanun ta su ka rufe. Washagari da sassafe Hauwa ta tafi gidan su. Da ke iyayen ta na arziki ne sai su ka ma ta tatas,su ka zarge ta da san kanta,mutum