Showing 36001 words to 39000 words out of 67328 words
Chapter 13 - Diya Mace Book Complete by khadija sidi .txt
a kafa.. ya ce no way! A fusace idanun ta har spark su ke dan bacin rai ta ce way! Bude ka gani! A kasalance ya rangwadar da kai bisa kan kujerar sa,ya ce Suger….ta ce Hajjo! Ba suger sunana ba,kowa da Hajjo ya ke kira na,so ka kira ni Hajjo ko ma child abuse da ka saba kira ko ka yi shiru! Ya murmusa ya ce child abuse is no more,wannan zaune gabana is a strong woman! Khalid ba kowa ba ne,Khalid is unique dax y zai kira ki da sunan da ba kowa ke kiran ki da shi ba Suger! Ta ja hannun kofa,tare da fadin ka bude min. Ganin ta matsa sai ya bude ma ta kofar ya ga iyakan gudun ruwan ta. Ta ko sa kai ta fito,yayya fi ya zama ruwa,wani irin iska mai sanyi ya buso jikin ta,kayan ta ya fara bin jikin ta,ta ja daga jikin motar Khalid ta sami wata yar lemar ma su sayir da recharge cards ta kebe,amma duk da haka ruwan na taba ta.
Daga mota ya ke kallan ta,he love d view,ta yi ma sa kyau kwarai,ba dan ya na tsoran kar ta kamu da sanyi ba da ya kyale ta yay ta kallan ta a haka. Ya yunkura zai fito kenan sai ya ga wata mota ta tsaya a gaban ta,an sauke glass din motar,abun da ya dada kular da shi yanda ya ga ta na ma mai motar murmushi mai kayatarwa!
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[7/25, 5:16 PM] Salmah Ateeku: [10:56pm, 6/5/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
4⃣6⃣
Ganin frnd din ta da ya dade da nace ma ta na yafuce shi,farin ciki ya lullube ta,a asibiti daya su ke aiki,amma shi a admin block ya ke aiki.Cikin jin dadin ganin sa Hajjo ta ce KB na ji dadin ganin ka wlh! KB ya dara tare da fadin maza shigo toh kar ruwa ya zane min ke. Dama tayin da ta ke jira kenan,dan ta fara jikewa sosai,ta yi saurin bude motar ta shige. A fusace Khalid ya fito daga ta shi motar,ya nufi motar KB amma ina KB be ma san da shi,tini ya karya kan mota ya haye kan kwalta abun sa. Rai bace ya bi motar da kallo,ruwa ne ke dukan sa amma sam be damu ba saboda zafin da kuna da ransa ke yi ya fi dukan ruwan. Sai da ya dau kusan minti biyar a tsaye,ya jike jagab,Hajjo sai dan waiwayen sa ta ke ta motar KB har sai da ya ce ko kin yi mantuwa ne? Ah ah,ta yi saurin ba shi amsa,mu je ba komai.
A fusace ya juya ya koma motar shi,da juyawa zai yi kawai ya tafi gidan sa,amma kishin ganin Hajjo ta shiga motar wani,wanda ba mamaki ma ba ta san shi ba dan ta kuntata ma sa ta bishi ya sa zuciyar shi tafasa,a dole ya bi bayan su dan ya tabbatar ya sauke ta lfy. Har su ka kai kofar gida ba su san Khalid na biye da su ba,can gefe ya faka,ya na ji ana ta horn maigadi ya ki ya zo ya bude gate,shi ma ruwa ya buye shi,dan haka sai Hajjo da KB su ka tsaya shawara,ya na ta zauna a gama ruwan,ta na bari dai na shiga yanda ruwan nan yayi yawa Allah kadai ya san lokacin tsayawan sa.
Khalid da ga na shi motar ya cika ya yi fam! Wai shin mai Hajjo ta ke nufi za ta zauna a motar wani kato! Ta na zaune motar wani cikin ruwan sama,sai shakar gamshin ta ya ke! Mtsw ya ja tsaki! Hakurin sa ya kare,ya yanke hukunci zuwa ya fito da ita da kan sa kenan sai ya ga ta bude mota ta fito,ta shige gida da sauri. Ajiyar zuciya ya saki tare da bin motar da kallo da ta zo shige shi ya na fadin Allah ya taimake ka kai dai,amma ka kuskura na kara ganin ka kusa da Suger ba za ka ji da dadi. Be shiga gidan Hajiyar ba ya tada motar shi cikin bacin rai da hanzari ya bar wajan. A hanya yayiwa Sani waya,ya ce da shi gobe kafin ya taho kano yayi jiran shi,zai shigo kumurya. Cike da mamaki Sani ya ce toh Allah ya kai mu. Ya amsa da amen. Yanda Hauwa ta ganshi jike rai a bace ta san ba lfy,ta yi kokarin jin musabbabin bacin ran na sa,ya ce da ita ta dan bar shi ya na so ya ji shi kadai,ta ce toh,Allah ya kyauta. Ta ja diyar ta ta bar shi ya ci kan sa,binibini sai ka ji ya ja tsaki,mtws! Ranar dai haka ya kwan da takaicin Hajjo wanda hakan shi ne karo na biyu.
Washagari da sassafe sai ga Khalid a kumurya. A tsakar gida Sani ya sa ma sa kujerar da ya ke bawa bakin sa na albarma ya zauna. Bayan ya gaisa da Indo,ya ke ce ma ta ta fa dan so ta yi kama da Hajjo,dan dai ta fi Hajjon kyau,dadi har ran Indo,kyakkyawa kamar Khalid ya ce ta na da kyau. Zaman shi da Sani ya ke fada ma sa dalilin zuwan sa,so ya ke a kai shi gurin iyayen Hajara. Sani ya ce toh fa. Ai mahaifiyar Hajara Allah ya ma ta rasuwa shekara goma sha uku kenan. Khalid ya ce Allah sarki,Allah ya ji kanta,sunan ta Neena ta ci kenan shi ne Hajara ke kiran ta Inna. Mahaifin ta fa? Sani yayi jum. Khalid ya ce ya ka yi shiru ne? Sani ya ce ai abun ne,toh mahaifin ta na nan,gidan nan gaba ne ba nisa. Khalid ya ce toh mashaAllahu za ka iya raka ni gun sa? Sani ya yi jugum,kamar mai shawara. Khalid ya ce kar ka damu,tsakanin mu ne,ko matar ka ban so ta san za mu wajan na shi,sai nan gaba,da alkhairi na zo,kamar yanda na ma ka bayani a baya auren Hajara zan yi. Sani ya ce ba komai,sai na raka ka din. Sani ya ce da Indo su na zuwa,su ka fita ba su zame koina ba sai gidan su Hajjo. Gidan ya koke ya lalace kamar ba Jama’a ciki,wai kuma a haka Mudi ya yi aure ya aje matar shi ciki haka shi ma Ayuba shi ma da matar sa cikin gidan. A waje su ka tsaya,su ka tura yaro ya mu su sallama da Baba,Yaro na shiga ya fito ya ce ai ga Alhaji Mamman din nan soro sai nishi ya ke ina ga ba shi da lfy ne. Godiya su ka ma yaro,tare su ka kutsa cikin soron,sai kuwa ga Baban nan kwance a wulakance sai nishi ya ke,be ma san wa ke tsaye kan sa ba. Subhanallahi,tare su ka yi saurin durkusawa gaban Baba,Sani ya na fadin yaushe kuma haka ya faru? Ko da wasa ba mu ji rashin lfyar ba! Shi kuwa Khalid ran sa ne ya dada baci da al’amarin Hajjo,ya Baban ta mahaifi na nan kwance cikin wannan wulakantacciyar rayuwa ba gata,amma ita ko a jikin ta, ta na likita,haba wannan wata irin duniya ce haka! Ya kalli Sani ya ce bayan Hajjo da Indo bai da wasu ‘ya’ya ne? Ya ce akwai Mudi da Ayuba,nan su ke zaune da matan sa. Khalid ya leka ya sami yaro ya ce ya yi sallama da Mudi ko Ayuba,dan tin zuwan su ba wanda ya leko,da sun zo da wani mugun abu ne da tuni sun aiwatar. Yaro ya dawo ya ce ba sa nan,sai matan su. Khalid ya ce ace su su leko. Sai ga lantana matar Mudi ta leko da daurin kirji ta na mita wai waye maigida baya nan sa ya ce sai ya gan mu…Ganin Sani tare da wani dandasheshen namiji sai ta shanye maganar ta. Yanda ya ganta dukundukun,ga daurin kirji,Khalid ya ce disgusting! Ita ko sai ta fara hannu,hannun ku,ashe Sani ne,ai daga Mudi har Ayuban ba wanda ke gida,eh sun je samo mana na afawa! Khalid ya ce sun san da rashin lfyar mahaifin su? Lantana ta kalli inda Baba ke kwance ta ce sun shi na mana,kullum cikin ba shi jike jike su ke ai,Mudi ne ma ya kawo shi nan ya kwantar,dudu ma kwanan sa nan uku kwance ba,sai dai a tayar a kwantar. Rai bace Khalid ya ce Sani taimaka min mu sa wannan bawan Allah mota mu kai asibiti,wa’yan nan ba su san darajar iyayen su ba,da ga su har matan na su. Lantana ce yo ai dai mun ma sa iya kan kokarin mu mu dai,so ka ke mu sa zani da majanyi mu goya? Banza su ka ma ta,yayin da su ka kama Baba,sai zarnin fitsarin da yayi a kwance ya ke su sa shi mota. Sai da su ka biya gidan Sani,ganin halin da Baba ke ciki Indo ta girgiza,Khalid ya ce ya aka yi ba ta zuwa ganin sa har ya kai haka bai da lfy?Indo ta ce wlh ta na zuwa duk da ko ta je din fada ya ke ma ta wai ta na damun shi da yawan zuwa,ko kwana hudu da ya wuce ta je. Tare su ka dunguma su ka taho kano,Indo ta bar babbar yarta tare da yara.
Su na zuwa kano AKTH su ka wuce,nan da nan aka kwantar da Baba emergency,darajar Jabir tuni likitoci su ka rufa kan Baba su na duba shi,abu na su. Khalid da Sani,da Indo su ka ja gefe,Har Khalid ya daga waya zai kira wayar Hajjo,sai ya ja tsaki ya kashe,an sha fada ma sa diya mace ta fi jin kan iyayen ta akan maza,amma sam ya ga bambamci gun Hajjo,hw comes? Hw can she be so cold to her biological father,ita ta yaya ta ke so na ta ‘ya’yan su ji kanta har su tausaya mana. Kai daga dowowar sa zuwa yanzu Hajjo ta tsaya ma sa a rai kan abubuwan ta da dama. Sani ya sallama,kar Hajiya ta ji shiru,ya ce kar ya fada ma ta sun kawo mara lfy,idan ya dawo zai ma ta maganar,gudun kar Hajiya ta ji irin abun da ya ke ji game da Hajjon.
Da wuri ta samu ta bar asibiti,hudu a gida ta mata,ta yi saurin yin wanka ta shirya cikin english wears riga body hug ruwan goro,da kuma free skirt bski,sai ta daura bakar sweater da ke garin ana sanyin damina. KB ne ya dame ta zai zo tin da ya sauke ta jiya,ita kuma ganin kirkin da ya ma ta dan a ramawa kura aniyar ta sai ta yarda yau daya dai yazo. Ta na kallan kanta a madubi,ta dau humra ta na dan shafawa jikin mayafin da za ta yafa wayar ta ya fara kara,ta duba ta ga sunan KB sai ta aje humran ta daga,ya ce gashi cikin farfajiyar gidan. Ta ce toh ga ta nan fitowa. Ta kuma kalle kanta a madubi,ta yi kyau kamar diyar turawa,ta sanya takalmi ta je ta fadawa Hajiya za ta fita.
DEDICATED to The women Of Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[1
[16/10 21:49] .: 1:15pm, 6/5/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
4⃣7⃣
KB zaune kan motar shi ya na jiran fitowar Hajjo,wata mota ta shigo gidan,ta faka gefe guda. Ganin Khalid ya fito sai da ya sha jinin jikin shi duk da dai ba su taba haduwa ba,be kuma san wanene shi ba. Shi ma Khalid tin shigowar sa gidan ya gane KB,dan haka kai tsaye wajan shi ya je,ganin ya nufo shi KB ya sauko daga kan mota tare da mi ka ma sa hannun tare da fadin salama’alaikum,fuska murtuke ya amsa wa’alaikumul salam. Wajan wa ka zo ne? KB ya dan yi jim sannan ya ce wajan Doctor Hajara. Khalid ya ce a matsayin ka na wa? KB ya ce ban dai san kai wane ne ba,so dax y zan amsa ma ka,a matsayi na na friend din ta. Khalid ji yayi kamar ya buge bakin sa,ya ce matar tawa ce friend din ka? KB ya gyara tsayuwa,tare da fadin matar ka,wlh ban san ta na da aure ba,ba ta fada min ba,Khalid ya ce ba a daura ba ne,wata biyu ya rage dax y ina ga ba ta fada ma ba,so ka nemarwa kan ka arziki ka janye kafar ka daga gidan kuma da ga wajen mata ta. Jin ba a daura auren ba sai hankalin sa ya kwanta,ya ce ba damuwa,sure bazan sake zuwa ba. Khalid ya ce madallah. Ya juya ya na tafiyar nan ta shi cike da takama ya shige gida,KB ya ce ba shakka dan ma su gida,shi gidan ma ya ke shiga kai tsaye,bara na ja rayuwata na yi gefe guda! Be san gidan su Khalid din ba ne. Ya shige motar sa ya ya fita lokaci guda kuma Hajjon ta fito,sai gani korar motar ta yi,cike da mamaki ba ta ma san Khalid na tahowa ba ta ke fadin me zai sa kuma KB ya tafi,bari na dauko waya na kira shi. Da jin kamshin turaren sa da ankarewa da shi lokaci guda ne,ta daga kai ta kalle shi. Ya bi ta da kallo tin da ga sama har kasa,har sai da ta kasa sakewa.
Fuska murtuke ya ce kar ki damu da ki kara kiran shi,na sallame shi har a bada ba zai sake dawowa gidan nan ba. Maganar ta bata ma ta rai matuka,har ta bude baki za ta yi magana,sai ta kuma ta fasa ta juya da niyyar komawa ciki,ya dada tsaida ta ta hanyar fadin yaushe raban ki da Baban ki? Dum maganar ta daki kunanta,ji ta yi komai ya tsaya ma ta cak na dan sakanni,sanna ta kara daga kafa ko taku uku ba ta yi ba ta ji ya sake fadin diya mace da jin kai aka san ta,musammam na iyayen ta,amma yanda na ki lamuran su ke kin sa ina kokon tan haka,ur father Hajara is very ill,shin ki na neman albarka kuwa?juyowa ta yi a hankali,dan bacin rai idanun ta har spark su ke,ta sake bude baki da niyyar magana,sai ta kasa. Yanda ya ga ta na kallan sa kamar kura ta ga nama,ga idanun nan na spark dan masifa sai ta ma sa kyau,ya ma kusa manta da bacin ran da ke tare da shi. Juyawa ta sake yi,dan gani ta ke magana be da amfani a yanayin da ta ke jin kanta,lalle zaman ta a gidan nan ya zo karshe! Da wannan kudiri cikin ranta ta shige ciki. Wato shirun da ta yiwa Khalid ya dada kona ma sa rai,shi tin da ya zo duniyar nan be taba ganin mace da ta ke bata ma sa rai kamar Hajjo ba,nd d more ta ke bata ma sa rai,d more he want to get close to her saboda shez so differant,an adventure for him. Rai bace shi ma ya shigo gidan,ganin Hajiya ba ta dukka falon sai ya wuce dakin ta.
Ita kuwa Hajjo ta na shiga dakin ta sai ta fashe da kuka,kuka mai ban tausayi,ta tsani Khalid har ranta saboda ya ta kura ma ta,ya shiga rayuwar ta,tin da dai nan din gidan su ne hade na ta ya na ta za ta yi ta koma kumurya ta na doko sammako kullum zuwa aiki. Gashi jin rashin lfyar Baba ma ya sosa ma ta rai,ko me ke damun shi? Allah sarki Innar ta,sai mutuwar ta dawo ma ta. Ta na kuka ta fara hade yan kayan ta,kan kace mai ta hade kayan da za ta bukata tsaf,kannan magariba ta gabato,ta dauro alwala ta yi sallah. Ta na kwance bisa daddumar da ta yi sallah sai ga Hajiya ta shigo,ta ce Hajjo kar dai kin yi bacci? Hajjo ta tashi ta na murmushi,ta ce idanu na biyu Hajiya. Ganin yanda idanun Hajjon ya yi jajur Hajiya ta ce kuka ki ke ko Hajjo? Dazu Khalid ke fada min mahaifin ki ba lfy,na san shi ya sa ki damuwa,kar ki damu Allah zai ba shi lfy. Hajjo ta murmusa tare da fadin amen Hajiya,dama ina so na zo wajen ki,ina so na koma kumurya na dan wani lokaci. Lfy? An mi ki wani abu ne Hajjo? Ai gwara ki zauna tinda mahaifin na ki AKTH ya ke kwance. Hajjo ta ce Hajiya dama saboda yaran yayar tawa zan koma can din,dan ina ga ita za ta na kwana da Baba,ni kuma ina kwana da yaran ta saboda aiki sai na ke biyo Baban Aysha mu taho,Hajjo ta yi karya. Ba a san ran ta ba dan sam bayanin Hajjon be yi ma’ana ba,ta ce toh shikenan,amma dai za ki dawo ko? Nan din kamar gidan ku ne,an dade an saba,na dauke ki ne kamar diyar ciki na. Cikin jin dadin maganar Hajiya Hajjo ta ce na gode Hajiya,nan din gidan ne ai,zan dawo da Baba ya sami sauki. Hajiya ta ce toh Allah ya ba shi lfy. Hajjo ta ce amen. Nan su ka ci gaba da hirar su kamar yanda su ka saba kamar diya da uwa.
Washagari Khalid ya ce AKTH billing office domin biyan bills din Baba,aka ce ai tin da sassafe aka yi settln bills din. Sai ya ce owk ba mamaki Jabir ne. Ko da ya yiwa Jabir maganar bayan ya duba Baba sun fito,sai Jabir ya ce shigowar sa kenan,be ma zauna ba. Sai Khalid ya ce ba mamaki daya daga cikin yaran sa maza ne. Indo ya kara tambaya,da ga ganin yanda ta amsa ya san ta san wanda ya biya din,tunanin sa ya tabbata,dan ce masa ta yi daya daga cikin yan uwa ne aka samu aka biya da sasafe. Khalid ya ce Allah sarki,wank mai neman albarka ne,Hajara kuwa ta zo ta duba shi? Indo ta ce tukunna dai amma za ta zo. Khalid ya ce toh Allah ya sa,sai ta ce abubuwa sun ma ta yawa, Hajaran sa ce halin ta sai ita. Uhum kawai Indo ta ce,ba dai a tone tone. Komawa gidan Hajiya da yayi ya tadda Hajjo ba ta nan ba karamin kunci ya shiga ba,har sai da Hauwa ta fara kokawa da al’amaran sa,tin da su ka dawo gida ya bi ya sukurkurce,idan ya na da damuwa ne ko kuma ta ma sa laifi ya fada ma ta,gani ta ke