Showing 57001 words to 60000 words out of 67328 words

Chapter 20 - Diya Mace Book Complete by khadija sidi .txt

da su ka dau hanya ya ruko hannun ta,Hajjo ta yi saurin kokarin fizgewa,ya ruke gam,ya ce am sorry,am realy sorry Suger! Ta ma sa banza,ta ma ki kallan sa. Da ya ga haka sai ya yi shiru. Sai da su ka isa gida,bayan yayi parkin za ta fita ya ce diya mace kenan,duk abunda Baba ya mi ki,ki ka iya cire komai a ran ki,ki ka manta, ji yanda ki ka damu da shi Hajara,diya mace daban ta ke,Allah ya kara azurta ni da wata bayan Neena. Sai da ta bude motar ta sa kafar ta daya waje ta,sai ta juyo ta kalle shi ta ce na iya cire wanda ka min daga rai na,na manta bare na mahaifina da na ke tsatson shi? Shiru yayi har ta fice bai sake tankawa ba dan ta rufe bakin sa.
Ta na shiga babban falo ta ga Hauwa na zaune,ta kafa ta tsare,sai cika ta ke ta na batsewa,yau girkin ta Khalid ya fice tare da amaryar sa har shadayan dare ba su dawo ba,ta kira ta kira wayar Khalid din be daga ba,ba ta san cikin aljihu ya aje wayar ba,ga shi a silent ta ke be sani ba. Sallama irin na dan Musulmi kawai Hajjo ta ma ta,ta shige na ta bangaran. Khalid na shigowa ta tare shi da masifa,inda ta ke shiga ba nan take fita ba,maimakon ya ba ta amsa,gudun kar rai ya baci kawai sai shi ma ya haye na shi bangaran,haka kusan sa Hauwa hauka yayi,gani ta ke Hajjo ta gama asirce Khalid,ya mutumin da ya gama lallaba ta dazu dazun nan,zai kuma shigo yanzu ya ma ta haka? Ba shakka akwai sa hannun malami! Sai kuwa ta shige na ta bangaran ita ma ta na rusa kuka.
Washagari da duku duku gari ko haske be gama yi ba Hajjo ta shirya,ta fito za ta asibiti. Da ke Khalid ya san halin matar ta sa da wutar ciki tin da ya dawo daga sallar asuba ya zauna a babban falo ya na jiran tsammani. Ganin ta fito sai ya tashi,ya na Suger an fito? Ta kalle shi cikin girmamawa amma ba sakin fuska ta ce ina kwana? Ya ce lfy lau Suger,wuce mu tafi ko? Hauwa za ta yi brkfast zuwa anjima sai na kawo mu ku. Ita dai ba ta tambaye shi ba dan haka shiru ta ma sa,shi kuwa ko a jikin sa,shi mai laifi ne burin sa ya shawo kan Suger ya farantawa Suger ko ta huce. Sai da ya duba Baba sannan ya juya zai koma,ganin Hajjo ba ta da niyyar raka shi,ya ce Suger dan taka min mana. Gudun surutu da mitar Indo sai kuwa ta biyo sa din,su na fita ta ce ni fa yau ina da call,so kar ka yi expectn zan kwana a gida. Yayi jim ya ce toh yanzu ki na nufin tin 8 idan ki ka fara aiki ba za ki dawo gida ba ko kin ta shi? Ta ce ai kasan 4 na ke tashi,so daga 4 zan fara call din,sai kuma 8 na safe zan gama shi. Ya ce sannan ki dawo gida? Ta daga kafada ta sauke tare da fadin ya danganta. Kai ya gyada kawai tare da fadin Allah ya kyauta,sai na dawo. Ta ce a dawo lfy. Ya na tafe ya na tunanin Hajjo,shi fa a aikin Hajjo babu abunda ya tsana kamar wannan cal din na ta,dadin ta ma a wata be fi ta yi sau biyu ba,amma dai ya na tsaya ma sa a rai.
Ko da gari ya waye sosai,wajan 10 sai gashi da Hauwa sun zo asibitin,wato sun aje Neena a makaranta. Ba su sami Hajjo ba ta tafi ta fara aiki,sai ya bar Hauwa wajan Indo,ya tafi office din Hajjo. Ga patience zauna akan layin ganin ta,ganin Khalid ba wanda bai bi shi da kallo ba,gaskiya ya hadu kwarai.kai tsaye ya kutsa,ya shige office din. Ta na duba wata tsohuwa Allah ma ya so ta gama da ita sai gashi tsakar office din. Ganin shi sai da gaban Hajjo ya fadi,dan duba tsohuwa ta ke amma ya na ranta,missing din shi ta ke sosai. Idanun sa kan Hajjo da ta wani basar kamar ba ta gan shi ba ya gaishe da tsohuwar tare da fadin Baba mata ta ta duba ki da kyau ko? Tsohuwa ta ce eh,ai akwai aiki,kai ne mijin ta? Cikin jin dadi an yabi Hajjo ya ce eh,tsohuwa ta ce kai amma ka yi sa’ar mata,Allah ya sa mu ku albarka. Ya na dariya ya ce ameen,amma dai Baba ai ita ta yi sa’a,dubanni fa kyakkyawa da ni? Tsohuwa ta ce eh wlh ga kyau ga ado,eh ta wannan dai ta yi sa’a,ya kashewa Hajjo ido,Hajjo ta yi rolling idanun ta,irin kai ka sani,ta ce iya za ki iya tafiya,sai a je a siyi magani Tsohuwa ta ce toh madallah. Ta tashi,tare da yiwa Khalid sallama ta fice. Tana fita ya zaga gaban Hajjo ya yi kissin kumatun ta tare da fadin u see Suger,har tsofaffi yabawa su ke da Khalid,you should b glad am urs….ta na ji wata za ta shigo tsohuwar na fadin ku dan dakata ya fito,mijin ta ne. Ajiyar zuciya Hajjo ta yi gami da fadin dan Allah Khalid ka tafi am too busy wlh,marasa lfy ke jira na fa. Ya ce ni ma mara lafiya ne,wani abu ya fito min a baki,da sauri Hajjo ta tashi ta na menene? Mu gani?daga zaune ya dan daga kai ya bude baki kamar mai nuna ma ta abu din. Hajjo ta dan matsa kusa da shi kamar ta na tsoran matsawa kusa sosai,ta ce ka ma kasa tsayawa na gani,ya ce matso kusa sosai za ki gani,ta na matsowa yayi saurin janyo ta,cikin zafin nama ya fara kissing din ta,ta na kokarin kwacewa ta kasa,dan kan sa ya sake ta,ta yi baya za ta fadi ya yi saurin ruko ta…..
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[7/25, 6:14 PM] Salmah Ateeku: [12:20pm, 6/14/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
6⃣3⃣
Ta fizge hannun ta tana mayar da numfashi,ta ce nan office dina ne,ba gidan ka ba ne,ba dakin ka ba ne,pls kar ka jawo min mutane su shigo su raina ni mana!dan Allah tashi ka tafi. Ya daga kafada ya sauke tare da fadin ke fa mata ta ce,na fi bukatar ki fiye da kowa. Hajjo ta ce plss ka fita. Ya tashi ya na murmushi ya ce akwai abunci wajan Indo,ki daure idan kin sami dama ki ci. Tare na ke da Hauwa,ta na mi ki ya mai jiki. Ya juya ya fice. Sai da ta dau kusan minti goma zaune sannan nutsuwa ta dawo ma ta,ta cigaba da duba jama’a.
Lokaci lokaci ta na zuwa ta na duba Baba,ranar har Hajiya sai da ta zo duba Baba,su Jabir,Nabila ne,Ayush hatta su Doc Hussaina sai da su ka shigo wajan sa,masinjoji da nurses ma ba a bar su a baya ba,kowa na zuwa duba baban Doc Hajara,sai dai ba a ji ba. Hajiya ce ta kai mu su abuncin rana,da za su tafi Nabeela ta ce ita za ta kawo na dare. Jikin Baba kuma ba laifi jikin na sa da sauki,ya na gane jama’a,ya ga yanda jama’a ke tururuwan zuwa duba shi,duk dan darajar diyar sa mace,diyar sa mace ce yau ta zama abun alfahiri ga jama’a,ta zama kamar tauraruwa kuma ya ke cin darajar ta,diyar da be san darajar ta ba,diyar sa Hajjo,ina ma matar sa Ameenutu na raye ta ga baiwa da daraja da yayiwa diyar su mace. Kai kawo na Khalid kuwa ba adadi,bini bini sai Hajjo ta ga ya zo ya duba su,har sai da ta ce ya huta haka da ta raka shi har mota bayan magrib. Ya ce toh gobe da sassafe zai dawo,ta ce Allah ya nuna mana. Su ka yi sallama suna missing juna gaba dayan su.
Washagari da asuba bangaran Baba da ya shanye ya fara motsi,Hajjo ta tadda Mudi ya dan jinginar da shi ya sallaci asuba. Kujera ta ja gaban sa,ganin ta farin ciki ya bayyana fuskar Baba,ya ce Hajjo,Allah ya mi ku albarka ke da yar uwar ki,Allah ya sa diyar ki ta mi ki yanda ki ka min,Hajjo kin cika diya,da na san haka dadin diya mace ya ke da ban kyamace ku ba,da na yi addua’a Allah ya bani diya mace ba adadi,ki yafe min diya ta,na zalince ki yafe min diya ta. Hajjo na murmushi,idanun ta cike da kwalla ta ce ba komai Baba,ni ya kamata na nemi yafiyar ka,na kaurace ma tsawan shekaru,dan Allah Baba ka yafe ni. Ya na murmushi ya ce haba ai tsakani na da ku sai albarka,diyoyi na kun min komai,hakan zan yi kashi na yi fitsari a sitira yar uwar ki Indo ta sa hannu ta wanke,da kuwa matan yayyan ku sai dai su kyamace ni,su ka ma hana yaran su jikokin na zuwa waje na,na fada ma mazajen su sai suce na fiya korafi…..sai ya fashe da kuka,kunya ta kama Mudi,Indo da Hajjo su ka shiga rarrashin Baba,har su ka samu yayi shiru. Haka suna dan hira sama sama,Hajjo ta ce bara ta karasa aikin ta ta zo,ta tafi ta na murna Baba sauki ya samu.
Wajan 7 ta koma wajan Baba,ya na ganin ta ya ce Hajjo kishi na ke ji,taimake ni da ruwa,ta dauko ruwan ta dan bashi ya sha,ya koma ya kwanta,Indo na murmushi ta ce din dazu yace ya na jin kishi fa,da na dauko zan bashi sai ya ce shi sai Hajjo ta zo. Hajjo ta ce Allah sarki ina ruwan Baba. Hannu ya daga kamar mai magana,Hajjo ta matsa kusa da shi sosai,sai cewa yayi Hajjo numfashi na neman ya gagare ni,numfashi na daukewa ya ke…ai kuwa sai ya fara gasping,gaba daya su ka rude,Indo ta ce Mudi kira likita kar mu rasa Baba,ta ma manta Hajjo likitan ce. Ita kuwa Hajjo jikin ta ne ya dau rawa,ta na san halin da Baba ya ke ciki,ba kan shi ta fara gani ba,ta sha gani marasa lfy na yi,ta kuma san karshen,dan haka sai ta juya ta fice da sauri sauri gudu gudu,a kofar da zai sada ta da waje ta yi karo da mutum har ta fadar ma sa da flask din hannun sa. Ya ruko ta,daga idan da za ta yi ashe Khalid ne,ya na menene Hajara? Me ya faru? Baba,Baba kawai ke fita daga bakin ta,ganin Mudi ya wuce su a guje,ga doctora har su hudu biye da shi sai sassarfa su ke dan karasawa ceton ran Baban Doc Hajara,Khalid ya gane me ke faruwa,ya janyo Hajjo jikin sa yayi hugn dinta ya na shafa bayan ta ya na fadin is owk,it is owk Hajara,yi masa addua!!!!
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[16/10 21:52] .: 2:33pm, 6/14/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
6⃣4⃣
A kumurya aka yi zaman makokin Baba,can Hajjo ta tare. Ta ga jama’a an mata kara,ba wanda be je mata gaisuwa ba,hatta Hauwa sai da ta kai mahaifiyar ta da yan uwan ta,bare su Nabeela da Ayush. Ayush ke fada ma Hajjo Suraj na ma ta gaisuwa,ta ce a ma sa godiya,Allah ya bada lada. Amma fa duk abunda ake Hajjo ta ki tayi kuka kamar dai rasuwar Inna,abun na matukar bawa Indo da Khalid tsoro dan sun na zuci ta ke. Sai da aka yi bakwai Hajjo ta koma gidan ta.
Da daddare zaune bisa gadon ta,ta hada kai da gwiwa,gaba daya ji take duniyar ma ta ishe ta. Khalid ya shigo ya zauna kusa da ita,ya ce Suger ya dai? Ta ce ba komai. Ya ce toh ki daure ki cire damuwa daga ranki,duk kan mai rai mamaci ne,mu ma ta mu ke jira. Har ran sa so ya ke ya kwana tare da ita dan ya debe ma ta kyewa dan ya san tin rasuwar Baba cikin mutane ta ke kwana,toh amma ba dama saboda he is man of his words,ya ce ba zai kwana dakin ta ba sai idan ita ta gayyace shi da kanta. Ya tashi tare da fadin bari na bar ki ki kwanta Suger,sai da safe. Ta ce toh. Sai da ya kai kofa ya ji ta kira sunan shi,ya juyo tare da fadin yes Suger? Ta yi kasa da ido ta ce dan Allah ka kwanta….ina nufin ka kwana dakin nan in ba damuwa…..ya san ba karamin abu zai sa Hajjo fadin haka ba,ya murmusa ya dawo ya zauna kusa da ita,ya ce ba dumuwa infact i wil love to. Ta ce amma fa a kasa za ka kwanta. Ta shi yayi ya na dariya,ya dau filo ya jefe kan carpet sannan ya ce duk da dai ban taba kwanan kasa ba,for you i wil nt mind. Ya kwanta sannan ya ce ki kwanta. Juyawa ta yi ta kwanta,gami da kashe wuta,amma sai bacci ya gagare ta,tai tajuyi,gaba daya wani irin tsoro ne ya addabe ta,burin ta taji mutum kusa da ita. Ko da ta tashi ta zauna tare da kunna wuta,ta ga Khalid be motsaba,ta tabbatar yayi bacci. Sai ta tashi a hankali,ta sauku kasa kan carpet inda ya ke kwance,itama ta kwanta bayan sa,ta juya ma sa baya kamar yanda shi ma ya juya ma ta,bayan ta jikin na sa,ta dai ji mutsin mutum kusa da ita,sai ta saki ajiyar zuciya,ta yi filo da tafikan hannun ta. Ko minta biyar ba ta yi da kwanciya ba ya jiyo ya sanya hannun sa ya zagayo ta jikin ta,har sai da ta firgita,ya ce shhhhh it is owk,babu abunda zan mi ki Hajara,jts relax owk? Ya janyo ta jikin sa,hannun sa zagaye da ita yayi hugn din ta,a sannnu a hankali Hajjo ta saki jikin ta. Sai kuma ta fashe da kuka. Kuka ta ke amma shi Khalid dadi ya ji,dan abunda su ke ta so ta yi kenan ta ki yi,tunda ta yi yanzu za su sami lfy kenan. Ya ta rarrashin ta kamar yar baby,har ta yi mai isar ta ta yi shiru. Khalid ya ce Hajara,ta ce ummm ya ce kiyi hakuri, ya ji ta yi shiru,ya cigaba da fadin pls ki yi hakuri kawai ki na ma Baba addua’a,owk? Ya ji shiru,yayi kissing wuyan ta,ta dan motsa kadan. Ya ce Hajara ina san ki! I love you soo much it is eating my hrt up. Ban san ya aka yi na fara san ki ba,ban kuma sanda na fara san ki ba,amma na san soyayyar ki na neman halaka ni Hajara,kin sauya min tunani kan abubuwa da dama,kin bude min ido,to see d world from every angle,u ar my bst half! Ya ce kin san me? Ya ji shiru,ya dan daga ya kalli fuskarta,sai ya ga ashe fa da iska ya ke magana,Hajjo kam tuni bacci ya kwashe ta,ya kara jin dadi ta sami bacci dan Indo ta ce ma sa ba ta bacci. Ya dada hugn dinta,ya karanto addua’ar bacci ya shafa ma ta da kan sa,sannan shima ya rufe na shi idon.
Washagari tashi ta yi ta ganta in da su ka kwanta,Khalid ya tafi masallaci. Cikin azama ta yi sallah ta yi wanka,ta na kitchen ya dawo,amma ba su hadu hadu ba sai wajan brkfast. Shi ya sauke ta aiki,ranar ta koma aiki,nan ma sai gaisuwa ake ma ta. Da ta dawo duk da dai girkin ta ne sai ta tadda Hauwa ta shiga kitchen din ta ma ta,ta ji dadi sosai dan dama ta na ta tunanin girkin. Ta ma ta godiya,Hauwa ta ce ba komai ita da tawo jiya jiya,ga shi ba ta gama jin zafin rashi ba,ai amfanin zaman taren kenan. Can bayan isha’i ta yi wanka ta na shirin kwanciya sai ga Khalid. Ganin ta yi shirin bacci tsaf,ga ta ta yi kyau kamar ya dauka ya boye sai gaba daya ya fara rikicewa. Ya ce Suger tashi mu yi sallah. Ta na daga kwance cikin bargon da tinda ya shigo ba shiri ta kudunduna ciki ta ce wlh na yi sallah,ya ce nafila za mu yi,ta ce ai har shafa’i da wutiri ma na yi. Ya sosa kyeya,ya ce wannan daban ne za mu yi,pls tashi mana. Tana mita da zunbure zunburen baki ta tashi ta dauro alwala. Bisa dadduma ta tadda shi ya na jiranta. Ta daura zani ta hijab,Khalid ya ja su sallah raka biyu. Bayan sun idar,ya dafa kan Hajjo ya karanta adduar neman yarda da albarkar ubangiji. Tin daga sannan Hajjo ta gano inda ya nufa,tuni ta tsorata,ta fara neman hanyar zillewa. Ta yi saurin hayewa gadan ta ko Hijab din ba ta iya cirewa,shi ma din ya san abunda ta ke nufi,da ga zaune inda su ka yi sallah ya ce Suger yau a gado za mu yi bacci? Hajjo murya a kasa ta ce ah ah tafiya za ka yi,yau dakin ka za ka kwana….ya na dariya ya ce ai kuwa ba ki isa ba yarinya,ya tashi da nufin hawa gadon Hajjo ta tashi da sauri za ta sauko ta gudu,ai kuwa sai ya bi ta yayi caraf ya kamota,ta na magiya ya na dariya su ka dawo bisa gado. Kokarin da ta ke na kwacewa ya sa shi danne ta ya dan sakar ma ta nauyi,kwakkwaran motsi ma ya gagareta,sai ta sa kuka. Da ya ga haka ya dan daga ta,ya ce shhhh am nt going to hurt you,I love you,I jst love you my wife…fuska cike da hawaye ta tsaya ta na kallan sa,maganar ta sa tai ma ta bazata,ganin yanda ta ke kallan na sa ya sa shi gyada kai tare da fadin yes i mean it,ina matukar san ki Hajara,ba zan cuce ki ba,bazan zalince ki ba,I jst want to hold nd love you…
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[7/25, 6:14 PM] Salmah Ateeku: [12:47pm, 6/14/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
6⃣5⃣
Jin kalaman sa,yanda ya ke fada da yanda ya ke shigar ta ya sa hankalin ta ya kwanta,har ya iya cire ma ta hijabin ba ta lura ba,haka ma zani,ya rage sai kayan baccin ta,sannan ya ja ta jikin sa,ya cigaba da fada ma ta dadan kalame ma su kwantar da hankali har ya samu ta gama sakin jiki dashi,cikin dabara ya fara kissing din ta,ita kuwa Hajjo da ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login