Showing 51001 words to 54000 words out of 67328 words

Chapter 18 - Diya Mace Book Complete by khadija sidi .txt

shekara da shekaru,ga daukan abu mai nauyi,ga tsallake tsallaken kwata mai girma dadai sauran su ya sa mu ke dan bawa yaran mu kayan matsi,shi ma din ba wai na matsi sosai ba,irin su ganyan magarya,ake tsarki da shi,da miski,dama kuma idan za ta yi gyaran jiki za ai mata dukkan da dirot ko farar kaya,wannan ma ya wadatar,ba a dinga tsugonno a wannan,a waccan, a shafa waccan,tusa waccan,garin neman gira a rasa ido,ku ga yarin ta matse gam kamar bango,wata dama a matsen ta ke sosai ba ta san kanta ta kara,sai daga baya a zo ana jinya,wasu har dinki ma,toh ina amfanin haka? In ma matsin sosai za ki yi gwara ki jira a kai ki ki san kan ki,ki gane irin ki sai ki yi matsin da hujja.
Toh ga gudun mawata gare ki Hajara amarya. Doctors su ka ce ita kadai ko har mu? Doc Hussaina ta ce har ku da ma da ku ke gidajan ku za ku iya yi,amma yanzu da ita na ke magana ta,duk su ka sa dariya. Doc Hussaina ta ce ki na ji na Hajara? Hajara ta ce eh. Ta ce idan biki ya matso kusa sosai,kafin a fara sai ki sami kankanar ki wanda ki ka san za ki iya shayewa kwallo guda,sai ki yi sallah raka’a biyu nafila,ki fafaye saman kankanan,ki dan caccaki cikin yanda ruwan zai tsatso,sai ki karanta suratul Khafi,Maryam da Rahman ki tofa ciki,ruwan da ya tsotso na kankanan sai ki disa cikin turaren ki da ki ka ware dan amfanin ki ke kadai,kamar humrah,bayan ki tabbata ruwan kankanan ya zuba ciki sai ki aje kayan ki. Ki shanye kankanar ki tsaf ki koshi,turaren ki kuma ki na amfani da shi,inshaAllahu mijin ki zai girmama ki,ya martaba ki,yayi respect din ki,za kuma ki sami daukaka wajan sa wanda shi ake fata. Gaba daya kowa ya fara kai gaskiya ni ma zan yi,ni ma zan yi. Hajara ta ce na gode Anty Hussaina,Allah ya kara girma. Doc Hussaina ta ce amen. Allah ya bada zaman lfy.
Hajiya ke neman ta ido rufe,da ta tashi daga aiki sai ta biya gidan ta. Hajiya ta na ta tsokanar ta wai Hajjo ta zama sirika. Wani nauyi da kunyar Hajiya ta ke ji sosai,ta ka sa sakin jiki su yi maganar auren da kuma sauran abunda Hajjo za ta bukata saboda kusan rabi tare su ka siya da Hajiya kafin ma Khalid ya dawo a fara maganar auren su. Da Hajiya ta ga dai Hajjo ta ka sa sakewa sai ta hada ta da kanwar ta,tare su ka cigaba da shirye shiryen biki,ba Jabir ba,har Hajiya sai da ta dunkula dukiya mai tsoka ta damkawa Hajjo dan shirye shiyen biki,ba shakka sun ma ta karamci kwarai. Gyara kam Hajjo na sha kwarai daga wajan Doc Hussaina,dake Doc Hussaina duniya ce.
Hauwa kuwa sai da Khalid ya hada ta da Hajiya tai ma ta nasiha sosai sannan ta sauko. Ana sauran sati guda daurin aure ta tare saban gidan Khalid. Gidan ya hadu ya tsaru kamar gidan turawa,da ke ma su abu da abun su,abu na so Khalid bluiders of d world. Bangare uku ne,bangaren Khalid a sama,sai kuma katan falo a kasa wanda ya sada ban garan Hauwa da Hajjo matan na Khalid,sai kuma katan kitchen ma dauke da dining area,dakin Neena ma bangaran Hauwa ya ke,Gidan cike ya ke fal da kayan more rayuwa,gashi very spacious. Hatta bangaran Hajjo Shi ya zuba kaya,ya dai aika Sani ya tambaya ma ta colour din da ta ke so.
Ranar juma’a aka daura auren Khalid da Hajara,Khalid ya biya sadakin sa dubu hamsin. Su Ayush ne amara,duk da ba wani bidi’a aka yi ba,daga wuni da aka yi a kumurya,sai walimar da aka yi gidan Hajiya sannan aka wuce da amarya akai Hajjo dakin ta. Kuka wajan Hajjo abun ba magana,rayuwa ta sake canzawa,ta shiga saban babi…
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[7/25, 6:06 PM] Salmah Ateeku: [12:56am, 6/11/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
5⃣7⃣
Hannu Hauwa aka damka amanar Hajjo,sai cika ta ke ta na batsewa ita da yan uwanta,habaici da guda kuwa yan uwan Hajjo sun sha. Ga wani ado da kyau da Hauwa ta yi kamar ita ta yi kanta dan kyau,sai a sannan Indo ta gane matsalar da Hajjo ke gujewa kan ta dan gaskiya Hauwa ta cika mace,su Doc Hussaina kuwa ba dan sun san wacece Hajjo ba sun kuma yarda da shirin da su ka ma ta da sai sun daura hannu a ka sun ce sun shiga uku.
Bayan su Indo sun kara ma ta fada sai su ka watse,su ka bar Hajjo tsakiyar gadan ta ta na sharbar kuka. Ango Khalid ya shigo cikin shigar angwaye na alfarma,sai ma ya dada zama yaro kamar wanda ya yi auren fari.Hauwa zaune bangaran ta,ita ma yan uwanta sun watse,Neena na dakin ta ta yi bacci,Hauwa ta sake ado ta yi kyau kamar ita tai kanta ango Khalid ya shiga ya same ta. Shi kan shi kyan na ta ya ruda shi,ya janyo ta jikin sa ta zille ta na malam yaya ne,ba fa ni ba ce da kwanan ba yau! Ya dara tare da fadin an ma fara min gori kenan. Ta ce ya bazan ma ka ba gori ba tunda irin rayuwar da ka tsarawa kan ka kenan. Ya murmusa gami da sake janyo ta jikin,ya na hussssh,say no more. Ina Neena? Ta ce ta dade da kwanciya ita dai kam. Ya ce toh ki fito falo ki same mu,bari na kira kanwar ta ki. Da kamar za ta ce ba za ta zo ba,sai kuma ta ga kamar hakan zai sa Hajjon ta raina ta,ta ce toh ta na fitowa.
Bangaran Hajjo ya shiga,ya tura komar a hankali,wani kamshi mai dadi ya daki hancin sa. Yayi sallama tare da shiga daki. Idanu ta daga ta kalle shi,wannan karan Khalid Khalid ne ke neman numfashi ba Hajjo ba,tsabar kyau da kwarjini irin na amare gaba daya ta sauya yanayin sa. An ma ta ado cikin farin leshi,ga farar lufaya an nada mata,ga gyaran jiki da ta sha wajan su Doc Hussaina fatar nan na ta wankan tarwada har wani sheki yake. Da kyar ya daure,ya na wani basarwa dan kar ta gane tarkon ta ta kama kurciya ya ce muna jiran ki falo amarya. Juyawa yayi ya fita ba tare da ya ji amsar ta ba.
Falon kasa da yayi dan zaman iyalan na sa duka ya zauna. Hauwa ce ta riga fitowa,ta zauna kusa da shi suna dan hirarrakin su,sai ga Hajjo ta fito,idanun ta a kasa,fuskar ta rufe da mayafi ta zauna a na ta kujerar da ga gefe,Khalid ya ce ta so ta zauna kusa da shi kamar yanda Hauwa ta zauna,ma’ana su sa shi tsakiya. Ran Hauwa ya sosa da kishi,wato dai sai ya jera su,ya nuna ma ta matsayin su daya,bare ma fitowar Hajjo yanda ta ji tana kamshi kamar diyar shuwa ya sa zuciyar ta tsinkewa. Ba musu da ke gaban uwar gidan sa su ke sai ta tashi ta koma kusa da shi din. Ya mu su nasiha sosai da fatan za su hade kan su,ya kuma roki Hajjo da ta kara yiwa Hauwa kara akan Neena,tin da duk an zama daya,dan Allah ta karanta. Cikin ranta kuwa cewa ta ke indai kara ne kunzo wajan ta,ita ba matsala gare ta ba.
Ya kare nasihar shi da addu’a. Hauwa ce ta fara tashi ta tafi,Khalid ya bi bayan ta. Ita ko Hajjo tashi ta yi ta koma na ta bangaran. Ta yi wanka fito daure da shawl dan yanda Khalid ya dade be fito ba sai ta dauka can zai kwana ta saki jikinta,ta zauna ta na shafa mai. Kamar da ga sama sallamar shi da shigowar sa lokacin guda ne…
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
Advertisements


SHARE THIS:
TwitterFacebookGoogle


RELATED













Skip to content
ummu-abdoul
MENU
Diya mace 4th
Posted by UMMU-ABDOUL on OCTOBER 17, 2016
​14am, 6/11/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
5⃣8⃣
Da sauri Hajjo ta tashi,ta kuma koma ta zauna ta na jan shawl din kan gwiwar ta. Da ganin na ta da kuma yanda ya ga ta rude sai ya bashi dariya,dariyar ta sa ya bawa Hajjo haushi,dama kuma kule ta ke da shi. Ta yi saurin jan lufayan ta ta rufe jikin ta tana mallam menene za ka shigo min daki ba sallama! Ya na murmushi ya ce na yi sallama Suger,ta ce me ya sa ba ka tsaya na ba ka izinin shigowa ba kawai za ka shigo min?ya ce gida na ne,auren ki na ke. Ta cije leba gami da ka fita ka bar min daki,pls ka fita! Ya ce ni ki ke kora Hajara? A daren auren na mu na fari ki kore ni? Idanun ta kwalakwala,sai a sannan ta tuna fa ashe wai daren auren ta ne,ta tuno yanda na ta ta kasance da Garbati,tuni idanun ta ya rufe,ta ce eh kai na ke kora,pls ka fita. Duk da hakan be ma sa dadi ba,amma jin kai ya sa ya ki nunawa,sai ma murmushi da ya sakar ma ta,ya karasa cikin daki,gaban ta ya kara faduwa. Ya lura da hakan,sai da ya kai dab da ita,ta dada dunkulewa cikin mayafi,ya na murmushi ya aje ledar gaban ta yana fadin ga abunci,na san yunwa ki ke ji. Ya sunkuyo fuskar ta,Hajjo ta runtse ido,kumatun ta yayi kissin ya dago ya na dariyar yanda ta sankare,kana ya ce suger,Khalid is a gentle man,so ki sa a ranki ba zan taba kwana cikin dakin ki ba sai dai idan ke ki ka gayyace ni da kan ki. Ya juya ya fice. Sai da ta tabbatar ya fita sannan ta saki jikin ta. Cikin azama gudun kar ya dawo ta sanya rigar baccin ta iya gwiwa. Sai da ta nutsu sannan ta bude ledar da Khalid ya aje,kaza ce gashasshiya da fresh milk,ta ci ta koshi,sannan ta dan taka a tsakar dakin gudun bacin ciki,ta kwanta ta sha baccin ta dake dama ta tara gajiya.
Sai da ta yi sati daya a gida ta koma kan aikin ta. Sam Khalid ba ya gaban ta bare kuma matar sa,kwana uku uku su ka raba kwanan duk da kuwa duk ranar kwanan Hajjo dakin sa ya ke kwana bisa ga alkawarin da yayiwa Hajjon,ita kuwa Hauwa da ta lura da haka,sai ta kara jin kan ta,wato da gaske dai ba san Hajjon ya ke ba tinda ya aje ta tamkar fanko ne kawai. idan ranar girkin Hajjo ne kafin ta fita ta ke musu brkfast da abuncin rana,da ke 7:30 ta ke fita,8 ta ke fara aiki. Da ta dawo 4 sai ta daura na dare. Kuma bisa al’adar su,tare a ke zama a ci abuncin kan dinig table da ke cikin kitchen din na su,nan Hajjo ta ke ganin kissa da kisisi na wajan Hauwa,ita abun har mamaki ya ke ba ga Neena na wajan ita ko kunya ba ta ji? Tai ta jan shi da hirar da be ma shafi Hajjo ba yanda za su ware,ita kuwa Hajjo ko a tafin kafarta,ita dai ta cika cikin ta tashi idan ma hadiye shi za ta yi tayi can ma ta.Khalid ya dame ta da korafin shi ba zai juri hawan adaidaitan ta ba,kullum wani gardi ya ke jin kamshin ta,dan haka lalle ta yi shirin koyar driving dan ba zai juri yay kai ta ya na dauko ta ba,haka kuma ba zai dau driver ba. Tsakanin ta da diyar ta nesa nesa,dan ita ganin ta take kishiyar uwa ba ma uwa ba,ita kuma Hajjon sai ta ke wa Hauwan kara,ta ke dauke kan ta daga kan Neenan.
Randa ta cika sati biyu a gidan ta,bayan ta gama girki an zauna anci,sai ta tashi ta shige bangaran ta ta bawa Hauwa waje ta yi abunda ta ke so. Ta na shiga ciki Khalid shi ma ya tashi,ya sake kaya cikin sport wears din sa ya fita jogging. Wanka Hajjo ta yi,ta sanya rigar baccin ta pink mara hannu da nauyi,ga laushi iya gwiwa ta tsaya ma ta,ta kama kan ta da ya ke a tsefe ta rasa mai kitso,ta yi kalaba guda biyu,abun ku da kan ba gashi sai kuwa su ka tsaya gudil gudil da su kamar kaho. Ita kanta da ta kalli kanta a madubi sai da ta yi dariya,ta yi kama da yar yarinya sak. Ta ja kujerar karatun ta gaban table,ta kunna system ta fara sana’ar na ta,wato research.
Bayan Khalid ya dawo,a tsakar dakin sa daga shi sai gajeran wando da shawl a rataye wuyar sa ya na shirin shiga yayi wanka,sai ya ji duk duniya idan be tsokano Hajjo ba ba zai ji dadi ba,dan yanzu ba wacce ya ke son zolaya kamar ita. Kawai sai ya fasa shiga na shi toilet din ya nufi bangaran na ta. Ta yi nisa cikin research,ba ta ankara ba ta ji an bude kofa,da sallamar sa da shigowar sa lokaci daya ne. Ta daga ido ta kalle shi,ganin yanayin shigar ta sa ta yi saurin yin kasa da ido. Murmushin nan na sa na tsokana ya sakar ma ta,tare da fadin nawa toilet din is faulty,i wil use urs in ba damuwa….ya na magana ya na nufar kofar bandakin,jin ta yi shiru ya juyo ya kalle ta,ya ga sam hankalin ta ma ba ya wajan sa,sai a sannan ya lura da kahon gashin ta biyu,ya ce like seriously Suger iyakan gashin ki kenan ko kuwa kin boye wani karkashin filon ki? Dagowa ta yi ta kalle shi,sai kuma ta tuna yanayin da ya ke ta kara saurin kau da kai,gaba daya magana ma ta kasa dan takaici da kuma takurar da shigowar sa ya sa ta. Ganin ta ma sa shiru ya shige ban daki ya rufo. Sai a sannan ta saki ajiyar zuciya. Kamar za ta koma falon ta,sai kuma ta fasa gudun kar yayi tunanin tsabar tsoran sa ya sa ta gudun. Amma gaba daya ta ma kasa gane komai,burin ta ya zo ya fita ko ta sami nutsuwa. Ile ko sai gashi ya fito daure da shawl,kirjin sa duk a waje ga ruwa na diga daga cikin sa,hannun shi ruke da dan karamin shawl din ta ya na goge kan sa. Da wayo ta saci kallan sa,su ka kusa hada ido ta yi sauri janye na ta ido. Ya na murmushi ya ce ba sai kin saci kallo na ba Suger,am ol urs,saki jikin ki u can stare as long as u want. Maganar ta sa sai ta bawa Hajjo haushi,ta yi karfin hali ta kalle shi ido cikin ido sannan ta ce ni Hajjo na saci kallan ka? Me zan kalla Khalid? U ar nt man enough for me…..sai da ta fada sannan ta yi dana sanin dan subul da baka da ta yi,da za ta iya shanye kalmomin ta na karshe da ta shanye ganin yanda idanun sa ke shining,fuskar sa dauke da mischievous smile ya nufo in da ta ke,dan tsoro kasa motsawa ta yi,kamar wacce aka sa igiya aka daure,har ya karasa kujerar da ta ke,ya sunkuyo da fuskar sa dabda na ta,Hajjo ta yi kasa da na ta idon gaban ta na dukan uku uku,ya sa hannu ya dago da haban ta ya na kokarin sanya kwayar idanun sa cikin ta,amma ta ki dagawa ta kalle,ta na jin saukar numfashin sa kan fuskar ta,ya ce maimaita abunda ki ka ce Hajara. Tsit ka ke jin Hajjo kamar wacce ruwa ya shanye,ya ce fadi na ji,who is nt man enough for u? Ta yi shiru,hannun sa bisa fuskar ta,ya fara wasa da yatsan sa kan lips din ta da yake kallo kamar mai nazari,kan ta ankara tuni ya mikar da ita ya hada da jikin sa ya fara kissing din ta. Da ke Hajjo ta ji saban abu,abun da sai dai ta gani ana yi a tv ta dauke kai ko kuma ta karanta a littafafai wai shi Khalid ke ma ta, ta fara kokarin zullewa har ta hakura ta dai na…
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[7/25, 6:12 PM] Salmah Ateeku: [11:30am, 6/14/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
5⃣9⃣
Ya kusa shagala ya manta da inda ya ke haka ita ma Hajjo da ta shiga wani duniyar,da kyar ya iya yaki da zuciyar sa,ya dago ya na kallanta,idanun ta runtse tana numfashi a hankali,ya maida ta jikin sa,yayi hugn din ta sosai kamar za ta shige cikin sa,sai da ya sami nutsuwa,cikin rada ya ce mata dis is jst a kiss Suger,ba dan Khalid is a gentleman ba da na gwada mi ki ya Man ya ke,amma a sannu Suger,cikin kunnan ta ya rada ma ta am much more dan Man enough for all the women in d world Suger……ya janye jikin sa a hankali,sai da Hajjo ta yi saurin dafa table dan gani take ba za ta iya tsayuwa ba, shi kuwa ficewa yayi da sauri kafadar nan a tsaye dan jin kai. Da fitar shi ta yi saurin hayewa gado,ita dai kam ta shiga nau’i,bargo ta ja ta dukunkuna,abunda ya faru tsakanin ta da Khalid ya sa ta dai na gane komai,ya tsayar ma ta da duniyar cak.
Shima wajan gugan na ta hakan ta ke,tin komawar sa daki ya kasa sukuni,he jst can’t blv Hajjo can b dis innocent yea Innocent nd sweet at thesame tym,sam da dukkan alamu yanda ta yi reactn ya san saban abu ne a wajan ta,hakan ya kara sa shi san more,he love every bit of it,He want her dan da kyar ya iya jurewa be koma ba,amma daran ranar sam bacci ya nema ya rasa,tunin Hajjo ne ya raya ma sa daren.
Washagari ko karyawa ba ta yi ba ta gudu wajan aiki gudun haduwa da Khalid,dake ta yi sa’a ba girkin ta bane. Dab da la’asar bayan ta dawo daga aiki,ta yi wanka,sai ta fito babban falon su,nan ta tadda Neena a na game,ta ce Neena ba gaisuwa? Hankalin ta kan game tace ai ban gan ki ba Aunty,sannu da zuwa. Hajjo ta ce sannun ki,ta sami waje ta zauna,sai ga Hauwa ta fito daga kitchen ta ce Neena a tashi a yi shirin islamiya. Neena ta make kafada,ni wlh na gaji. Ga mamakin Hajjo sai ji ta yi Hauwa ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login