Showing 33001 words to 36000 words out of 67328 words

Chapter 12 - Diya Mace Book Complete by khadija sidi .txt

brother i have,ka san Allah? Kar ka sake ka matsawa yarinyar mutane saboda selfish interest din ka,ta na da wanda ta ke so,u better stay away from her. Khalid ya daga kafada,wannan na ka ra’ayin kenan,wat if shez interested? Bare na san she is,dole shi is cos ko wata mace burin ta ta sami miji kamar ni,ol women wants an outstanding man as a husby,kasan ma ta nawa ke sona ina mu su yabs bare kuma ni da baki na ce zan aure ta,God she should even b grtful,ai ina fada ma ta za ta hau murna,I tell u bro!
Jabir ya murmusa,ya ce ba ko ba Hajjo ba? Ayi mu gani,.. Da haka su ka isa gidan Jabir,zai fita Khalid ya ce ya za a yi a min hanyar Hajara ne? Na ga da kai ake kama kafa….Jabir ya ce for ur imformation,yarinya na da correct man,a Doctor so kar ka bata lokacin ka!Khalid ya ya yi mika ya na mischievous murmurshi ya ce ko kai ne correct man din,d so called doctor sai ka saurara ka bar wajan bare kuma wani bare,Khalid ne fa kanin ka,taba neman mace na rasa ba! Sai dai ban nema ba! Jabir ya murmusa ya ce wannan karan ka ma rasa! Khalid ya ce no ka bani five month za ka ga Hajara a gida! Jabir ya na dariyar yanda Khalid ke da gadara,ya ce get lost! Ya na dariya Khalid ya tada motar shi,ya na a gaida uwar yan mata,Jabir ya daga ma sa hannu ya shige gidan sa. Khalid ya kama hanya da tunanin kudirin da zuciyar sa ta yanke,if realy goin to hav a second wife,den she should b Hajara.
DEDICATED to The Women Of virtue💁👰🙋(group).




















Skip to content
ummu-abdoul
MENU
Diya mace 2nd post
Posted by UMMU-ABDOUL on OCTOBER 17, 2016
​[16/10 21:47] .: /25, 5:15 PM] Salmah Ateeku: [7:32pm, 6/5/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
4⃣4⃣
Da zancen Hajjo cikin ran sa ya kwana,washagari Allah Allah ya ke yamma ta yi ya samu ya je gidan Hajiya ya ma ta zancen Hajjo ya ji ta bakin ta kafin ya yiwa Hajjon magana,dan ya san sai da yamman ake samun Hajjo a gida in dai ba weekend ba. La’asar sakaliya a gidan Hajiya ta ma sa,ya ko ci sa’a Hajjo ta dawo. Maganar ta sa ta yiwa Hajiya dadi,toh amma sai ba ta nuna ma sa sosai ba kar yayi taking advantage of it ya yi tunanin Hajiya za ta sa baki. Ta ce auta ba laifi idan za ka kara aure dan matar ka ba ta haihuwa,hakan ma dole ya faru tinda kowa ya na so ya ga zuri’ar sa ta cigaba from generation to generation,zabin ka na Hajjo shi ma ba laifi,amma ka same ta da kanka ku sasanta,dan ni na san Hajjo na da manemi,idan ta ga za ta aminta da kai,tin da waccan iyaye ba su shiga ba,fyn tsakanin ku,idan kuma ta ce ah ah,ban da takura,ka nemi wata. Ni dai fatan alkhairi mu ke,bazan sa baki ba sai Hajjo ta amince dan kanta dan sa baki na zai iya sawa ta yarda ko da kuwa ba ta so. Khalid ya ce Hajiya ta za ma ta so ai,am very sure of dat. Hajiya ta dara ai dama kai dai kam u ar olways full of urslf,toh Allah dai ya sa. Khalid ya ce amen. Hajiya ko za ki yi kiran Hajjon sai na sheda ma ta ko? Bara na jira ta a karamin falo,Hajiya ta ce toh bari na kira ta din.
Hajjo kwance bisa gadan ta,ta gama waya da Suraj kenan ya fada ma ta wata daya ya rage ya dawo,sai sakar yanda za ta tarbe shi ta ke cikin ran ta,dan a zahiri ta fara sabawa da Suraj sosai ta damu da shi ba kamar da ba. Wayan da ke kan bedsyd din ta ne ya fara ringn,da ga kwance ta sa hannu ta dauka gami da karawa a kunnen ta,ta ce Hajiya na zo ne? Daga dayan bangaran Hajiya ta ce Khalid ne ke san magana da ke,ya na jiran ki karamin falo. Hajjo ta dan yi jim..Khalid? Ni kuma? Ta ce tam Hajiya,zan same shi yanzu. Ta aje wayar ta na tunanin me kuma ya faru? Ko ya dawo ma ta da Innar ta ta ne? Bari dai ta fita ta ji. Da ke ba kayan arziki ne a jikin ta ba,sai ta ja hijabin ta har kasa ta sanya,kai tsaye ta fito ba tare da ta damu da ta duba kamannin ta a madubi ba.
Ta na shiga falon kamshin turaren shi ya daki hancin ta,ya harde kafa daya kan daya kan kujera,sanye da kanana kaya da ke matukar ma sa kyau. Ido su ka hada,ya sakar ma ta murmushi,ta ki maida ma sa da murmushin,sai ma sallama da ta ma sa,ta sami waje a kasa ta zauna gefe guda. Ya ce ya ki ka zauna a kasa? Dawo nan mana ya nuna kujerar da ke kusa da shi. Hajjo ta murmusa,dimpol ya bayya wanda ke kara ma ta kyau,no am owk nan ma. Ina wuni? Ya aiki? Ya amsa da lfy lau,ya na ki aiki? Ta ce Alhamdulillah. Sai kuma su ka yi shiru,Khalid ya zuba ma ta ido,kawai Neena ce zaune. Ya ce shez jst lyk you. Ta daga ma sa gira tare da fadin sorry? Ya ce diyar ki Neena,is precisely lyk you. Hajjo ta murmusa,ta ce na sani,is dat y u called me? To tell me am jst lyk her ko kuma wani abu ne ya same ta? Khalid ya dara,shi kawai mamaki ta ke bashi,child abuse ce haka ta ke iya kallan sa ido cikin ido ta bashi amsa daidai da ta shi,har wani sa’in ta watsa ma sa da yar magana? Kai gaskiya boko yayi,jami’a ba wasa ba ce. Ya ce no,ba ma saboda ita na ke neman ki ba,it is abt us,maganar mu ce ni da ke. Gaban Hajjo ya fadi,amma sai ta basar dan kar ya gane,ta ce us? Ni da kai? Hope all is well. Ya ce yes ol is well,na yanke shawarar auren ki ne a matsayin ki na mahaifiyar diyar da na ke so.
A hankali ta daga ido ta kalle shi,maganar ta ma ta kama da tatsuniya,be yi mamakin ganin ta sa dariya ba,dariyar ta ta mai ban sha’awa,wushirta da dimpol din ta du su ka bayyana su ka kara kyawata kyan ta. tsayawa ya yi ya na duban ta kawai fuskar shi dauke da mischievous smile,dama ya sani,ya san she will celebrat idan ya ce zai aure ta,ko wace mace za ta yi,dama dai Jabir ya na nan ya gani da idanun sa. Ga mamakin sa da dariyar ta ta ta tsaya sai ya ga ta tashi ta na nufin juyawa ta fita,yayi zatan tsabar farin ciki ne ya sa za ta koma daki dan ta yi celebratn da kyau,ya ce wait,ba shi kenan ba ai Hajiya,wen za a fara maganar aure? Ta juyo ta na murmushi,Khalid? A karo na farko da ta kira sunan shi,wanda shi kan shi be lura da haka ba sai a yanzu,hakan kuma ya sa shi shiga wani yanayi na kasa gane shin wai ina matar nan ta dosa ne? Lokacin kuwa ta fahimtar da shi.
Ta ci gaba da fadin wannan shi ake kira expensive joke,pls ina respect din ka,for d fact dat diya ta consider u a father,nd kai kuma ka yi taking responsbility din ta as if kai ne mahaifin ta,so i beg of u let us maintain dat,nxt tym in ka na da jest try someone else nt me,ta kare da murmushi. Gwiwar sa ta fara sanyi,wato shasha ma ta dauke shi ashe,hw dare her! Shi ma din tashi ya yi,ya tsaya gaban ta,ya ce expensive joke? Jest? Tin da mu ke na taba mi ki wasa ne Hajara? Hajjo ta ce Hajjo,kira ni da Hajjo ba Hajara ba pls,haka kowa ya ke kira na. Zan cen tin da mu ke babu,dan ba mu ta zama tare ba,daga nesa nesa dai jst lyk now,dax y na ce kar ka soma. Khalid ya ce ba wasa na ke ba toh,i mean it,marry me. Hajjo ta murmusa ta ce y should i of all people marry d mighty Khalid? Duk da ya san zolayar sa ta ke,ya gyara tsayuwa ya ce saboda Neena,nd ina so na sami yara nawa na kai na su zama tsatson su daya da Neena,kin san mata ta ba ta haihuwa,i want u to bear my kids. Hajjo ta dara,ta ce toh bazan aure ka ba. Cike da mamaki ya ce wannan amsa haka kiri kiri? Saboda me ya sa? Ta ce saboda you ar nt my type,i can’t even manege someone lyk you. Tsayawa yayi ya na kallanta,ya ma rasa amsar da zai ba ta har ta juya ta fice. Komawa yayi ya zauna,Hajjo ta ma sa bazata matuka,shin dama akwai macen da zai ce ya na so ya aura ta ki? Kai ko Hauwa da ta hadau ten over ten ba ta ma sa aji ba,bare kuma karan kada miya Hajjo. Ya saki ajiyar zuciya,obviously Hajjon da ya sani a da wato child abuse da wannan Hajjon ar two differant worlds! Rai bace ya tashi ba tare da ya yiwa Hajiya sallama ba ya bar gidan.
Tin shigar ta daki ta haye gado ta yi kwanciyar ta,wai ita Khalid zai kalla ya ce zai aura tsabar ya yi niyyar ya wulakanta ta,shi kan shi ya fi ta kyau bare matar shi da Allah ya bawa baiwar kyau,mtws ta ja tsaki,in har wulakanci ne d toh wlh sai dai kar ta san kar,dan ita ba kowa ba ce,ba kuma ta isa a kira ta kowa ba ba za ta zauna a wulkantata ba. NO WAY!
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[7:49pm, 6/5/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
4⃣5⃣
Ganin Khalid ya tafi ba sallama Hajiya ta san ba a yi ta dadi ba,dan haka sai ta nuna kamar ba ta ma san zancen ba. Hakan ya sa Hajjo sakewa,ta ma mance da maganar ta da Khalid. Da ranar da ya kamata su dawo da Neena ya yi su ka ji shiru sai Hajiya ta fara fada,za ta yi kiran Khalid din ta ma sa tatas Hajjo ta ce wlh Hajiya da kin kyale su,ki bar su zuwa sanda zan yi aure ta dawo wajan nawa,tin da da nan din da can duk daya ne,Hajiya ta ce anya kuwa Hajjo? A biye yanda su ke so? Dama fa nufin na su kenan. Hajjo ta ce ba komai Hajiya,mai san na ka ai ya gama ma ka komai,tsakanina da su sai fatan alkhairi. Hajiya ta ce toh madallah. Ta kira wayar Khalid,ya na dagawa ya ce Hajiya yi hakuri,kin ji ni shiru Hauwa ce ba ta jin dadi na ce zan bari zuwa gobe…Hajiya ta ce toh ai abunda ku ke so ne ya faru,Hajjo ta ce ku kyale ta har zuwa auren ta sai ta dawo gurin maman ta. Saukar numfashin shi har sai da ya fito ta bangaran Hajiya,ya ce kai amma ta kyauta,zan fadawa Hauwar,a mana godiya,Hajiya ta kashe waya ta na fadawa Hajjo yanda Khalid ya hau murna. Murmushi kawai ta yi,ikon Allah wani diyoyi ma ta ya tsana,ga wani kuma ko diya macen be samu ba,sai kwalafacin ta wani ya ke,Allah mai yanda ya so.
Ranar lahadi gidan Jabir Hajjo ta wuni,ta na can suna shan hira da Nabeela,ta zama kamar yayar ta,kamar yanda Jabir ya zama yayan ta. Suna zaune a falo sai ga Khalid ya aje Jabir,ya na mitar idan ba zai sake mota ba da ga yau ba zai sake dana shi a tasa motar ba diyar Jabir ta fito da gudu ta ba Baba Anty Hajjo ta siyo min choculate,ai kuwa sai Khalid ya ce ina ta ke Anty Hajjon? Ta ce ta na ciki ai,ta ce sai Baba ya dawo za ta tafi. Be yi niyar tsayawa ba saboda hadari da ya ga ya taso,amma jin haka sai ya faka ya fito,Jabir na fadin shegen maza,yanzun ai ga shi ka fito. Ya na murmushi ya ce my wife to b a gidan ka,dole na shiga. Diyar Jabir ta shiga da gudu ta na Mama ga Baba har da uncle Khalid!
Jin haka gaban Hajjo ya fadi,tini ta nutsu ta ja mayafin ta ta rufe kan ta,Khalid? Ba ta yi niyar sake ganin shi ba,raban ta da shi tin ranar da ya zo ma ta da yashasshan zance,wlh da ta san zai zo da ba ta tsaya jiran Jabir ba….Nabeela ta na fadin yau Khalid a gidan nan,tin dawowar sa ban sa shi a ido ba,gwara ma dai Hauwa da Inna sun zo,babbar diyar Nabeela ta ce mama Neena ake cewa ba Inna ba. Nabeela ta ce aw Inna fa ta koma Neena,duk dariya su ka sa,sallamar Khalid da Jabir da shigowar su lokaci daya ne. Ya na shiga idanun sa su ka isa izuwa inda ta ke,be da buri da ya wuce ya kalle ta ya ga yanda ta ke reactn duk sanda ya san ya idanun sa cikin na ta,gashi d more ya ke ganin ta d more ta ke kara ma sa kyau,ganin ta ya yi cikin riga da wando na pakistan ja,mayafin yane bisa kanta gashi gashin goshin ta yayi lublub abun sha’awa ka yi zatan irin gashin nan ne na gaske. Kamar ta sani sai ta ki kallan ma in da ya ke,ta na murmushi ta ke yiwa Jabir sannu da zuwa,ya na yauwa Sannu my sister,ya na fama da yara da maman su,wata ruke da hannun sa na hagu,wata na dama,wata kafa,ga maman su ruge da jakar sa da ta karba,sauran yaran biye da su su ka shige ciki kowa na nashi surutun, aka bar Hajjo da Khalid a falon. Sai a sannan Hajjo ta daga ido ta kalle shi,ganin yanda hankalin sa gaba daya ya karkata ga inda su Jabir su ka shiga,ta ga yanayin da ya ke ciki,ta tabbata Jabir da yaransa ne su ka bashi sha’awa,rashin ‘ya’ya sam be da dadi,sai ta dan tausaya ma sa,amma na kankanin lokaci saboda ita ta shagala ta na kallan sa,har ya kama ta,sai ji ta yi yace am i dat handsum suger? Ta yi sauri kau da kai cikin jin kunya ta ce sannu da zuwa,ya aiki? Ya murmusa,yan da ya ga ta na kallan na sa ne ya ma sa dadi kwarai,ya ce hamdan.
Jabir ya fito biye da Nabeela,sun hada yara da kayan dadi sun rabu da su a daki. Nan ya zauna tare da Khalid Nabeela ta kawo mu su abunci,Hajjo ta tashi za ta ba su wuri Jabir ya ce ta zauna abun ta,yay ta jan ta da hira,yanda ya ga ta sake da shi ya sosawa Khalid rai,wato shi ne dai ba ta so,ba ta ra’ayi,ko ya sa baki a zancen sai ka ji ta yi shiru,Nabeela ce ma mai kokarin sa shi cikin hirar.
Sanda su ka gama cin abunci Hajjo ta fara shirin tafiya,Khalid ya ce dama dai gida za shi bari su tafi tare. Hajjo ta ce ah ah,ita ba gida za ta ba,Khalid ya ce ko ina za ta ba damu,he is free. Nabeela ta kalli Jabir da alamar tambaya irin wats up wit dem,ya daga kafada ya aje lyk i donno. Jabir ya gyara murya ya ce my sister gwara ya aje ki din,ga hadari kar ruwa ya taba ki. Da ke ta na jin maganar Jabir,ba mu su ta ce tam yaya na. Khalid ya kalle shi tare da fadin toh yayan ta da fatan xa a gyara ko a canza mota,Madam ki dena hawa motan sai ya sake wata. Nabeela ta sa dariya,Jabir da Hajjo kuwa ba wanda ya dara,sai ma Jabir da ke fadin na ki na canza din,ta dena hawa,diyoyi na sa hau. Da haka da haka ayi sallama, ya sanya Hajarar sa gaban mota,su ka dau hanya. Sai shan kam shi ta ke,shi kuwa zuciyar shi tas,ga iska da ke tashi,gari yayi baki,hadari ya hadu sai kugi yake. Ana yayyafi kadan kadan,kamshin ta da ya mamaye motar gami da yanda AC ke ratsa cikin ba karamin nishadi ya kara ma da ba.
Idanun sa kan titi ya ce an gama jan ajin ko da saura? Ba tare da ta kalle shi ba ta ce ban gane ba. Ya ce har yanzu ajin ba a gama jan sa ba? Ar u still nt ready to obey ur hrt? Dan na san deep inside u ki na so ki aure ni,am every woman type,so don’t give dat clumsy excuse dat am ur type! Hajjo ta kalle shi tare da fadin nt every woman,nd mind you am nt in ur dat “every woman” Khalid ya ce big lie! Yayyafi ya karu sosai,ya kara da na sani Suger,ko ya ki ka so ki boye feelns din ki na sani,i can read u lyk a novel! U hav feelns for me,you hav crush on me. Rai bace Hajjo ta ce ka manta diabates ba Suger ba,i hav no feeln or wat so ever for you,so stop mistaking! Shiru ya ma ta,har ta na tunanin ya rasa ta cewa,sai kuma ya kallo ta ta hanyar danna idanun sa cikin na ta,yanayin fitar numfashin ta tini ya dan tsagaita,ya ce wat abt d way u catch ur breath wen i look at u? Ya saki murmushi mischievously tare da mai da idanun sa bisa titi,ya ce let it go Suger,ke ma kin san u lyk me! Rai bace,bakin cikin yanda da ta yi reactn ya sa ta fadin tsayar da motar ka! Fita zan yi! Cike da mamaki ya ce ki fita ki je ina kuma cikin ruwan nan? Ta ce da zama guri daya da kai gwara dukan ruwa,ka tsaya ko na bude na fita a haka. Ganin fuskar ta ba wasa,sai ya sauka gefe ya yi parkn. Ta yunkura za ta bude motar ya danna lock,wai ina zaki? Shin in kin fita ina za ki sami abun hawa cikin ruwan nan. Ta ce ina ruwan ka? Zan fita kuma zan sami abun hawa ba tare da bata lokaci ba,idan kuma ban samu ba zan taka daganan har hotoro GRA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login