Showing 18001 words to 21000 words out of 67328 words

Chapter 7 - Diya Mace Book Complete by khadija sidi .txt

wannan abar da ki ka haifawa kan ki ki bar min gida! Wani irin farin ciki ne ya lullube Hajjo,ji ta yi kamar an cire ma ta kaya,cikin sauri kafin Gatbati ya sake shawara ta tashi ta na fadin kai amma fa na gode Allah ya saka da alkhairi. Ya na huci ya ce idan ma ba’a ki ke min amen,na dai ci moriyar gangan,kar na dawo na same ki a gidan nan wlh! Ya fice tare da banko kofa.
Dan farinciki ta ma rasa da mai za ta fara,Ghana must go din ta ta ja ta shiga zufa komatsenta,sannan ta hade kayan Inna cikin fanteka guda. Ta fito da sauri neman Mairo ta karbi diyar ta. Mairo ba ta nan sai dai Kande. Saki? Kande ta kame baki cikin jimami,Iyalle ta fito jiyo maganar Kanden,ta ce ya na ke jin batun da Allah ba ya so ne? Wa aka sau? Tana fara’a kamar wacce aka yiwa albishir din hajji ta ce ni ce,wlh ni ce dai Garbati ya sau…lahailahaillallhu! Kai Garbati ya isa maras hankali! Ya sauki da danyan jego?? Ba inda za ki….. gwiwowi biyu a kasa Hajjo ta durkusa, ta na magiya ta na tafa hannu,dan Allah dan annabi dan ya rasulillahi Iyalle ki bari na tafi,wallahi na rantse da Allah ya ce ya sau niii…sai ta sa kuka. Iyalle ta ce ah ah dai na kuka,ai sai ki tafi din,za ki tafi,Allah dai ya sa haka shi ne kairi. Hajjo ta tashi ta na goge hawaye ta ce amen,dan Allah ina Mairo ta kawo Inna sauri na ke wlh,ai yanzu za ta dawo,Iyalle ta ba ta amsa,makota na aike ta,jin sallamar Mairo ta ce mata ga ta nan ma. Cikin sauri tace Mairo sinto min ita tafiya zan yi,ta sinto ta tana tambayar lfy? Ina Hajjo za ta? Ita dai ta yi ciki da diyar ta ta bar Kande na mata baya ni.
Sai ga Hajjo ta fito goye da Inna,fantekar kayan Inna bisa kanta,ga Ghana must go a hannu,ta durkusa gaban Iyalle ta ce toh Iyalle a iya zaman mu idan na bata mi ki ki yafe ni,sai kuma Allah ya sada mu da alkhairin sa. Iyalle ta tada ita ta na fadin ni ce da neman yafiya Hajjo,a yayyafe mu. Hajjo tace la ba komai wlh dama bu ku bata min ba,Allah ya yafe ma na gaba daya. Gaba daya jikin su yayi sanyi,Mairo har da kuka,ita ko Hajjo yau ta ke sallah,da haka da haka su ka yi sallama Hajjo ta kama hanyar ta.
Rashin Inna ya sa Hajjo maimakon ta je gidan su sai ta tafi gidan Indo,dan ko ta je gidan ba dadi za ta ji ba,sai ma kyara da tsangwama daga wajan Baba. A dakin girki ta tadda Indo,ganin ta da kaya niki niki ta kama ta sauke ma ta fantekar ta na fadin lfy kuwa uwar Inna? Hajjo ta na dariya ta ce Garbati dai ya sau ni! Kai kai kai amma ba dan saki abunda Allah ba ya so bane da na yi guda,kai amma na mi ki farin ciki,mu je daga ki fada min garin yaya. Ta dau fantekar su ka shige dakin Indo.
Ko da Indo ta ji dalilin sakin sai cewa ta yi kan sa yayiwa ai,can da su gada. Ki kwantar da hankalin ki nan gida na za ki zauna,sai na gyara mi ki daki daya,idan Sani ya dawo sai mu je mu fadawa Baba. Dan murna Hajjo ta rungume Indo,ta ce na gode Allah ya saka da alkhairi,yan uwa dadi gare shi. Indo ta ce haba Hajjo ai yiwa kai ne. Ya Inna? Ta daina kukan dare? Hajjo ta sinto Inna da ta ke ta famar baccin ta,ta mikawa Indo ta ce gata ba ta daina ba,ita ta yi baccin ta da rana,da dare yayi ta hana ni sai dai a tashi a yi hira. Indo ta dara ta na kallan Inna,ta ce ayya Allah sarki ina ruwan Inna,Allah dai ya raya ma na ita,Hajjon ta ce amen amen.
Da Sani ya dawo ya ji batun Hajjo,ya goyi bayan zaman ta a gida,ya kuma ce maza su je su fadawa Baba kar su yi laifi,dan haka Hajjo da Indo su ka kwashi kafa su ka je gun Baba. Be mu su tarbar mutunci ba,sai ma fadan da ya hau su da shi,wai ai ya ji batun sakin,me zai mu su yanzu da su ka zo su ka sa shi gaba? Tin wuri Hajjo ta je ta nemi afuwan mijin ta ya dawo da ita dan shi ba zai iya hidima da ita ba ya yi da wannan diyar ta ta ba,ka sayar da akuya ta dawo ta na cinyema dusa.
Kai a kasa Indo ta ce dama Baba na zo ne neman alfarmar a bar Hajjo ta zauna gida na….yoo da shi ne ba ki yi bayani tin wuri ba? Baba ya katseta,ai ba sai ma kin tambaya ba,tai ta zama har mahadi ya bayyana,ni menene nawa a cikin tin da aljihuna ya kubuta! Jiki a sanyaye su ka ma sa sallama.
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[7:20pm, 5/18/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
2⃣6⃣
ya ce a sauka lfy,su ka fita,sam ba soyayyar Baba cikin ran Hajjo,bare yau ma da ya gama fita daga ranta. A soro suka gamu da Mudi,shi ya raka su hanya,Indo ta fada ma sa halin da ake ciki. Yayi bakin ciki da halayyar da Baba ke nunawa diyoyin sa mata,yay ta bawa Hajjo baki har su ka yi sallama.
Gidan Indon Hajjo ta yi zamanta,har ta gama Idda Garbati be zo biko ba bare kuma batun kome,diyar sa kuma ta yi wata hudu,amma tsinke be taba siya mata ba. Da yammacin ranar lahadi Hajjo zaune cikin dakin da Indo ta ba ta,ta na yiwa Inna wasa,Indo ta shigo ta na umm su Hajjo ma su diya! Ta na dariya ta aje Inna ta ce wlh ki ga fa har zama ta ke….Inna ta yi luuuu za ta fadi Hajjo ta ruko ta da sauri ta na dariya. Indo ta ce Auta hankali! Maza ki karasa ma na yar Innar ta mu mu yi biyu babu. Duka dariya su ke. Duk da ba wani abu na daban ta ke ci ba,kwanciyar hankali ya sa ta canza ta yi kyau,gashi haihuwar da ta yi ya sa jikin ta yayi kyau,ta yi diri mai kyan gaske.
Indo ta ce Sani ne ke kiran ki. Hajjo ta ce aw ya dawo? Ai ban sani ba da na ma sa barka da sauka,gani nan zuwa. Indo ta ce kar fa ki tsaya sirniki,So ya ke ya fita, Hajjo ta ce Indo ho toh mu je gaba daya,ta biyo ta dauke da Inna.
A tsakar gida kan tabarma su ka tadda shi,hannun sa ruke da tasbaha. Hajjo ta zauna daga farkon tabarma yayinda ita kuma Indo ta zauna sosai bisa tabarma. Sannu da zuwa Babn Aisha,sunan da ta ke kiran sa kenan,da ke diyar Indo ta fari sunan ta Aisha,sunan Indon ta ci. Cikin sakin fuska ya amsa ma ta,su ka gaisa sosai. Ya kara da Hajjo za ki iya aikatau a cikin birnin kano? Ta na murna,abun nema ya samu kila za ta bar kumurya ko ta rage wasu bakin ciki da su ka sami wajan zama cikin zuciyar ta,ta ce wlh babu aikatau din da bazan iya ba. Shi kan shi Sani sai da ta bashi dariya bare kuma Indo,tace ka ji azarbabi,kya dai yi shiru ki ji karashen batun ko? Hajjo ta ce tam! Sani ya cigaba da fadin gidan da na ke musu direbanci ne,mai gidan ya jima da rasuwa,kusan shekara goma kenan ma muna tare,duk ‘ya’yan Hajiyar Maza ne su uku,biyu magidanta ne,sai kuma autan ta dan saurayi nan da wata hudu shima zai yi aure,kuma ba a kasar zai zauna ba shi ya sa ma su ka damu a samo ma ta yar aiki da za ta na debe ma ta kewa duk da de ba wani aiki ba ne a gidan ba yara. Baki washe Hajjo ta ce yasin zan yi! Ah ah toh ya za a yi da Inna? Tambayar Indon da ta katsewa Hajjo farin cikin ta kenan kafin Sani kuma ya dawo ma ta da farin cikin ta da ta jin amsar sa na dama sai da ya fadawa Hajiyar,ta ce ba komai indai na yaba da hankalin ta,na kawo ta sai ta ji nawa Hajjon ta ke so a matsayin albashin ta…ko nawa ne wlh ni zan yi! Caraf Hajjo ta amshe. Indo dai ba son tafiyar Hajjon ta ke ba,sai ta kara da za ta na biyo ka ne kullum kuna tafiya tare kuma? Sani ya ce ah ah su wacce za ta na kwana su ke so…ai ba komai sai na kwanan ma,yaushe za mu tafi? Ta na magana ne yayinda ta yunkura ta tashi,Sani ya ce duk sanda ki.ka shirya. Toh bari na fara shiri yanzu sai mu tafi gobe,ta tashi da sauri ta shige ciki.
Indo ta ce toh fa,ka ga rawan jiki,toh Allah dai ya fisshe mu alkhairi. Sani ya tashi ya na fadin ameen,kar ki damu Indo,mutane ne ma su kirki,ba za ta sami matsala da su ba. Indo ta ce Allah ya sa,Sani ya amsa da ameen,sai na dawo,ta ce adawo lfy.
Tin asubar fari Hajjo ta shirya tsaf ta shirya diyar ta,dan dakar ta iya bacci ma saboda zumudi da Allah Allah gari ya waye,wai Hajjo ce za ta shiga birnin kano,wayyo dadi abunda ta ke fadi cikin ran ta kenan. Da gari yayi haske sosai Indo ta kama mata karin kumallo dan Hajjo ta gagara fita ta dauka da kanta,sai da Indo ta tsaya kanta sannan ta ci,ita kawai a tafi a tafi. Indo ta bata kayan shafa,har da turaren shafawa su “aba rai dadi” da “danduwala” ta mata fada sosai,ta kula da kanta da kuma Inna,birnin kano girma gare shi,shi ake kira timbin giwa ko da me ka zo an fika,gwara ta bi hankali. Toh kawai ta ke cewa dan ba ma ta jin ta,ita dai kawai a tafi. Har mota Indo da ‘ya’yan ta su ka rako ta,suna ta daga ma ta hannu,baki washe ita ma ta ke daga musu,ta takure gidan baya Inna zaune bisa cinyarta…. su ka nufi birnin dabo,gari mai mata mai mota,gari ba kano ba dajin Allah!
☁☁🌞 ☁ ☁
☁ ✈ ☁ 🚁 ☁ ☁ ☁
🏬🏨🏫🏢🏤🏥🏦🏪
🌲 / l🚍 \🌳👭
🌳/ 🚘 l 🏃 \🌴
🌴/ l 🚔 \🌲
🌲/ 🚖 l \🌳
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[7
[16/10 21:46] .: 25, 9:38 AM] Salmah Ateeku: [2:41pm, 5/27/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
2⃣7⃣
Ko da su ka shiga garin baki Hajjo ta saki,idanu bude kamar za su fado ta ke kalle kalle,garin acike ya ke taf da jama’a,kowa da irin sa da irin salon shigar sa,ga motoci ga hayaniya,ga gidajen sama,kai kano sai ka ce duniyar ce gaba daya? Tambayar da take maimatawa cikin ranta kenan. Ita ko Inna tinda ta ji iskar mota ta noke jikin maman ta sai bacci.
Hotoro G.R.A sunan unguwar da Sani ya shiga. A gaban Wani katan gida,mai dauke da ado da bishiyoyi na fure ya tsaya ya na danna hon,da sauri maigadin gidan ya bude gate,Sani ya karasa ciki. Dan al’ajabin kyauwun gidan ihu ne kawai Hajjo ba ta sa ba,tin da ta ke ba ta taba gani gida irin wannan ba,toh sai dai a kalandar da su Mudi ke kawo gida daga boko,wai amma yau ga ta ita ce cikin gidan. Da wannan tunani ta ji Sani ya tsaya ya na fadin Hajjo ga mu a kano,a sa takalmi a sauko ko? Cikin rawar jiki ta fara jijjiga Inna,ke Inna tashi ki ga aljannar duniya! Inna ta motsa ba tare da ta farka ba,hannun ta kamkame jikin Hajjo. Sani ya fito ya bude mata kofar yayin da ta sauko ta na mitar nauyin baccin Inna kamar na uban ta Garbati! Dariya Sani ya ke ma ta,ya taimaka ya fito ma ta da kayan ta da na Inna,ta saba Innar a baya ta sa zani ta daure. Sani a gaba hannu dauke da ghana must go din Hajjo,ita kuma biye da shi,ta daura fantekar kayan Inna bisa kanta su ka shige cikin gidan,tana mamakin yanda Sani ya san kan gidan dan lunguna da su ke ta kutsawa dan ta san kafin ta gane sai fa an kwala duk da Inna ta ce ta na da kan gane waje.
Wani bangare su ka shiga,sai ga su tsaye cikin falo mai dauke da bangare biyu, Sani ya fara sallama,dan kallan kauye Hajjo har da tuntube da wani flower pot da ke aje gefe guda. Hankali dai!wata murya mai tarin nutsuwa da sanyi ta daki kunnen Hajjo,tini idanun Hajjo su ka shiga neman mai murya.
Babban falo ne mai dauke da bangare biyu wanda gilashi fari ya raba,na fari an ma sa ado da fararen kujeru masu kyau da kayatarwa,ga lallausar carpet da ke shimfide kalar ganye a kasan kujerun,sai kuma dayan bangaran falon da ke dauke da wasu irin kujeru kanana sosai ga kuma wasu kanana tintin da ke watse amma cikin tsari,idan kana zaune cikin bangaran za ka iya ganin abun da ke faruwa a cikin dayan bangaran ba tare da na wancan bangaran ya lura ba. Dan haka har Hajjo ta gama kalle kallen ta ba ta ga kowa ba,sai da su ka fito.
Dattijuwa ce wayayyiya fara sol,kakkaura mai kyauwun gaske,idanun ta sanye da farin gilashi ta fito,biye da ita danta ne mai kimanin shekara talatin aduniya,kamar shi daya da ita,hatta yanayin tsayin su daya,ba dogo ba ba kuma gajere ba,shima ya na da dan jiki,da ka gan shi ka ga magidanci. Dattijuwa ta na fara’a ta ce wa’alaikumul salam Malam Sani,yau ka so ka makara,ta bi Hajjo da kallo,gaban Hajjo ya fadi,ba shakka muryar ta ce wanda ta ji,kwarjini ta ma ta matuka,bare kuma danta da ke ma ta kallon kurilla.
Sani ya durkusa yanda ya saba ya gaishe da Dattijuwar,bayan sun gama gaisawa su ka gaisa da dan na ta wanda sani ya kira da suna Jabir. Ganin haka Hajjo ma ta gaida su,sai a sannan Sani ke ma Hajiya bayanin dalilin makarar ta sa,ya tsaya tahowa da Hajjo ne….
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[2:54pm, 5/27/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
2⃣8⃣
Dattijuwar ta ce ah ku shigo daga ciki mana,abokiyar debe min kewar kenan? Jabir ya ce ban tari numfashin ka ba Mallam sani,amma wannan ai ta yi yarinta da yawa,wacce fa za ta taya Hajiya aiki fa aka ce,wannan ko ai ba ta wuce a yi renan ta ba itama! Kuma wai goyo na ke gani a bayan ta..Gaban Hajjo ya fadi,Malam Sani ya budi baki zai yi magana Hajiya ta katse shi da fadin kyale shi Mallam Sani,karaso ciki,ai na ce da ku zan iya zama na ni kadai na ku ka takura sai an samo min kuma ka fara sara tin kan su zauna,shigo abun ki yarinya. Hajiya ta wuce ta zauna kan doguwar kujera shi ma Jabir din kasa ya samu gaban ta ya zauna. Sani ya aje Ghana must go din Hajjo daga gefe,shi ma ya sami matsuguni,yayin da ita kuma Hajjo kici kici ta sauke fantekar da ke kanta kasa,sai kuwa Inna ta tsala kuka alalle Hajjo ba za ta zauna ba,itama Hajjo ji ta yi kamar ta tsala na ta kukan ganin yanda da ga Hajiyar har Jabir su ka zuba ma ta ido,ta ce wayyo ni Inna dan Allah ki taimaka min ki yi shiru! Jin haka sai Hajiya ta dara,ta ce sinto ta mana,ki ba ta ruwa ta sha kin san akwai zafi kila ma yunwa ta ke ji ki ba ta nono! Baki bude Jabir ya ke duban ta dan har yanzu be gama gasgata zatan shi na Inna diyar Hajjo ba ce,sai da ya ga ta sinto ta da rawar,ta sanya ta cikin mayafi ta fara ba ta nono. Ya ce kai jama’a wlh Hajiya diyar ta ce kuwa. Hajiyar dariya ta yi ta ce toh da diyar ka ce? Ta ce shekarar ki nawa? Ta tambayi Hajjo,Hajjo ta ce shekarata goma sha uku…..Jabir ya ce tashin hankali! Hajiya kuwa ko a jikin ta,ta ce Allah sarki,ni ma ina da shekara sha uku na haifi diya ta ta fari sai dai ba ta zauna ba,bayan shekara daya kuma na haifi Sabir yayan Jabir…ita dai Hajjo uhum kawai ta ke cewa ta na yake. Hajiya ta ce da Sani ai ba matsala Hajjon ta ma ta. Jabir ya ce Hajiya yarinya ce ga goyo,maimakon ta taya ki aiki ai sai dai ma ta saki,mai wannan yarinyar za ta iya fisabilillahi?
Ta na gani za a ma ta biyu babu ba ta san sanda ta ce na iya ko wani aiki yasin! Ko aikin gidan su Garbati ma kaf ni na ke yi,Baban Aisha shi ne sheda ta ko? Ta dubi Sani idanun ta cike da magiyar ya sa baki. Sani ya ce kwarai kuwa,ai ba da ganan ba idan dai aiki ne Hajjo ba ta da san jiki…Hajiya ta ce bare ma ba wani aiki a gidan,ni ce fa dal sai Auta,shi ma din be fiya zama ba bare ma auren sa ya matso,to indai zan zauna da yar aiki toh Jabir da wannan diyar zan zauna,ta yi min ni dama dan ni ake yi ko? Jabir ya gyada kai tin da Hajiya ta dage,toh lalle hakan za a yi. Ya ce toh zan fadawa Sabir an samu,nawa za a ke biyan ta? Hajiya ta dubi Hajjo ta ce yarinya ya sunan ki ne? Hajjo ta ce Hajara,amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login