Showing 39001 words to 42000 words out of 67328 words
Chapter 14 - Diya Mace Book Complete by khadija sidi .txt
kamar zugo shi ake ma,sam ya rage ba su kulawar sa,ba ta san shikam hankalinsa na kan Hajjo ba,be da buri da ya wuce ta zama ta shi,so ya ke Neena ta zama ta shi,haka kuma ya sami ‘ya’yan sa na cikin sa. Amma lokacin fadawa Hauwa be yi ba,saboda haka sai ya ta bata kowani excuse da ya zo bakin sa.
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[7/25, 5:18 PM] Salmah Ateeku: [11:29pm, 6/5/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
4⃣8⃣
Kwanan Baba biyu a AKTH ya fara gane mutane,Diabetes da hypertention ne su ka fara damkar sa. Bayan warwarewar sa be da magana da ya wuce na Hajjo,bini bini ya ce ko yaushe zan sa diya ta Hajjo a ido? Diya ta Hajjo kaza,diya ta Hajjo kaza,musammam da ya san waye Khalid,hakan ya na sosawa Khalid rai,ya kasa gane shin wai menene tsakanan diyar nan da mahaifinta ta har ta kasa zuwa ta duba shi. Sati daya yayi a AKTH ya sami sauki sosai,ya dage lalle shi fa a sallame shi,ya gaji da asibitin. Da aka duba aka ga zai iya tafiya din sai aka sallame shi din,ya na ta ciwa Khalid albarka. Mudi da yayi jinyar sa tare da taimakon Indo su ka hada na su ya na su su ka komo gida.
Satin Hajjo biyu a kumurya,Sani ta ke biyowa,wani lokacin kuma ta hau motar haya,musammam idan za ta dawo. Sam zirga zirgar ba dadi dan haka kullum cikin zargin Khalid ta ke akan takurawa rayuwar ta. Tin da ta koma Kumurya be taba waiwayan ta ba bare ya kira ta waya,duk da tana kokarin kau da tunanin daga ran ta sai da ya dan dame ta,ta na dai yawan waya da Hajiya. Zancen Inna kuwa kullum ya na ranta,ta na so ta je ta ganta,amma ta na gudun abun da zai biyo bayan haka,dan haka ta yanke hukuncin yin aure da Suraj ya dawo diyar ta ta dawo kusa da ita.
Allah ya dawo da Suraj,ya na Allah Allah ya ga Hajjon sa,ta ke fada ma sa ta na kumurya,ya ce garin mosoya ba ya nisa,washagarin ranar da ya dawo ya kama weekend,ya bakunci Kumurya. Duk yanda Hajjo ta so ta sawa ranta murna da doki ganin Suraj sai da ya gagara,amma ta yi kokarin ma sa kwaliyya,ta yi kyau matuka dan tin zaman su a soran gidan Indo Suraj ke yabata,ta ma sa kyau kwarai kamar ya dauke ta ya tafi da ita inji shi. Ita ko Hajjo sai kokarin ma sa hira ta ke,da ta so ma sa maganar rayuwar ta na baya,sai wani abu cikin ranta ya hana,har ta yanke shawarar bari sai ya sake dawowa wani karan ta ma sa. Zaman ta da Suraj lami sam ba wani chemistry,har so ta ke su hada ido da shi ko za ta ji yanda ta ke ji ta hada ido da Khalid,amma ina d combition din sam be hau ba. Zai tafi ta rakoshi bakin mota,ya dauko tsaraba jaka guda ya ba ta,ta karba ta na waiwaiwai wannan duk nawa ne? Ko lefe ka fara ragewa ne? Ya na dariya ya ce ai kin fi karfin wannan ma kin sani,lefe kuma ai sai kin ture gimbiya. Duka su ka yi dariya. Tsayuwar wata tsalleliyar mota da ta yi biyun ta Suraj ce ta ja hankalin su duka,ita dai Hajjo ba ta taba sanin mai mota irin wannan ba,so sai ba ta kawo wajan ta ma aka zo ba.
Tin da ya shigo lungun gidan ya hangi Hajjo da wani ran sa ya baci. Ya zo duba Baba ne,ko gidan be iya karasawa ba ya biyo ya fara ganin Suger da yayi sati biyu be sa ta a ido ba.Ya dubi Neena da ke kwance a baya ta na sharar baccin ta,ya murmusa yayin da ya juya ya gyara ma ta kwanciya,ba shakka wannan karan da ita zai yi garkuwa ya harba wannan dan gajeran saurayin na Suger. Fitowa yayi cikin isa da shan kamshi,ganin sa gaban Hajjo ya fadi,shikenan ya biyo ta,Allah kadai ya san da me ya zo kuma yau. Shi kan shi Suraj sai da Khalid ya ma sa kwarjini saboda yanayin sa da cika ta kamala da Allah ya ma sa. Shekarunsa 37 amma yafi kama da dan 30 saboda baiwa da Allah ya ma sa sam baya tsufa. Sanye cikin farar shadda dinkin tazarce,abun ku da dogo sai ta ma sa kyau. Wajan na su ya karaso ya na kokarin sanya idanun sa cikin na Hajjo ga wani mischievous smile din nan da ya saba ma ta duk san da ya shiryo wata shiryayyiyar. Da sauri Hajjo ta yi kasa da na ta ido,hannu ya ba shi,gami da yin sallama. Suraj ya karba ya amsa da fara’ar sa. Ya kalli Hajjo ya ce Suger ya dai? Is dat a way to great d man you so much miss? Da sauri ta daga ido ta kalle shi,ya kashe ma ta ido daya,duk a kan idan Suraj,ya ce ban gane ba pls,Hajjo who is dis man? Hajjo ta ma rasa me za ta ce,kawai ta yanke hukuncin fadan gaskiya,ta ce shi ne autan Hajiya….kuma uban diyar ta Ameena!Khalid Ya ba da na shi gudun mawar. Ihu ne kawai Hajjo ba ta kurma ba,dan cikin ranta ihun ta ke,maganar Anty Hussaina ke ma ta ihu a kunne na “kar ki bari ya ji a bakin wani…”wanin ma kuma ya kasance Khalid shikenan yau Khalid zai cuce ta! Hajjo ta ce wasa ya ke,as in kar ka saurare shi,ina tuni zuciyar Suraj ta motsa,ya ce da Khalid i beg ur pardon! Wata diya ka ke magana akai? Khalid ya ce aw ba ta fada ma ba? Who exactly ar you? Hajjo ta ce Suraj pls kar ka saurare shi,ka bari ma yi maganar daga baya. Suraj ya ma ta banza,ya ce da Khalid sunana Doctor Suraj,wanda zai auri Hajjo nan ba da dadewa ba. Khalid ya murmusa tare da fadin nan ba da dadewa ba amma u don’t knw abt us? Ba ta fada ma ba? Me haka ya ke nufi Suger? Idanun Hajjo na spark ta ce Khalid don’t temper wit my future,i wil nt forgive you for dat! Worry not Suger,kawai ina taimako ne wajan fadawa saurayin ki abunda be sani ba,am aure be san da diyar mu ba! Rai bace da batun Khalid,Suraj ya ce pls ka fito baro baro ka fada min abunda ka ke so ka fada. Khalid ya na murmushi,ya nuna motar sa ya ce je ka duba bayan motar can,amma ka tabbatar diya ta ba ta tashi ba. Suraj ya juyo ya kalli Hajjo,ta girgiz kai ta ce ba gaskiya ba ne,kar ka je…ya juya ya nufi motar,ko da ya leka sai ga diya kwance ta na ta baccin ta,ya bude motar ya kalli fuskar Neena sosai,tamkar Hajjo ya ke kallo,dan dai wannan fara ce kuma yarinya ce shakaf da sai ya ce yar biyun Hajjo ce! Abun da ya zo ran sa shi ne kanwar Hajjo ce,duk da dai Hajjo ta fada ma sa ita ce auta,Allah kasa kanwarta ce addu’ar da yayi a fili kenan,Hajjo is too young to b her mother. Ji ya yi kamar ya tada Neena,sai kuma ya fasa ya dawo wajan su Hajjon da tuni idanun ta ya kawo ruwa. Hajjo ta ce let me explain plsssss Suraj. Khalid na gefe murmushi fal fuskar shi,yau dai kam tarkon da ya sa ta kam katan zaki ba kurciya ba. Suraj ya ce Hajjo,tambaya daya zan mi ki,ki kuma gaggauta fada min gaskiya,aaa ko ah ah,waccen diyar da ke kama da ke sak,diyar ki ce? Ya Allah ka sa ta ce ah ah! Kallan Hajjo ya ke kamar rayuwar sa depend on her answer. Hajjo ta yi kasa da ido,ji ta ke kamar kasa ya bude ta shige ciki,abun kadan da ya kamata ta fada ma sa tuntuni ya zama babba. Suraj ya ce ke na ke sauraro Hajjo! Murya a kasa ta ce eh Ameena diya ta ce…
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[11:55pm, 6/5/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
4⃣9⃣
Juyawa ya yi ba tare da sake furta komai ba ya shige motar sa. Hajjo na fadin dan Allah ka tsaya na ma ka bayani Suraj! Tuni ya figi motar sa ya tafi. Cikin tsana Hajjo ta ke kallan Khalid,ta ce dan me ya sa haka? Me na tsare ma? Me na taba ma ka da na cancanci wannan hukunci daga gare ka Khalid? Ya ce marry me,jst marry me suger! Ni na san da ‘ya’ya na cikin ki,kuma bazan bari ba sai inda karfi na ya kare,sai kin haifa min su Suger….kallon sa ta yi irin kallan da ake yiwa wanda su ka sami tabin hankali,ta ce Allah ta baka lfy! ta juya ta shige gida a fusace,ta na ji ya na kwalla ma ta kira ta ma sa banza,ta na shiga gida ta karasa daki da gudu sai ta fashe da kuka. Indo ta shigo da sauri ta na fadin lfy! Lfy Hajjo! Me ya faru! Cikin kuka Hajjo ta ce Indo Allah ya raba ni da Gatbati tin da dadewa amma yanzu ya hada ni da Khalid! Ya matsa min,ya isheni! Na tsane shi! Na tsane shi fiye da yanda na tsani Garbati tin da ya raba ni da Suraj.Kai gaskiya wannan bawan Allah ya yi lefi,amma zauna bar kukan,zauna ki bani lbry. Ba ta dena kuka ba har ta gama ba wa Indo labari tin daga sanda Khalid ya dawo har zuwa yau da ya raba ta da Suraj,me san ta dan soyayya ba dan ya na so ya aure ta saboda wani bukatar shi na daban kamar Khalid ba. Indo ta ce toh ki yarda ki aure shi mana Hajjo,menene a ciki tin da ya na kaunar diyar ki…bazan aure shi din ba,ni bazan taba auren mutum mai ji da kai da dagawa irin Khalid ba! Gwara ma kar na yi auren kwatata!!! Ba fa so na ya ke ba,kawai dan matar shi ba ta haihuwa zai aure ni,ga machine ta haihuwa ya samu ba! Ya aure ni ya hada ni da matar nan ta sa kamar balarabiya su ji dadin wulakanta ni,duk lalacewar rayuwa ta Indo na fi karfin wulakanci. Cikin tausayawa Indo ta ce yi shiru Hajjo,ki ta addu’a da istikara Allah ya zaba mi ki ma fi alkhairi. Hajjo ta ce babu alkhairi a tare da Khalid…kul Indo ta katse ta,ki dai yi addua na ce,zabin Allah ya shi ne zabi,Allah ya zaba mi ki. Hajjo ta ci gaba da kukan ta.
Tin shigar Hajjo gida Khalid ya ja motar shi, shi ma ya je yayi abunda ya kawo shi,wato gaida Baba,har yau ma sai da ya tambaye shi Hajjo,Khalid ya yi mamakin ta na garin ma amma ba ta zo ta duba shi ba? Halin Hajjo sai ita. Da kyar Neena ta yarda Baba ya ruke hannun ta da ke Khalid tada ita yayi da su ka isa gidan dan Baba ya ga jikar ta sa. Ita ko Neena ce wa ta yi sam ba kakan ta ba ne,ita kakan ta na kano,wato mahaifin Hauwa,da shi ta saba, har cikin ranta tsoro Baba ya ke ba ta.Baba ya ce Allah sarki mai sunan ki mutuniyar kirki,ba dai ta cutar ba sai da a cuce ta,Allah ya ji kanta da rahama. Khalid ya amsa da amen. Neena ce ta matsa su tafi,dan haka ba dadewa su ka juyo abun su,zuciyatt sa cike da tunanin ko wani Hali Hajjo ta ke?
Bayan ta sha kuka ta koshi ne ta yi kokarin kiran wayar Suraj,amma a kashe. Ta kira ta Ayush ta ba ta lbryn abunda ke faruwa,ta ce haba shi yasa Ya Suraj ke nema na,ya zo da magariba ba na nan,kar ki damu zan ma sa bayani inshaAllahu zai gane. Hajjo ta ce toh Allah ya sa. Su ka yi sallama. Sai a sannan ta bude jakar ta,Jewellery ne ma su kyan gaske Indian design,da kuma turare iri iri,sai kuma takalma da pakistans na gani na fada. Hajjo ta yi ajiyar zuciya ta re da fadin Allah sarki Suraj,Allah ya sa ka gane,amen.
Suraj kuwa tin da ya je gidan su Ayus ba ta nan ya koma gida ya kasa zama,abun da ke daure ma sa kai shi ne ta yaya wannan za ta zama diyar Hajjo? Ai wannan ta yi rabin shekarun Hajjo,ta yi yarinta a ce ta na da diya kamar wannan,dama ba budurwa ba ce? Ta taba aure? Toh ma ta ce Khalid autan Hajiya ne,shin ta yaya ya zama mahaifin diyar Hajjo?me ya sa ba ta taba sanar da shi ba?da wannan tambayoyi ya sake komawa gidan su Ayush cikin daren,dan ba zai iya kwana ba su yi maganar ba. Ya ko ci sa’a ta na nan. Ta ji dadin ganin sa duk da ba dan ita ya zo ba,dan case din sa da Hajjon sa ne. Bayan zaman su yay ta jero ma ta tambayoyi,har dai ta banbance ma sa zare da abawa,ta bashi lbryn yanda aka yi Hajjo ta ke da diya kamar Neena,kuma Khalid ya kira kansa ne mahaifin Neena ba dan komai ba sai dan shi ne ke rukon Neena,kuma ya ke san auran Hajjo.
Jikin sa ya yi sanyi ya ce amfanin bayani kenan in a relationshp,sam boye boye be da dadi,da ta fada min tuntuni da duk haka be faru ba,wai dan ta taba aure ba ya na nufin zan dai na san ta ba,I love her nd i wil olways love her. Ayush ta gyada kai ta na murmushi,duk da kuwa maganar ta dan taba zuciyar ta,ina ma ta ji wannan maganar da ga bakin wanda ta ke so,kuma ace da ita ya ke,da burin rayuwar ta ya cika. Bayan yayiwa yan gida sallama Ayush ta raka sa har mota,ya ce gobe zai koma ya sami Hajjo,amma kar ta fada ma ta,zai ma ta suprise visit ne. Ta na murmushi ta ce ka gaishe ta,su ka yi sallama ya tafi ta dawo gida zuciyar ta fal da san maso wani.
Washagari Hajjo na asibiti Hajiya ta yi kiran wayar ta,ta ce idan ta tashi ta biyo gidan ta za su gidan kanwar Hajiya su ga wasu kayan kitchen da kanwar ta ta ta shigo da su. Da kamar ta ce da Hajiyar ba za ta sami damar zuwa ba,sai kuma ta guji bacin ran Hajiyar,dan ita ta tsaya tsayin daka Hajjo ta fara siyan kayan aure tin da ta fara daukan albashin ta,ta kuma sa Hajjo a dashi na daidai yanda Hajjon za ta iya. Duk wata shawara ita take bawa Hajjo ita take sa ta a hanya. ta amsa ma ta da toh,zan zo Hajiya. Bayan aje wayar ta ce ya Allah kar ka sa na hadu da wannan dan anacen har na je na tafi.
Kayan kitchen din ko sun mata,dan har kwasar wasu ta yi,saboda ita ta gida ce aka ma ta ragi. Bayan dawowar su ta aje su dakin da ta ke taro. Ta ce Hajiya bara na kama hanyar na tafi kar dare ya yi. Hajiya ta ce jira ma na Sani ya dawo sai ku tafi tare. Hajjo ta ce ay na zaci ya tafi,bari na jira shi. Nan su ka zauna ita da Hajiya suna tadi,Hajjo na cin abunci. Har ta gama shiru shiru Sani be dawo ba. Sai Sallaman Khalid su ka ji,Shikenan gashi abun da na ke gudu ya zo! Hajjo ta fada cikin ranta. Ba kunya kamar babu lefin da yayiwa Hajjo ya raba ta kusa da ita ya zauna kusa da Hajiyar sa,bayan sun gaisa Hajjo ta daure ta gaishe shi,ya amsa,tare da fadin yar kumurya ta dawo kenan. Hajiya ta ce ba dawowa ta yi ba,Sani ta ke jira ya dawo su tafi,kuma na ji ma wayar sa a kashe. Khalid ya ce wani Sani kuma da ya tafi tin bayan la’asar? Hajiya ta ce haba dan Allah? Ya ce wlh,sai ma da ya biyo ta gida na da ke na neme sa. Hajiya ta ce Allah sarki na tsaida Hajjo,rashin sani. Kwayar idanun sa na rawa ya ke kallan Hajjo da tuni ta ji komai ya gama jagole ma ta,ga shi akwai wani file da za ta yi submitn gobe goben nan,kuma ta baro sa a gidan Indo. fuskar sa cike da murmushin mugunta ya ce Hajiya kar ki damu,dan dai nan da Kumurya ai sai na kai Hajjon ta ki. Da sauri ta daga ido ta kalle shi,ya kashe ma ta ido,ta ce Hajiya wlh na hakura zan kwana! Hajiya ta ce wa zai kawo mi ki file din da za ki yi submitn goben? Ta ce na kira Baban Aysha ya taho min da shi. Khalida ya sa hannu a aljihu ya fito da waya ya ce ga wayar Sani tare da ni,ya ji dadin girkin Hauwa ya manta kan kujera,abun da ya kawo ni gidan nam kenan na kawo ma sa na kuma mi ki sallama Hajiya,gome zan leka Abuja.
Hajjo ta girgiza kai,ita dai kwanannan ba ta da sa’a kamar ta buge bakar karya da bakar mota. Hajiya ta ce Hajjo ba komai dare bai yi ba ai,ba a dade da kiran sallah ba,idan kun idda sallar magaribar sai a kai ki. Toh Hajiya,amsar ta kenan,ta tashi ta shige ciki,ta bar Hajiya na yiwa autan ta godiya na kai Hajjo da zai yi,fadi ya ke Hajiya ai yiwa kai ne… ni ma fa haka na gani,yiwa kai indeed.
Tin da su ka dau hanya ba wanda ya yiwa wani magana,sai da su kusa isa Kumurya Khalid ya ce Suger? Ta ma sa banza,ya kara da Hajara? Ta daga ido ta kalle shi,ya murmusa ya ce ashe idanun ki biyu,na zaci kin yi bacci. Ta ce dama za ka yi shiru mu karasa kawai. Ai na mi ki shiru ne kar in zo na mi ki magana na kunna ki ki ce na tsaya ki sauka a dajin,amma tin da mun kusa shiga gari,i can open up! Ta ma sa shiru. Ya ce fushi ki ke wai dan na raba ki da wannan gajeran saurayin na ki? A hasale ta ce Suraj ba gajere ba ne! Khalid ya murmusa sannan ya ce