Showing 24001 words to 27000 words out of 67328 words

Chapter 9 - Diya Mace Book Complete by khadija sidi .txt

Indo ta amsa ta fito da sauri,a tsakar gida ta ci karo da Baba,ta durkusa da niyar gaishe shi,amma sai ya fara sirfo ma ta zagi,uwar ki! Uwar ki na ce Indo! Ina nan da rai na za ku tozarta ni? Indo ta ce me ya faru Baba? Ya ce ina Hajjo? Indo ta dan tsorata,tin tafiyar Hajjo be taba waiwayar ta ba sai yanzu,ko ya ji wani abu ne? Ba da ke na ke magana ba? Ya daka ma ta tsawa! Ta na kame kame tace Hajjo Baba ai ta na nan. Ungo nan! Ya ma ta dakuwa,ai na san komai, na ji lbryn kin turata birni,kin tura ta yo karuwanci ko? Auzubillahi minallahshaidanirrajim! Indo ta ce karuwanci fa Baba. Baki na kumfa ya ce ke ce shedaniyar ke da ki ka tura ta karuwanci,eh in ba haka ba waye na ku a kano?,dan haka na riga na sallama ta,sai dai kuma ki fada ma ta ta dawowa tsohon mijin ta Garbati da diyar sa! Dan jiya uban sa ya zo min da maganar,dan haka sai ki fadawa asararriya! Na ba ta daga yau zuwa rana eh na yau ta kawo diyar nan! Ya juya fuuuuu ya fice ya bar Indo cike da damuwu,ta ma kasa tashi. Jim kadan Hajjo ta fito goye da Inna ga jakarta makale,Indo ta tashi da sauri ta na tambayar yaya na gan ki haka? Rai bace Hajjo ta ce Kumurya zan bari ni da diya ta,ba kuma zan sake dawowa,dan wlh ko Baba be isa ya amshi diyar nan daga hannu na ba,bare Garbati! Indo ta ce ba a yi haka ba,dama ba za ki ba su ba,amma….ina fuuu Hajjo ta fice ta na sinbatu kamar wacce ta zare,har waje Indo ta bi ta ta na kiranta,amma ta ma ta banza,gani ta ke da ta tsaya za a kwace Inna.
Sai da ta ganta a Kano ta fara nutsuwa,ta na isa gidan Hajiya ta ce da Hajiya ta fadawa Hauwa za su iya tafiya da Inna. Hajiya ta yi murna,ita ko Hauwa harda dan ihun ta. Hajjo dai duniya ce ta ma ta zafi,ta sha kukan ta a daki ta koshi har sai da Hajiya ta kama ta ta na kukan,ta ce me yayi zafi Hajjo,in ba ki so ai sai a fasa tafiya da Innar. Da ke Hajjo akwai zurfin ciki,gudun kar Hajiya ta goyi bayan Baba ta ce a mai da Inna sai ce ma ta yi ba wannan ba ne,kawai har ta fara kewar Inna ne,ga makarantar kwana da za ta shi ma din da ke ba ta saba ba ya na damunta,Hajiya ta ce awho,ai dole ki yi kyewa,tai ta bata baki har ta ware.
Ta hadewa Inna kayan ta tsaf,amma sai Hauwa ta yi waya ta ce kar a damu da kayan Inna,ta nan ta na siya ma ta sababbi saboda sati biyu ya rage su koma. Hajjo ta yi godiya Hauwa ta ce ai ita ce da godiya. Jabir ne ya kai Hajjo Garko,har ta tafi ba su hadu da Khalid ba,sai dai sakon godiyar sa sa ta ji daga wajan Hauwa da ta zo ma ta sallama da godiya,ta kuma tafi da Innar. Daga uwar har diyar ba wanda be yi kuka ba,dan dai ita Innar ba ta ma san abunda ake nufi ba. Amma ita dai Hajjo ta yi mai isar ta,duk da dai ta san hannu mai kyau ta ke,da dai ta bawa Garbati diyar ta gwara ta bawa Hauwa.
Sati biyu da tafiyar Hajjo su Khalid su ka tafi da Inna. Sannu a hankali Hajjo ta aje komai ta sa karatu gaba,dama ga kwakwalwa tini makaranta ta san da ita,duk quiz ne ba a fita sai da Hajjo,gashi ta dage da haddar alqur’ani,dalibai da malamai kowa na yin ta,ga ta sam ba wasa bare kuma sa tunanin maza ko san su cikin ranta. Kuma ba ta da kawaye saboda ba ta san kowa ya san tarihin rayuwar ta. Duk sanda aka yi hutu gidan Hajiya ta ke zama. Sanda ta kai Ss2 ne Jabir ke tsokanan ta ko dai za a sake tsallaken ne a shiga jami’a? Hajjo ta ce dan Allah ko ma ba za a yi tsallaken ba dan Allah ta na son gwada jarabawar. Jabir ya ce sai dai fa idan kin yi ki tafi kawai,dan na sa za ki ci wannan guruwar,MBBS din ko an sake shawara? Ta na dariya ta ce MBBS din dai,idan ka ga zan iya,in kuma ka ga ba zan iya ba sai ka ba ni shawara. Cikin jaddadawa ya ce ina ai da wannan kwakwalwar ta ki babu abunda ba za ki iya ba Hajjo? Hajjo ta ce kai kar ka sa kaina ya fashe,Jabir ya ce da ya fashe za mu tattara mu kwashi karama. Hajjo dai da ta ga zolayar Jabir ba mai karewa ba ce,sai kawai ta hada na ta ya na ta ta shige wajan Hajiya.
Da yarda Allah Hajjo ta rubuta jamb ta ci sosai,dama MBBS ta cike,ta na cikin yin exam din ne su Hauwa su ka zo hutu,Inna ta cika shekara hudu Hajjo na shekara shabakwai. Sam ta ki zama gidan Hajiya ta kuma ki Hajjo sai dai Hauwa ko Khalid,da ke exam ya sha gaban Hajjo sai abun sam be dame ta. Ana gobe za su yi exam din maths ne,kan Hajjo yayi zafi ta dukufa ta na ta solving problems sai ga Hauwa ta shigo da sallamar ta, hannun ta ruke da na Inna. Hajjo ta dago ta na murmushi,ganin Inna sai farin ciki ya bayyana fuskar ta,ta ce wa’alaikumul salam Inna ta oyoyo ta tashi da sauri. Ganin Hajjon ta yo kan su,da sauri Inna ta noke jikin Hauwa ta na ummm Momma,Hauwa ta ce haba Neena! Maman ta ki za ki yiwa kiwa? Ganin yanda Innar ta ki ta sai ran ta ya sosa amma sai ta boye ta na murmushi ta koma ta yi zaman ta,ta ce ai ta manta da ni,shekara biyu ba wasa ba,Innar tawa Neena ta koma? Bakin gado Hauwan ta zauna,ta daga Inna da ta koma Neena a yanzu a yanzu ta dora kancinyar ta,ta ce wlh yaran neighbor ne ke kiran ta haka,da ke kin san turawa sun ka sa cewa Inna sai su ka maida shi Neenan. Hajjo ta yi yake,Allah sarki,cikin girmamawa yanda ta saba ta gaishe da Hauwa,Hauwan tai ta bata lbryn Inna,ita ko Hajjo da Allah sarki ta ke bin ta,cikin ranta ta tafasa ta ke,wai ita ce wata ke bawa lbryn diyar ta sai ka ce ita ta haife ta,toh an yi an gama karfe abar ta za ta yi,har wani Momma ta ke ce ma ta.
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[16/10 21:47] .: /25, 9:44 AM] Salmah Ateeku: [7:34pm, 5/31/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
3⃣8⃣
Budar bakin Hauwa sai cewa ta yi Hajjo na gode kwarai,Allah ya saka mi ki da alkhairi,wlh ba karamin gurbi Neena ta cike a rayuwa ta ba,thanks to you da ki ka iya yarda na tafi da ita,ta sanadiyyar haka i knw wat it feels lyk to b a mother,to hold nd hug a little one dat cal u mother,idanun ta su ka ciko da kwalla,ta kara da ba dan Neena ba ina ga da duk wannan ba zan san su ba. Subhanallahi! Hajjo ta fada yayin da ta daura hannun ta kan na Hauwa,me zai sa ki ce haka? Ya kamar kin sare da ikon Allah? Ai Allah ne ke bayarwa,dan kin yi shekara hudu ba ki haihu ba be kamata ki fidda tsammani ba,ma su yin goma tukun su haihu su ce me? Kwallar da ya makale idanun Hauwa ne ya gangaro bisa kuncin ta,ta ce ba fidda rai na yi ba,kuma har gobe ina addua,sai dai mun je manya hosptals da dama a london ana duba mu,duk sun tabbatar ba zan iya samin ciki ba bare na haihu,matsalar kuma ta wa ce ba daga gun Khalid ba. Jikin Hajjo yayi san yi,ta tausayawa Hauwa,ko wace diya mace da kaddarar rayuwar ta,ita na ta kaddarar kenan,rashin haihuwa. Ta nisa tare da fadin kar ki damu,in da rai da rabo,
Allah mai bayarwa shi zai ba ki. Ta na murmushi ta goge hawaye ta ce ameen Allah ya amsa,dan ma Khalid be da damuwa akan maganar,ya ce ba su dame shi ba,tin da Allah ya ba shi ni shikenan,ba maganar kara aure,ta kare ta na murmushi. Hajjo ta ce mashaAllahu,na ji mi ki dadi,Allah ya bar ku tare,ta ce ameen,ta dan yi shiru sannan ta ce ban sani ba ko za ki yarda na kara tafiya da Neena,kamar za ta hana,amma sai ta ga menene amfanin hanawar? Kar kishi da kyashi ya sa ta cuci diyar ta,dan gashi ta zama kamar diyar turawa dan kyau da kiba,gashi ita ma din fama ta ke da boko,dan haka sai ta ce me zai hana? Ke ma din ai kin zama maman ta,murna da farin ciki ya bayyana fuskar Hauwa,tai ta godiya har abun ya fara bawa Hajjo mamaki,ta tashi ta ce maza Neena zo mu tafi mu bar Mama ta yi karatu,ta ji ta na gani ta fita da noke jikin ta,ko daukar ta Inna ta ki bari ta yi.
Hajjo na tsaka da jarabawa su Khalid su ka koma. Ta yi post UME ta ci aka bata admssion a BUK,foculty of medicen,za ta karanta MBBS,ta yi sa’a ta ci WAEC din ta,Jabir ya biya kudin registratoin,Hajjo ta zama yar Jami’a,ta waye ta goge kwarai,nan ta hadu da wata Aysha ana kiranta Ayush,su ka kulla amunta mai karfi. Tin da ta fara sau biyu kawai su Hauwa su ka zo hutu,shi ma din ba wani dadewa su ka yi ba,ta na makaranta ne ta ga kira international num ta wayar da Hajiya ta ba ta,ko da ta daga sai ta ci muryar Khalid,a dar dar ta gaisa da shi gani ta ke kamar zai ce ma ta wani abu ne ya sami Inna,ga mamakin ta sai ji ta yi ya ce ya na so ne ya sa Neena makaranta,amma be san surname din ta ba,Hajjo ta yi jim,har sai da Ayush da ke zaune kusa da ita ta fara tambaya lfy? Shi ko Khalid da ya ji shiru sai ya katse wayar a tunanin sa jin shi ne ba ta yi,ya ce ya kira anjima. Da Ayush ta damu Hajjo da tambaya,a karo na farko sai ta ba ta lbryn rayuwar ta gaba daya,Ayush har da zubda hawaye,ta ce lalle Hajiya da zuri’ar ta daban su ke,kin ga kuwa ni anawa shawarar Hajjo gwara ya sa ta da sunan shi,tin dadai a hannun shi ta ke yanzu. Shawarar Ayush din ta bi,da Khalid ya sake kira sai ta ce ya sa sunan shi,dama dai abunda ya ke so kenan,ya ji dadi sosai,har da yar fara’ar sa,wasa wasa dai Neena na kara zama tamkar diyar sa. Hajjo da Ayush na ta tare rai da rai,kuma kullum Ayush cikin ba ta lbryn wani cousn din ta da take so ta ke,shi ma Doctor ne,duka yan gidan su ma haka sun maida MBBS kamar gadon gidan su,dan san shi da ta ke ma shi ya sa ta ke course din,amma shi be ma san ta na yi ba,kuma ta ki fadawa Hajjon sunan shi,ita dai Hajjon abun mamaki ya ke ba ta dan tun da ta ke ba ta taba san wani da namiji ba,bare kuma irin na Ayush wanda ba a ma san ta na yu ba. tare su ka yi 3 yrz a Buk old sites (pre-clinicals),sai kuma su ka koma teaching hosptal na Amenu kano,sun yi 3years har sun shiga na hudu,housemanship su ke,shi ma din watanni kadan ya rage su gama. Sannan Hajjo na da shekara ishirin da da uku,diyar ta Inna kuwa na da daya.
Tsabar kawacan Hajjo da Ayus ba wanda be san su tare ba,komai na su daya,haka ma group din su,da ke Ana raba whole Class into 2 groups first Lyk internal medicine Vs Surgery
a level 4 and 6 While a level 5…into Paediatrics vs Obstetrics and Gynaecology (O&G) kuma a kowani department. Akwai sub speacialities….sai a ka qara raba su into no Of speacialities available Lyk into 5 or 6 haka Then sai suke rotating into kowannen su….every 2 or 3weeks.
Kamar yanda su ka saba,yau ma tare su ke tafe,Hajjo na ma ta mitar wani young doctor da ke takura ma ta da kallo,sai dai ba su hadu ba,ita ta na mamakin me ya sa doctors ke da masifar san mata ne? Aysuh ta dara tare da fadin isn’t dat obvious? Irin wandannan docs din nay da basu yi aure da wuri ba…sun tsaya yin boko,ko toossing din babe ma basu iya ba….sai ta zo asibiti,kin ga kuwa dole su duba,Hajjo ta ce toh Allah dai ya sauwake! Ayush na dariya ta ce da Allah ni kuwa ki nuna min wannan Doc din na ki…ya Salam! Hajjo ta kau da kai,gashi nan wlh,daga idun Ayush wa za ta gani? Cousn din ta ne ma ashe Doc din da Hajjo ke magana akai.
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[6:42pm, 6/1/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
3⃣9⃣
Baki ne,be fiya tsayi sosai ba,amma sai dai ba a kira shi gajera ba,ya na da hanci da manyan idanu,kuma da ka gansa ka ga bafulatanin mutum. Ya na murmushi ganin Ayush din tare da Hajjo,ya karaso gun su ya na fadin aminan juna,Doc Ayush ya ki ke ya kawar ki? Baki budi Hajjo ta ke kallan Ayush,ganin yanda ta ke ma sa murmushi ya kara ba ta tabbacin ta san shi,caf Allah da ya so ma ba zagin shi ta yi ba,da ta sha kunya,godewa Allah da ta ke nan,ta na ji Ayush ta amsa da Yaya Suraj,lfy lau,kawata ma haka,ya su Mama? Idanun sa kan Hajjo ya ce lfy lau,kawar ta ki ba ta magana ne? Hajjo ta yi yake ta ce ina gajiya? Ya na murmushi ya ce ko kefa,lfy lau,ya kokari? Ta ce Alhamdulillah. Ya mayar da kallan sa ga Ayush ya ce kanwata akwai maganar da na ke so mu yi,so zan zo na same ki a gida. Cikin jin dadi ta ce toh ya Suraj sai ka zo. Ya kalli Hajjo ya ce sai mun sake haduwa? Ta ce sai anjima,Ayush ta ce a gaida su Mama,ya ce za su ji,su ka! Wuce idanun sa kan Hajjo. Hajjo ta ce Ayush? Dama kin san shi? Ayush ta ce cousn dina ne fa,ina famly din su ne na ce mi ki ar ol doctors,Hajjo ta ce aw fmly din crush din ki? Ko dai shi ne ma? Ta yi saurin ce wa nooo ba shi ba ne,yayan sa ne. Hajjo ta ce toh Allah ya sa dai ayi da mu. Ayush ta ce shi da be ma san ina yi ba,toh amen dai.
Maganar Suraj dai akan Hajjon ne,ya je ya sami Ayush ya ce da Allah ya za a yi shi wlh kawar ta ya ke so,nd da gaske ya ke. Duk da maganar ta ma ta ba zata,sai ta ce toh ba komai,za ta ma ta magana,ya kara da dan Allah ta taimaka,da gaske son Hajjo ya ke matuka. Washagari da Ayush ta yiwa Hajjo magana,sai ta ce ba wannan maganar,ba maganar maza ko so ko aure gaban ta…nan Ayush ta shiga ma ta nasiha,idan ta ce za ta yi haka ta sabawa mahaliccin ta,shi da ya halatta aure,da kuma manzo sallallahu’alihuwasallam da ya sunnata shi,haka kuma ta yi butulci. Da wannan Hajjo ta ce toh za ta yi kokari ta canza ra’ayi. Aysuh ta ce dan Allah for my sake dai ki bawa Suraj dama,wlh mutumin kirki ne,he is very differnt ko cikin fmly ma,he is nt jst a doctor,ya yi specialising a radiology,he is a great Radiologist. Cikin zolaya Hajjo ta ce ya kai Crush? Ayush ta murmusa ta ce He is exactly lyk him. Hajjo ta dara saboda ke Ayush,zan gwada ba shi chance. Ayush ta rungume ta ta na godiya,wayar ta ta dauka ta sawa Hajjo numbar Suraj din,ta ce dama shi tin jiya ta ba shi na Hajjon,Hajjo ta ce lalle,da kuma na ki fa? Ayush ta ce na san ba za ki ki ba ai.
Wasa wasa soyayya ta fara nisa tsakanin Hajjo da Suraj,duk da kuwa Hajjon kara kawai ta ke ma sa,she is tryn to give him a chance. Su Hajjo sun gama housemanship,daf da za su fara service aka tura Suraj India wani course,tafe ya ke cikin mota tare da Hajjo, ya na ta ma ta surutu,lbryn dptment din su ya ke ta ba ta,yanda su ke gudanar da aikin su musammam wannan infertility test da su kewa mace mai matsalar haihuwa,ana kiran test din HYSTERO SELPHIGOGRAPHY(HSG),ya ci gaba da fadin abu ake sawa kamar pencil dan ya fi biro girma,saman sa kamar allura,kasa kuwa abu ne kamar screw,ana sa ruwan magani ciki,shi ake sawa mace,ta vagina,ya bi ta cervix,ya je ovary ya kutsa ta falloprain tube har zuwa uterus wato mahaifa. Idan ya shiga sai a murza ruwan maganin ya fita ya je both ovaries,idan akwai blockage as in wanda ya hana a sami ciki sai machine din mu radiograps ya dauka,idan blockage din kadan ne,ruwan maganin zai iya kau da shi,idan blockage din mai yawa ne,toh sai an yiwa mace surgery. Kai jama’a Hajjo ta dafe haba,diya mace na ganin ta kan ta! Suraj ya gyada kai,yes u can say dat again dan gaskiya duk macen da aka yiwa wannan sai ta yi ciwan mara kwarai,wasu ma har bleeding su ke,kai da wuya ma ayi ba a yi bleeding ba gaskiya. Hajjo ta saki ajiyar zuciya,to ko dan irin wannan ya kamata mata su dage su zama likitoci,da mace ta ke sakarwa namiji jiki yay ta jagwalgwalawa,a ma shiga hakkin addini! Dariya Suraj ya sa har da dan bingirewa,ya ce haba Doc Hajara,ya ki ke magana kamar ba ta mu ba? U knw better ai,kin san wani abu kuwa? Ta ce um um,ya ce yawan cin aikin dptment din mu deals wit issues lyk dat,wit females,amma duk sanda mu ke aiki Allah na dauke ma na sha’awa,wlh mantawa mu ke ma wai mace ce gaban mu,amma akwai abu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login