Showing 27001 words to 30000 words out of 67328 words
Chapter 10 - Diya Mace Book Complete by khadija sidi .txt
biyu da we can’t help bt notice. Hajjo ta ce me kenan? Suraj ya gyada kai ya ce na fari shi ne kazanta,wlh Hajjo wa su matan ar too dirty abun har kunya ya ke bani,in ta mamaki shin wai ya maigidan su ya ke? Haka ya ke zama da su? Hw can a woman b dat dirty?,mace ta bude kafa sai ka ji wari na fita? Tsabar kazanta. Hajjo ta ce uhum,kunya ce ta kama ta,dan gaskiya wasu matan ko shaving ba su yi,dan ta taba jin wata nurse ta na ta mitar ta zo karbar haihuwar wata ta kasa banbance gashin baby ne ko gashin uwar baby ne da ya taru ya rufe ko ina!duk da ba a fiya so a yi shaving din tas ba,saboda shi ma gashin is a protection,ya na hana cuta shiga directly,so an fi so a yi saisaye,a dan bari kadan,as in KADAN dai,dan shi tsafta cikon musulin ci ne.
Ta ce sai me kuma? Menene na biyun? Ya murmusa ya ce tsafta,wasu mata su na da tsafta kwarai,dole ka yi respectn din su. Dax y bazan iya auren ko wata mace ba sai doctor yar uwa ta,kin san doctors ar generally neat,saboda sun san yanda rashin tsaftar ke da matsala! Dax y dole na auri Hajjo,ke na ki tsaftar ma daban ya ke,Hajjo ta murmusa ta ce ta ya ka sani? Ya ce haba alamar karfi ai ya na ga mai kiba Hajjo. Ya kalle ta ya ce Hajjo kin dai ki bari na turo,kin ga da an yi gaisuwa ina dawowa sai a daura ma na aure. Murshi ta yi ta ce gwara ka dawo din sai a yi mai duka lokaci guda,cikin ranta kuwa tunanin yanda za ta fada ma sa wacece ita ta ke,tunda be san ta taba aure ba,bare a zo maganar ta na diya budurwa mai kimanin shekara goma sha uku….ko kuwa? Tambayar sa ta doki kunnen ta,cikin rashin gane abunda ya ke fada ta ce na’am? Suraj ya ce hmmm u mind is nt hear,me ki ke tunani? Ko kin fara missin dina ne tin kan a je ko ina? Murmushi ta yi,ta ce ina jin ka fa,ya ce in ki na ji na me na ce? Ta ce wannan ne ban ji ba,ya dara ya ce ba kya jin kenan Hajiya. Cewa na yi toh ana dawowa za a fara maganar auren,i can’t wait to b ur hero! Murmushi kawai ta ma sa. Ya ce da auren mu fa za a sha budiri,bikin Doc. Suraj da Doc Hajara! Hajjo ta ce eh sai mu yi ankon lapcoat ba…kut kin ma isa?! Cikin asibiti za a yi bikin da za mu sa coat? No ba wannan maganar. Hajjo ta ce ni kuwa shi zan sa,ka rubuta ka aje,ranar auren Doc Suraj ni Hajjo sai na sa lapcoat wajan shagali,gwara kowa ya san bikin na gida ne! Ya ce da an yi rigima,da haka ya sauke Hajjo gidan Jabir,da za ta fita ya ce da Allah ta gaida maigidan shi,wato Jabir,dan yanzu ya ma kai matsayin consultant,Hajjo ta ce zai ji. Sai da Suraj ya tafi da wata guda su Hajjo su ka shiga camp,ta yi sa’a kano aka bar ta,bayan sun fito aka yi postn din ta Abdullahi wase specialist hospital. Ayush kuma aka kai ta Murtala Muhammad specialist hosptal.
Bautar kasa ta yi nisa kwarai,Hajjo na karbar allowee,rabi ta bari cikin account din ta,rabi kuma ta yi dan hidimar ta da shi na zirga zirgan kudin mota,sannan ta na yawan aikawa da Indo kudi,Kumuryan ne dai ta daukewa kafa,sai fa idan Allah ya kawo Indo kano ko kuma ta bawa Sani,haka kuma ta na yawan yiwa yaran Jibril hidima,yanzu yaran sa da Nabeela ta haifa sun kai shida,biyar mata,sai kuma Namiji shi ne karami.
Hajjo zaune cikin Doctors a asibiti,dukkan nin su babu wanda be girmi Hajjo ba,kuma su na da aure,dattijiwar cikin su Doc Husaina yaran ta goma ma,haka sauran daga mai uku,sai huda sai mai daya. Kamar yanda su ka saba da sun zauna sai a fara maganar maza,aure,rashin mutuncin maza,maganin da’a,zancen manyan mata dai barkatai,dan ma su na saurarawa in dai Hajjo na waje saboda da dan jikin ta,duk da dai akwai ta structure mai bala’in kyau ganin ta su ke yarinya,dan ba wanda zai kalle ta ya ce ta taba aure bare kuma ace ta haihu. Sai kawai su ka yi zaton kirar ta ce haka. Yau din ma maganar su ke, da hira ta yi hira,Doc Husaina ta ce um um dai kan fanka,ku fa san abunda kuke fada ga Hajjo kar ku sa ta tsorata da aure. Su ka ce aw ai mun munta muna tare da yar budurwa,Hajjo cikin ranta ta ce yau dai bara na fadawa wannan matan wacece Hajjo, ta ce Anty Hussaina ni fa ba budurwa ba ce…
DEDICATED to The Women OF Virtue💁👰🙋(group)
[7:15pm, 6/1/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
4⃣0⃣
Gaba daya ido su ka zubo ma ta,Doc Hussaina ta ce garinyaya Hajara? Hajjo ta murmusa ta ce ai na taba aure har da diya ma na ke da, Ameena sunan ta. Ganin yanda fuskar su ta nuna ta gane ba su yarda ba,sai kuwa ta ba su lbryn rayuwar ta,babu wanda be yi kwallaba cikin su,Doc Hussaina ta ce sannu Hajara,sunnun ki Hajara,amma gaskiya ya kamata a dinki wannan tear din,kin yi sakaci da yawa,hakan zai iya ba ki matsala sosai,wai ma tsaya,shi wanda za ki aura,Suraj sunan sa ko?ya san da wannan maganar? Hajjo ta yi ajiyar zuciya ta ce wlh Anty Hussaina na kasa fada ma sa,har ya tafi,ya dai san matsayi na a gidan Hajiya. Gaba daya su ka ma ta ca,wannan na fadin kai ba ki kyauta ba,wannan na Hajara ina ake haka? Wata na ki gaggauta fada ma sa dan ku sami fahimtar juna. Doc Hussaina ta tashi,ta ce Hajara biyo ni office dina. Bin na ta tayi,su ka zauna suna fuskartar juna,Hajara? Doc Hussaina ta kira sunan ta,ta amsa da na’am,Doc Hussaina ta ce kin yi kuskuran rashin fadawa Suraj,menene dalilin ki amma? Hajjo ta ce wlh ni kai na na kasa gane dalili,ni dai kawai fada ma sa din ne ya min nauyi,shi ya sa ma da ya ce zai turo gaisuwa na ce ya dakata ta dawo,Anty Hussaina daga ina zan fara ne? Wajan wa zan tura shi dangin Baba na? Bare kuma Baba na da ya ce ma zaman kai na na ke,ya so raba ni da diya ta,sanadiyyar haka gashi yanzu bare ke ruke da diya ta,wlh ko Mama ba ta kira na bare ta yarda ma ta zauna guna idan su ka zo hutu,ta riga ta saba da mai rikon ta,ina ga har da haka ma ya sa suka rage zuwa hutu,ta gane abun na sosa min rai. Doc Hussaina ta gyada kai,ta ce ki manta da duk wannan,ki aje komai ki fuskanci rayuwar ki,ki yi kokari ki shedawa Suraj wacece ke,kar ki bari ya ji a baki wani,ba zai ji dadin abun ba. Hajjo ta ce ya na dawowa zan fada ma sa inshaAllahu. Doc Hussaina ta ce wannan kenan,sai zancen tear din ki,ya ki na Doctor za ki aikata aikin matan da ba su san darajar kan su ba? Ba su san ciwan kan su ba? Ya za ki zauna da tear for such a long tym?gaba daya iskar duniya ta gama shigar ki na tabbatar kin ma zama tukunyar iska da guguwa da yayin duniya,idan ma cuta ne haka zai sami wajan zama Kin san darajar wajan nan kuwa gare ki diya mace? Ke bari na aje mi ki girma da kunya na fada mi ki,wallahi ba kya bi na bashin rantsuwa Hajara,ko miji ne ya ji an sami dan sako-sako raina matar ya ke,ba kunya bare tsoran Allah sai a fara mi ki habaici da gutsiri tsoma,ni dinnan da ki ke gani na gama haihuwa,da na ga Oga na shirin fara kawo min rai ni zuwa na ke a kara ni a dinke ni tsaf!na yi jinya ta,sai ki ji dif dif da ni,nan kuma sai Oga ya fara min da’a,na yi haka ya kai sau buyi yanzu tinda na daina haihuwa,wai wani lallami na namiji duk dan me su ke? Dan wajan ne fa! Kunya ta lullube Hajjo,ta yi kasa da ido. Doc Hussaina ta ce ba zancen kunya fa ki dago ki kalle ni,am old enof to b your mother,ita diya mace da gyara aka san ta,kullum aji ki tsaf mana,bare da bakin ki ki ka bamu lbryn dalilin da ya sa auren ki ya mutu,gaskiya da sake sai kin gyara,so gobe ki zo da shirin ki,zan din ke mi ki tear dinnan,sai ki dan dauki hutu in ya healling kya dawo ki. Hajjo ta ce toh Anty Hussaina,kin ga sai na fadawa mijin yaya ta ki na gama min ya wuce da ni kumurya dan ba zan iya jinyar gidan Hajiya ba,Doc. Husaina ta ce toh Allah ya nuna mana. A haka su ka rabu.
Hajjo na zuwa gida ta ke shedawa Hajiya gobe da yamma daga asibiti za ta wuce Kumurya,Hajiya ta ce lalle ziyara ta tashi kenan,gwara ana zumuncin ai,Allah ya kai mu,Sani za ki bi? Hajjo ta ce eh,idan ya zo da safe sai na sa kayan tafiyar cikin motar,kin ga da an tashi kafin ta tafi sai ya biyo ya dauke ni. Hajiya ta ce toh ba laifi,Allah ya nuna mana,ta ce amen amen. Ta kira Ayush ta fada ma ta,duk da dai kawancen na su ya ja baya sosai,ita kan ta Hajjo ta kasa gane dalili.
Da fargaba Hajjo ta kwana,gani take kamar wani haihuwar za ta yi. Sai da ta jira Sani yazo ta fada ma sa plan din ta sannan ta tafi. Gaban ta na faduwa ta ke komai a asibitin,zuwan Doc Hussaina tini hankalin Hajjo ya gama tashi,ita kuwa sai tsokanar ta ke,maza maza ta tashi su shiga daki,yau ba aiki. Kamar wacce kwai ya fashewa a ciki,ta bi Anty Hussaina,zani a gefe ta haye gado ta na jiran ta,bayan Doc Husaina ta shirya,hannu cikin hands gloves,ta ce oya oya gyara,Hajjo ta ce wayyo dan Allah ki dai na cewa na gyara,sai na ji kamar Garbati! Doc Husaina na dariya ta bude kafar Hajjo ta ce gwara dai ki tsaya! Kar ki bata min rai na! Sai a sannan ta gane tsabar tsokana ne irin na Doc Hussaina,sai kawai ta yi ma ta shiru,ta na ji ta mata allurar kashe zafi,sai gyada kai ta ke dan azaba duk da an ma ta allurar,dan kamar ba a mata ba,tin tana jurewa sai ta fara ihu,ta na wayyo,wayyo ni Hajjo,wayyo ni diya mace na cin kwakwa,ta na ganin tasko,yi min a hankali dan Allah Anty Hussaina! Wayyo! Doc Hussaina ta na aikin ta,ta ce kin ciki raki,pls ki yi shiru,ki bari na mi ki stiches dinnan yanda za ki ji dadin sa…Hajjo ta ce uhum,na ce tam! Da azaba tai azaba,jin yanda allurar ke shiga ya na fita ta fatar ta,ga wani dan ja da Doc Hussaina ke yi duk sanda ta zira ta fitar, kamar ta na dinke kwarya,sai Hajjo ta fara kamar fada fada,dallah Anty Hussaina ki min a hankali na ce! Haba mana!!wannan rashin imani har ina,Wayyo Inna ta! Yau ina ganin gwale gwale! Ta na yi ta na tsuke kafa Doc Hussaina na kara budewa ta na wlh zan kyale mi ki abun ki Hajara! Ta ce eh dan Allah ki kyale ni! Na ce ki kyale ni mana! Da haka ta lallaba ta dinke ta tas,ta samu ta kwantar da ita dan ta huta,jin ciwan ta ke har tsakiyar kwakwalwar ta.
Bayan wasu awanni ne,ta dan nutsu Doc Hussaina ta ja kojera ta zauna gaban Hajjo,ta ce Hajara? Hajjo ta ce ummm,ta ce ke likita ce,kin san yanda za ki kula da kan ki,ba sai na fada mi ki ba,amma dai zan dan tuna mi ki,yau banda zirga zirga,in ki ka cika motsi mai karfi wlh dinkin lalacewa zai yi,sai an sake,ni kuma kin ga bana gajiya. Hajjo ta ce uhum. Doc Hussaina ta kara da zama cikin ruwan zafi Hajara,kar ki yi wasa da shi,pls don’t use dettol! I repeat my slf don’t use dettol,kin san hw powerful it is,ya yi karfi da yawa,gwara ki sa dan gishiri cikin ruwan kafin dinkin ya warke zare ya zare. Sai kuma bagaruwa,ai kin san shi ko? Hajjo ta gyada kai alamar eh,Doc Husaaina ta ce yauwa,ya na da kyau sosai,amma yafi kyau ga wacce ta haihu ko akawa dinki saboda karfin sa,in yayi yawa ya na sane mace,so u can use it for a week ki hada da ganyen magarya,ki tafasa idan ya huce as in yayi yanda za ki iya zama sai ki zauna har sai yayi sanyi sai ki fita,in ya so daga bisani ki na amfani da ganyen magarya shi kadai,twice a day,safe da yamma,sai kuma ki yi hannun riga da ruwan sanyi,kar ki sha mai sanyi karara in ya zama dole ki sha,ban da kuma kama ruwa da ruwan sanyi,kin gane ko? Hajjo ta gyada kai. Doc Hussaina ta kara da Allah ya bada lfy,bara na bar ki ki huta,ta bar Hajjo ta na tunanin rayuwar diya mace..
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[16/10 21:47] .: :29pm, 6/1/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
4⃣1⃣
Da yamma Sani ya zo tafiya da Hajjo,Doc Hussaina ta hada ma ta da wasu magunguna,ta ce za ta kira ta,Allah ya bata sauki. A daddafe Hajjo ta shiga gidan Indo,Indo sai sannu ta ke ma ta,shi kuwa sani gaba daya tausayin mata ne ya lullube shi. Sati daya Hajjo na yin yanda Doc Hussaina ta ce sai ga zare ya fita,amma fa ta ji jiki,idan ciwan ya tashi ma ta ji ta ke kamar ta yi hauka.
Sati biyu ta sami sauki,a na ukun ta warke garau,ita kanta sai ta ji ta daban,ta fara jin ta cikakkiyar diya mace mai daraja. Su na waya da Suraj sosai,amma ko da wasa ta ki bari ya san ba ta da lfy. A sati na hudun ta komo kano,ran da ta je aiki kuwa sai tsokanan ta su Doc. Hussaina su ke,wai ya su ka ga har ta zama sisi ne,tafiya ta sake ana yanga,sai ma su gwada tafiyar ta sanda aka ma ta dinki,ita dai Hajjo ba ta da ta cewa. Ranar da ta koma gida Hajiya ke ma ta albishirin da dawowar su Khalid,ya dawo Nigeria gaba daya Suraj zai karbe shi,shi ya koma can,in ya so Khalid ya ke duba na nan din. Murna gun Hajjo kamar me,atlast Innar ta za ta dawo gida,dama dai ta na shirin cewa a dawo ma ta da diyar ta. Ranar da su Hajjo passin out,ta karbi certificate din ta na NYSC,Hajjo ta zama Doc Hajara,dama dai abun na Allah ne.
ranar jirgin su Khalid ya sauka,amma dai gidan su su ka wuce ba su zo gidan Hajiya ba tukun,asibitin da ta yi service ne su ka riketa. Ita kuma Ayush AKTH ta sami na ta aikin. Suraj na ta ma ta mita,wai shi in da ya ke aiki nan za ta yi,da ya dawo za ta dawo AKTH itama,gwara matar shi na kusa da shi,ita ko da toh ta bi shi kawai.
Ranar asabar Hajjo ba ta je aiki ba,ta na cikin kitchen ta na wanke wanke duk da dai yanzu ta tashi daga mai aikin Hajiya ta koma likita mai aikin gwamnati,amma hakan be sa ta daina yiwa Hajiya dukkan aikin da ya dace ba,ta zama kamar diya wajan ta,zancen albashi tin ta na secondry sch ta daina karba,tsakanin ta da Hajiya sai alkhairi.
Atamfa ce a jikin ta,dinkin doguwar riga mai igiya a baya,ta kafo dankwali har gaban goshi,ga gashin nan dan tsut ko kamu daya be kai ba an ma sa jerry,gashin da ke kwance goshin ta wanda shi ne ke rufa ma ta asiri ya yi lublub a kwance abun sha’awa,sai ta yi kyau sosai duk da ba kwalliya ta yi ba. Ta dukufa ta na wanke wanke,kamar daga sama ta ke jiyo maganar mutane,ta dai san tabbas baki aka yi,kuma dama dai Jabir ya zo yana tare da Hajiya cikin dakin ta,dan haka sai ta cigaba da aikin ta.
Jin gidan shiru Hauwa ta sami waje ta yi zaman ta a falo,Neena ta langwabe jikin maman ta a shagwabance, Khalid da ya kara girma da kyau,ya kara manyanta,ga shi zama cikin turawa rayuwar turai ta shiga jikin sa sosai. Ya kalle su ya ce ku ka ga yanda ku ka wani langwabe,ke Neena leka kitchen ki ga ko Hajiya na cen,na ji karar ruwa. Neena ta tashi,sanye ta ke cikin riga da wando,kai ba dankwali an faka gashi a kyeya,ga alamun girma sun fara bayyana a cikin ta,amma yanda Hauwa ke shagwaba ta ya sa ta tashi a sangarce,uwa ba kwaba. Kai tsaye kitchen din ta je,ta shiga ba tare da ta yi sallama ba,ganin Hajjo na wanke wanke sai ta tsaya kawai bakin kofa.
Hajjo Ji ta yi kamar ba ita kadai ba ce ba,ta juyo su ka yi ido biyu da fuska mai kamar na ta sak,diyar ta kuma Innar ta. Inna? Inna ta ke ce? Wani irin farin ciki ya mamaye Hajjo,ta aje wanke wanke ta taho ta na Inna? Zo mana! Ina ita dai yarinya Neena ta san ana kiranta ba Inna ba,gashi kuma ba ta san Hajjo ba,ganin ta nufo ta,ta juya ta fice da sauri,ta kusa bige Khalid da ya biyo sahun ta,ganin yanda ta fito da sauri sai ya karasa kitchen din ya na sarkin kin mutane wa ki ka gani kar dai Hajiyar tawa ta ke gudu….ganin ta tsaye ya sa shi zuke maganar,ita ma kuma Hajjon tsayawa ta yi ta na kallan sa bakin bature ne wannan ko kuwa mai kama da shi,dan bakin bature dai da ta sani be kai haka manyan ta ba, be kuma kai haka kyau da kwarjini ba. ganin na ta ya ma sa bazata,be taba tunanin zai ga irin wannan fuskar ba bayan wanda ya sa ba gani,she is jst lyk his beloved one,lyk his Neena…shin wannan wacece? Kar dai maman Neena ce,Child abuse?tambayar da ya ke yi wa kan sa kenan cikin ran