Showing 12001 words to 15000 words out of 67328 words

Chapter 5 - Diya Mace Book Complete by khadija sidi .txt

ba dama,Garbati ya ce Hajjo! Kar ki bata min rai na,ke Iyalle ki ma ta magana mana!
Iyalle ta ce ni da ka ce za ka hado ni da Baban ku? Ina ruwa na ban kuma sa baki,ga ka ga ita ai. Ya ce ke Kande turo ta nan! Hajjo ta kamkame Kande ta na ta ki ta turo ni din,ba za ta turo ni ba,ni wlh ban bin ka,mugu azzalumi. Garbati ya fusata da jin kalaman Hajjo,ya ce Hajjo kar fa ki zage ni!ke Kande matsa ki ga ai ba karfina ta fi ba,ya ture Kande saura kadan ta fada kan Mairo,Mairo ta farka ta na fadin wayyo Allah Iyalle a mafarkin ma Garbati ba zai bari na huta da bala’in sa ba! Ita duk ana ta mafarki ne,ganin Garbatin a kanta ya na shirin rarimar Hajjo ta yi gefe da rarrafe kar ya hada da ita. Da sauri ita ma Hajjo ta yi ta kanta,amma ina sai da ya caf ko ta ya daga ya aza a kafada,ta na ihun neman ceto. Iyalle fadi take kai amma Garbati ba ka da imani,ka bar yarinya ba za ka bar ta ba? Ya ma ta banza yayi ficewar sa…..
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[16/10 21:43] .: 5, 12:42 AM] Salmah Ateeku: [5:40pm, 5/15/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
1⃣7⃣
Dallah malama ki rufa ma na baki! Ya daka mata tsawa yayinda ya aje ta bisa gadan ta,ko a jikin Hajjo,maimakon ta yi shiru sai ma kudundunewa ta yi,ta dada daga murya,Garbati ya dube ta rai bace ya ce Hajjo! Na ce ki min shiru! Wai me na ce zan mi ki toh? Ko kina tunanin zan kara ne? Yo dallah ni ma mutum ne! An fada mi ki ke kadai ki ka wahala sokuwa kawai mai shegen san kanta! Ai dai wlh dan nima ba na jin dadi ne da sai kin bani hakkina in ya so na ga karshen gudu!ki min shiru Hajjo! Ya juya tura kofa ya sa sakata,sannan ya haye gadon sa yanda ya saba ba tare da ya rage kayan jikin sa ba. Sai mita ya ke wai an raina ma sa hankali,kan ka ce mai tini barci yayi awan gaba da shi,sai da Hajjo ta fara jin munsharin sa kamar kukan rago sannan hankalin ta ya kwanta ta dai na kuka,ta sauko cikin sanda ta yi kwanciyar ta bakin kofa. Haka su Iyalle ma,ko da su ka daina jin kukan Hajjo sai su ka yi kwanciyar su,ba Hajjo ba ko suma hakurin zama da garbati su ke.
Hajjo ta yi sa’ar Garbati,ya kwashe kusan sati daya da dori ba tare da ya sake kusantar ta ba,tawarke,kuma ta cigaba da ayyukan ta da ta saba,duk da haka dai a takure ta ke muddin dare yayi,gani take zai iya sake zuwa ma ta. Ile kuwa ta na cika sati biyu Garbati ya dawo da jarabar sa,kuma ba ya tashi zuwa ma ta sai dare ya raba yanda babu mai ceton ta,tin ta na gudu dakin Iyalle ya na zuwa ya na dauko ta har ta ma dai na gudu,da gari na fara duhu gaban ta ke fara faduwa ta san lokaci ya kusa. Hatta Iyalle tausayin ta take ji saboda haka ta sassauta ma ta ayyukan da ta ke ba ta,Haka ta share watanni hudu gidan Garbati.
Wata ranar alhamis Hajjo ta tashi da kasala da matsanancin ciwan ciki,ga shi sai ta na jin zuciyar ta na tashi,sam ba ta sha’awar cin komai,dan ko ta ci ma ba ya zama. Ta na kwance cikin dakin ta,gaba daya duniyar ta ma ta kunci,sai ga Indo. Sai da ta gaisa da su Iyalle sannan ta shigo dakin,a tunanin ta ma bacci ta ke,sai ta ga idanun ta biyu,Indo ta ce aw ki na ji na Hajjo ai na aza bacci ki ke,yau ba za a tarbe ni ba kenan,an gaji da gani na….
Hajjo ta tashi a hankali ta na murmushi ta ce haba ai ke na fi son gani duk duniyar nan idan aka dauke Inna,wlh ban jin dadi ne…Indo ta zauna bisa gadon,ta ruke hannun ta,ta ce me ke damun ki? Ko da Hajjo ta ma ta bayani,sai ta tambaye ta yaushe ta yi al’adar ta karshe? Hajjo ta kame baki,wannan abun? Ai tunda na yi be kara zuwa ba wlh,dama ana yi ne a tayi a tayi?
Indo ta murmusa ta ce eh duk wata ya kamata diya mace ta ke yi. Hajjo ta ce ai kuwa ni sau daya na yi,kin ga wata uku kenan da yi ma,toh idan ba ka yi wata wata sai me zai faru? Indo ta ce ai dole kowani wata cikakkiyar diya mace mai lafiya ta yi,indai ta kai munzali,sai dai ko ba ta kai ba,ko kuma shekaru sun ja ta dai na,ko kuma ta na dauke da juna biyu…
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[5:48pm, 5/15/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
1⃣8⃣
Juna biyu!! Hajjo ta dafe kirji. Indo ta gyada kai ta ce haka Hajjo,tabbas ciki gare ki tinda kin ce ba ki sake gani al’adar ta ki ba. Farin ciki ne ya fara bayyana fuskar Hajjo dan ta na san ita ma ta haifo na ta yar jinjirar,sai kuma daga bisa damuwa ta maye gurbin farin cikin na ta,ta ce Indo ni ma haihuwa zan yi? Garbati zai daina zuwa guna duk dare tin da ina da cikin ko? Indo ta murmusa,haihuwa za ki yi Hajjo nan da wata shida ko bakwai inshaAllahu,ya danganta da watannin cikin na ki ayanzu,zance Garbati kuma ki yi hakuri Hajjo,ko wata diya mace da ki ka gani gidan ta haka ta ke rayuwa da mijin ta,ke ma za ki saba ne ai. Kwalla na fita da ga idanun Hajjo ta ce wlh Indo na kasa sabawa,kullum azaba kawai na ke sha,ba na so,ba na son yanda Garbati ya ke min. Indo ta dafa kafadar ta tace kar ki damu,ai ba a banza ba,aure bautar ubangiji ne. Hajjo ta share kwalla ta ce sai dai bautar ubangijin,bari na kawo mi ki ruwa,za ta tashi Indo ta dakatar da ita,ta ce ki na fama da kan ki,ban jin ishi,na hutasshe ki,Hajjo ta koma ta zauna,cikin tausayawa Indo ta ke kallanta,a dan kankanin lokaci girma ya kama Hajjo,gaba daya ta canza,ta yi sanyi kamar ba ita ce yarinyar nan mai tarin kuriyaciya da wasa ba,lalle aure shi ne maganin mace!ga shi kuma ta zo ma ta da mummunar lbry….na ce ya Inna? Tambayar Hajjo ce ta katse tinanin Indo,Indo ta yi ajiyar zuciya,ta ce toh,Inna dai ba lfy,kusan watan ta daya ta na fama…na shiga uku na! Hajjo ta dafe kirji,me ke damun ta? Tooh wa ya sani ne ma,wai fa dan kurji ne ya fito ma ta a wuya,da ya ishe ta da zafi ta bincine shi,shi ne fa ya zame ma ta ciwo,abu kullum sai rami ya ke. Wayyo Inna ta!Hajjo ta daura hannu biyu bisa kai,amma Inna ta kai wata ba lfy shi ne ko ki fada min Indo,Allah sarki,tashi mu je na gan ta dan Allah.
Indo ta girgiza kai,kin gan ki ko? Shi ya sa ma Inna ta ce kar a fada mi ki,ta san yanzu sai ki daga hankalin jama’a,ina za ki ba ki tambayi mijin ki ba,ki jira ki tambaya sai ki je. Hajjo ta turo baki ta ce yasin ko ya hana ni bazan yarda ba,ai tintini na ke tambaya ya ki ya bar ni! Indo ta ce yi hakuri Hajjo wannan karan zai barki. Da kyar da lallami ta samu Hajjo ta hakura ta fara jiran dawowar Garbati,a karo na farko kenan da Hajjo ke jiran dawowar ta sa.
Ba shi ya dawo ba sai cikin dare,ganin Hajjo ido biyu sai yayi tunanin shi ta ke jira akan abun da ya saba ma ta kullum kenan yau ba sai ya tada ita ba,ita ma ta na so kenan. Ya na murmushi,hakoran sa yalaye suka bayyana,ya ce Hajjo mata ta ta kai na,ni ki ke jira ko? Zuciyar ta daya ba tare da ta gane inda ya dosa ba ta ce eh,ya ce ina zuwa,bari na ci na dare,ya ja kwanan tuwan da aka aje dan shi,ya na budewa daddawa ta daki hancin sa,ya ce daddawa sarkin kamshi,ya shiga kai loma kamar wani mayunwaci,dan takaici ma Hajjo sai sauke kan ta tayi,gashi alahimis ne raban shi da wanka kwana shida kenan,sai gobe juma’a zai yi. Ya na gama cin abunci ya wanko hannu ba kuskuran baki,sai gashi ya dawo,ya na washe baki,ya sunkuyo ta hanyar dafa gadan Hajjo ke kai ya ce da Hajjo toh gani na zo toh toh gyara!ya dago ya na cire babbar rigar sa.
Hajjo ta dan ja da baya jin yanda ya ke tashi,ta ce in gyara kuma? Magana za mu yi… Garbati ya ce Hajjo yanzun ga a gwiwa na ke,idan na gama biyan bukata ta ma yi maganar,ki gyara min mana karfa ki bata min rai na! Hajjo ta sa kuka,ya ce aw haka za mu yi? Ni ko ban fasawa. Yanda ya saba ma ta yau ma haka yayi,ya na barin ta tashi da sauri ta fice sai bakin rariya,nan taita amai kamar hanjin cikin ta zai fito,ta dau kusan minti goma a bakin rariyar sannan ta koma daki,ina tini gogan na ta yayi nisa da baccin,ta so ta tashe shi,amma sai ta sake shawara gudun kar a kuma,sai kawai ta fito ta yi wanka dan duk san da Garbati ya kusance ta ba ta iya bacci sai ta yi wanka komun dare,ji take kamar ita ma din warin Garbatin ta ke.
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[5:55pm, 5/15/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
1⃣9⃣
Da sassafe da amai Hajjo ta tashi,ta na durkushe gaban rariya,Iyalle da Kande tsaye kan ta suna ma ta sannu,Garbati ya fito ya na mika,ya ce Iyalle,wai me ke sa yarinyar nan amai ne haka? Iyalle ta dan taba bayan Hajjo ta na sannu Hajjo,ta dubi Garbati ta na fara’a tace ai Garbati girma ne ya hau kan ka,matar ka dai ta yi tsintuwa,eh juna biyu gare ta. Garbati baki washe ya ce ashe? Kai ashe ni ma na isa da,bari na je na fadiwa Nuhu,ni ba sa’an shi ba ne! Ya juya zai fita ba ko sallar asuba bare wanke ido,Hajjo ta tashi da sauri ta ce Garbati dan Allah ka barni na je na duba Inna ta ba ta da lfy. Ya juyo ya ce ke ki bari na dawo ma yi maganar da Allah! Yayi ficewar sa,Iyalle ta ce Ameenatu ba ta ji dadi ba ashe? Allah ya sauwake. Cikin kunci Hajjo ta amsa ma ta da amen ta shige dakin ta.
Nuhu zaune gaban shagon sa Garbati ya zo ya same shi,ya ce kai mutumin nan ni fa jindadi ya same ni! Ya bashi hannu su ka taba,Nuhu ya mi ka ma sa asuwaki ya ce kai goge wannan bakin na ka da ke tashi kafin ka karni! Zama ya yi kusa da Nuhu,ya ce shege ai ni da kai duk kanwar ja ce!! Da lbry na zo dallah! Aje asuwakin yayi da dai ya ga Garbatin ba karba zai yi ba,amma fa suna magana ya na dan kau da kai,ya ce wani dadi kuma? Garbati ya ce ina fatawar da mu ka samu game da mace mai ciki? Nuhu ya ce aka ce sun fi armashi….Garbati ya daga kafa ya dire ya na wata irin dariya ya ce toh yasin Hajjo ciki gare ta!!!! Nuhu ya dara ya ce shege Garbati! Murnar ta ka ta za ka zama uba ne ko kuwa na matar ka ta dado armashi? Garbati ya shafa kyeya ya ce yo ni ina ruwa da wani zama uba! Ka ji wani dundurusu da kai,wake ta wannan,ni murna ta na dada jin dadi da zan yi ne,dan wlh bazan rangwanta ba sai na samu rabo na kan ta haihu,caf ga ni’ima daga sama ina zan yi wasa!
Nuhu ya gyada kai,Allah sarki dadi inji barawan zuma,wlh ko ni ne haka zan yi,dan haka kai fa Allah ya kashe ya baka. Garbati ya ce wlh mutumina,shi ya sa ko karyawa ban yi ba na taso ka taya ni murna,kai dan uban ka kace a ma ka aure! Nuhu ya ce ahh ni tukunna dai,bari dai ka ci gaba da lasa min lbrn kafin na yi. Garbati ya bashi hannu su ka gaisa sannan ya ce abubuwa dai na wuce ka,ni kam bari na koma gidan,Nuhu ya masa a sauka lfy,dama Allah Allah ya ke ya tafi ko ya sha iska.
A gidan kuwa Hajjo Alhaji Baso ta kaiwa korafi,dan ta ga take taken Garbati ba zai barta ta je wajan Innar ta ta ba,Alhaji Baso ya ce ya ko ji lbryn rashin lfyar na ta wajan Alhaji Mamman,ah ya kamata ta je,ina Garbatin? Hajjo ta ce ai ya fita,sai kuma gashi ya shigo,ganin Hajjo durkushe gaban Mahaifin sa ya fara menene toh? Baba me ta ce na yi?
Alhaji Baso ya ce ba komai,ta dai tambaya ne za ta gida,dan haka ka barta ta tafi. Budar bakin Garbati sai cewa yayi toh Baba ka fada ma ta ta dawo da wuri,ka ga dai ciki ne da ita….Alhaji Baso ya ce an ki a ce din! Sakarai me ya hada cikin na ta da tafiya gida? Ciki ya shige ya na fadin kar ma ta dawo ne dare yayi ta ce ta gaji,atoh dan yasin bazan hakura ba….Alhaji Baso ya yi kamar be ji shi ba ya ce ta yi maza ta shirya ta tafi abunta kafin lokacin masallaci. Tana murna ta ce toh,ta tashi da sauri ta fara shiri,shi ko Garbati sai kashedi ya ke ma ra,karfa ta je ta zauna,dan shi fa bazai saurara ba. A haka a haka Hajjo ta samu ta fito….
Ko da ta shiga soran gidan su,ji ta yi tafiya ma bata lokaci ne,ta manta da auren da aka lika mata,da wani cikin da ake cewa ta na da shi,ta zura a guje ta na fadin Inna!! Inna ta!!!Inna!!
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[16/10 21:45] .: 3pm, 5/15/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
2⃣0⃣
Inna na kwance tana fama da kan ta cikin uwar daka,gidan ba kowa su Mudi sun tafi makaranta,jin murya kamar na Hajjo ta tashi da sauri ta fito tsakar gida,nan ta ci karo da Hajjo,Hajjo ta daka tsalle ta rungumo Inna,ta manta da ciwan da ke wuyan na ta,sai da Inna ta ce hankali dai da ciwo bisa wuyan Innar taki,sannan Hajjo ta sake ta da sauri ta na fadin yi hakuri Inna,na manta ne wlh.
Inna ta na fara’a take kallanta,ta ce Hajjo hankali,Allah sarki auta,zo mu shiga ciki. Ta ja ta suka shiga ciki,nan fa aka fara hirar ya bayan saduwa,Hajjo ta na mata mitar ta ki ta zo ta ganta gashi Garbati ya ki ya barta ta zo,wlh ita ba ta san shi,Inna ta ce ki yi hakuri diya ta,komai zai wuce ai da yardar Allah,babu abunda ya ke madauwami. Sai a sannan Hajjo ta ce Laa Inna ban ma gaishe ki ba,ina wuni? Inna ta murmusa ta ce Hajjo hankali,auta hankali,Allah sarki Hajara ta,Lfy lau diya ta,Hajjo ta ce ya jiki? Inga ciwan? Inna ta ce da sauki,ta sunkuya ma ta dan ta ga ciwo,ganin yayi rami sosai sai hankalin Hajjo ya tashi,ta ce Inna Baba ya kai ki kemis kuwa? Shi ne ya ke saki zazzabi wannan ciwan? Inna ta ce eh ya na sawa Mudi ya na raka ni ai,kar ki damu auta,ai ba wani abu ba ne. Hajjo ta ce toh,Allah ya sauwake. Ta cire mayafi ta aje gefe sannan ta haye gadan Inna ta ce Inna yau dai bari na dana gadan Inna ta,Inna ta ce maza dana auta. Sai da ta kwanta ta kwada ma ta kira,ta ce Inna! Inna ta na daga kasa ta ce na’am auta! Hajjo ta rufe fuska da tafikan hannun ta,ta ce wai kin ji wai ciki gare ni!!!!
Inna ta kame baki,maganar ta ma ta ba zata,amma sai ta buye ta ce toh! Auta hankali! Allah ya raba lfy. Na ce dai kin rage hargowar nan taki,kin ga dai kin girma,ki na hakuri ki kuma bi mijin ki Hajjo,na ce dai ba kya ma sa wannan tsiwar ta ki ko? Ta ji shiru ba amsa,ko da ta dago ta duba sai taga Hajjo ta yi baccin ta. Inna ta shafa fuskarta zuciyar ta cike da tausayin Hajjo.
Hajjo ta sha baccin ta koshi,sai da la’asar ta tashi,su Mudi da Ayuba sun dawo daga makaranta,sai tsokanar Inna Mudi ya ke,wai ta ga auta dai hankali ya kwanta,shi ko Ayuba Hajjo yay ta zolaya. Bayan ta ci abunci ta amayar ne Mudi ya fita ya siyo ma ta ‘ya yan itatuwa,ta na zaune cikin yan uwa cikin jin dadi ana hira ta na cin ‘ya ‘yan itatuwan da Mudi ya siya ma ta sai ga Baba nan kamar an jefo shi,ganin sa tini Hajjo ta nutsu,gaba daya fara’ar da ke fuskarta ta gushe,a tsorace ta tashi sannan ta koma ta tsugunna ta ce sannu da zuwa Baba,
Rai bace ya ce ke ce da sannu ke da ki ka baro gidan mijin ki tin safe ki ka rashe a nan,toh gashi can kofar gida ya biyo sahun ki,ki tashi ki bishi. Idanun Hajjo yayi rau za ta yi kuka ta ce wlh Baba ba tin safe na zo ba,ga dai Inna nan ita ce sheda ta. Ke rufa min baki! Ya daka ma ta tsawa,ni ina ruwa da lokacin zuwan ki,maza tashi ki bi mijin ki! Hajjo ta sa kuka,cikin girmamawa Inna ta ce Mallam za ta tafin ne ai,amma dai ya bari ku gaisa ko? Wa? Da wa za a gaisa wai? Inna ta ce da kai wai Mallam. Baba ya ce ahab ka ji wani zance,wani gaisawa kuma za mu yi da ya wuce wanda mu ka yi yanzu,ke wuce ki tafi.
Inna ta dauko mayafin Hajjo ta rataya ma ta,ta na fadin dai na kuka ki tafi gidan ki Hajjo,shi zai fishe mi ki alkhairi,Baba ya shige ciki ya na fadin na fito na same ki sai kin gane kuran ki. Hajjo ta ki motsawa,sai da Inna ta fara nuna ma ta bacin ran ta sannan ta yarda Mudi da Ayuba su ka raka ta. A kofar gidan kuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login