Showing 21001 words to 24000 words out of 67328 words
Chapter 8 - Diya Mace Book Complete by khadija sidi .txt
Hajjo ake kira na. Hajiya ta ce toh Hajjo nawa ki ke so a biya ki?
Hajjo ta dubi Sani,dan ita ba ta ma san nawa za ta ce ba. Sani ya gyada ma ta kai,sannan ta ce ko nawa ne Hajiya zan karba. Hajiya ta ce ah ah gwara dai ki fada kar a kware ki Hajjo,kin san dai kwana za ki na yi,kuma duk wata za a ke baki kudin ki,kuma ni da kike ganina ban da matsala musammam idan ki na da tsafta,za ki ji dadin zama da ni. Hajjo ta ce Hajiya ni kam wlh ko nawa ne Allah sa albarka. Hajiya ta ce toh shikenan tin da kin ki ki fada,kin ga ko an kware ki ba laifin mu. Sani ya ce kwarai kuwa. Hajiya ta ce da Jabir sai su yanke nawa za su ke biyan ta,daga yau za ta fara aiki.
Sani ya koma kan aikin shi,ita ko Hajjo dakin da za ta ke kwana Hajiya ta kai ta,daki ne mai hade da ban daki a ciki,ga wani sanyi mai dadin gaske da ke ratsa Hajjo wanda ta gaza gane sanyi daga ina ya ke busowa gashi dai zafi ake bare ta ce ta taga ne aka salima tagogin a rufe su ke. Hajjo tsaye ita da Inna tsakar dakin,wannan daki ai yayi a hada nawa da na Iyalle da na Baban Garbati! Wannan girma ai anyi asarar fili! Haka dai tai ta tabe tabe da kalle kalle,hatta bandakin abun kallo ya zame ma ta,ita kuwa Inna sai gwaran cin ta take. Ba a jima ba sai ga Hajiya ta dawo dauke da sinkin sabulun wanka,ta ce da Hajjo ta yi ta kuma yiwa Inna,sai ta fito ta ci abunci ta nuna ma mata gidan. Hajjo ta karba tare da ma ta godiya. Sai dai wankan kusan gagara yayi,da kyar ta samu ta yiwa Inna,ita kuwa sai dan kwaskwarima ta yi,dan gani ta ke da ta saki jikin a bandaki za ta ji ta a kasa,ta fito ta na mita an bi an lallaye ban daki da tangaran sai ka ce wajan hutawa! In dai ba ka mutu ba ka sha kallo…..
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[3:09pm, 5/27/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
2⃣9⃣
Sati biyu Hajjo ta fara sabawa da rayuwar gidan,haka kuma sannu a hankali Hajiya ke nusar da ita yanayin yanda ya kamata ta kasance a matsayin ta na diya mace,uwa,kuma mai aiki,da ke Hajjon mai saurin dauka ce hakan ya sa da an gwada ma ta shikenan za ta dauka. Hajiya kuma ba ta da matsala,tausayin Hajjon ma ta ke ji,sai ta ke tuno ma ta sanda ita ma ta ke kamar ta,sai dai ita din da gatan ta ga kuma soyayyar miji amma duk da haka ta ji jiki bare kuma Hajjo ta take rayuwa daga ita sai diyar ta ta. Ga wata soyayya da ke kulluwa tsakanin Hajiya da Inna,da ke Hajiya ba ta taba samin diya mace ba,wacce ta haifa din ba ta zauna ba,kuma ta na sha’awa matuka,samin Inna kusa da ita sai ya sa take kaunar yarinyar,ta na yawan ma ta wasa,idan Hajjon ta na aiki gun Hajiyar ta ke barin Inna,sai ka ji suna ta dariya abun sha’awa.
Da yamma Sani zai koma Kumurya,sai Hajiya ta ce ya aje Hajjo shagon da ake ma ta din ki a tarauni,in ya so sai ta hawo adaidaita ta dawo tin da Hajjon ta fara gane gari,Inna goye a baya,Hajiya ta ba ta naira dari ta ce idan ba za ta gane ba ta ce ya shigo da ita ta kwanan magi.
A hanya Hajjo ta ke ta yiwa Sani tambayoyi,ta ce ‘ya’yan Hajiya uku,amma ita daya ta gani,ina sauran biyu? Sani ya na tuki ya ce ai babban dan na ta shi ne Sabir,a Abuja ya ke zaune da iyalin sa,matar shi daya da yara uku,suma duka maza ne, can ya ke aiki karkashin company da baban su mai rasuwa ya bari,shi mutum ne mai hakuri kwarai da kawaici,be fiya magana ba,da mahaifin su ya rasu bayan an raba mu su gado sai suka hada karfi da karfe su ka ci gaba da tafiyar da company din,karkashin jagorancin Sabir,duk da be yi wani karatu mai zurfi ba,a diploma ya tsaya. Hajjo ta ce menene diploma? Sani ya ce wani mataki ne na karatu na gaba da sakandiri. Hajjo ta ce ayyo. Shi kuma Jabir fa? Sani ya ce Jabir shi ne dan Hajiya na biyu,matar shi daya da yara biyu mata,na ukun kuma ko yau ko gobe. Mutum ne mai haba haba da surutu,likita ne a asibitin koyarwa na malam aminu kano. Hajjo ta kame baki likita? Kai gaskiya ya burge ni wlh. To waye autan kuma?
Sani ya jinjina kai,yace wato sarkin kumbo da kwalisa kenan,ga kumbo,ga kyawu,ga jin kai,ga takama ga isa! Caf girman kai kenan? Hajjo ta tambaya cikin mamaki. Sani ya ce ah ah gaskiya Khalid be da girman kai,amma fa ya na ji da kan sa matuka,dan duk cikin yayun sa ba wanda ya kai sa nuna isa da tinkaho,akasali ma ko su ma yan uwan na sa kokawa su ke,ga tsafta ko zama a tabarma ba ya yi kar ta bata ma sa karin guga,ga kyamkyami,be sha ko cin abu acikin ko wace roba saboda yan da ake sarrafa su. Ina ga shekarun sa ishirin da shida a duniya,be dade da gama bautar kasa ba,ina wannan karatun na zanen gine gine? Ya ma ya ke da suna? Hajjo ta ce yo ni ina na sani?
Daidai bakin shagon da zai sauke Hajjo ya faka,ya ce yauwa Ar-chi-tec-ture! Toh shi ya gama,auren sa be ma kai wata hudu ba yanzu…Hajjo na shirin fita daga motar,ta ce ya ban taba ganin shi ba shi ma? Sani ya ce ya na can Abuja ai,da ke shi ma karkashin company din na su ya ke aiki,na ji ma da an yi auran na sa ba a kasar za su zauna ba,can dayan bangaran company na su da ke a kasar landan zai yi aiki. Hajjo na jinjina kai ta fito tana fadin manya kenan,toh Allah ya sa a yi da mu. Dan Allah a gaida Indo da yara Allah ya kiyaye,Sani ya ce amen za su ji,ta dai kula da hanya,Allah ya tsare,ta ce amen,ya tafi ta shiga shago ta karbo din kin Hajiya. Ba ba tare da bata lokaci ba ta sami dan adaidai ta ya mai da ta gida.
Ko da ta ce nawa za ta bashi,ya ce ta kawo naira hamsin,sai Hajjo ta kame baki,hansin fa Mallam? Yo ruwa ka hayar da ni? Yo toh ko ruwa ka hayar da ni alkur’an ban biyan hansin bare kuma nan da nan baki da hanci,da na sani ma silafowa na yi da kafa abuna,yasin sai dai na ba ka ishirin! Kut amma fa wannan yar kauyen ma ki na neman rigima,ya kashe adaidai ta ya fito,ya ce ke wlh na fiki kauyengi da gidadanci ki biya ni kudina ko na more ki! Hajjo ta dada gyara tsayuwa,da daure goyan bayan ta tamau,sannan ta daura hannu a kugu ta ce wa za ka more? Ni? Toh uban kuturu yayi kadan bare na makaho!shege ka fasa! Yasin ishirin zan ba ka,ka ga dari ne ma a hannu na sai ka miko min canji zan ba ka! Kan ka ce me? Rigima ta kaure tsakanin Hajjo da dan adaidai ta. Wata galleliyar mota ta zo,da alama gidan Hajiya ta ke san shiga,amma tsayuwar mai adaidaita a bakin gate ya hana shi,yayi horn amma ko a jikin sa,da dai ya gane rigima ya ke da yar yarinyar da ke tsaye ta ruke kugu sai tsiwa ta ke gaban sa,sai ya ja tsaki ya fito a hasale. Kai Mallam da Allah ka ja gefe kai yanzu ba ka ji kunyar sa’i sa da wannan yar tatsitsiyar yarinyar ba? Sai a sannan da ga Hajjon har abokin fadan na ta su ka san da tsayuwar sa,baki bude Hajjo ta ke kallan sa……Dogo ne,dogo sosai wane Garbati,fari ne amma irin wanda baki ya ratsa,fari mai duhu kamar na bakaken turawa haka,ya na da kyau matuka,ga hanci har baka,kan shi ya dan tara gashi baki wuluk,amma kadan irin dai na samarin zamani,be da kiba amma ya na da kafada irin mai kirar zakin nan. Amma ita Hajjo shigar shi ta fi burge ta,shiga ne na kanana kaya wanda su ka karbe shi matuka…ba fa wani kunya dan samari,wannan ba yarinya ba ce tin da ta san ta toye min hakki na,kowa dai ya san daga tarauni zuwa nan GRA hamsin ake biya,na fada ma ta ce wai ishirin za ta biya ni,ni kuwa wlh sai ta bani kudi na daidai ko na more ta!maganar dan adaidaita ya dawo da ita da ga kogin tunanin da ta fada. Tsaki ya ja ya sa hannu a aljihu ya fiddo da kudi naira dari biyu ya mikawa dan adaidaita ba tare da ya kalli Hajjon ba,ya ce gashi ka ruke har canji! Ya shige motar ya ja gefe ya faka. Mai adaidaita ya ce Allah ya cece ki yarinya,Hajjo tace yarinya na bayan uwar ta,kai dai Allah ya ceta da yau ka yi biyu babu! Suna musayan magana har ya fito ya shige gidan ba tare da Hajjo ta ankara ba. Mai adaidaita ya tada babur din sa ya na kiran Hajjo matsiyaciya,ta na kai ne matsiyaci! Sai da ya tafi sannan ita ma ta shige gida.
DEFCATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[7
[16/10 21:46] .: :49pm, 5/31/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
3⃣6⃣
Ranar aka yi dinnar,Hajjo da Dada da yara aka bari a gidan,washagari aka kai amarya gidan ta a court road. Bayan sati daya kuma jirgin su ya kyeta hazo. Bayan hayaniyar biki ya lafa,Hajjo ta je kumurya domin fadawa Indo maganar makarantar da za ta koma,Indo ta ce ta yi dabara Allah ya taimaka dai,ya za ta yi da Inna? Ta ce Hajiya ta ce ana barin ma ta ita,ta ce toh madallah. Bayan dawowar ta Jabir ya kai ta makarantar abokin sa,prestige gurls collage,duk da dai ba ta ci test din da aka ma ta ba aka samu aka makala ta a JS 1,Jabir ne ya biya kudin uniform da books din ta,da ke abokin sa ne,ya kuma ce Hajjo cousin din shi ce sai ya dauke ta on schlarship. Hajiya ta ji dadi kwarai,gashi makarantar kusa ce,dan haka Hajiya ta sa Hajjo ta yaye Inna indai makarantar ta ke so ta yi da gaske ga shi dama babu abun da ba ta ci kuma ta saba da Hajiyar,sai ta ke barin ta gun Hajiya,Inna na wata tara aka yaye ta. Kullum da tashi da asuba ba ta komawa bacci ta ke hawa kan aiki,kafin lokacin makaranta ta gama kome ta tiwa Inna wanka,sai ta je makarantar ta,2 na rana ana taso su ta dawo gidan Hajiya,da la’asar kuma ta je islamiyar da ke kusa da gidan Hajiya.
Rayuwar makarantar na matukar bawa Hajjo wahala,Hajjo ba turanci,ba ta iya ba,ba kuma ta ji,so ko ya ta dan jagwalgwala sai ka ji dalibai sun dare suna ihu,gashi an hana hausa,in ka yi sai ka biya naira goma,tin Hajjo na biya ta ga ana shirin tatiketa abun ba na hankali ba ne ai kuwa sai ta dage da kwaba turancin ta,a rana be fi a karbi naira hamsin ba,shi ma din da kyar da sudin lodayi. In ka ji Hajjo na told me wen I say d hausa mana!!!!!! Toh fa an kama Hajjo ta na hausa an rubuta sunan ta,an zo an ce ta biya,da kuwa har dari biyu karbe ma ta ake,wato ta yi ya taru. Kullum in ta je gida tai ta gwarancin turancin ta ko Allah ya sa a daina karbe ma ta kudi. Sam ba wani alamar Hajjo ta yi aure,bare ta na da diya,tini ta saje da daliban,amma kauyencin Hajjo ya sa ta yi suna a makarantar,ko ina ka bi ka ji ana ina spoke the hausa,sunan da aka sa ma ta kenan. Da aka yi exam din first term Jabir ya zo ya karbar ma ta result,ba labari Hajjo ta dauke ajin,da ke ya san background din it was very poor,sai be damu ba,haka second nd third term ma. Ana shirin ma ta repeatn Jabir ya roki arziki da a barta,what is important shi ne kawai ta zo makarantar.
Da su ka shiga JS2 sai Hajjo ta ba da mamaki,ta fara jin turanci sosai,kuma tsabar kar a karbi kudin ta ba ta jin kunyar kwaba turancin ta,ga ta gwana ce,kwaruwa ce wajan maths,kan ka ce mai sai ga Hajjo ta fito sahun goman farko,duka terms din. Jabir da Hajiya sun ji dadin kwazon Hajjo,da aka fara siyar da form din Junoir WEAC na science bord abokin Jabir ya ce a siya Hajjo ta gwada,da ke abun na Allah ne sai sai kuwa ta ci,ta sami Gurl science Garko. Murna gun Hajjo be musantuwa. Duk da JS 2 ta ke an gwada ne kawai a ga ya kwakwalwar ta ta take gashi kuma sun sauke alqurani a makarantar islamiya,su na shirin fara hadda da littafai na addini.da Jabir ya ga ta ci sai kawai ya ce kawai ta tafi abun ta. Lokacin Hajjo ta cika shekara goma shabiyar,Inna kuma an yi biyu,da Hajjo ta ga za ta makarantar kwana sai ta yanke hukunci mayar da Inna kumurya wajan Indo,Hajiya ta ce a bar ma ta ita,Hajjo ta ce ita ma za ta so haka,amma gaskiya ba za ta iya dorawa Hajiya dawainiya ba,sanda dai ta na prestige zaman Hajiya da Innar na dawainiya na awanni ne,yanzu kuwa shekaru ba wasa ba ne. Da haka din aka yanke hukuncin mayar da Inna kumurya. A wannan karan ne Khalid da Hauwa su ka sauka gida Nigeria domin yin hutun su na karshen shekara bayan sun shekara biyu a london. Murna gun Hajiya be musantuwa,dan da saukar su gidan Hajiyar su ka fara zuwa,sai dai har su ka tafi ba su hadu da Hajjo da Inna ba sun je Kumarya.
Ana saura kwana hudu Hajjo ta tafi Garko,Jibril da Hajiya su ka ba ta kudi ta yi siyayya,Sani ya kai ta kasuwa,a gida wajan Hajiya. Hauwa da Khalid su ka zo gidan. Hauwa ta kara fari da kyau sosai, Tin da ta kyallara ido kan Inna ta ke ta bibiyar ta,dama tin usul ta na san yarinyar,gashi auren su 2years amma shiru ko batan wata ba ta taba yi ba,duk da dai shi Khalid be damu ba ya ce lokaci ne be yi ba,da yayi Allah zai kawo ma su albarka. Shima din dake Inna tashi ce,tin shigowar su ya ke makale da ita. Suna zaune tare da shi da Hajiya,Inna ta yi bacci kan cinyar sa. Hauwa ke tambayar Hajiya ina maman Inna kuwa? Tin da mu ka dawo ba mu hadu ba. Hajiya ta ce kai haba? Ai kuwa da kyar za ki gane ta idan ki ka ganta,Hajjo ta ta zama yar birni yar boko,ta ma tafi kasuwa siyo provisions za a shiga Ss1,ta sami admision. Hauwa ta ruke baki kai ya aka yi ta yi sauri haka? Ai ba ta dade da fara karatun ba na gani. Hajiya ta ce da ke she is naturally gifted,tsallake ta yi kamata yayi ta shiga JS3. Hauwa ta ce owk,ya za a yi da Inna? Gun ki za ta zauna? Hajiya ta ce haka na so,amma ta ce ba ta so ta daura min nauyi,za ta maida ita Kumurya wajan yayar ta. Budar bakin Hauwa sai cewa ta yi dan Allah Hajiya ni ta bani ita na tafi da ita ta na debe min kewa,ta kalli Khalid a marairaice ta ce ka sa baki a ba mu Inna.
Shi ma Khalid din kamar ta shiga zuciyar sa ne,ya na zancen cikin zuciyar shi da za a ba shi Innar,ta na taya Hauwar sa rayuwa,dan ta na kadaici acan duk sanda ya tafi aiki. Ya ce eh Hajiya za mu so a mana wannan alfarmar,a roka mana dan Allah. Hajiya ta ce toh abun ne da kamar wuya,amma bari Hajjon ta dawo sai a mata maganar,ai kuna nan ma za ta dawo. Khalid ya tashi dauke da Inna,ya ce eh Hauwa na nan,ni yanzu zan fita ne,anjima na dawo na dauke ta. Hajiya ta ce adowo lfy,Hauwa ce ta raka shi su ka kwantar da Inna,bayan ya kwantar da ita ya jawo ta jikin sa,yayi kissing goshi ta tare da fadin worry nt baby-luv,ke ma very soon za ki haifa min mai kama da ke,so ko an hana mu Inna,ba fata na ke ba,kar ki damu owk? Hauwa ta murmusa ta ce owk Beb,Allah ya amsa. I love you big,ya yi hugn din ta tare da fadin I love you more. Hannun ta cikin na sa ta raka shi har mota.
DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group)
[7:23pm, 5/31/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭
3⃣7⃣
Da Hajjo ta dawo ta tadda Hauwa cikin girmamawa ta gaishe ta,ita kan ta Hauwa ta yi mamakin yanda Hajjo ta canza she is realy transforming,ga kyau ga touch of wayewar da boko ya fara ba ta. Tare da Hajiyar Hauwa ta yi wa Hajjo zancen Inna,amma Hajiya ta ce kar ta ji nauyi,idan ba zai yiyu ba ta fada diyar ta ce,ba wanda ya taya ta wahalar kawo ta duniya. Hajjo ta ce toh su bari ta je Kumurya ta fadawa yayar ta,duk yanda su ka yi sai ta fada ma su. Amma har ran ta ba ta san a raba ta da diyar ta har zuwa wani kasar. Da haka su ka rabu washagari da safe Hajjo da Inna su ka hau motar haya sai gasu a Kumurya.
Ita dai Indo zancen dadi ya ma ta,ta ce ke Hajjo wannan abu ai ba wanda za a ki ba ne,da ki aje diyar ki a wannan kauye ta tashi ba wani ilimin kirki da rayuwa mai inganci ai gwara ki dankata amana inda za ta sami rayuwa mai kyau da inganci,kin san dai mutanan nan mutane ne ma su kirki da aminci,wlh kawai ki yarda a tafi da ita…Salama alaikum! Sallama ce ta katse Indo,jin muryar mai sallamar tini Hajjo ta mi ke,ta suri Inna su ka buye bayan kofa. Sallamar aka kara dokawa,