Showing 1 words to 3000 words out of 64514 words

Chapter 1 - BONONO BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MAMAN AFRAH f.pdf

30 Mar 2025

5087

[2/5, 8:11 AM] MOM MASHKUR & AFRAH: *BONONO*


(RUFIN ƘOFA DA ƁARAWO)


NA


MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.


*SADAUKAR*

Daga farko har ƙarshe sadaukarwa ne ga MARYAM HAFIZ (Merry tah) Alkairin Allah ya kai
gare ki Allah lulluɓe rayuwar ki da tarin ni,imomi da albarkatu Allah raya mana Abdallah fatan
alkairi.

Daga marubuciyar:

Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Ƴar zaman wanka
Da sauran su.



PAGE 1


Da tsananin murna da farin ciki nake hango shi jingine da motar da ya zo ɗaukana saboda a
yau ne muka kammala karatun mu na secondry school da yake boarding school nake yi. Sai dai
ina jin mummunar faɗuwar gaban da take neman ta kawo mini cikas, a gabaɗaya tarin kalaman
da na yi ta shiryawa zan yi amfani da su wajen tona masa asirin zuciyata, ina tunkarar sa bugun
zuciyata yana tsanan ta. Duk da ina jin tsoro da fargaba a kan hakan amma dai na shirya
tunkarar komai don na mallakawa zuciyata wanda take da buri, kuma shi ne dai wanda ta daɗe
tana dakon soyayyar sa haka kuma tun zuciyata tana jaririya na raine ta da soyayyar Yaya
ABDULHAKEEM sai dai kash!. Ban taɓa furta masa ba.

Yau kwana na yi ina tufka da warwara ina saƙar jaki a kan irin yadda zan furta kalaman tun jiya

da Abba ya faɗa mini a waya cewa Ya ABDUL ɗin ne zai zo ɗauka ta .

"Oyoyo Ya ABDUL" Na ce ina ƙanƙame shi ta baya da yake ya bani baya ne, ina sakin jakar da
na riƙo a hannuna don shi bai ma san na zo wajen ba hankalin sa yana ga waya.

"Oyoyo HEEDAYA" Ya ce yana raba ni da jikin sa idanun sa kafe a kaina.

"Ya ABDUL" Na ce ina jin wani yanayi na yadda ya kira sunan nawa sai in ke ji kamar duk
duniya babu wanda yake kiran sunana in ji ya iya faɗa, tare da ba kowane harafi haƙƙin sa
sama da Ya ABDUL.

"HEEDAYA an girma an kammala school" Ya faɗa yana riƙo hannuna tare da lakato hancina,
idanuna na lumshe kafin na buɗe su tarrr na sauke a kan kyakkyawar fuskarsa da kullum take
mini gizo tamkar ranar na fara ganin ta. Hannu na miƙa na ɗauki jakar sakin hannun nawa ya yi

Sai da muka gama saka kayan nawa gabaɗaya a but ina ta masa mitar bai zo ɗaukana da
wuri ba, duk yawanci ƙawayena sun tafi, haka dai muka yi sallama da sauran da suka rage
wanda ba a zo ɗaukan su ba, na shiga motar muna ɗagawa juna hannu cike da kewa.

Hanya ya nausa motar muka kama tafiya domin zuwa garin namu mai suna Dutse, dama a
garin Gumel nake karatu. Tun da ya fara tafiya motar ta yi tsit baka jin komai sai ƙaran A.C
tafiya muke yana tuƙi cike da nutsuwa. A hankali na waiga na saci kallon fuskarsa gabana ya
yanke ya faɗi ganin tamkar duk shaƙuwata da shi ina jin nauyin furta masa kalmar so.
Kasancewar Ya ABDUL ɗan gidan ƙanin mahaifina sannan gidanjen mu sun kasance maƙotan
juna. Tun ina ƙarama ta na taso cikin kulawar sa saboda ya kasance mai son yara, zan iya
cewa bayan iyayena a duniya babu wanda ya kai Ya ABDUL da Aunty RABEEYA sona da nuna
mini kulawa Aunty RABEEYA uban mu ɗaya da ita sai dai kowa da mahaifiyar sa.

"Bakin surutu dai yau ya mutu mus, ko duk kewar rabuwa da ƙawayen ne?" Ya ce yana ɗan
waiwayo ni tare da sakar mini murmushi. Ni ma kaina na samu da sakin murmushin amma na
yaƙe wanda iyakar sa fatar baki, saboda yadda zuciyata take cike da son furta kalaman da suke
nuƙurƙusar ta.
"Ya ABDUL, ina so na yi maka magana" Na faɗa gabana yana faɗuwa. Rage gudun ya yi, tare
da ɗan kallona kafin ya mayar da kallon nasa bisa hanya ya ce


"Ina jin ki" Shiru ya biyo baya kalaman sun yi tsauri wajen furtawa, nauyi da kunyar sa nake
amma ina gani wannan ce damar da nake da ita in furta masa daga ni sai shi a yau ba sai gobe
ba, saboda na san ƙa'idar Abban mu daga ka gama secondry school yake maka aure gwara in
tanadi mijina a hannu kar in je in zauna a gida irin na Aunty RABEEYA.
"Baka mini kayan candy ba" Na samu kaina da furta hakan ba don haka na yi niyyar faɗa ba

sai don na rasa ta inda zan fara ina son gane bakin zaren amma kuma na kasa, nauyi da
kunyar sa nake ji.

"HEEDAYA yanzu kayan candyn ne kike faɗa dakyar ai kin san ke ta hannun damana ce, na
shirya miki abin da zai faranta miki, kin san na je india lokacin da ya kamata na yi miki
abubuwan da za ki rabawa ƙawaye, jiya na dawo amma na ce ni zan ɗakko HEEDAYANA" Ya
faɗa yana sakin murmushin nan da yake narkar da zuciyata. Wani daɗi ya baibaiye mini ruhi a
rayuwa ina son ya ce mini HEEDAYAR sa duk da ba da manufar soyayya irin ta aure yake faɗar
hakan ba amma hakan yana daɗaɗa raina fiye da tunanin mai tunani. Na sani cewa yana ji da
ni kowa ya san hakan a family namu, tun ina mitsitsiya ta wajen sa ne wurin share kuka na shi
ne mai lallashi da lallaɓa ni idan ina kuka, wani lokacin ya saɓani a kafaɗar sa har sai na yi
bacci sai dai bai san cewa tun wannan ƙaunar da shaƙuwar da na yi da shi daga lokacin da na
yi wayo komai ya canja na yi nutso a kogin son sa tamkar dai a rijiya mai gaba dubu da za ta yi
wuyar fitowa.

Ta nuna masa farin ciki da jin daɗin furucin sa, amma ba haka aka so ba ƙanin miji ya fi miji
kyau!. Har suka shigo garin Dutse tana jin takaicin rashin sanar da shi ƙudurin ta. Suna shiga
get ɗin tangameman gidan nasu tun kafin ya gama parking ta hango Aunty RABEEYA ta taho
da murnar ta, sai dai HEEDAYA tana fitowa ta juya mata baya tare da zunɓuro baki alamar ta yi
fushi.

"HEEDAYATA!" Aunty RABEEYA ta furta lokacin da ta ƙaraso ta rungume HEEDAYA amma ta ƙi
cewa komai.

"Ya ABDUL wa ya taɓa mini ƴar lele"

"Ba ruwana kun fi kusa" Ya ce yana dariya tare da buɗe but ɗin lokacin har Na'eema,
Mubashshar, da Ihsan sun fito domin taryarta.

"Bake ba ce kika ƙi bin Yaya ɗakko ni"

"Ayya sorry kin ji na tashi da ciwon kai ne sannan Ya ABDUL ɗin ne ya sa mu zauna don shirya
abubuwan da za a tarɓe ki amma a yi wa Aunty afwa" Ta faɗa tana rausayar da kai gefe.
Murmushi ta saki tana rungume Aunty RABEEYA tana jin ƙaunar ƴar uwar tata duk da iyayen su
mata basa jituwa kuma basa son ƙaunar nan da take tsakanin ƴaƴan.
Kayan nata suka ɗauka aka nufi cikin gidan kowa yana murna Ya ABDUL bai shiga gidan ba
sai ya juya ya tafi gidan su domin zuwa ya watsa ruwa.

Suna shigowa har lokacin hannun ta sarƙe da na Aunty RABEEYA, da Hajiya Baturiya
mahaifiyar su Aunty RABEEYA suka fara cin karo ta fito daga part ɗin ta riƙe da plate za ta nufi
part ɗin Abba. Tun daga nesa ta fara aikawa da HEEDAYA mummunan kallo na tsantsar tsana.
Ita ma ramawa ta yi a fakaice ba tare da ta bari Aunty RABEEYAR ta gani ba don sauran

ƙannen nasu tuni sun riga su yin part ɗin Hajiya Zainab mahaifiyar su HEEDAYA. Amma a fili
ganin sun zo dab da juna cikin kissa da nunawa Aunty RABEEYA girmama mahaifiyar ta sai ta
ce.

"Momma ina yini" Ko kallo bata ishe ta ba don dama tana zuwa dab da su ta ɗauke kai bayan ta
jefawa Aunty RABEEYA tata harara na ganin ta da HEEDAYA.Ɗan jim HEEDAYA ta yi na
alhinin abin da Momma ta mata.

"To mene ne na damuwar? Ai in da sabo kin saba da halin gidan mu, ba za su taɓa canjawa ba
suna nan a yadda suke sai dai mu tun da Allah ya haɗa kanmu ai ba za su raba mu ba,
HEEDAYA babu abin da zai raba ni da ke babu abin da zai kankare ƴan uwantaka ta jini da
nake miki ina ƙaunar ki zan iya sadaukar da komai a rayuwa ko mene ne in har zai saka ki farin
ciki" Aunty RABEEYA ta faɗa tana sakar mata murmushi kasancewar ta fi ƙaunar HEEDAYA
sosai a kan ƙanwar ta Na'eema wacce suke ciki ɗaya.

Sai da ta raka ta har ƙofar falon Hajiya Zainab wacce suke kira da Umma, sannan ta dakata
ba don ta so ba za ta juya, riƙe mata hannu ta yi ta ce

"Haba Aunty ya za ki dakata daga nan mu je ki raka ni mana har ɗakina" Ta ce tana zumɓura
baki.

"Zan je mu ƙarasa haɗa miki kayan tarɓar da muka shirya miki ni da Yayan ki" Ta faɗa tana
kallon ta, ba don ta gamsu ba ta saki hannun ta suna yi wa juna murmushi, Aunty RABEEYA
tana juyawa HEEDAYA ta shige falon da gudu cike da murna da farin cikin dawowa gida
gabaɗaya, ba da sunan hutu ba don ta tsani boarding school ɗin nan kawai don ba yadda za ta
yi ne ta san halin Abban su idan ya ce kulle dole ne mutum ya ce casss ko ba ya so. Su ma su
Umma abubuwan da suke yi tsakanin su da na yaran sai a bayan idanun sa ne suke yi a gaban
sa sai su dinga kissa da kisisina sai dai ɗan abin da ba a rasa ba.


Da murna suka rungume juna ita da Umma, bayan nan ta zauna suna ta hira ita da
Mubashshar da Ihsan. Ɗakin ta ta nufa ta shiga don ta watsa ruwa har ta cire kayan, ta ɗauki
towel ta ɗaura za ta shiga banɗakin sai ta nufi jakarta da aka shigo mata da su, ɗaukan jakar ta
yi ta fito da hoton Ya ABDUL ta tsaya kallo tana rayawa a ranta.
'Da sannu ba da gajiyawa ba zan sanar da kai sirrin da yake raina, ina son ka ina mugu-mugun
kishin ka, zan iya komai a kan ka zan iya fafatawa da kowa a kan ka, babu wata da zan bari ta
raɓe ka idan kuwa wata ta yi gigin yin hakan sai na koyar da ita darasin da har ƙarshen rayuwar
ta ba za ta manta ba' Ta faɗa tana sakin murmushi tare da shafo hoton ta mayar da shi cikin
jakar ta ajiye ta shiga wankan tare da ɗauro alwala ta fito. Shiryawa ta yi ta saka doguwar riga
sanna ta yi sallah. Wajen ƙarfe biyar Aunty RABEEYA ta zo part ɗin su riƙe da wata ƙatuwar
leda, ko da ta samu Umma a babban falo ta gaishe da ita ko kallon arziƙi bata samu ba bare ta
saka ran za ta amsa sai ma nuna mata hanyar waje da ta yi tana cewa

"To baƙar munafuka annamimiya wato ƴata ta dawo za ki fara mini diddibtun munafurci kina nan
zaune a gida ke ba karatu ba ke ba auren ba, kin rasa mashinshini ga shi nan har ƙanwar
bayanki ta gama karatu ta dawo gida za ku jera har ma ta samu miji ta tashi, to kar ki kuskura ki
zo ki goga mata baƙin jini irin naki ta rasa mijin aure ko ki hure mata kunne" Umma ta faɗa cike
da bala'i. Ihsan da fitowar ta kenan ta samu wuri ta zauna tana taɓe baki ta ce.

"Umma ni ma da nake zuwa day school yanzu saura shekara biyu na kammala"

"Yo ai sai ku duka ku tashi kun barta sai dai ko Alhaji ya bada sadakarta don bana jin za ta
auru" Kai Aunty RABEEYA ta sunkuyar tana jin ƙunci da raɗaɗin maganganun da take ji tamkar
ana watsa mata ruwan dalma a zuciya, duka shekarun nata ashirin da ɗaya ne fa, kawai don
dai Abba ba ya bari a cigaba da karatu sai dai mutum ya yi a gidan miji shi ya sa ake ganin
hakan amma da karatu take zaman gidan ma ba zai gundure ta ba bare har ake ganin ta kasa
samun miji duk da samarin suna ziryar zuwa amma dai daga ta musu maganar aure sai su
daina zuwa ita ma bata san mene ne dalili ba sai dai ta san Allah ba ya bacci kuma yana sane
da ita. HEEDAYA da take ɗakin ta tana gyara kayanta take jin tashin maganganu a falo hakan
ya sa ta fito tana fitowa ta ga Aunty RABEEYA ta juya za ta fita, da sauri ta ƙarasa tana kiran
sunan ta tare da riƙo hannun ta, cak ta tsaya sai dai bata juyo ba kuma bata ɗago fuskarta ba
sai hawaye da yake tsiyaya.


"Haba Umma kin san dai ai wurina ta zo ko? Ko don ƙaunar da take mini ta cancaci ta samu
rangwamen wasu abubuwan daga gare ki" HEEDAYA ta faɗa tana kallon Ummar, tare da
juyawa ta shiga aikawa Ihsan saƙon harara.

"To uwata faɗa mini abin da ban sani ba, ke ai wawiya ce don ana nuna miki farin haƙori shi ya
sa kike ganin soyayya ce, bayan ta ciki na ciki so take ta gama shiga jikin ki sai ta ida nufinta, in
kin manta in tuna miki ƴar kishiyata ce fa, an faɗa miki kishi wasa ne? Ko an faɗa miki ƙiyayyar
kishi wasa ce, za su iya duk yadda za su yi su shiga jikin mu kafiin cim ma burin su"
"Haba Umma bai kamata ba wanna abin da kike tun ban kai haka ba take nuna ƙaunarta da
kulawar ta gare ni, da a ce tana da wani nufin a ganina da ta daɗe da bayyanawa...

"Ga shi in ji Ya ABDUL sarƙa da ɗankunne da agogon ni na baki, ki shirya ki same mu a gidan
Ammie" Aunty RABEEYA ta faɗa cikin muryar kukan da ta kasa dannewa.

"Aikin banza shi ma ABDULHAKEEM ɗin ai munafuki ne, ai wallahi tun da uwar sa ta
munafurce ni to babu yarda tsakanina da shi gabaɗayan ku lumbu-lumbu ne wutar ƙaiƙayi bata
kama ba ta haɗe wuri da hayaƙi" Umma ta faɗa tana jin zafi da raɗaɗi a zuciyarta kasancewar
ta uwar gida, sannan kafin a auro Momma mahaifiyar su RABEEYA wacce ita ce amarya, to
Umma bata da ƙawa kuma abokiyar shawara sama da Hajiya Fati wato mahaifiyar ABDUL
kamar ba facaloli ba haka kan su yake a haɗe, amma daga bisani da aka auro Momma suka yi

wani rikici da Ammien da Umma shikenan sai alaƙa ta ɗinke tsakanin Ammie da Momma aka
dawo ana zaman doya da manja da Umma da Ammien wannan dalilin ne ya sa Umma ta tsani
ABDUL gabaɗaya bare kuma RABEEYA da dama kishin da yake tsakanin iyayen yake tasiri har
kan ƴaƴan su.

Kowa ya tsani ɗan kowa, basa duba zama ya haɗa, ƴaƴa sun girma babu wacce za ta fitar da
kowacce amma kullum kishi yana nuƙurƙusar su sun kasa ba zuciyar su haƙuri su yi zama cikin
salama da aminci.

Aunty RABEEYA bata jira cewar HEEDAYA ba ta damƙa mata ledar ta juya da sauri jin kuka
mai sauti yana neman ƙwace mata. HEEDAYA rasa bakin magana ta yi ta juya fuuuu fa tafi
ɗakin ta. Duk da tana jin abin da aka yi wa Aunty RABEEYA har ƙasan ranta amma jin wani
sassanyan daddaɗan turare mai narkar da zuciya ya ziyarci hancin ta gabaɗaya sai ta shagala
da son ganin turaren tun da dai in aka ɗauke sarƙa da ɗankunne da agogo sauran duk Ya
ABDUL ne ya bata kenan turaren nan daga gare shi ne.

Wasu turaruka ne guda uku masu bala'in ƙamshi sannan daga ganin su masu tsada ne, sai
wani leshi da aka yi wa riga da skirt ɗinkin ya tsaru daidai jikin ta da mayafin su, sai takalmi sai
kwalin waya iphone 16 sai kuma sarƙa da ɗankunnen da agogon wanda Aunty RABEEYA ta
bata. Daɗi ya cika mata zuciya a duniya in akwai kyautar da ta fi so ita ce ta Ya ABDUL sai
kuma ta masoyiyar ta Aunty RABEEYA.

A gaggauce ta shirya, kayan sun yi matuƙar karɓar ta, wayar ta jona a caji bayan ta mayar da
sim ɗin ta na cikin wayarta da take amfani da ita idan ta zo hutu. Fitowa ta yi tana buɗaɗa
ƙamshi, lokacin da ta fito babu kowa a falon sai TV tana aikin ta. Duk can ta samu sauran ƴan
uwan nata har da Ya ABDUL da ya shirya shi ma ya yi matuƙar kyan da ya sa ta shagala da
kallon sa, bata ba kanta wahala wajen shiga gaishe da Ammie ba don ta san ko ta je ma dakyar
ta amsa. Ƙwarya-ƙwaryar fatin da aka shirya mata na kammala karatun wanda ya faranta ranta
matuƙa, har da ƙaton cake aka mata mai ɗauke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login