Showing 18001 words to 21000 words out of 64514 words

Chapter 7 - BONONO BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MAMAN AFRAH f.pdf

30 Mar 2025

5090

dinner haka ce ta kasance duk inda amarta da ango suke ƙafar su
ƙafar HEEDAYA.

Ranar asabar wacce ta ita ce ranar ɗaurin aure. Tun da sanyin safiya Umma da HEEDAYA
suke ƙusƙus suna tsara yadda komai zai kasance, wato yadda za ta kai wa Aunty HEEDAYA
abin da za ta ci riƙa da layar maganin a hannun ta. Ƙarfe sha ɗaya da rabi shi ne lokacin da za
a ɗaura aure.
"HEEDAYA ki fara zuwa ki dubo inda take ki tabbatar tana nan kuma kin ga dai yadda gidan
nan yake a ciki ki tabbatar babu wanda kika yi wa magana" Umma da ta jata cikin banɗakin ta
take raɗa mata don ma kar wani ya yi laɓe a ɗaki ya ji su.

"To Umma bari na sake dubowa ɗazu dai na hango shigar ta part ɗin Abba Hajja ce a can take
kiran ta "HEEDAYA take tabbatar mata da ta ga Aunty RABEEYA ta je wajen Hajja kakar su
mahaifiyar Abba.

"Umma bari na je tana part ɗin Abba ita kaɗai tana zaune Hajja ta zaunar da ita, ita kuma Hajjar
ta je ta ɗakko wani turare za ta shafa mata a goshi wai haka ƴan da suke yi zamanin su Hajj...

"Ba dogoj surutu za ki tsaya ba tun da Abban naku sun fita ki yi sauri ki je ki aiwatar" Umma ta
katse ta don yanzu hankalin Umma gabaɗaya a tashe take ta fi so har sai an aiwatar da aikin
nan na ƙarshe tun da an gama na duka ganyen. Da sauri HEEDAYA ta zaro layar daga ƙugunta
da ta soke ledar, fito da layar ta yi ta damƙe tare da ɗaukan cake guda ɗaya ta fito daga part ɗin
Umma tana ta sauri sai gifta mutane take ana mata magana amma babu wanda take tankawa
hankalin ta ya yi part ɗin Abba. Zaune ta samu Aunty RABEEYA tana danna waya cake ɗin ta
miƙa mata ba tare da ta ce komai ba, Aunty RABEEYA cike da jin daɗin kulawar da HEEDAYA
ta mata ta miƙa hannu ta karɓa ta sanya a baki ta fara ci sai da ta cinye. Ganin haka HEEDAYA
ta juya da sauri ta nufi bayan gidan ta haƙa rami ta binne layar ta taso ta baro wajen. Ɗakin
Umma ta nufa tana zuwa ta rungume Umma da suke tare da Hajiya Aisha gabaɗaya daga
Hajiya Aisha har Umma su ma rungume ta suka yi cike da murna don sun san aiki ya kammalu
saura jiran sakamako.

"Ayyiriri-yiriyiri!!!." Hajiya Aisha da Umma suka rangaɗa guɗar farin ciki wanda hakan ya jawo
hankulan gabaɗaya ƴan falon sai dai babu wanda ya nufi ɗakin sai Aunty Hafsa tana buɗe ƙofar
suka haɗe rai Umma ta shiga jefa mata harara siyam-siyam ta juya bayan ta girgiza kai alamar
basu kyautawa!.

Ƙaran tsayawar motocin ƴan ɗaurin aure da yake a babban masallacin juma'a aka je aka
ɗaura da kiɗan ganguna haɗe da muryoyin maroƙa da suke tashi cikin lasifika. Ita ce ta assasa
faɗuwar gaban mutane uku da mugun ƙarfi Umma, Hajiya Asha da kuma mai gayya mai aiki
wato HEEDAYA a yanzu babu abin da kunnuwan su suke son ji sama da jin an ɗaura auren
HEEDAYA da ABDUL duk da sun san babu makawa yin hakan tun da sun tabbatar da ingancin
aikin da aka yi kuma an aiwatar. Amma duk da haka suna jin fargabar sakamakon!.

Muryar wani maroƙi da ya durfafo cikin gidan suka baza kunnuwa kamar na zomo suna son jin
da wa aka ɗaura?

"Allah ya kawo mu, aure ya ɗauru tsakanin ABDULHAKEEM Mukhtar da amaryar sa...



MAMAN AFRAH
09013181851
[2/10, 2:13 PM] MOM MASHKUR & AFRAH:
https://chat.whatsapp.com/F7TUZezpOWLKYnyTNFuy2Y



BONONO


(RUFIN ƘOFA DA ƁARAWO)


NA


MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.


*SADAUKAR*

Daga farko har ƙarshe sadaukarwa ne ga MARYAM SANI HAFIZ (Merry tah) Alkairin Allah ya
kai gare ki Allah lulluɓe rayuwar ki da tarin ni,imomi da albarkatu Allah raya mana Abdallah
fatan alkairi.

Daga marubuciyar:

Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Jalli joga
Da sauran su.
*09013181851*



PAGE 6


Su duka ukun sai suka yi tamkar an dakatar da gudun numfashin su, domin kuwa kowanne
sai ya yi tamkar za a sanar da mutuwar wani makusancin sa duk sun shiga mummunan yanayin
son jin sunan wanda maroƙin zai ambata.

"Tsakanin ABDULHAKEEM Mukhtar da amaryar sa RABEEYA Bashir" Wannan furucin maroƙin
ya daki gabaɗaya ƙwaƙwalwa da zuciyar su Umma, lokaci guda kunnuwan su suka yi dumm ya
zamana sun daina jin kowane sauti. Amma saboda ƙarfin hali sai suka fara kokwanton abin da
suka ji kowanne sai yake ganin ba daidai kunnen sa ya jiyo masa ba, kowanne yana jin kawai
dai tsabar son jin abin da za a faɗa ne ya sa suka shiga ruɗani.

Kallon - kallo suka shiga jifan junan su da shi kowanne yana son ɗan uwan sa ya bashi
tabbacin gaskiyar abin da kunnen sa ya ji.

"Auren masoya kuma ƴan uwa an yi auren zumunci ABDULHAKEEM da RABEEYA Allah kawo
mu ranar suna" Suka ƙara jin furucin maroƙin daga lasifikar nan irin wacce maroƙa suke yawo
da ita a hannu.

Idanu Umma ta zaro da sauri ta tashi tsaye tana yaƙi da hankalin ta ganin bai gudu ya barta ba
don ji take tamkar dai ƙwaƙwalwar ta za ta samu taɓuwa saboda furucin da ta saurara mai cike
da ruɗani!. Lokaci guda kuma HEEDAYA da hawaye ya wanke mata fuska take fusgo
numfashin ta dakyar suka miƙe ita da Hajiya Aisha.

"Na shiga uku Umma!." HEEDAYA ta faɗa jikin ta yana karkarwa ƙirjin ta yana wani hawa da
sauka.

"Mun shiga uku dai!" Umma da Hajiya Aisha su ma suka faɗa hankali tashe.

"Hajiya Aisha ashe bokan nan maƙaryaci ne? Mu zai yaudara? Ya sa muka saki jiki da aikin sa
ashe ƙarya ya zabga, da a ce na san aikin sa ba zai yi ba da tuni ko a bangon duniya ne sai na
je na samo magani, amma ya sa sai da ranar ta zo lokaci ya ƙure ga shi babu dama ko hali
yarinyar nan su haɗa miji tun da uban su ɗaya, kin san dai ko a garin mahaukata HEEDAYA ba
za ta auri mijin RABEEYA ba" Umma ta faɗa tana kallon Hajiya Aisha tamkar za ta kai mata
dukan tsiya saboda kawai haushin ta take ji don ranta ya yi mugun ɓaci.


"Hajiya Aisha ta ce

"Hajiya Zainab kin san dai ba zan kai ki in da bani da tabbas ba, kin fi kowa sanin na san
kusufa-kusufa lungu da saƙo na malamai da bokaye masu aiki tamkar yankan wuƙa" Duk
maganganun nan da suke HEEDAYA tana tsaye tamkar zautacciya ta rasa wane kalar tunani za
ta yi gabaɗaya bata gane mai suke cewa tamkar wata taɓaɓɓiya haka ta koma, basu ankara ba
sai gani suka yi luuu ta yanke jiki ta faɗi sumammiya!.


A kiɗime suka durƙushe a gaban ta suna jijjijgata, Hajiya Aisha ganin Umma ta fara kuka
hankali tashe da gudu ta nufi banɗaki ko takalmin ƙofar banɗakin bata saka a ƙafar ta ba, ruwa
ta kwalfo a kofin wanka ta fito a ruɗe tana zuwa ta sheƙawa HEEDAYA. Farfaɗowa ta yi a firgice
tana faɗin
"Na shiga uku Umma wata ta auri zaɓina, Ya ABDUL ba ni ba wayyo zan mutu ba da ni aka
ɗaura ba wayyo na gama yaudarar zuciyata yau zan kasance a gari ɗaya, a unguwa ɗaya a
gida ɗaya kuma a ɗaki ɗaya da Ya ABDUL ashe dai mafarki ne burina ba cika zai yi ba" Ta furta
cikin kuka.
"HEEDAYA ki yi haƙuri na yi iya yina ban taɓa zaton hakan ba zai cika ba wallahi ban taɓa
kawowa aikin nan ba zai ci ba, gabaɗaya na saki jiki da cewa an ɗaura da ke an gama ban san
za a samu akasi ba ban san za a samu saɓanin tunanina ba HEEDAYA" Umma ma ta faɗa tana
hawaye tana tuna cewa shikenan zumuncin ƙawancen Hajiya Fati da Hajiya Baturiga zai ƙara
ƙarfafa, ashe dai duk shirin su ya tashi a banza da siyen kayan ɗaki da na kicin da komai da
komai ba ma wannan ne abin jin ba sai magungunan matan da suka ɗirkawa HEEDAYA don
sun ɗauka yau za ta kwana gidan miji ashe dai lisaafi da hasashen su ne.

"Na tsane ta Umma na tsani Aunty RABEEYA na tsane ta wallahi"

"Ni ma na tsane ta HEEDAYA da a ce ya halatta ku auri miji ɗaya da wallahi ko ta halin ƙaƙa sai
na samo mafitar da sai an ɗaura da ke, sai kin rigata shiga gidan sai dai ta zo daga baya amma
ke ce uwar gida dole ta zauna a ƙarƙashin ki sai dai kash!. Bakin alƙalami ya bushe f...

"Umma ki daina ambaton auren miji ɗaya ni fa bani da kishiya a duniya ba zan taɓa zama da
kishiya ba a rayuwata mijina ni ce amaryar sa kuma ni ce uwar gidan sa " Ta faɗa cikin kuka da
tashin hankali.

"Ku yi haƙuri don Allah dole mu samu mafita a yau kuma a yanzu!" Hajiya Aisha ta faɗa tana
tashi tsaye tare da kama ƙugu da hannu biyu tana ɗaga kai sama irin tana tuna yadda komai zai
wakana. Kallon baki da hankali Umma ta jefe ta da shi tana kawar da kai wani tuƙuƙin baƙin ciki
yana ƙara ratsa zuciyar ta, don tana ganin ita ce silar komai da ba don ta kai ta wajen da ta
karɓo maganin ba, da bata ma saka ran cim ma buri ba daga ita har HEEDAYA.

"Dole ne ya san abin yi don a yanzu ba sai an jima ba za mu koma wajen sa"

"Wai maganar wa kike? In dai wannan tsohon ne na yafe aikin da ya mana a kwana ashirin da
bakwai ma bai yi ba sai wanda zai yi yanzu ai bakin alƙalami ya bushe, tun ran gini tun ran
zane, kin san dai an riga an ɗaura auren nan kuma ya haramta su aure shi su biyu kasancewar
su jini ɗaya...
"Haba ƙawata ki daina mini magana cikin hargagi kina neman ɗora laifi a kaina bayan ni ma
burina da fatan bai wuce irin naki burin ba"

"Na ji! Yanzu mene ne abin yi?" Umma ta tambaya tana ɗago kai ta kalle ta har lokacin tana
rungume da HEEDAYA da take ta shashshekar kuka tamkar ranta zai fita irin yadda sautin
kukan yake fitowa daga asalin ƙarƙashin zuciyar ta.

"Za mu koma wajen malam"

"Ki kira shi da sunan sa na asali kuma na yanka wato boka don wannan bashi da haɗi da
malamai"

"To na ji! Mu koma wajen boka shi zai faɗa mana komai "

"Ni ban ga amfanin komawa ba tun da wuri ya ƙure!" Cewar Umma.

"Ki ƙara bani dama!"

"To shikenan amma kin san yanzu waje cike yake da jama'a kina ji sai kaɗe-kaɗe da
bushe-bushe yake tashi shin idan ma Alhaji ya gan mu in ce ina zan je tun da dai ya san ana

taro ba za mu je ko ina ba bana son ya ɗora zargin sa a kan mu"

"In sha Allah ba zai gan mu" Ba don Umma ta gan su ba ta amince haka ta lallaɓa HEEDAYA a
kan cewa ta daure za su je su dawo a kan gadon ta kwanta kamar matacciya suka fito suka rufo
mata ƙofar. Yadda gidan yake a cike amma su hankalin su ba ya kan kowa hankalin su ya yi
wajen bokan su.


Lokacin da suka fito cike da fargabar kar Abba ya gan su amma sai suka samu motocin suna
ta ɗaukan ƴan ɗaurin auren zuwa wajen da aka tanada don cin abincin ƴan ɗaurin auren. Don
haka Abba ya shiga mota shi ma daga can suka hango tsayawa suka ɗan yi duk motocin suka
yi gaba sai ragowar wanda ba a ɗauka ba da maroƙa da almajirai haka da kuma yaran anguwa
da suka zo. Motar Hajiya Aisha suka shiga ta fige ta 360 suka kama hanyar barin cikin garin. A
daidai inda suka yi parking ranar nan yau ma a wajen suka yi bayan sun sha kwaɗa ihu kamar
wasu sabbin ƴan tauri, ya amsa musu da ihun sannan suka shiga da baya. Kan su suka yi wa
mazauni a gaban sa Umma da take cike fam da haushin sa don ranar nan girman sa take gani
amma yau sai ta ji ya faɗo wanwar a gunta sheƙeƙe ta kalle shi cikin raini da izgilanci za ta fara
magana don a ganin ta ha'intar su ya yi ya cinye kuɗin su amma babu biyan buƙata ga shi ya sa
sun ɓata gishirin su a dahuwar ƙaho da tuni sun nemi mafita amma yanzu ya sa wuri ya ƙure!.

" Dakata!. Bana son jin bayani tuni na san komai" Ya faɗa yana ɗaga mata hannu. Wani kallon
da wa muka zo ta masa, ba don ta so ba ta kama bakin ta ta masa ɓam a hakan ma don Hajiya
Aisha tana tausar ta da ido amma duk da haka ta ci alwashin matuƙar ya raina musu hankali da
shaci faɗin sa to tabbas sai ta masa wankin babban bargo ba wai a kan kuɗin ba ita damuwar ta
rashin cikar burin nasu a kan aikin!.

"Ba ma aiki a zo da maganar banza! Mun fi ƙarfin a tuhume mu, mutum ya tabbatar ya aiwatar
da komai cikin hikima kafin ya zo mana da maganar banza matsawar aka samu tangarɗa ba a
bi sharaɗi ba to dama ba za a samu yadda ake so ba shi ya sa ma na gargaɗe ku na nannaga
muku sharaɗin don ku kiyaye! Amma sai da aka samu matsala" Ya faɗa lokacin da yake kallon
cikin ƙwaryar gaban sa.

Wani kallon rashin fahimtar inda zancen sa ya dosa suka shiga jefa masa kafin Umma ta ce

"Wallahi boka ta aiwatar da komai yadda ka faɗ...

"Ƙarya ne!." Ya faɗa a harzuƙe yanayin yadda ya yi maganar a tsawace cikin wata murya ya da
suka razana don Hajiya Aisha har ta kai bakin ƙofa babu shiri, ita kuma Umma ta tashi tana
neman faɗuwa tsabar tsoratar da suka yi don sai suka ji maganar har amsa kuwwa ta yi, duk
zaton su ma aljannun da yake aiki da su zai kirawo musu. Sun san kuwa karo da aljani ba
sauƙi.

"Ku dakata kar wacce ta fita" Ya faɗa wannan karon sai suka ji muryar sa ta sauya daga ta
dattijo zuwa muryar saurayi. Da karkarwa suka dawo suna mamakin yadda suka tsorata haka,
kowacce mazaunin ta ta koma tana rarraba ido.


Da ido suka kafe shi ganin yana yin wani rubutu a kan ƙwaryar da take da wani abu kamar
madubi. Kamar daga sama sai suka ga HEEDAYA ta bayyana a cikin madubin. Kallon kallo aka
shiga yi tsakanin Umma da Hajiya Aisha saboda kowacce cikin su ta tabbatar HEEDAYA ce
sanye da kayan da suka baro ta a gida, kafin su mayar da kallon kan ƙwaryar tana sanye a cikin
ta, ta fito tana ta waige -waige kamar marar gaskiya. Baki a sake suke kallon ta tarwai tamkar
su ɗakko ta ko su mata magana ta amsa don tamkar bidiyo haka suka gani. Part ɗin Abba ta
dosa tana ta faman waiwaye, su duka gaban su ne yake faɗuwa don basu gane inda bidiyon ya
dosa ba, duk a zaton su yanzu bayan sun baro ta ne ta ware daga damuwar da take har ta fito
amma dai suna son ganin mai yake son nuna musu ita Umma a zuciyar ta ma tana taraddadin
kar ya cutar mata da ƴa tun da ta ji yana batun an masa ƙarya.

A falon Abba suka hango ta sai kuma Aunty RABEEYA zaune a kujera, tana hango shigowar
HEEDAYA ta washe baki cike da murnar ganin ta, da haka suka ga HEEDAYA ta nufi wajen ta
ba tare da ta ce komai ba ta miƙa mata abu sai da ta karɓa suka gane cake ne sai lokacin suka
gane ashe lokacin da ta tafi aiwatar da aikin layar nan ne. Idanu suka ƙara zubawa ganin Aunty
RABEEYA ta karɓa tana ci hankalin kwance sai kallon HEEDAYA take tana mata murmushi mai
cike da so da ƙauna. Sai da ta cinye suka ga HEEDAYA ta juyo ta fito a wajen part ɗin ne suka
hangi Daddy(Alhaji Mukhtar Daddyn ABDUL ) Ya nufi part ɗin yana ta baza babbar rigar kiciɓus
suka kusa yi da HEEDAYA.

"HEEDAYA, HEEDAYA, HEEDAYA" Ya shiga kwaɗawa HEEDAYA kira da ta saka gabanta ko
kallon sa bata yi ba cak HEEDAYA ta tsaya ba tare da ta waiwaya ko furta wata kalma ba.

"Sa'an wasan ki ne ni, ina miki magana za ki wofantar da ni? Hajja tana ciki?" Ya tambaya a
harzuƙe rai a ɓace. HEEDAYA kai ta shiga girgizawa ba tare da ta juyo ba.

"Ni kike ba amsa da kai HEEDAYA bakin ki aikin mai yake?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login