Showing 3001 words to 6000 words out of 64514 words
Chapter 2 - BONONO BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MAMAN AFRAH f.pdf
da sunan ta a jiki wannan duk aikin Ya ABDUL
da Aunty RABEEYA ne .
Sai da aka kira magriba suka tashi, an ci an sha an yi hotuna, gida suka dawo ɗakin ta ta
shige bayan ta gabatar da sallaha ta kwanta tare da kunna wayar. Ta fara danne-danne sai ta
jiyo muryar Umma tana ƙwala mata kira. Fitowa ta yi ta same ta a falo ita kaɗai ce.
"HEEDAYA" Umma ta kira sunan ta amsawa ta yi tana mayar da hankali kan Ummar.
"Ina fata kin fitar wanda kike so, kin san dai halin Abban ku ni bana son duk abin da zai zama
matsala kuma bana son ki bar mini abin gori daga kishiya da facala. Ina so cikin wanda suke
neman ki, ki tabbatar kin samu wanda za ki faɗawa Abban ku a matsayin abokin rayuwar ki idan
an tambaye ki, bana so a ce kin zauna a gida na fi so kamar yadda dokar sa take daga an
gama secondry a yi aure ina fatan ba za ki bani kunya ba" Murmushi HEEDAYA ta yi tana jin
daɗin hirar nan dama ta daɗe tana son faɗawa Umma muradin ta amma sanin tsakanin ta da
Ammie ya sa take ta dakon son a ranta amma dai yanzu za ta yi ƙarfin hali ta tari aradu da ka,
ta faɗa mata zaɓin ta in ya so ko mai za faru ta shiryawa hakan in ya so sai ta tunkari Ya
ABDUL ɗin da hujja tun da dai ta san ba zai taɓa maido mata da ƙoƙon barar tayin soyayyar ta
ba, kuma duk runtsi ta shiryawa kowane ƙalubale domin cikar burin ta na auren sa.
"Umma ina da wanda nake so, na daɗe da zaɓar sa a matsayin abokin rayuwata kuma uban
ƴaƴana" Wani murmushi Umma ta saki tare da dafa kafaɗar HEEDAYA ta ce.
"Dama ni na san ba a rasa nono a ruga, tabbas! Na san da cewa ba za ki taɓa rasa mai auren
ki ba, ai ke ta daban ce babu mu babu barin abin gori a dangi na yin kwantai, shin wane ne shi?
Ɗan gidan waye?"
"Umma ba shi ya ce yana sona ba, bai taɓa sanin ina son sa ba sai dai na san ba zai guje ni ba
duk runtsi" Galala Umma take kallon ta jin kalaman da suka raunata ƙarfin gwiwar da take ji na
samun mijin da ƴarta ta yi sai dai shin wace irin mgana ce wannan.
"Kina da hankali HEEDAYA wanda bai san da matsayin son da kike masa bane za ki fitar a
matsayin mijin aure!? Yanzu a ɗan lokacin nan soyayyar sa za ki nema ko fitar da shi ga Abban
ku a matsayin miji? Kin san Abban ku dai ba zai saurara miki ba ko? Wai waye ma?" Ta faɗa
cikin hargowa.
"Umma neman soyayyar sa ba zai mini wahala ba ni na sani"
"Saboda zuciyar sa a hannun ki take ko?"
"Ba haka bane, amma ina da yaƙinin hakan, sannan ba ɓoyayye bane makusanci ne makusanci
na a alaƙa makusanci a zuciyata"
"Tambayar ki nake waye so nake in san waye?"
"Ya ABDULHAKEEM" Ta furta muryarta tana rawa don ta san ta taro aradu da ka, ta ɗakko
dala ba gammu tabbas akwai sarƙaƙiya, cakwakiya da babban ƙalubale a wannan muradin
nata. Wani irin hangaza kafaɗar ta Umma ta yi kafin cikin sauri ta miƙe tsaye har zanin ta yana
neman faɗuwa saboda yadda maganar ta duke ta a ƙirji, yadda ta ji sunan a bazata bata taɓa
zaton HEEDAYA mahaukaciya ce ta ajin ƙarshe ba sai yau! Ɗan gidan facalar ta? Wanda a
yanzu bata da maƙiyar da take da ita sama da ita, wacce suke zama tamkar wuta da ruwa da
basa haɗuwa wuri guda, bayan sun zama abokan gaba, wanda take jin daga ABDUL har
mahaifiyar sa tamkar ta kawar da su daga doron duniya amma shi ƴarta za ta zaɓa a matsayin
miji?.
Ya kuka ji labarin? Kun karɓe shi? Mai kuka hasaso zai faru a gaba? Kun gane ruguntsumin
da muka kawo kanmu? Ba wannan ne ainihin makamar zaren ba, wannan shi ne wasa farin
girki a cikin labarin shi ne somin taɓi sai dai a gaba za mu gano mene ne dalilin ambaton labarin
da suna *BONONO RUFIN ƘOFA DA ƁARAWO* waye ɓarawon? Waye bononon? Wa aka
rufe? Waye ya rufe amsoshin suna gaba sai dai ba zan baku kunya ba in sha Allah.
MAMAN AFRAH
09013181851
[2/6, 2:08 PM] MOM MASHKUR & AFRAH:
https://chat.whatsapp.com/F7TUZezpOWLKYnyTNFuy2Y
BONONO
(RUFIN ƘOFA DA ƁARAWO)
NA
MAMAN AFRAH
First Class Writer's Asso.
*SADAUKAR*
Daga farko har ƙarshe sadaukarwa ne ga MARYAM SANI HAFIZ (Merry tah) Alkairin Allah ya
kai gare ki Allah lulluɓe rayuwar ki da tarin ni,imomi da albarkatu Allah raya mana Abdallah
fatan alkairi.
Daga marubuciyar:
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Jalli joga
Da sauran su.
*09013181851*
PAGE 2
"HEEDAYA ashe mahauciya ce ke?Ashe ƙwaƙwalwar ki bata aiki? Shin notinan kan ki ne
suka sunce ko yaya? ABDULHAKEEM ne kike so har kike muradin aure? Kin manta irin
murɗaɗɗiyar gabar da take wanzuwa a tsakanin mu da uwar sa yanzu? Hatta maganar fatar
baki bata haɗa mu da ita, ko hanya muka haɗa kin sani tamkar bamu taɓa sanin juna ba ko da
gidan nan ta zo iskar da ta bi hanyar part ɗina ma bata kallo sai dai ta je wajen Hajiya Baturiya,
shi ne kike so ki ja mini abin kunya da gori ki sa suke yada mini magana suke mini bita da ƙulli
dukan kabarin kishiya, to ahir ɗin ki na yarda ki so ko wane namiji a doron duniya kuma zan
tsaye miki tsayin daka in ga kin mallake shi amma ban da ABDULHAKEEM ko soyayyar ƴan
uwantakar da kike masa na tsane ta bare soyayya ta aure da haɗa zuri'a har abada!" Umma ta
kai ƙarshen maganar tana haki tamkar wacce ta yi tseren gudu.
"Ba zan iya ba Umma na riga na afka sai dai auren sa ne kaɗai mafit... Tun kan ta ƙarashe
maganar da ta fara Umma ta ɗauke fuskarta da wani gigitaccen marin da sai da kunnuwan ta
suka yi dummm.
"Idan kika ƙara furta kalmar soyayyar ABDULHAKEEM a wurin nan sai na tsine miki HEEDAYA"
Ta faɗa tana huci tare da nuna ta da yatsa.
Ƙasa ta zamo daga kan kujerar har lokacin hannunta dafe da kuncin ta da ya sha marin,
hawaye suna kwaranyo mata wanda bata jin za ta samu salamar zubar su matuƙar ba Umma ta
amince da zaɓin ranta ba. A kan gwiwoyinta ta dira tare da sunkuyar da kanta ta ce
"Ki yi haƙuri Umma, ki mini afuwa please amma ba zan gushe ba ina furta kalmar so ga Ya
ABDUL ba har sai ranar da na bar lumfashi a doron duniya" Tana kai wa nan ta miƙe cikin kuka
da ɗan gudu za ta tafi ɗakin ta. Taku ɗaya biyu Umma ta yi ta damƙo wuyan rigarta ƙiiii ta janyo
ta bata mata masauki a ko ina ba sai a gabanta.
"Baki ji lokacin da na ce miki zan tsine miki ba?" Ta tambaya tana aika mata harara cikin zare
idanu.
" Ai na ce ki mini afuwa!, saboda numfashina sarƙe yake da linzamin ƙaunar sa ba zan iya ba
Umma, ba zan iya daina son sa ba in kika raba ni da shi zan kasance cikin ƙunci da mummunan
tashin hankali har abada!" Ta faɗa tana rushewa da kuka.
"To ko za kike mutuwa kina falkowa ba za ki taɓa auren ABDULHAKEEM ba!." Umma ta faɗa
tana sakin wuyar rigar HEEDAYA tare da kama hanyar ɗakin ta fuuuu tamkar za ta tashi sama
domin yau HEEDAYA ta caje mata kai ta ɓata mata rai sai dai ba za ta taɓa raunata a kan
wannan maganar ba tabbas ba za ta kasance cikin mutanen da ake ce musu ɗan kuka shi yake
jawa uwar sa jifa ba!.
Bata samu zarafin tafiya ɗakin ta ba a wajen ta durƙushe tare da sakin wani marayan kuka
zuciyar ta tana raya mata ta tashi ta tafi gidan su Ya ABDUL ɗin ta furta masa abin da yake
ranta, ko shi zai iya yin wani ƙoƙari wajen ganin ba a daƙushe wannan maganar ba. Har ta karɓi
shawarar zuciyar ta tana shirin tashi sai ta ji muryar Na'eema tana sallama a ƙofar falon. Da
sauri ta share hawayen ta, amsa mata ta yi.
"Abba ya ce yana kiran kowa da kowa" Tana faɗar haka ta juya ta fice. Cikin sanyin jiki ta shiga
ɗakin Umma da sallama tsaye ta same ta a ɗakin tana gewaya ɗakin tamkar wacce take wurin
dutsen safa da marwa da alama dai maganar da ta faɗa mata ce take ci mata tuwo a ƙwarya.
"Abba ya aiko yana kiran kowa da kowa" Ta faɗa cikin sanyin murya tare da juyawa za ta fita
ganin ba amsa mata Umma za ta yi ba.
"Idan har ya kasance taron da ya kira ya shafe ki ma'ana domin ki aka yi, wallahi idan kika yi
gigin buɗe wannan bakin naki kika furta cewa ABDULHAKEEM kike so sai dai ki nemi wata
uwar ba ni ba" Bata furta ko ƙala ba ta juya ya fito daga ɗakin amma a ranta tana raya muddin
Abba ya tambaye ta wa take so to sai dai Umma ta yi haƙuri, amma bata da wanda za ta furta
sama da Ya ABDUL. Ihsan ta kira da Mubashshar ta shige ɗakin ta a maimakon ta tafi part ɗin
Abba. Wayar ta ta ɗakko ta kamo sunan Ya ABDUL ta shiga doka masa kira da zummar ta fara
sanar masa a waya kar ta je sai ta faɗawa Abba ya kira shi ya tamabaye shi kuma a samu
akasin lissafi, ya ce bai san da maganar ba. Amma ta san muddin ta faɗa masa to ba zai yi
ƙasa a gwiwa ba daga an tambaye shi zai aminta da hakan saboda ta san ba zai taɓa ƙin ta ba.
Tana kara wayar a kunne ta ji ana sanar da ita wayar a kashe, wata nannauyar ajiyar zuciya ta
sauke tare da ajiye wayar ta taso ta fito tana rayawa a ranta muddin Abba ya nemi sanin wa
take so wa ta zaɓa a matsayin miji to za ta faɗa masa gaskiyar abin da yake ranta sai dai ko a
mutu ko a yi rai.
Tun da ta nufi part ɗin Abba bata ci karo da kowa ba, da alama duk an hallara ita kaɗai ake
jira. Ita dama Abban ma tun lokacin da za ta tafi gidan su Ya ABDUL wajen partyn da aka shirya
mata, kafin ta tafi ta shiga ta gaishe shi bata ƙara sanya shi a idanun ta ba. Tsit kake ji falon
baka jin maganar kowa tamkar babu kowa a ciki sai ƙaran A.C kawai don ko TVn tana yi amma
an cire volume gabaɗaya. Da sallama ta shiga falon, baki ta ji an haɗa wajen amsa mata, gaban
Abba ta je ta durƙusa ta gaishe da shi, kanta a sunkuye har ta samu waje ta zauna a ƙasan
cafet kusa da Aunty RABEEYA, da yake gabaɗaya yara a ƙasa suke zama manya ne kawai a
kujera. Aunty Hafsa ita ce babba a gidan, daga ita sai Aunty RABEEYA sannan HEEDAYA sai
Na'eema sannan Ihsan sai Mubashshar. Aunty Hafsa, HEEDAYA, Ihsan, Mubashshar su ne
ƴaƴan Umma Aunty RABEEYA da Na'eema su ne ƴaƴan Momma.
Tun da ta zauna kanta a sunkuye yake tun shigowar ta da ta haɗa ido da Umma ta aika mata
wani kallo mai alamar gargaɗi, sai kuma bayan ta zauna Aunty RABEEYA ta jefa mata
murmushi sai dai bata samu damar mayar da martani ba, saboda fargabar da take ciki.
Gyaran muryar da Abba ya yi tare yake ya tafi da bugun zuciyar ta sai dai tana ta addu'a a
zuciyar ta.
"Ba komai bane ya sa na tara ku a nan sai don magana mai muhimmanci, amma kafin wannan
maganar ina so in fara ba RABEEYA dama domin jin daga bakin ta, saboda sanin kan kowa ne
maganata tamkar yankan wuƙa take sannan bata da bambanci da rubutu a kan dutse wanda ba
ya goguwa!" Ya ce yana ɗago kai ya sauke a kan Aunty RABEEYA da gaban ta ya yi
mummunar faɗuwa, don dama ta riga da ta sanya a ranta cewa taron nan don ita aka yi shi.
Babu wanda ya ce uffan sai Abba ya ɗora da cewa.
"RABEEYA kin samu wanda za ki bayyana a wajen nan matsayin mijin aure?"
Wani miskilin murmushi Umma ta saki a ɓoye wanda Momma ce kaɗai ta gani kuma dama ta
yi domin ta ne, saboda ta san dai maganar samun mijin RABEEYA akwai ya babu ne kakar
wajen uba. Wani tuƙuƙin baƙin ciki ne ya tokare a maƙoshin Momma jin furucin Abba da kuma
murmushin da Umma ta mata wanda ta san baya rasa nasaba da murmushin ƙeta. Da sauri
Momma ta ɗauke idanun ta tana kallon cafet ɗin da yake malale a tsakiyar falon.
"Abba ban samu ba, wanda suke zuwa kowa na tunkara da maganar aure sai ya daina zuwa"
Ta ce muryar ta tana rawa don idan akwai abin da ta tsana a duniya a zo tambayar ta mijin aure
sai take ganin kamar ita ta fi kowa baƙin jini.
"To shikenan RABEEYA dama na baki damar hakan ne kar in zartar da hukunci sanin kan kowa
ne bana yin auren dole, amma tun da dai baki fitar ba ni zan zaɓa miki ko ma in ce na zaɓa miki
don shi ne maƙasudin zaman mu a nan yanzu" Kai ta sunkuyar hawaye yana malala mata a
kumatu tana kallon yadda suke ɗisa a kan cafet. Umma kuwa tamkar ta tashi ta taka rawa haka
ta ji tsabar murna da farin ciki jin za a yi wa ƴar kishiyar ta auren dole.
"Abokin ka ne Alhaji?" Umma da ta so ƙara ƙonawa Momma rai ta faɗa.
"Na baki damar magana ne? " Ɗif ta yi tun da burinta ya cika dama so take ta yi tambar domin
ta sosa ran Hajiya Baturiya.
'Na shige su wannan yarinya za ta bar mini abin faɗa wato yanzu wataƙila ma tsoho ne ya zaɓa
mata' Momma ta faɗa a zuciyar ta. HEEDAYA duk da halin da take ciki amma sai ta ji tausayin
Aunty RABEEYA duk da cewa ta ji daɗin jin cewa taron ba don ita aka shirya ba wataƙila sai
nan gaba za a kira nata taron.
"RABEEYA na zaɓa miki Yayan ki ABDULHAKEEM a matsayin mijin da za ki aura ki rayu da
shi!." In ka ɗauke Na'eema, Abba, Ihsan , Mubashshar sai da kowa ƙirjin sa ya buga da ƙarfi
musamman HEEDAYA da ji da ganinta suka mata ƙaura na wasu daƙiƙai. Ita kanta bata san
lokacin da ta tashi tsaye ba amma cikin ƙarfin hali ta koma ta zauna tana jin zuciyarta tana zillo
tamkar za ta hudo ƙarjin ta ta fito waje. Momma wani sanyi ne ta ratsa zuciyarta ko ba komai
ƴarta ba tsoho za ta aura ba, sannan kuma ɗan gidan aminiyarta Hajiya Fati bugu da ƙari
kyakyawan matashi mai cikar haiba da kamala ya haɗa komai da wuya a samu macen da za ta
ƙi shi. Umma kuwa ranta ne ya sosu tare da mugun ɓaci tana ganin ma kamar da gangan aka
mata haka ko dai ana son mata bita da ƙulli dukan kabarin kishiya ne tabbas!. Ta san ruwa ba
ya tsami banza wato haɗa baki aka yi don zumuncin Hajiya Fati da Hajiya Baturiya ya ƙara
ƙarfafa su ƙara jin daɗin nuna mata wariyar launin fata.
Aunty RABEEYA kuwa sai ta rasa a wane yanayi take farin ciki ko saɓanin haka? Ta tabbata
idan har ta ce ba za ta ƙaunaci ɗan uwanta da aure ba tabbas ƙarya take!. Ya ABDUL ba za ta
taɓa ƙin sa ba nagartaccen namiji ne da ya haɗa komai na nagartar miji na gari, sai dai shi ɗin
zai karɓe ta a matsayin mata? Zai yarda ya aure ta? Zai kyautata mata har ta samu farin ciki a
cikin gidan sa? Shin ba zai goranta mata ba cewa ta rasa miji taimakon ta ya yi ya aure ta?.
Waɗannan cukurkuɗaɗɗun kalmomin su ne suke kai kawo a birnin zuciyarta. A hankali ta ɗago
idanun ta, ɓangaren da mahaifiyar ta take zaune don gano yadda ta ɗauki maganar ai sai ta ga
fuskar Momma ganin ta sakar mata wani murmushin farin ciki da jin daɗi sai ta ji wani sanyi a
ranta tare da jin ƙwarin gwiwa. Ganin Umma ta doka mata wata harara da kallon tsana da sauri
ta ɗauke fuskar ta ƴar uwar ta Na'eema ta kalla ta ga tana wani rausaya kai alamar jin daɗin
furucin Abba.
"Na amince Abba!.'' Ta furta muryar ta tana rawa gabanta yana tsananta bugu. Duk da ta san
amincewa da rashin amince wa abu guda ne a wajen Abba domin ta san yadda ya faɗa ba zai
sauya