Showing 24001 words to 27000 words out of 64514 words

Chapter 9 - BONONO BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MAMAN AFRAH f.pdf

30 Mar 2025

5095

kewar ta ko nuna ya damu da nisan
tazarar da ya shiga tsakanin su tsawon tafiyar da ya yi. Waɗannan abubuwan su suke ci mata
tuwo a ƙwarya kuma su take son samu bakin zaren su duk da bata so ta tsawaita zargi
kasancewar zargi haramun ne, amma ya zame mata dole, kuma ya zama wajibi ta yi karatun ta
nutsu domin ta gano bakin zaren domin ta gano irin binne tan da yake yana nuna mata shi
kawai dai bai damu da mace ba ne, shin idan bai damu da mace ba a kan mai zai aure ta ya
kawo ta gidan sa ya turke ta ya kasa sauke nauyin buƙatar ta ya bar ta da buƙatar sa danƙare a
zuciyar ta, kenan da ita da marar aure basu da bambanci? A yau dai ta yi wa kanta alƙawari ko
shi ne ƙuda wajen ƙwawa sai ya bata haƙƙin ta ko don magungunan da ta bankama.


HAMEED bai tashi fitowa ba sai da aka kira magriba, tana sallah ta ji fitarsa da alama

masallaci ya tafi, da sauri ta fito daga ɗakin ta, da ƙullin maganin tada sha'awa na maza da ta
siya wajen wata mai maganin mata, da kuma na ƙarfin maza ta nufi ruwan shayin da take dafa
masa mai ɗauke da lifton da kayan ƙamshi maganin ta zuba ta gauraya ta dawo ta ajiye a ɗakin
nata. Ta san duk runtsi sai ya sha shayi da dare yake kwanciya, ko da ba zai ci komai ba, a tea
flask ta juye ta ɗakko kayan abincin ta jera a dining kan kujerar ta koma ta zauna tana jiran
dawowar sa. Sai da aka yi isha'i ya shigo da murmushi a fuskar sa ta amsa masa sallama wani
haɗe rai ya yi don ya san zancen gizo bai wuce na ƙoƙi wato dai za ta zo masa da buƙatar
auratayya ya san ta da jaraba shi ne take ta washe baki shi kuma gaskiya bacci ma yake son yi.

"HAMEED ya za ka haura sama ga abinci na jera a dining?" Ta jefa masa tambayar ganin ya
nufi sama gadan-gadan. Kamar ba zai amsa ba sai da ya ƙara tafiya sannan ya tsaya ba tare
da ya juyo ba ya ce.

"Bana jin yunwa" Yana gama faɗar haka ya juya zai ci gaba da tafiya. Gabanta ne ya faɗi jin
furucin sa, hankalin ta ya tashi saboda ko yanzu marar ta ta fara ciwo, saboda maganin da ta
sha, duk da ta san ko da ya bata haɗin kai ba ya bari ta samu biyan buƙatar ta don ba ya
ɗaukan wani lokaci amma dai a ƙalla za ta samu sassauci don ita bata cikin matan auren da
suke neman maza a waje ko kuma yin lalata da wasu mazan ta waya don biyan buƙata ko ma
neman jinsi da jinsi wato lesbian ko kuma biyawa kai buƙata duka ba al'adarta ba ce.


"Shayin naka fa?" Ta furta a ɗan diririce don bata taɓa zaton zai ce ba zai ci abinci ba.

"Ki kawo mini ɗakina" Yana faɗar hakan ya tafi ba tare da ya jira cewar ta ba. Wata nannauyar
ajiyar zuciya ta sauke tare da nufar dining ɗin ta ɗauki shayin da ƙofi da kuma kwalin sugar sai
tea spoon da nascafe a kan ƙaramin faranti ta haura saman.

Abin mamaki a kulle ta tarar da ƙofar zuciyarta ta danne ta ƙwanƙwasa, da ya buɗe
maimakon ya bata hanya ta shiga ɗakin sai ya miƙo mata hannu alamar ta bashi. Ɗan dim ta yi
ta ce


"Ina son shigowa na zuba maka, kuma fa ko ƴar hira bamu yi ba da ka dawo"

"Bana buƙata, kuma ina buƙatar hutu bana son yawan hayaniya" Bata ce komai ba ta miƙa
masa ya karɓa haɗe da rufo ƙofar. Juyawa ta yi tana ta mamaki duk da ya ci a ce zuwa yanzu ta
saba da halayyar HAMEED ɗakin ta ta nufa ta zauna tana zaman jiran zuwan sa tun da mai
maganin ta ce da kansa zai neme ta ƙaryar namiji ya sha maganin nan ya iya bacci ba tare da
ya buƙaci mace ba don haka sai ra zauna ta zuwabawa sarautar Allah ido tana jiran ta inda
HAMEED zai zo tana son gane mai maganin ƙarya take ko kuwa maganin yana aiki bata yi
asarar kuɗin ta ba?!.

*MARYAMA*


Gabaɗaya ta rasa inda za ta saka ranta da furucin da Inna ta yi a kanta, wai ita
MARYAMA take ɗauke da ciki, cikin ma na haihuwa to a ina kuma ta yaya tun da ita dai babu
wani namiji da ya taɓa riƙe ko da hannun ta ne bare kuma har ta samu ciki. Sai dai idan ana
shan cikin a cikin ruwa wannan kuwa. Sai dai ganin Baffan ya yanke jiki ya faɗi hankalin ta ya yi
mummunan tashi ta nufe shi za ta dafa shi sai dai Inna Tasalla ta saka hannu ta ture ta,
Maimunatu ma da ta ƙaraso wurin hankali tashe tana zuwa ta ƙara hangazata sai da ta faɗi
wanwar.

"Kar ki kuskura ki ce za ki taɓa mini ubana!. Kuma ki sani duk abin da ya samu mahaifina ki yi
kuka da kan ki banzar bazara kawai ai dama tsintacciyar mage bata taɓa mage" Maimunatu ta
kai ƙarshen maganar tana jefa mata harara. Hawaye ne suke sintirin zubowa daga idanun ta
duk da tana cikin ruɗin furucin Inna na cewa tana ɗauke da juna biyu, duk da tana kokwanton
kasancewar hakan amma sai dai tashin hankalin ta ya fi ruɓanya da faɗuwar Baffan ta tausayin
sa game da jin haushin kanta sun taru sun mata rubdugu a zuciya ganin ita ce silar shiga
damuwar sa duk da ba laifin ta ba ne ita ma bata san hawa ba bare sauka.


"MARYAMA!" Baffa ya kira sunan ta yana miƙa mata hannu alamar ta kama hannun sa. Da
sauri ta taho tana kiran sunan sa.

"Wai Malam kai yanzu duk abin da ta yi har kana da ƙarfin halin kiran ta tare da kama hannun
ta?" Inna ta tamabaya tana taɓe baki haɗe da kama haɓa.


"Baffa ka ganni fa ni ma a kusa da kai" Maimunatu ta faɗa tana kama hannun da ya miƙawa
MARYAMA.

"Yo ina fa zai ganki Maimunatu ai wannan jarababbiyar ta ɗauke masa hankali ni ma matar sa
baki ga ba ta ni yake yi ba" Ta ce tana bankawa MARYAMA harara. MARYAMA hannun Baffa
ɗayan ta kama da yake Maimunatu ta riƙe ɗayan.

"MARYAMA!. Kin ji abin da Innar ku ta ce?"


"Baffa wallahi babu abin da na aikata...

"Na san halin ki MARYAMA na san abin da za ki aikata da wanda ba za ki aikata ba sai dai
yanayin yadda ta faɗi maganar ne ya daki zuciyata tunanina ko fyaɗe aka miki baki faɗa ba har
ciki ya shiga, tsorata da ruɗun da na shiga don kar fa na kasa ɗaukan amanar da na ɗauka, kar
fa na kasa riƙe ki da gaskiya kamar yadda na yi wa kaina alƙawari" Ya faɗa yana yin ɗan tarin
da yake jin ya riƙe masa ƙirji dakyar yake yi.


"Wallahi Baffa babu wanda ya mini fyaɗe!" Ta faɗa tana hawaye.

"Ƙarya zan miki ke kin isa in miki ƙarya ba kallon ke ba ko shi Malam ɗin da ya ajiye ki bai isa in
masa ƙarya ba" Inna ta ce tana zazzaga masifa da bala'i tamkar ta ari baki.

"Maimuna je ki asibitin cikin gari ki ce ina kiran Jazuli likita" Dakyar ta amsa masa ta tashi tana
zunɓura baki kasancewar bata son aike.

"Yo ita ba da cuta ba ita da shan magani, ai ita wacce ta kwaso abin kunyar sai ta je ta kira shi,
kuma wallahi matuƙar aka tabbatar da cikin nan ba za ta zauna a gidan nan ba sai dai ta san na
yi, tun da ka ƙaryata ni duk inda za ka je za a faɗa maka cikin ne dai da ita, in ban da lalacewar
zamani da mu a can da wani likita muka sani ko mene ne indai ana da ciki daga mun gwala
idon mace mun san mene ne" Ta ƙarasa faɗa tana juyawa ta bar wajen cike da jin haushi.

MARYAMA tana riƙe da Baffa da yake yashe a wajen, ko da ta ce za ta taimaka masa ya tashi
cewa ya yi ta bari. Ba a ɗauki lokaci ba Jazuli da Maimunatu suka shigo da sallama. Jazulin ne
ya taimakawa Baffa ya dawo da shi kan tabarma nan Baffan ya faɗa masa abin da yake son ya
yi wa MARYAMA amma cikin sirri ba ya ma so a san wane irin gwaji za a mata kar ko da ƙarya
ne mutane za su zarge ta saboda yanzu kiwon mutum ake ba na dabba ba bare ita da
gabaɗaya ƙauyen ido yake a kanta abu kaɗan ake faɗin ƴar tsintuwa, shegiya ce ba ta da uba!
Duk da Baffan ya yi iya yin sa don dakatar da hakan amma abin ya ci tura! Duk da ya san dai
daga amai ba a ce sai ciki ba amma dai furucin da Inna ta yi ya sa tana son a yi gwajin ko
hankalin sa ya kwanta, duk da ya san Inna akwai kinibibi da abubuwa marar kyau sai dai ya san
da wuya ta faɗi ƙarya sai dai kawai ta yi kissa.


Duk da shi kansa Jazulin ya yi mamaki kuma dai da ya ɗan duba idanun ta ya so ganin wata
alama amma ya fi so ya yi gwajin ko ya tabbatar. Asibitin ya koma ya ɗakko jakar sa ta aiki ya
dawo ya sanya MARYAMA ta yi fitsari ya gwada da PT abin mamaki da ruɗu PT ya nuna layi
biyu raɗo-raɗo alamar tabbas akwai ciki!. MARYAMA jingina kawai ta yi da bango tana salatin
annabi S.A.W a ranta amma ita kanta ta rasa duniyar da take. Baffa kuwa ƙirjin sa ya masa
nauyi yana ji a ransa wannan ne ajalin sa don ba zai iya zama ya rayu da ganin wannan abin
kunyar ba. Jazuli jinin ta ya ɗauka ya koma lab na asibitin amma sakamako yana fitowa nan ma
ya ga tabbas da cikin!. Cikin tsawon watanni uku.

Tun da aka tabbatar da cikin MARYAMA ta rasa sukuni a rayuwar ta jaraba da masifar Inna su
ne suke ci mata tuwo a ƙwarya uwa uba rashin lafiyar da ta samu Baffa ta sanadin sakamakon
samun cikin ta.


A wani daren alhamis ta lallaɓa zuwa ɗakin Baffa wanda cutar ta kwantar da shi don
numfashi ne kawai yake aiki a jikin sa.

"Baffa ban aikata komai ba wallahi, ka yarda da ni" Ta furta tana kuka marar sauti hannayen ta
cikin nashi ta sani bata da wani uba bayan shi bata da wasu dangi bayan shi bata da mai so da
ƙaunar ta sai shi hasali ma ƙyamatar ta ake saboda ba a san asali da tushen ta ba. Cikin
muryar sa da bata fita sosai ya kira sunan ta, sai da ta kara kunne ta a bakin nasa take iya jiyo
abin da yake faɗa.


"MARYAMA"

"Na'am Baffa"


"A cikin akwatin ƙarfen can ta saman lokata, akwai ledar Viva wannan ledar tana ɗauke da
kayan jariri da zanin goyo da wani ƙaramin zoben azurfa, a ranar da na tsince ki a bakin ruwa a
ƙarƙashin bishiya shekaru goma sha takwas da suka wuce, kina sanye da kayan a jikin ki zobe
a babban yatsan ƙafar ki shi kuma zanin kina kwance a kan shi an lulluɓe ki da ɗaya gefen
zanin. A lokacin muna ƙauyen Mai tsamiya inda aka ƙyamace ki wasu suna cewa ba ta hanyar
aure aka haife ki ba shi ya sa aka jefar da ke, tun da a lokacin ko cibiya ba a yanke miki ba.
Gabaɗaya ƙauyen aka ɗora mini karan tsana wasu suna faɗin ba tsintar ki na yi ba ni ne na yi
wa wata cikin ta kawo mini ke shi ne na yi wannan ƙaryar, shi ne farkon husumar da Tasalla ta
tada a kan cewar sai na mayar da ke inda na ɗauke ki saboda na ɓata musu suna, kuma ta san
cewar tsintar ki na yi. Goggon ki Shafa ta riƙe ki hannu biyu. Maganganun da suka karaɗe
ƙauyen shi ne ya sa muka bar can muka dawo nan. Har yadda ya kai kika fara wayo da sauran
abubuwan da idanun ki suke gani na tsangwama daga mutane har kawo yau. Ni kaina
MARYAMA har yau ban san wa ya haife ki ba ban san asalin ki ba shin iyayen ki suna raye ko
sun mutu Allah ne masani sai dai ba na jin akwai wasu iyaye da za su wofantar da abin da suka
haifa tsawon lokaci har yau basu neme shi ba. Na ajiye kayan can a matsayin tarihi har sai
ranar da nake saka rai wato bayyanar iyayen ki ko wani daga cikin dangin ki in nuna su a
matsayin shaida sai dai kash! Ɓullowar wannan mummunar al'amari jikin ki MARYAMA ya sa na
cire rai daga rayuwa don a yadda nake ji yanzu ba na jin zan iya wayar gari da numfashi a
jikina, na sani baki aikata ba ko qur'ani zan iya dafawa a kan shaidar ki MARYAMA amma kuma
haƙiƙanin gaskiya ban san ta ina ne hakan ya faru ba don ba a samun ciki sai an yi tarayya
mace da na miji amma ke ta yaya haka ya faru? Ki yi haƙuri da rayuwa da yadda rayuwa za ta
ƙara juya miki a bayan raina tabbas na san za ki shiga ƙalubale da tashin hankali amma Allah
yana tare da ke MARYAMA kuma in sha Allah ina ji a jikina watarana za ki haɗu da dangin ki za

ki yi farin ciki" Tun da ta kara kunnne ta a jikin bakin sa take jin maganganun nasa tamkar
bugawar guduma yadda suke shigar ta suna dukan ƙirjin ta da duk wata gaɓa ta jikin ta, tashin
hankali marar misali ya ziyar ce ta. Da sauri ta saki hannayen sa ta rungume shi tana faɗin.



"Baffana kai kaɗai ne dangina kai nake so kar ka tafi ka barni wallahi ban aikata ba" Kuka take
da iya ƙarfin ta, har Inna da ta fito fitsari daga ɗakin ta da jiyo kukan nata wani uban tsaki ta ja
don babu abin da take ji sai haushin su daga MARYAMAR har Malam Nuhun. A duniya babu
halittar da ta tsana sama da MARYAMA ita ce farkon wacce ta saka ake mata gugar zana a duk
inda ta saka ƙafa ana mata bita da ƙulli dukan kabarin kishiya.

"Ba zan taɓa yarda ba dama MARYAMU akwai dai wani ɓoyayyan al'amari wanda ni da ke
bamu san shi ba, sai dai na san watarana za ki san ko mene ne na san a lokacin ƙasa ta daɗe
da rufe idanuna amma ki saka a ranki na yarda da ke" Yana gama faɗar maganar nan sai ta ji
ya fara kalmar shahada, da iya ƙarfin ta ta dage tana faɗin

"Kar ka barni Baffa" Sai dai jin daga kalmar shahadar da ya yi bai ƙara cewa uffan ba sai ji ta ɗif
kamar an yi ruwa an ɗauke, jin jikin sa ya saki ta ɗago da sauri tana kallon fuskar sa ta hasken
fitilar da take ajiye a gefen sa, idanunsa a rufe ruf tamkar mai bacci. Jijjiga shi ta shiga yi da iya
ƙarfin ta a ƙoƙarin ta na ganin ya farfaɗo don tana fatan ya zamana suma ne ya yi ba mutuwa
ba...






*HEEDAYA*


Dafe da kuncin take kallon Umma wacce ranta yake suya tamkar ƙosai a ruwan
tafashashshen mai. Sai huci take tamkar wata zakanya.

"Umma!. Laifin mai na miki da har na ci hukuncin duka? Baki tausayawa halin da nake ciki ba
na yin ɓarin makauniya da ƙaddara ta yi da burina amma kike ƙara mini maimakon na samu
sasaauci daga gare ki, duk a tunanina ma tafiyar da kuka yi kun samo mafita amma da alama
saɓanin haka aka samu shin ga mari ga tsinka jaka Umma da wanne zan ji?" HEEDAYA ta faɗa
tana kafe Umma da rinannun jajayen idanunta wanda a halin yanzu ma suke cike taf da
hawaye.

"Ke kika cuci kan ki HEEDAYA ke kika wofantar da burin ki, ke ce dai kika saka ƙafa kika yi fatali

da ɗaurin auren da ya so hawa kan ki a yau" Umma ta faɗa a harzuƙe tana nuna ta da yatsa.
Dummm gabanta ya bada wani sauti ta ƙara shiga wani gararin wanda ya fi wanda take ciki
muni da fargaba. Furucin ya yi tsauri bai kamata ko ana sharri ba a ɗaura mata ko a ɗaura
alhakin laifin a wuyanta ta san da cewa muddin akwai wani mahluƙi da zai so cikar burinta to ko
waye shi bayanta zai bi, tun da ita ta san irin gwagwarmayar da faɗi tashin da zuciyarta take
fama da shi a kan ƙaunar Ya ABDUL.

"Kin san gabaɗaya na zargi cewa aikin ne ba a yi daidai ba, ashe dai ke kika karya sharaɗin shi
ya sa aikin bai yi ba, da yanzu an daɗe da ɗaurawa da ke sai dai yanzu bakin alƙalami ya
bushe" Umma ta faɗa idanun ta suna kawo ruwa. Da sauri HEEDAYA ta dafa kafaɗar Umma,
Umma duk da ta so tankwaɓar da hannun HEEDAYA amma sai ta tsinci kanta da kasa hakan.

"Umma wane sharaɗi na karya kuma wallahi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login