Showing 9001 words to 12000 words out of 64514 words

Chapter 4 - BONONO BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MAMAN AFRAH f.pdf

30 Mar 2025

5091

son shi ba, amma sai su hau dokin zuciya su ringa kiran
budurwar a waya suna mata barazana da cewa ta rabu da mijin su ko su mata wani mummunan
abu, wasu ma har gidan su budurwa ko bazawar suke zuwa su yi cin mutunci. Shin mai ya sa
ba za su gane cewa mazan ne masu laifi ba? Su ne suke cewa suna son matan, sannan mai ya
sa ba za su hana mazan nasu zuwa wajen matan ba sai dai su ringa tadawa macen hankali
bayan ita ma zuwa aka yi aka ce ana son, shin sai yaushe mata za su gane cewa ƙarfe ɗaya ba
ya amo?, Kawai don mijin ta zai auri ƙawar ki sai ta ce da haɗin bakin ki wato shi ba shi da laifi
sai ke da ita ne masu laifi bayan baki san hawa ba baki san sauka ba"


"Ai in kika ji abubuwan da mata suke yi a kan maza sai kin kama baki, kullum mata suna ƙarar
da gishirin su a dahuwar ƙaho ne, yawanci mace ce ta fi damuwa da namiji a kan shi mijin ya
damu da ita. Kullum mata ne suke shan magungunan mata don su farantawa mazan su, wasu
ma basa duba da rashin ingancin maganin ko illar da zai yi wa lafiyar su, sai dai su yi ta
bankawa cikin su da ƙasan su abubuwan don kawai su birge namijin a ƙarshe kuma ya shuka
musu rashin mutunci, ko su haɗu da wata cutar sanadin amfani da maganin a ƙasan su, ke
hatta planing da mata suke na haihuwa kin taɓa jin namiji ya saka abin planing? Ko ya sha wata
ƙwaya ta hana haihuwa, sai dai mata su sha, sai dai mata su saka a dantsen hannun su kai
wasu har da wanda ake saka musu a bakin mahaifa komai dai mata ne suke yi don su birge
maza amma kuma kullum matan ne a cikin damuwa da taskun rayuwa da tunane tunane da
saka kishi a rai da hana zuciya sakat mazan kuma ko a kwalar rigar su sai shegen wulaƙanci"

"Wallahi" Hajiya Aisha ta faɗa.

"Yanzu dai wani hanzari ba gudu ba kin san dai Alhaji idan ya shata layi babu mai ƙetarawa,
yanzu tun da har ya yi wannan maganar to babu makawa sai an yi kin ga kenan mun bar kashi
tun ran kwasa" Umma ta faɗa tana jiran jin abin da Hajiya Aisha za ta ce.

"Hahahaha, shi Alhaji Bashir ɗin shi ya yi kansa? Ko dole ne aka ce miki sai mutum ya zauna
jiran dama, ai mutum shi yake samarwa kansa dama"

"Kamar ya?" Umma ta tambaya cike da son jin bakin zaren.

"Wurin malami za mu je a gobe mu sa ya hargitsa komai ta ɓata komai ya mayar da komai kan
HEEDAYA a yi auren da ita kin ga za ta yi farin ciki sannan za mu nuna wa Hajiya Fati a tafin
hannun mu take"

Wata dariya Umma ta ƙyalƙyale da ita kafin ta ce.

"Kai wallahi kin biyani Hajiya Aisha gabaɗaya na ji damuwata ta wanke, amma da baki ji yadda
nake cikin ƙunci da ɓacin rai ba, ke kin ga da muka fito daga part ɗin Alhaji yadda Hajiya
Baturiya take wani ɗaga kai tana fankama ita ala dole za su yi tuwona maina da aminiyar
zancen ta"
"Rabu da ƴan iska, za su ga yadda ido zai juye da mujiya" Haka suka sha tsare-tsaren su kafin
su yi sallama a kan cewa gobe Umma za ta je ta ɗauki Hajiya Aisha su wuce wajen malamin.


HEEDAYA sai da ta sha kuka tamkar ranta zai fita kafin ta tashi da luhu-luhun idanun ta, ta
shiga dokawa Aunty Hafsa waya.

"Hlo ƴar gatan ƙanwata"

"Aunty" HEEDAYA ta faɗa tana fashewa da kuka.

"Subhanallahi mai yake faruwa ne?" Ta tambaya hankali a tashe.

"Aunty ina cikin damuwa" Ta faɗa tare da kwashe komai ta faɗa mata cikin kuka.

"HEEDAYA dama ABDUL ne kike so? "

"Wallahi Aunty ji nake zan iya mutuwa in ban same shi ba"


"Haba HEEDAYA yanzu ai sai ki haƙura tun da dai Auntyn ki RABEEYA za ta aure shi...

"Ni ba Aunty ta ba ce kuma wallahi na tsane ta zan iya yin komai don ganin na mallaki Ya
ABDUL ciki kuwa har da kisan kai...

"Kina da hankali HEEDAYA kina cikin hayyacin ki kuwa?"

"Aunty na mutu a kan son shi wallahi, da ƙaunar sa nake rayuwa komai nake zuciyata tana
haɗe da tunanin sa, komai na rayuwata da na tsara da shi nake tsarawa sai yanzu a rana ɗaya
a dare ɗaya a ce zan rasa shi ba zan iya ba Aunty"

"Ki nutsu ki dawo hayyacin ki, maganar RABEEYA fa ake ko ƙwaƙwalwar ki ta samu taɓuwa ne
kin manta cewa ƴar uwar ki ce ta jini uban mu ɗaya da ita babu yadda za a yi ku auri miji ɗaya
kuma Abba ba zai taɓa janye maganar sa ki auri ABDUL ɗin ba...

"Aunty ki bar ambata Ya ABDUL zai auri wata, ni kaɗai ce matar sa bana son ya auri kowace
mace sai ni kuma ita ma Aunty RABEEYA na tsane ta yanzu saboda ina kishin sa kishi irin
wanda ban san wane iri ba ne"

"Bari kawai zan yi magana da Umma" Aunty Hafsa ta ce tana yanke kiran jin tana ta mata
magana tamkar ba a hayyacin ta take ba. HEEDAYA kuwa Aunty tana kashe wayar ta jefar da
ita a kan gadon ta cigaba da kuka.


Umma zaune take bakin gado tana ta doka murmushin jin daɗin shawarar da suka yanke ita
da Hajiya Aisha, har ta fara hango irin mulkin mallakar da za su yi wa Ya ABDUL. Kiran Aunty
Hafsa ne ya shigo wayar ta.

"Hafsa"

"Umma barka da dare ya gida"

"Lafiya lau yau duk bamu gaisa ba ma ina kishiyar tawa Ikram"

"Ta yi bacci" Shiru ya ɗan biyo baya kafin Aunty Hafsa ta ce.

"Umma wai mai yake faruwa ne HEEDAYA ta kira ni tana kuka?"

"Wayyo HEEDAYA da ta yi haƙuri ma burin ta yana dab da cika"

"Ta ina Umma?" Kwashe komai ta yi ta faɗa mata.

"Haba Umma wannan ba daidai ba ne...

"To uwar ƴan wa'azi da nasiha kin fimu sanin ya kamata ne, ke mai ya sa bakya kishin uwar ki

sai ta wasu? Bakya kishin ƴar uwar ki sai wata"

"Ba haka ba ne Umma kin ga HEEDAYA yanzu ta yi candy kafin ta ɗan huta ai mijin ta zai fito
kuma duk furucin nan da take yi zafin so ne daga ta ga ya auri RABEEYA za ta haƙura"

"Hafsa babu ruwanki a cikin maganar nan sai inda ƙarfina ya ƙare dama ban hango kyan wuri a
kunnen jaka ba sai yanzu da aka buɗe mini komai na gani tangararai" Aunty Hafsa jin Umma ba
fahimtar ta za ta yi ba ta mata sallama ta kashe wayar tana fatan Allah ya ktauta ya ganar da
su.
Suna yin sallama ɗakin HEEDAYA ta tafi a falo ta samu Mubashshar da Ihsan suna kallo, tana
shiga ta mayar da ƙofar ɗakin ta rufe, zaunawa ta yi a bakin gadon ta ɗago HEEDAYA tana
lallaɓa ta.

"Kar ki kuskura ko a mafarki ki cire son ABDUL a ranki ko ki saka dangana, ai kawai ki ƙarawa
wuta fetur na tsaye miki sai mun ga abin da ya turewa buzu naɗi" Sosai HEEDAYA ta ji daɗin
wannan albishir.


Washe gari Umma ta tambayi Abba a kan cewa za ta je gidan Hajiya Aisha ta duba ta ba
lafiya, amma idan direba ya kaita a can zai baro ta" Nan ya amince tare da cewa ta mata sannu,
lokacin da ta fito rataye da jakar ta da ta lodowa kuɗaɗe za ta tafi sai ga Hajiya Baturiya ta fito
daga part ɗin ta ganin Umma sai Momma ta ɗaga murya ta ƙwalawa RABEEYA kira fitowa ta yi
Momma ta ce.

"Na tafi gidan aminiyata kuma surukar ki Hajiya Fati" Ta faɗa tana dariya da gayya don ta
ƙonawa Umma rai. Umma ko kallon ƙurar da ta ɗakko ta bata yi ba, don ta ga ko mayafi babu a
jikin ta ba ma fita za ta yi ba kawai neman magana ne ita ma RABEEYA da ta fito ta gane mai
Momma ɗin ta yi juyawa kawai ta yi ta koma ciki.

Direba yana sauke ta ya koma tana shiga ta ga Hajiya Aisha har ta shirya a motar ta suka fito
suka tafi Hajiya Aishar ce take tuƙa su saboda zuwa wajen sirri ba a ɗaukan direba. Tafiya mai
nisa suka yi har sai da suka fita daga garin na Dutse, sun yi tafiya sosai kafin su bi wata siririyar
hanya. Babu komai a dokar dajin sai wani ɗakin ƙasa guda ɗaya jal. Dab da ɗakin ta yi parkin
suka fito baka jin komai sai kukan tsuntsaye. A bakin ƙofar suka tsaya maimakon yin sallama
sai ihu suka shiga kwaɗawa su duka.

"Ihu-ihuuuuu"

"Ihuuuuu" Aka amsa da ihun daga can cikin ɗakin alama ce da aka musu da cewa su shiga.

"Hajiya Aisha amma wannan malami ne kuwa kodai boka ne?"

"In uban boka ne ma mu dai ba biyan buƙata muke nema ba, kuma da wa ya ce miki akwai
malamai yanzu ai ƙalilan ne malamai na Allah da annabi sauran duk buge ne duk sahun bokaye
suke.

"Da baya-baya ake shigowa" A hakan suka shiga ɗakin wani tsoho ne tukuf zaune a gaban
wata ƙwarya ɗakin duk tarkace ne da wani gadon kara a ajiye. Sai da suka zauna sannan
Hajiya Aisha ta buɗe baki za ta fara magana.

"An sanar da ni komai bana buƙatar ƙarin bayani" Bai buƙaci maganar su ba ya ɗora da cewa.

"HEEDAYA za ta auri ABDULHAKEEM babu makawa amma sai idan an bi sharuɗan da zan
gindaya, matsawar aka kuskure to ki sani ba zan iya dakatar da komai ba na fasawar auren da
ƴar uwar ta RABEEYA" Kallon kallo aka shiga yi tsakanin Umma da Hajiya Aisha.

"Kun amince?" Kai kawai Umma take gyaɗawa kamar wata ƙadangaruwa ko jin sharaɗin bata yi
ba.

"Wannan ganyen guda ashirin da bakwai ne, adadin ranar da aka sanya wato sati huɗu, idan
kika irga bakwai sau huɗu ya kama kwana ashirin da takwas kenan wato wata guda, ban da yau
kullum za ta ɗauki ganye ɗaya ta yi fitsari a kansa tana mai ambaton sunan ABDULHAKEEM
ɗin sai ta saka a shadda sai ta zuba ruwa ya tafi. Tsawon kwanakin nan kar ta masa maganar
soyayya kar ta tunkari kowa da maganar a rana ta karshe kuma za ta riƙe wannan layar a
hannun hagu sai ta samu wani abu na ci ta tunkari RABEEYA ta miƙa mata kar ta kuskura ta yi
magana duk runtsi ko uhum kar ta ce, tana ba RABEEYA abin ita kuma RABEEYA za ta ci abin
daga RABEEYAR ta ci sai ta yi sauri ta je ta binne layar to babu makawa da ita za a ɗaura
auren!" Ya kai ƙarshe yana ƙara jaddada kar a ƙetara sharuɗan...


MAMAN AFRAH

09013181851
[2/9, 9:57 AM] MOM MASHKUR & AFRAH:
https://chat.whatsapp.com/H8hTgWtMZ3s7uhyedcPR17



BONONO


(RUFIN ƘOFA DA ƁARAWO)

NA


MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.


*SADAUKARWA*

Daga farko har ƙarshe sadaukarwa ne ga MARYAM SANI HAFIZ (Merry tah) Alkairin Allah ya
kai gare ki Allah lulluɓe rayuwar ki da tarin ni,imomi da albarkatu Allah raya mana Abdallah
fatan alkairi.

Daga marubuciyar:

Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Jalli joga
Da sauran su.
*09013181851*



PAGE 4


Duk da Umma ta ji daɗi amma kuma tana ta taraddadi a kan sharuɗɗan. Tafiya suke amma ta
kifa uban tagumi, rage gudun Hajiya Aisha ta yi ta ɗan juya ta kalle ta.

"Wai ya haka ne ƙawata ko hankalin ki bai kwanta da aikin ba ne? Ko kuwa dubu ɗari biyar ɗin
da ya ce a bashi ne kike ganin ya yi yawa?"

"Haba ke kuwa ai ko wani ne ya ce miki zan yi mita a kan kuɗi kya shede ni kin fi kowa sanin
kuɗi ba matsalata bane kuma a kan aikin nan ko miliyan nawa yake buƙata zan bashi don
burina da kuma mafarkin HEEDAYA ya cika amma hanzari ba gudu ba ni kar fa a je a samu
matsala kin san dai yadda na miki bayani na fuskanci yarinyar nan ta mutu a kan son sa anya
za ta bi sharuɗan da aka gindaya kuwa na ganin bata furta masa so ba ko ta faɗawa wani
magana dangane da soyayyar?"

"Ana ga yaƙi kina ga ƙura, kar fa ki manta ita ma burinta a bai wuce samun ABDUL ɗin ba ai
indai ta ji sharuɗan dole za ta kiyaye ko don ganin muradin ta ya cika" Shiru Umma ta yi tana
nazari kafin ta saki wani murmushi ta ce

"Ai shi ya sa bana nadamar samun ki a rayuwata tabbas kaifin ƙwaƙwalwa da basirar ki kaɗai
ya ci a jinjina miki, lallai na ƙara yarda cewa tuwon girma miyar sa nama!" Suna ta tattaunawa
har suka iso cikin gari gida ta so ta biya ta ajiye ta sai ta wuce amma sai Umma ta sanar da ita
abin da ta cewa Abba na duba ta za ta yi bata da lafiya. Sai da ta huta sannan ta kira direba ya
zo ya ɗauke ta bayan sun tsara abubuwan yadda za su kasance don Hajiya Aisha ta ce shiri za
su fara na bikin tun da suna da dahir da tabbas na cin maganin nan don aikin sa tamkar yankan
adda ne ma ba na wuƙa ba.


Cike da annashuwa ta shigo gidan ko da ta haɗu da Hajiya Baturiya a maimakon ta aika
mata saƙon harara sai ta sakar mata wani shu'umin murmushi, tare da sanya idanun ta cikin
nata ta ce.

"Ka ga Hajiya Baturiya aminiyar Hajiya Fati, iyayan amarya kuma iyayen ango!" Tana gama
faɗar hakan ta cigaba da tafiya tana wani murmushin da ita kaɗai ta san manufar sa. Hajiya
Baturiya kuwa mamaki ne ya kashe mata jiki don ta san ruwa ba ya tsami banza ko kaɗan bata
yarda cewa akwai alkairi ga murmushin Umma ba, ta san akwai wata a ƙasa amma sai dai
mene ne a ƙasan? Waye zai bata amsar tambayar wannan cike da kallon tuhuma ta bi bayan
Umma har ta ɓacewa ganin ta kafin cikin ƙarfin hali ta ɗaga sagaggun ƙafafun ta ta cigaba da
tafiya tana ta faman saƙe-saƙe. Ko da ta shiga falo ganin Na'eema tana zaune tana cin pizza
sai ta ɗauki wayar ta ta nufi bedroom ɗin ta don wannan wayar sirri ce bata son kowa ya ji.
Hajiya Fati ta dokawa kira.

"Hajiya Baturiya uwar amarya da angon sati huɗu... Maimakon ta bata amsa sai ta ce

"Akwai matsala fa"

"Wace iri?"

"Mutuniyar ki tauraruwa mai wutsiya ce na ganta ta dawo gidan nan cike da annashuwa bayan
ba haka ta fita ba anya babu wata maƙarƙashiya kuwa? Gaskiya daga ganin yanayin ta akwai
wata a ƙasa"

"Wace irin maƙarƙashiya?"

"Ke kin san Hajiya Zainab ba kanwar lasa ba ce bata barin ta kwana yanayin yadda ta mini ɗazu
ya nuna mini kamar tana da wani shiri" Ta kwashe yadda suka yi ta faɗa mata, shiru ya biyo
baya tana ɗan nazari da tunani sai kuma ta ce.

"Anya kuwa bana jin akwai wani shiri da za ta yi a kan mu, na fi alaƙanta hakan da borin kunya,
amma dai ke kin san in har a kan auren ABDUL da RABEEYA ne kissa da kisisinar ta ko wani
shirin ta na ɓoye ba zai sa a fasa ba kin san dai yadda Daddyn ABDULHAKEEN DA Abban su
RABEEYA suke da kafiya da jajircewa babu wani abu da zai sauke su daga aƙidar da suka
sanya gaba" Ta ce tana ƙara tabbatar mata don a tunanin ta ko kissa za ta yi a fasa auren bata
taɓa kawowa ai za ta je wurin boka ko malam ba, sannan kawainiya abu na fili suka sani wato
tana kishin alaƙar su ne shi ya sa bata son auren amma basu san cewa akwai wani boyayyan
burin ba na son da HEEDAYA take yi wa ABDUL ɗin.

"To shikenan Allah nuna mana wannan rana dai da rai da lafiya a ɗaura auren yaran su tare
hankalin mu ya kwanta"

"Amin ya rabb" Da haka suka cigaba da tattaunawa a kan shirye-shiryen tun da suna gani
lokacin babu wani yawa sannan suna so su yi komai na kece raini.



Umma tana shiga falo ta samu Aunty Hafsa ta zo, suna zaune ita da Ihsan da Mubashshar sai
Ikram tana ta wasa HEEDAYA kuma tana kwance kan doguwar kujera.

"Oyoyo Umma" Ikram ƴar shekara biyar ta faɗa tana ƙanƙame Umma.

"Inyeee kishiyar ke ce a gidan nawa kika zo aure mini miji" Umma ta faɗa tana dariya tare da
shafa kanta.

Zaunawa ta yi tana cewa

"Wash na gaji wallahi"

"Sannu da dawowa suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login