Showing 12001 words to 15000 words out of 64514 words
Chapter 5 - BONONO BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MAMAN AFRAH f.pdf
shiga mata inda Aunty Hafsa ta gaishe da ita.
"Umma sai na zo na ga bakya nan duk zuwan da na yi da wuri" Aunty Hafsa ta faɗa bayan sub
keɓe.
"Eh na tafi uzurin gabana, ke da na faɗa miki yadda abubuwa suke tafiya kika shiga faɗin Allah
ya ce annabi ya ce kike mini nasiha da wa'azi haba Hafsa kamar dai kin fini son Allah ko tsoron
sa ne, kar ki manta fa ubangijin nan na kowa ne " Umma ta ce tana faɗa mata inda suka je da
Hajiya Aisha a kan aure ya dawo kan HEEDAYA"
"Umma babu macen da za ta auri mijin da ba nata ba, duk runtsi idan har mijin ta ne sai Allah
ya juya al'amarin ba wai sai an je neman taimakon wani ba, yana da kyau bawa ya nemi
taimakon a wajen Allah, amma yarda da wanin Allah shirka ne da Umma kuma duk wanda ya je
wajen boka sallar sa ta kwana arba'in bata karɓuwa ni a ganina da HEEDAYA da RABEEYA duk
ɗaya ne!."
"Au Allah Hafsa? Ni kuma sai na ce duk ban san waɗannan abubuwan ba to tun kan ki diro
duniya na san su"
"To amma mai ya sa ba za ki yi amfani da sanin ba Umma, ai amfanin ilimi aiki da shi"
"Wai nema kike ki kafirta ni Hafsa ce miki na yi ban yarda da Allah yake komai ba amma dai an
kin san an ce malamai magada annabawa ne, kuma da kike batun rashin karɓuwar sallah mai
bakin ki ya ce? Ta kwana arba'in kika ce sallar ba wai an daina karɓa kwata-kwata ba, amma
kin san Allah gafurur rahim ne ko, kuma ki sani akwai bambanci tsakanin HEEDAYA da
RABEEYA kwatankwacin tazarar sama da ƙasa ni ba ɗaya bane a wajena HEEDAYA ce ƴata! In
baki sani ba ki sani mutane da dama sun bar yin sallah domin cikar burin su na duniya sau
nawa ƴan siyasa suke cin karen su babu babbaka, saboda neman mulki malamai da bokayen
da suke musu aiki su hana su sallah ta tsawon kwanaki ko watanni ma, sau nawa ake zuwa
maƙabarta a haƙo gawa a yi asiri da wani sashe na jikin ta, mutane da dama ni fa zan yi sallar
amma karɓa ne ba za a yi ba yo wasu umarni da barin sallar ake musu kuma su barta".
"Umma da wanda Allah ya ƙi karɓar sallar sa da wanda boka ko malam ya dakatar da shi yin
sallah ni a ganina duk abu ɗaya ne basu da bambanci tun da shi ma wanda ba a karɓa ai ba za
a saka masa ladan yin sallar a mizanin littafin aikin sa, shin idan wa'adin ɗayan su ya cika a
wannan lokacin wato Allah ya karɓi rayuwar sa ya mutu mai?"
"Kafiri" Umma ta faɗa a harzuƙe don ta gaji da jin i Hafsa iiiii jgudun kar su yi tasiri a kan ta ta
sanya ta fasa aiwatar da shirin ta.
"To bambancin musulmi da kafiri sallah ce da sauran ibadu amma sallah ita ce kan gaba da
komai a cikin ayyukan bayi, ita ce farkon abin da ake duba wa a cikin aiyukan bayi idan sallah ta
yi to sanna saura su biyo baya idan bata yi ba komai ya ɓaci mai ya sa ba za mu kiyaye ta ba?
Duk fa wata cim-ma manufa ko buri idan aka je nema wajen boka ko malam to ana hana yin
wata ibadah ne saboda shaiɗanu ne ake aikin da su b...
"Ya ishe ki haka Hafsa!" Umma ta faɗa a ƙufule tana ɗaga mata hannu alamar dakatarwa.
Ƙwallah ce ta ciko idanun Aunty Hafsa ganin mahaifiyar tata ta yi nisa bata jin kira.
"Nan gidan ubanki ne ba zan hana ki zuwa ba amma in kin san za kike shigar mini hanci da
ƙudundune ki tashi ki fita mini a ɗaki" Ta faɗa cikin ɓacin rai tana nuna mata hanyar ƙofa. Da
sanyin jiki ta tashi tana ta faman bata haƙuri ta fita daga ɗakin tare da rufo mata ƙofar.
Haka Hafsa ta yi wunin gidan rai babu daɗi domin haka Umma ta ƙi sakar mata fuska babu
yabo babu fallasa ta san cewa kawai saboda bata so ta faɗa mata gaskiya ne.
Sai da ƙafa ta ɗauke Umma ta kira HEEDAYA ɗakin ta sai da ta rufe ƙofa har da saka mukulli
sannan ta ɗakko jakar da ta saka maganin a ciki. Bayani ta shiga yi mata dalla-dalla tare da
faɗa mata sharuɗɗan da aka gindaya.
"HEEDAYA ki tabbatar kin aiwatar da komai kamar yadda aka tsara kar ki kuskura ki ƙetare
komai"
"Umma kenan!. Ai babu tangarɗar da za a samu in dai daga gare ni ne saboda wannan abu ne
dama da na saka a cikin kaina cewa ko ta halin ƙaƙa sai na mallaki Ya ABDUL ciki kuwa har da
bin malaman da bokaye bare kuma na samu mai shige mini gaba? Ai wallahi sai na jajirce na
tsaya tsayin daka don ganin burin mu da ni da ke ya cika kuma Ammie sai ta kwashi kashin ta a
hannu matsawar na shiga gidan ɗanta sai ya dawo mijin ta ce...
"Kuma mijin mace ɗaya" Umma ta faɗa tana ɗan kai mata duka tana dariya.
"Wannan ma ai faɗa ma ɓata baki ne Umma don bai isa ya zauna da wata mace ba bayan ni
kisshin bala'in da yake nuƙurƙusata a zuciya wallahi bana jin zai iya barin Ya ABDUL ya san
wata mace bayan ni ni fa ina ganin ƙoƙarin ki Umma, da kika zauna da kishiya ni ba zan ma iya
ba gani nake kawai sunana gawa idan za a mini kishiya, shi ya sa na ci alwashi daga ranar da
aka ɗaura mini aure zan ajiye zugar ƙawayena wanda basu kai ga samun shafawar fatihar aure
ba don wallahi matsawar yarinya bata da aure in dai ƙawata ce babu ni babu ita wala a zahiri ko
online na daina kula ƴan mata sai matan aure"
"Inyeee lallai abin naki azimun ne HEEDAYA ban ga laifin ki ba ai kishi kumollon mata ne kuma
duk wacce ta tsaya kallon ruwa kwaɗo zai mata ƙafa, ai in dai aka ɗaura auren nan da ke dole
na tashi haiƙan na neman miki wurin zama na dindindin daga ke ba ƙari" Umma ta ce tana bata
hannu suka tafa, rungume ta HEEDAYA ta yi cikin farin ciki tana jin haƙiƙa mahaifiyar ta ta share
mata kukan ta a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. Gabaɗaya maganin ta bata tare da mata nannago a
kan ta kula sosai.
HEEDAYA ko da ta kai maganin nan ɗakin ta a drower ta saka tana ji a zuciyar ta matsalar
ta ta zo ƙarshe. Kayan bacci ta ɗauka ta saka a jikin ta ta kwanta. Nocking ƙofar ɗakin ta ake
bugawa a hankali kamar ba a so tasowa ta yi ta buɗe ganin Aunty RABEEYA sai ta ji wata irin
tsanar ta a ranta, shi ya sa ma a yau ta ƙi kwata-kwata su haɗa hanya saboda abin da take ji a
ranta. Amma tuno da sharuɗɗan da Umma ta faɗa mata sai ta washe baki.
i"HEEDAYA tah" Aunty RABEEYA ta faɗa tana jin daɗin ganin walwala a fuskar HEEDAYA
ƙarfin halin rungume ta HEEDAYA ta yi ɗakin suka shigo suka zauna a bakin gadon tana ta
tambayar ta dalilin da ta sa jiya ta sauya mata da kuma dalilin kukan ta nan ta sanar da ita cewa
kawai ta rasa mai yake damunta shi ne dalilin kukan nata. Ba don ta yarda da hakan ba sai don
ta san cewa HEEDAYA ba za ta mata ƙaryar wani abu da ban ba bata san cewa yanzu wannan
ba HEEDAYAR da ta sani ba ce a baya. Hira suka shiga yi a nan har take bata labarin Ya
ABDUL ya zo ya ce yana son ta da bakin sa sannan ta faɗa mata yau ma wuni suka yi suna
waya, sosai HEEDAYA ta ji wani abu ya tokare mata sai dai ta yi saurin wayincewa ta ce mata
bari ta shiga banɗaki ta fito da to ta amsa ita kuma da ta shiga bayin ta shiga share hawaye sai
da ta ɗan taɓa kuka ta wanke fuskar ta sannan ne ta ji sauƙin tuƙuƙin da ranta yake mata goge
fuskar ta yi ta fito.
"Amma dai ba fitsari kaɗai kika yi ba har da kashi ko?" Aunty RABEEYA ta faɗa da wasa tana
dariya.
"Kai Aunty HEEDAYA ta ce tana dariya, nan dai suka yi sallama ta tafi. Sauƙin da HEEDAYA ta
samu a ranta shi ne mafitar da Umma ta samo mata da tunanin fara aikin gobe don cim ma
manufarta.
Washe gari HEEDAYA ta buɗe drower cike da murna tana son ɗauko ganye ɗaya ta yi amfani
da shi kamar yadda Umma ta sanar mata cewa ta masa fitsari ta saka a shadda ta kora ruwa.
Sai dai mai abin al'ajabi sai bata ga ledar mai ɗauke da magungunan ba, hankali tashe ta shiga
bincike kayan drower amma ledar magani ta ce ɗaukeni in da kika ajiye ni. Tamkar sabuwar
mahaukaciya haka ta shiga watso gabaɗaya kayan drowar a rikice amma bata ga ledar ba wani
irin zaro idanu ta yi gabanta yana faɗuwa duk ta hautsi ne ɗakin har ma drower da bata saka
ledar a ciki ba sai da ta shiga bincikawa amma bata ganta ba...
A kiɗime ta fito daga ɗakin ta ɗakin Umma ta nufa. Umma wacce yau take jin ta cike nishaɗi
da shauƙin samun mafita tana zaune a gaban madubi tana ɗaura ɗankwali baram ta ji ƙaran
hankaɗowar ƙofa ta ji tana waiwaya wa ta ga HEEDAYA ta shigo tamkar wacce aka biyo duk ta
birkice ga hawaye suna sintiri a kumatun ta . Gaban Umma ne da doka da mugun ƙarfi har bata
san lokacin da ta yi wurgi da ɗankwalin hannun ta ba ta taso ta tunkaro HEEDAYA wacce ita ma
ita ɗin ta tunkaro.
"Mene ne HEEDAYA?" Umma ta tambaya hankalin ta ita ma a tashe tana fatan dai ba wata
matsala ba ce ta kunno kai ma'ana ba amfani ta yi da maganin ba a adaidai ba da kwa sun
shiga ɗari uku ma ba uku ba, don sam bata taɓa kawowa ma cewa shi kansa maganin ne ba a
gani ba.
"Umma na rasa magani... Tun kafin ta ƙarasa maganar Umma ta zaro idanu tare da saka hannu
ta finciko HEEDAYA ta ce
"Kina da hankali kuwa HEEDAYA gidan uban wa kika kai maganin? Kin san ina ne makomar
hakan?"
"Umma wallahi na rasa shi a drower ta na ajiye... Tun kafin Umma ta ji ƙarshen maganar ta juya
har da gudun ta HEEDAYA ta take mata baya suka doshi ɗakin HEEDAYAR. Bincike ta shiga yi
bayan HEEDAYAR ta nuna mata in da ta ajiye maganin amma ba ya nan. Na shiga uku ni
Zainab" Umma ta ce tana ɗora hannu biyu a kai ta saki wani kuka mai cike da ihun takaici
saboda ta san komai ya kwaɓe tun da ba a ga magani ba, murna ta koma ciki tun da komai ya
ruguje tun da dai magani ya ɓata tun ba a fara aiki da shi ba haƙiƙa da alama murna ta koma
ciki. Ita ma HEEDAYA kukan ta saki.
"Bayan kin dawo ɗakin nan da maganin babu wanda ya shigo?" Umma ta faɗa lokacin da wani
tunani ya faɗo mata.
HEEDAYA da ta rikice gabaɗaya sai sannan ta yi tunanin cewa ko wani ne ya shigo ya ɗauka
tunda ta san dai da hannun ta ta ajiye kuma ma waye zai ɗauka bayan babu wanda ya san ta
ajiye.
"Tambayar ki nake?"
"Umma Aunty RABEEYA ce kaɗai ta shigo"
"Ta yi mai?" Umma ta tambaya hankali tashe.
"Kawai hira muka yi take tamyata dalilin da ya sa na mata fushi da kuma faɗa mini...
"Faɗa miki mai"
"Umma bana son furtawa da bakina"
"Ba za ki faɗa mini ba sai na saɓa miki"
"Cewa ta yi wai Ya ABDUL ya ce yana son ta" Ta faɗa kamar ta rushe da kuka saboda ɗacin
faɗar cewa ya ce yana son Aunty RABEEYAR .
"Dallah rufe mini baki an faɗa miki da ana sakewa da mutane ne ai ga shi nan ta zo har ɗaki ta
ɗauke ledar maganin" HEEDAYA jin furucin Umma a take ta zaro idanu tunowa da ta yi cewa ta
shiga banɗaki ta bar Aunty RABEEYA a ɗakin. Gaban ta ne ya shiga bugawa da ƙarfi zuciyar ta
ta shiga hautsinawa tana ta ƙoƙarin son tuno wani abun amma ruɗanin da ta shiga ya hana ta
tuna komai.
"Shikenan ta rusa komai" Muryar Umma ta katse ta.
*ƘAUYEN KANYA*
Inna Tasallah ce zaune a gaban wuta tana fifitawa ruwan sai tafasa yake tana son yin tuwon
amma shiru har yanzu Maryama bata dawo daga niƙan ba. Maimunatu ce ta fito daga ɗaki tana
wani yatsina ta ce
"Inna ina wannan marar galihun za ta kai mini ruwa in yi wanka"
"Tana can yawon gantalin ta mana kin ganni ina zaune zaman jiran ta kawo mini niƙa amma
shiru kake ji maye ya ci shirwa" Ta faɗa cike da faɗa. Sallamar Maryama ɗauke da roba a kanta
shi ya hana Maimunatu maganar da ta yi niyyar yi. Babu wanda ya amsa mata a cikin su sai
saƙon harara da suke aika mata su duka tamkar idanun nasu zai faɗo ƙasa. Idan da dabo ta
saba da wannan abubuwan amma sai dai ita damo ce sarkin haƙuri.
Wurin Inna ta ƙarasa sai da ta durƙusa da hannu biyu ta miƙa mata robar tana mai cewa
"Inna ga niƙan" Hannu Inna ta miƙa kamar za ta karɓa aikuwa ta ɗaga hannun ta saukewa
Maryama yatsun ta biyar a fuskarta.
"Shegiya mai baƙar zuciya in ban da baƙin ciki da takaici a ce tun daɗewa in aike ki amma sai
yanzu kika ga damar dawowa?"
"Wallahi Inna injin cike yake da layi ɗaya injin ya lalace kowa nan yake kaiwa shi ya sa layi ya yi
yawa"
"Ƙarya kike baƙar munfuka uwar shegiyar ƙarya" Maimunatu ta katse mata magana.
"Yo sai kin faɗa ma waye bai san munafurcin ta ba, tana can dai yawon bin maza" Inna ta ce
tana mata wani kallon tsana. Kai ta sunkuyar tana tuna cewa tun da Goggo Shafa ta rasu
shikenan ta cigaba da fuskantar tsangwama duk da tana rayen ma tana samun hakan amma ba
kamar yanzu da ƙasa ta rufe idanun ta ba.
"Wuce ki kai mata ruwan wanka ki zo ki yi tuwon don babu bawanki a gidan nan da zai miki
tuwo dama ganin baki dawo ba ne ya sa na ɗora tukunya" Da to ta amsa kafin ta tafi ta kwalfi
ruwa wanda gama jidar ruwan ta yi kenan aka aike ta niƙan kullum haka take ƙarewa a tsaye
abinci ma babu mai bata. Ruwan ta kai mata ta dawo ta yi talgen ta bar shi yana dahuwa ta
daka daddawa da sauran kayan miyar ta haɗa wata wutar ta ɗora tukunyar miyar ta koma gefe
ta doka tagumi tana kallon Inna da Maimunatu suna cin alala wanda wannan ta san abincin
la'asar ne suke ci bayan sun ci na rana ita kuma ko na rana bata ci ba rabon da abincin tun
ɗumamen safe da Baffa ya ci ya rage mata ta ci.
"Ungo kar in ƙware kin zauna kin kafe mutane da wanna ƙwala-ƙwalan idanun" Maimunatu ta
faɗa, Maryama kuwa jin ƴaƴan hanjinta kamar za su tsinke saboda yunwa ta tashi ta je na miƙa
hannu gutsiren alalar ta dangwara mata a hannu. Tasowa ta yi ta dawo mazaunin ta tana kallon
gutsiren alalar tana tuno maraicin da ta yi na rashin Goggo Shafa duk da ba ita ta haife ta ba
amma dai tana nuna mata gata haka ta ɗaga alalar ta saka a bakin ta wacce gutsira biyu ta yi
ta cinye ta suɗe hannun ta je ta wanke hannun ta dawo ta cigaba da aikin.
Baffa ne ya shigo da sallama hannun sa riƙe da buhu da yake daga cin kasuwa yake. Wani
daɗi da sanyi ta ji a zuciyar ta ta tabbatar ko ba komai yanzu zai bata wani abu ta saka a cikin
ta.
Durƙusawa ta yi ta gaishe shi ds masa sannu da zuwa ya amsa cikin sakin fuska, buhun ya
buɗe ya fito da rogo ya fiddo da rake ya bata tana murmushi ta saka hannu biyu ta karɓa tana
murna samun abin da za ta saka wa cikin ta. Inna kuwa sai harara take aika mata a fakaice
tana wani taɓe baki.
Zaunawa ta yi ta fara tura rogon tamkar za ta haɗa da hannun ta saboda yunwa, Baffa kuwa
sai da ya bata sannan ya miƙawa Inna buhun don dama ya san idan ya bata ba lallai ta ba
Maryamar ba. Sai da ta cinye rogon tas sannan ta je ta ɗauki ruwa ka sha, lokacin Baffa ya
shiga wanka.
Tana dawowa ta zauna kawai sai ta ji cikin ta ya ƙulle ya murɗa mata sai kuma ta ki zuciyar ta
tana tashi kafin ta tashi har amai ya ƙwace mata. Da gudu ta yi wajen dabobi ta shiga kelaya
amai. Baffa da fitowar sa kenan ya hango ta tana ta amai tamkar za ta amayo kayan cikin ta. Da
sauri ya yi wajen ta yana kiran suna