Showing 6001 words to 9000 words out of 64514 words

Chapter 3 - BONONO BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MAMAN AFRAH f.pdf

30 Mar 2025

5088

ba, amma ta faɗa masa ne don bai kamata ta yi shiru ba shirun tamkar wofantar da
maganar ne a ganin ta.

Kallon fuskar tauraruwar ta masoyiyar ta HEEDAYA ta yi a nan ta ga abin da bata yi zato ba
abin da ya saka ta a ruɗani wato ganin hawaye suna ƴar tseren fitowa daga idanun HEEDAYA.
Mamaki da al'ajabi ne suka dirar mata a lokaci guda.

'Mai ya sa HEEDAYA kuka? Ko zaton ta ba zan amince da Ya ABDUL ɗin ba shi ya sa take
zubar da hawayen tausayin za a mini aure da wanda ba na so?' Ta tambayi kanta a zuciyar ta
tana miƙa hannu a hankali ta kamo hannun HEEDAYA saboda yadda take jin zubar hawayen
HEEDAYA har ƙasan ranta, amma wanda ya ga kama hannun HEEDAYA da ta yi shi ya ga
janyewar HEEDAYA sosai abin ya taɓa mata zuciya har bata san yadda za ta fasalta abun ba.

Sai dai hasashen ta bai taɓa bata cewa HEEDAYA son Ya ABDUL ɗin take ba, da son shi take
ta tabbatar da ita wacce za ta fara sani ita dai kokwanton da ta shiga ya yi yawa har ta fara
tunanin ko dai Umma ta zaunar da HEEDAYA ne ta mata kuɗuba a kan ta daina kulata.

"Allah ya miki albarka Allah kuma ya sa abokin rayuwa na arziƙi ne wanda sai mutuwa ce za ta
raba ku, mun yanke hukunci ni da mahaifin sa a kan cewa nan da sati huɗu masu zuwa za a
ɗaura aure!" Cewar Abba.

"Allah ya tabbatar da alkairi Allah sa abokan junan arziƙi ne" Momma ta faɗa kai kana jin
muryarta ka san tana cike da shauƙi da farin ciki. Ido Abba ya tsare Umma da shi dakyar ta
daure ta ce

"Allah sa alheri" Ta faɗa tana jin ɗaci a zuciyar ta. Yanzu kam ta san shikenan ruwa ya ƙarewa
ɗan kada, gutsiri tsoma sai inda mai ya ƙare shiga motar mahaukaci, yanzu ne za su ƙara haɗe
mata kai, ita ba ta ƴar ta take yi ba ma da ta soyayyar ABDUL ɗin a zuciyarta ta tunanin yadda
zumunci zai cigaba tsakanin kishiyarta da facalar ta, tabbas ta yi da na sani a kan yadda ta
ɗauki Hajiya Fati a baya amma yanzu ta koya mata hankali da yi mata karatun ta nutsu.


Dining aka koma aka fara cin abincin dare, HEEDAYA ta zauna ne kawai tana wasa da cokali
a plate ɗin ta saboda ko loma ba za ta iya kai wa bakin ta ba. Aunty RABEEYA yanayin da ta
shiga na hukuncin da aka yanke a kanta ya sa ta kasa cin komai musamman ma da ta ga
HEEDAYA cikin wata iriyar damuwa, bare dama dukan su ba yunwa suke ji ba saboda ɗan
ciye-ciyen da suka yi wajen partyn HEEDAYA. Hajiya Baturiya har wani ƙwasƙwas take da
cokali in za ta ɗauki abincin duk don ta ƙonawa Umma rai.


Abba ne ya yi wa Mubashshar umarnin ya je ya ɗauro alwala su tafi masallaci, don shekarar
sa goma Mubashshar ɗin. Sauran kuma suka taso suka fito Momma ce riƙe da hannun Aunty
RABEEYA tana wani nuna murna a fili.

"Ka ga amaryar ɗana ABDULHAKEEM abin mu tuwona maina ni da aminiyata Hajiya Fati" Ta
ce tana yi wa Umma wani kallo ta wutsiyar ido Umma kuwa fuuuu ta fice su har tana neman
faɗuwa. HEEDAYA da ta fito tana haɗa hanya tsabar ɓacin rai ta zo ta wuce ta gaban su tana jin
Aunty RABEEYA tana kiran ta amma ko kallo bata ishe ta ba bare ta saka ran za ta amsa mata.


Ko da ta zo falon bata ga Umma ba hakan ya sa ta shige ɗakin ta tana zuwa ta kwanta
rubda ciki tare da fashewa da wani matsanancin kuka. Kukan take ko za ta ji sasaauci da
salama, amma tamkar ana ingiza son Ya ABDUL a zuciyarta sannan a yau ɗaya tak ta ji ta tsani
Aunty RABEEYA .Ƙaran wayar ta ne ya katsr mata kukan da take yi amma bata kawo wayar a
ka ba, don yanzu ba ta wayar ba take, amma jin kiran daga ya katse yake ƙara shigowa sai ta

tashi fuskar sharɓar da hawaye ta ɗakko wayar sunan Ya ABDUL da yake reto a kan screen ɗin
wayar ne ya sa zuciyarta mummunar bugawa.

Ya ABDUL kuwa bai san wainar da ake toyawa ba, bai san Abba sun yi magana da Daddyn sa
ba bare ya san har sun yanke hukunci uwa uba kuma har ya san Abba ya sanar da Aunty
RABEEYA za a haɗa su aure. Yau kawai ya ji a ransa ya dace ya je wa Aunty RABEEYA da
maganar soyayya a raɗin kansa don bai ga wata makusa ko naƙasu da aibu ba da za ta kasa
auruwa har ake matsa mata ta fitar da miji. Tun da ga shi ya gama karatun sa har yana aiki a
asibitin sa ya kamata kawai kowa ya ji bazata cewa shi ne zai auri Aunty RABEEYA sai dai yana
fatan ta karɓe shi da hannu biyu shi ne ya yanke shawarar kiran HEEDAYA domin ta raka shi ya
miƙa ƙoƙon barar sa duk da kasancewar Yaya a wurin ta amma babu raini a tsakani. Ya san
HEEDAYA za ta fi kowa farin ciki. Sai da ya shirya tsaf yana buɗaɗa ƙamshi shi ne ya shiga
kiran wayar HEEDAYAR ganin shiru bata ɗauka ba shi kuma ya ƙudurta a ransa cewa ba zai
wuce yau ba sai ya sanar mata, hakan ya sa ya kira Aunty RABEEYA da take kwance a
doguwar kujera a falo gabaɗaya hankalin ta yana kan HEEDAYA da ta yi fushi kuma babbar
damuwar ta bata san mene ne dalilin fushin ba, ga Momma ta dame ta da maganar
shirye-shiryen biki. Kiran da ya shigo wayarta ne ya dawo da ita hayyacin ta daga nutson da ta
yi a kogin tunani. Ganin sunan Ya ABDUL har sai da numfashin ta ya yi barazanar kufce mata
saboda yadda ta tsorata kiran ya zo mata a bazata, tunani barkatai suka cushe mata
ƙwaƙwalwa a kan ko ya kira ta ne ya kora mata gargaɗi.

Kasa ɗagawa ta yi har sai da ta tsinke wani kiran ya shigo, Ya ABDUL kuwa har ya fitar da ran
za ta ɗauka sai kuma ya ga ta ɗauka. Aunty RABEEYA wayar ta kai kunnen ta hannunta yana
karkarwa tana jiran jin abin da zai faɗa mata. Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke wanda har
sai da ita kanta ta ji ƙaran saukar ajiyar zuciyar.
"Ganin nan zuwa in same ki a falon baƙi" Haka kawai ya ce cikin bada umarni ya kashe wayar.
Duk da bata gama tantance dalilin zuwan nasa ba amma a ƙalla ta ji sanyi da rangwame don ta
ɗauka da faɗa zai balbale ta.


"Ina za ki je?" Momma ta jefa mata tambayar.

"Ya ABDUL ne yake kirana" Ta faɗa cikin sanyin murya. Wani murmushi Momma ta yi bata ce
komai ba. Jikin ta sanyi ƙalau ta nufi falon, ko da ta je shiga kawai ta yi ta zauna da yake ma
falon hanyar get yake zamanta ke da wuya ko minti uku ƙwarara bata yi ba ya shigo da sallama.
Kanta a sunkuye har ya shigo ya yi wa kansa masauki a kujerar da take dab da tata.
HEEDAYA kuwa tana ta ƙoƙarin haɗa kalmomin da za ta yi amfani da su wajen sanar masa
damuwarta har kiran ya yanke wayar ta ajiye zuwa can ta ƙara ɗakkowa ta bi kiran lokacin yana
falon baƙin tare da Aunty RABEEYA kiran nata ya shigo.

"Hlo Ya ABDUL"

" Gani a gidan ki zo ina falon baƙi akwai magana mai muhimmanci" Haka kawai ya ce ya kashe
wayar. Bata san ta aka yi ta tashi ba amma dai ta ganta a tsaye ƙiƙam ko wayar bata ɗauka ba
ta fito gabanta yana faɗuwa ta nufi falon baƙin tana rayawa a ranta wataƙila ya zo ya ce yana
son ta ne, ya zo ya furta mata kalmar so ne...



MAMAN AFRAH

09013181851
[2/6, 10:12 PM] MOM MASHKUR & AFRAH: BONONO


(RUFIN ƘOFA DA ƁARAWO)


NA


MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.


*SADAUKARWA*

Daga farko har ƙarshe sadaukarwa ne ga MARYAM SANI HAFIZ (Merry tah) Alkairin Allah ya
kai gare ki Allah lulluɓe rayuwar ki da tarin ni,imomi da albarkatu Allah raya mana Abdallah
fatan alkairi.

Daga marubuciyar:

Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Jalli joga
Da sauran su.

*09013181851*



PAGE 3

Gabaɗaya zuciyar ta ta kwaɗaitu ne da son jin furucin sa a gare ta, ba furucin komai ba face
na so da ƙauna tana fatan hakan, idan kuwa har ya furta to ai shi ba mace ba ne da za a ce za
a masa dole, kin ga ita Aunty RABEEYA sai ta haƙura wannan ne abubuwan da take rayawa a
ranta har ta ƙaraso falon. Ɗaga labulen ta yi tsabar hankalin ta ma ba ya tare da ita saboda
zumuɗi da fargaba ta manta da yin sallama. Sai dai abin da ta gani wanda idanunta suka yi
tozali da shi, ya so zautar da ita domin kuwa ta kiɗima. Ganin Ya ABDUL zaune a kujerar dab
da Aunty RABEEYA da ta sunkuyar da kai tana wasa da hannun ta shi kuma ya ƙura mata
idanu yana jifan fuskarta da wani irin kallo mai ƙunshe da ma'anoni da dama, ko wanda ba shi
ake yi wa kallon ba idan ya gani ya san so ne mai zallar cike da ƙauna bare kuma wanda ake yi
wa kallon.

"Ina son ki RABEEYA ina ƙaunar ki ina son na aure ki a kwana kusa, domin ki dawo kusa da ni
mu rayu a inuwa ɗaya... Wannan furucin da yake faɗa yana wani murmushi su ne suka daki
kunnuwan HEEDAYA ta ji tamkar wanda aka watsa mata tafashashshen ruwa a jiki, karkarwa ta
shiga yi jin jikinta ya ɗauka tamkar mazari, lokaci guda wani abu ya zo ya tokare a zuciyar ta
ƙwaƙwalwar ta ta toshe ta ma rasa wane abu ya kamata ta yi, a hankali ta saki labule ba tare da
sun san da zuwanta ba bare har su ganta juyawa ta yi da gudu ta nufi part ɗin su.

Ɗakin ta ta shiga ko rufewa bata yi ba ta kwanta tare da sakin kuka mai cin rai, tana jin wayar
ta tana ta ruri bayan jimawa kaɗan amma ko ɗagowa bata yi ba ta san ba zai wuce Ya ABDUL
ba, wanda a yanzu take jin haushin sa don ya mata gagarumin laifi, laifin kuwa bai wuce na
furtawa wata ƴa mace kalmar so ba kalmar da ta yi ta dakon ranar da zai furta a gare ta amma
hakan ya gagara ta ci burin furta masa ita ko da ba zai amince ba, amma yau ya furtawa Auntyn
ta RABEEYA wannan wace irin baƙar rana ce? Sai dai abin mamaki sai ta ji duk duniya babu
wanda take jin tsanar sa sama da Aunty RABEEYA ba don komai ba sai don wanda take so
wato Ya ABDUL ta furta kalmar so a gare ta.


Ya ABDUL kuwa bayan ya gama kiran HEEDAYA ganin bata zo ba sai ya yanke shawarar
isar da saƙon nasa tun da ji yake ya ƙagu ya furta mata. Shirun Aunty RABEEYA da yadda take
sakin wani sassanyan murmushi ya tabbatar masa da maganar sa ta samu matsugunni a wajen
ta, hakan ya sa bayan ya isar da saƙon ya ƙara kiran HEEDAYA jin bata ɗauka ba sai suka
shiga tattaunawa tana faɗa masa abin da Abba ya faɗa mata ɗazu sosai ya ji daɗin jin wannan
batu sai ya shiga godewa Allah.


A can su Ya ABDUL bayan Daddy ya faɗawa Ammie abin da suka yanke shi da Abba na

haɗa Ya ABDUL da Aunty RABEEYA sosai ta ji daɗi tamkar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha.

Umma kuwa abin duniya ne ya haɗe mata goma da ashirin, sosai take jin baƙin cikin wannan
auren da za a haɗa saboda ta san sai sun ƙara haɗe mata kai. Wani irin takaici take jin don
yanzu in akwai abin da yake ci mata tuwo a ƙwarya bai wuce haɗin kan Hajiya Fati da Hajiya
Baturiya ba. Jin ta kasa jurewa da sauri ta shanye damuwar ta ɗakko wayarta ta shiga dokawa
Hajiya Aisha ƙawarta kira, bugu ɗaya biyu ta ɗauka tamkar wanda take jiran kiran dama.

"Barka da dare ƙawata kin wuni lafiya?"

"Ba lokacin gaisuwa bane babu lafiya"

"Subhanallahi! Mai yake faruwa ne ƙawata?"

"Wani bala'i ne ya tunkaroni" Nan ta kwashe abin da yake faruwa ta faɗa mata, har furucin
HEEDAYA a kan soyayyar ABDUL ɗin. Wani uban ashar mai maiƙo Hajiya Aisha ta narka kafin
ta ce.

"Amma ke dai wallahi ban san ranar da ƙwaƙwalwarki za ta fara aiki babu gargada ba, yanzu a
ce HEEDAYA ta miki wannan furucin maimakon tun kafin shi Alhaji Bashir ɗin ya tara ku ki je ki
tunkare shi da maganar, da a ce kin kirani a lokacin kin faɗa mini da na baki shawarar yadda za
ki yi, ai shi ya sa a rayuwa ba a so mutum ɗaya ya yanke hukunci da kin ga idan ya ji wannan
furucin dole ya dakatar da maganar shegiyar kwantan yarinyar can RABEEYA amma yanzu kin
bari komai ya caɓe"

"Haba Hajiya Aisha ya ana nuna miki annabi kina runtse idanu? Ina nuna miki gabas amma kina
kallon kudu? Maganar yaron can ɗan gidan Hajiya Fati fa nake miki amma kina batun in amince
da batun HEEDAYA. Shin har kin manta butulcin da Hajiya Fati ta yi wa ƙawance na da ita? Kin
manta yadda kishi ya rufe mata idanu ta turbuɗawa idanun ta toka ta shuka mini rashin mutunci
a kan abin da bani da masaniya tun daga nan sai baƙar gaba ta koma suka jone da kishiyata,
amma yanzu kike batun amincewa da auren su in ce na aurawa ƴata wa? Ɗan maƙiyata k...

"Don Allah dakata Hajiya Zainab, duk kin harzuƙa sai zuba kike ba comma ba fulstop mai ya sa
wani lokacin tunanin ki irin na yara ne? " Ɗif Hajiya Zainab ta yi ranta yana ƙuna wai ita ce mai
tunani irin na yara Hajiya Aisha bata jira ta amsa mata ba don bata ma bata damar ba ta cigaba
da faɗin.
"Ita Hajiya Fati ba saboda mijin ta Alhaji Mukhtar ya ga ƙawarki Hajiya Bilkisu ya ce yana so ba
ne asalin rigimar, duk da ke baki san ma sun haɗu sun ƙulla soyayya ba amma da batun aure
ya tashi ta ɗora laifi a wuyanki tana ganin da haɗin bakin ki za a ci amanarta a mata kishiya,
duk irin amincin da yake tsakanin ku amma ta sa ƙafa ta yi fatali da su, ta shuka miki rashin
mutuncin da kika biye mata kuka kwashi ƴan kallo, kuma daga ƙarshe auren bai yiwu ba saboda
masifar faɗan da aka sha yi ba sai ta koma ta jone da kishiyar ki ba?..

"Sai wani maimaicin abin da ya wuce kike na fi so kawai ki faɗa mini abin da zai rage mini zugin
da nake ji a zuciyata amma kina mini lissafin abin da na sani" Hajiya Zainab ta katse ta.
"Ki cigaba da saurare na za ki ji bakin zaren, to idan yanzu HEEDAYA ta auri ABDUL kin ga
mun jefi tsuntsu ɗaya da dutse biyu. Na farko ɗan ta ya dawo hannun mu tun da yana auren
HEEDAYA a nan ne za a yi amfani da shi a ƙuntata mata, ɗanta ya zama mijin ta ce ya manta
da ita yake bautawa sirikar sa wato ke kenan da matar sa wato ƴarki kenan, takaici baƙin ciki
duk za su taru su mata rubdugu, sannan na biyu kin aurawa ƴarki muradin ta" Tun da ta fara
faɗar maganganun Umma ta yi tsai tana jin yadda take zaro magana tamkar wata computer
sosai take jinjinawa ƙwaƙwalwar ƙawar tata saboda kaifin basira tana kuma mamakin ya aka yi
ita bata yi wannan tunanin ba ya aka yi tun da HEEDAYA ta faɗa mata tana son ABDUL sai
kawai ta hau dokin zuciya take ta sukuwa?.

"Kai ƙawata gaskiya ƙwaƙwalwar ki tana ja" Umma ta ce tana jinjinawa lamarin.

"To ai shi ya sa nake faɗa miki mugu shi ya san makwatar mugu, ai in ita sakarai ce bata amfani
da tunani wajen yanke hukunci to wallahi da sannu sai mun nuna mata shayi ruwa ne, sai mun
zame mata ciwon ido sai ta yi da na sanin ci miki mutunci a rayuwa. Ban san mai ya sa mata
wasun su basu da tunani ba wai duk lokacin da za su samu labarin mijin su yana da budurwa ko
zai ƙara aure, ko kaɗan basa duba cewa shi fa mijin nan nasu shi ne ya je ya ce yana son
macen ba wai macen ce ta ce tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login