Showing 27001 words to 30000 words out of 64514 words

Chapter 10 - BONONO BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MAMAN AFRAH f.pdf

30 Mar 2025

5102

duk yadda aka ce haka na y...

"Babu wani nan HEEDAYA kin yi wa Daddyn ABDUL magana"

"Wallahi ban masa magana ba" HEEDAYA ta faɗa hankali tashe duk ta ruɗe, don ita bata ɗauki
uhm-uhm ɗin da ta ce masa a matsayin magana ba bare har ta yi zaton za ta karya sharaɗi.

"Na ga komai a wajen boka tamkar muna nan aka yi uhm-uhm ɗin da kika faɗa ita ce ummul
aba'isin komai ai na faɗa miki ko uhm kar ki sake ki ce"

"Na shiga uku na ɓata aikina da kaina ya za a yi yanzu Umma?" Ta tambaya tana zaro idanu
tana jin ina ma ana mayar da hannun agogo baya da kuwa ta sauya wannan abin da ta yi sai
dai kash aikin gama ya gama.

Hajiya Aisha ce ta turo ƙofar ta shigo. Bakin gadon ta ƙarasa ta zauna jiki sanyi ƙalau don
yau dai sun faɗo ƙasa wanwar ga shi sun iyo gayyata ta fitar hankali kaf ƙawaye da abokan
hulɗa babu wanda basu gayyata ba ta san wuyar ta la'asar ta yi jama'a za su fara musu dafifi ga
kayan rabo da suka yi kamar ba gobe sai dai ta san za a zo a tarar da su jingum-jingum indai ba
dariyar yaƙe za auke yi ba ta san da wuya fuskar su bata fallasa asirin zuciyar su ba. Amma
tana fatan taro ya watse ba tare da matsalar da suke ciki ba ta bayyana kanta.


"Babu yadda za a yi" Umma ta faɗa tana tahowa ta zauna kusa da Hajiya Aisha tare da sakin
ajiyar zuciya.

"Wallahi ba da son raina ba haka ta faru Daddyn ne da shegen faɗa a hakan ma dakyar na tsira
da na san hakan da na yi zai ɓata aiki wallahi da ko kashe ni zai yi ba zan ce komai ba" Ta faɗa
tana dawowa inda suke ta kifa kanta a cinyar Hajita Aisha tare da fashewa da matsanancin
kuka. Bubbuga bayanta Hajiya Aisha ta shiga yi tana lallashin ta.

"Ki yi haƙuri boka ya ce akwai aure tsakanin ki da ABDULHAKEEM" Hajiya Aisha ta faɗa cikin
lallashi. Da sauri HEEDAYA ta ɗago tana kallon ta da alamar son ƙarin bayani gabanta tana
faɗuwa ta ce.

"Ta yaya? Bayan an ɗaura masa da Aunty RABEEYA ko sakin ta zai yi?" Ta tambaya.

"Mu kan mu bamu da amsar tambayar nan HEEDAYA haka dai ya ce kuma shi kansa bai san
yaushe ne ba amma ya tabbatar mana da haka" Shiru ta yi tana nazari tare da son gano bakin
zaren da kuma manufar bokan a kan furucin nasa sai dai ƙwaƙwalwar ta bata hasaso mata
komai ba.

"Yanzu ki tashi ki koma ɗakin ki, sannan ki saki jiki ki cigaba da aiwatar da al'amuranki cikin
natsuwa kar ki yarda a fahimci akwai damuwa a tare da ke bare har magauta suke tunanin
baƙin ciki kike da auren" Hajiya Aisha ta ce


"Wallahi ba zan iya ba ba zan iya ɓoye damuwata ba hakan ma ƙarfin hali ne kawai amma dai
ko kaɗan ba zai ɓoye ba dama bahaushe ya ce labarin zuciya a tambayi fuska" HEEDAYA ta
faɗa tana tashi ta haura kan gadon ta kwanta rubda ciki. Ranta tana ƙuna tana jin yadda son Ya
ABDUL yake ta safa da marwa a tsakanin birnin zuciyar ta.

Ƙaran wayar ta ne ya dakatar da ita. MEEMA ce ƙawarta ɗagawa ta yi.

"HEEDAYA wai kina ina ne halan baki ji sanarwar ɗaurin auren nan ba, shin baki san kwaɓar ki
ta cika da ruwa ba"


"Na sani MEEMA duk wanda suka zo domin gayyatar da muka musu wato ƙawayen mu ki ce
musu bani da lafiya ina kwance na samu bacci" Tana jin MEEMA tana ƙoƙarin magana amma ta
datse kiran tare da jifa da wayar a kan gadon ta cigaba da kukan zuci wanda ya fi na zahiri ciwo
da suka a zuciya.

Da yamma taro ya yi taro ko ta ina mutane ne, gida ya cika da jama'a amarya RABEEYA nemab
duniyar nan ta yi wa HEEDAYA amma bata ganta ba hasali ba wayarta a kashe har Ya ABDUL
ma sai da ya tambaye ta ganin jiya duk inda suka saka ƙafa a wajen kamu sai ta ɗora tata
amma yau kamar an yi ruwa an ɗauke. Su Umma ma sai yaƙe suke yi wa baƙin su amma kana
ganin su ba haka aka so ba wai ƙanin miji ya fi miji kyau!.

Sai da dare aka fara riɗin tafiya kai amarya, amarya ta shirya cikin shiga ta alfarma, Aunty
Hafsa da baki ya ƙi rufuwa ita ce mai taya ta komai kuma ta ji daɗi da aka ɗaura auren da ita
duk da ta ga HEEDAYA da Umma har ma da Hajiya Aisha suna fushi da ita amma wannan mai
sauƙi ne wai cire wando ta ka, hatta Ihsan ma sai wani cin magani take Mubashshar ne ma
yana wajen Abba. Naeema sai shiga ake ana fita ita da Momma har sai da dare ya yi suka
tsagaita lokacin ana ta fafutukar kai amarya. Amarya da addu'a aka shigar da ita tafkeken gidan
ta wanda ya ji kaya kamar ba gobe sai ƙamshin turaren wuta ɗan mai duguri ne ya cika ko ina.
Kowa ya watse aka bar amarya ita kaɗai hatta ƙawayen amarya babu wanda ya zauna.


An bar ta ita kaɗai zaune a tsakiyar luntsumeman gadon ta tana ta addu'a a zuciyar ta haɗe
da godiya ga ubangiji da ya nuna mata wannan rana mai matuƙar tarihi a rayuwar ta. Duk da
tana ta mamakin yadda aka rako ta ɗakin ta ba tare da masoyiyar ta HEEDAYA ba don a wani
ɓangare na zuciyar ta ma tana jin babu daɗi ganin bata ga HEEDAYA ba.

Za ku ji mun shigo da sabbin fuskoki ckn labarin mu, to kowa da rawar da zai taka a ciki, da
sannu zan ke feɗe muku biri gar wutsiya kun san dai taken alƙalamin MAMAN AFRAH ba ya
rubuta shirme

MAMAN AFRAH
09013181851
[2/13, 9:10 AM] MOM MASHKUR & AFRAH:
https://chat.whatsapp.com/F7TUZezpOWLKYnyTNFuy2Y



BONONO


(RUFIN ƘOFA DA ƁARAWO)


NA


MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.


*SADAUKARWA*

Daga farko har ƙarshe sadaukarwa ne ga MARYAM SANI HAFIZ (Merry tah) Alkairin Allah ya
kai gare ki Allah lulluɓe rayuwar ki da tarin ni,imomi da albarkatu Allah raya mana Abdallah
fatan alkairi.

Daga marubuciyar:

Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Jalli joga
Da sauran su.
*09013181851*



PAGE 8



*MARYAMA*


Amma duk jijjigar da take masa babu alamun ko motsawa zai yi lamarin da ya ƙara saka ta
shiga tashin hankali, gabaɗaya ta firgice tana kukan tamkar ranta zai fita. Inna da ta fito daga
bayin da ɗaki za ta shige amma jin kukan MARYAMA ya tsananta sai ta ƙara jan tsaki tare da
nufar ɗakin Baffan a nufin ta ta koro ta daga ɗakin don a tunanin ta, jikin sa ne ya matsa take ta
faman maganganun nan da kuma kukan. Sai dai ganin kansa ya langaɓe gefe bata bi ta kan
MARYAMA ba ma nufar sa ta yi ƙirjin ta yana bugawa ta shiga dudduba shi sai dai abin da ta
gani ya mugun ɗaya mata hankali domin kuwa ta tabbatar da cewa rai ya yi halin sa, don har
dafara ta fito masa. Wani kuka ta fashe da shi tana kiran sunan sa MARYAMA ita ma ganin
hakan ta tabbatar Baffa ya yi bankwana da duniya mutum ɗaya tamkar da miliyan a wajen ta,
masoyin da duk duniya bata da kamar sa. Maimunatu da take bacci tun tana jin kukan su
sama-sama har ya zamana ta buɗe idanun ta da sauri ta fito daga ɗakin Inna, ta nufi ɗakin
Baffa inda a can take jiyo kukan da ya karaɗe gidan tamkar gidan makoki, duk da zato da
tunanin ta bata taɓa kawowa Baffa mutuwa ba duk ta zaci jikin sa ne ya matsa sosai sai dai
tana zuwa ta yi mugun gani wanda aka haɗu da ita aka cigaba da kokawa.

"Shegiya baƙar ƙaddara annoba, mai mugun hali maciya amana, kin kashe mini uba kin ji daɗi
dama ke shegiya ce baki da shi uban, tashi ki fice a ɗakin tun da babu ƙwandalar ubanki a
wajen gina ɗakin" Maimunatu ta faɗa cikin muryar kuka tana jin kamar ta rufe ta da duka.

"Ta sa baƙin cikin, ɗan gaba da fatihar da ta samo ya yi ajalin sa wallahi kin cuce mu MARYAMA
haƙƙin Malam ba zai barki ba" Inna ma ta faɗa cikin kukan tana jan hanci. Dakyar ta iya miƙewa
jiri yana ɗiban ta jin ta take tamkar ba a raye take ba ji take tamkar a wata duniyar ta daban
take, ɗacin da magagin mutuwar Baffa haɗe da zargin ita ce silar mutuwar sa ya taru ya haɗe
mata.

Ko gabanta bata gani haka take jefa ƙafafun ta, ɗakin Goggo ta nufa wanda ya kasance
makwancin ta ita kaɗai a yanzu a baya kuma kafin mutuwar Goggo tare suke kwana a ɗakin.
Tana shiga ɗakin ta durƙushe a wajen tare da sakin kuka mai cin rai, ta sani tabbas cewa kuka
ga mamaci ba alkairi ba ne, ba a hana kukan mutuwa ba amma irin kukan nan da ake
iface-iface ana an mutu an lalace babu kyau sam!.

Tana daga ɗakin tana iya jiyo sautin kukan su Inna, ita kuma tana daga ɗakin nata tana yi wa
Baffa addu'a da nema masa gafarar ubangiji sai dai ta kasa dakatar da zubar hawayen ta. Tana
jin ƙaran buɗe ƙofar gidan da alama fita aka yi kiran wani jim kaɗan ta ji an shigo tana iya jiyo
muryoyin maza. Ita dai bata fito ba sai doshin asuba, idanun ta sun yi luhu-luhu. Har aka shirya
Baffa tana daga can ƙofar ɗakin Goggo a zaune don mugun tabon da jama'ar gari suke mata
bisa jahilci ko cikin mutane bata shiga, idan kuwa ta shiga ta san tabbas ranar za ta yi ta jin
baƙaƙen maganganu. Yanzu ma daga inda take matan wasu daga ciki suna jifanta da wani kallo
suna taɓe baki wasu suna raɗa. Ko gawa ba a ɗauke ba amma mutane basa tuna tasu
mutuwar, basu su san cewa watarana ko yau ko yanzu ma tasu tana iya riskar su.

"Iyalan mamacin su shigo su masa addu'a" Muryar liman ta katsewa MARYAMA tunani. Kamar
wacce aka tsikara haka ta miƙe tsaye tana son yi wa Baffa kallon ƙarshe duk da ta san ba lallai
ta samu hakan ba. Inna da Maimunatu ne sai wasu ƴan uwan sa guda biyu suka nufi ɗakin da
sauri ta bi bayan su ita ma. Kwance yake sanye da likkafani har fuskar an rufe wacce ita ta so ta
ƙara yin tozali da ita sai dai Allah bai nufa ba domin kuwa an gama shirya shi tsaf.

A gaban gawar ta durƙushe tana shirin fara masa addu'ar kuka ya kufce mata.

"Sanadin abin kunyar da ta jawo ne Malam ya haɗiyi zuciya ya mutu!" Inna ta faɗa cikin muryar
kuka. Umarni aka mata ta tashi ta fita saboda yadda Maimunatu da Inna suke kuka suna
maganganu haka ta fito jiki a saɓule ta zo ƙofar ta tsaya bayan sun fito aka ce a bayar da hanya
za a fito da gawar daga can gefe ta tsaya hannunta ɗaya a tsakiyar kanta, a haka aka fito da
makarar da aka saka Baffa gida ya ruɗe da koke-koke Inna da Maimunatu sai riƙe su aka yi
ganin kukan nasu ya zartar hankali. Bakin ƙofar gidan ta je ta tsaya tana kuka marar sauti. Tana
jin yadda mata suke yi da ita a kan cikin jikin ta da kuma wai baƙin cikin ta ne ya kashe shi wai
bata yi halacci ba. Tana nan tsaye har aka tafi da shi har sai da ta daina hango su, bata bar
wajen ba sai da aka kawo zanin da aka lulluɓa masa.


" Kukan munafurci kike ai ki haɗa kayan ki ki san inda dare ya miki wanda kike zaune don shi

ɗin kin kashe shi kin huta, kuma sanin kan ki ne baki da gadon sa! Ai ni dama na san barewa ba
za ta yi gudu ɗanta ya yi rarrafe ba, yadda ta samar da ke ta ɓarauniyar hanya shi ne ke ma
kika ɗakko naki cikin za ki samar da wani ko wata ta ɓarauniyar hanyar" Inna da ta samu
MARYAMA zaune a ɗaki ta faɗa mata.
"Don Allah Inna ki yi haƙuri wallahi ban san inda zan je bani da kowa kuma bani da komai" Ta
faɗa cikin roƙo hawaye yana zuba don ganin ta tausaya mata amma babu wani tausayi ta ce ta
bata minti ashirin ta fice musu daga gida ta tsani ganin ta. Kayanta ta haɗa ta fito daga ɗaki ta
ƙarasa gaban tabarmar da su Innar suke zaune ta ce
"Inna Baffa ya ce mini in ɗauki kaya a akwaitin ƙarfen saman lokar sa"

"Ba sai ki je ki ɗauka ba indai wannan kayan ne da yake ajiye da su shekara da shekaru" Jiki
babu ƙwari ta je ta ɗaukko ta fito ta saka a cikin kayan nata.

"Inna zan tafi don Allah ku yafe mini wallahi ba ni...

"Har duniya ta naɗe ba zan taɓa yafe miki ba, kin yi silar rabani da mahaifina" Maimunatu ta
faɗa tana aika mata kallon tsana Inna kuwa ko kallo bata ishe ta ba sauran matan wajen ma
maimakon su bada baki sai zuga suka shiga yi. Haka ta tashi ɗauke da kayan a hannun ta har
ta kusa fita ta juyo tana yi wa gidan kallon ƙarshe tare da ficewa.
A ƙofar gidan ta samu maza zaune a tabarma. Haka ta wuce tana sunkuyar da kai ta nufi
hanyar bayan gari tana iya hango hanyar maƙabartar daga nesa tana jin kewar Baffan ta
maganin kukan ta, Baffan ta mai share mata hawaye Baffan ta mai yarda da ita mai faɗa da
kowa don ganin ya kare ta amma yau an wayi gari ƙasa ta rufe masa idanu. Tafiya take a
ƙafafun ta bata san ina za ta dosa ba, bata kuma san ina za ta je ba sai dai ta san ko ina za ta
je dole ta yi tazara da garin don daga garin nasu da ta baro har sauran ƙauyukan waɗanda
suke maƙotaka da shi duk sun san wace ce ita kuma ta san babu wanda zai yarje ta zauna
masa a gida kai hatta gari ma sai an yi da gaske, can ma ana ƙyamatar ta sanadin bata da
iyaye ba a san su waye iyayen ta ba bare yanzu kuma ita ce mai ɗauke da cikin!.



*HEEDAYA*

Bacci ya ƙauracewa idanun ta, ranta a ɓace yake tana jin tamkar ta zama tsuntsuwa ta je
gidan Ya ABDUL ɗin ta hana su gabatar da komai ko ta samu saasuci amma ina!.


Baƙin cikin da take ji a zuciyar ta kwatankwacin baƙin ciki da ɓacin ran da wacce aka yi wa
kishiya take ji a ranar da amaryar ta tare. Haka ta kwana da zulumin Aunty RABEEYA ta hau
matsayin ta yanzu kam ƙiyayyar da take mata ta zama biyu don ta kusanci mijin ta yanzu zafin

yana damfare da zafin kishin Ya ABDUL da take jin hawa da sauka na farashin soyayyar sa
tamkar wanda ake rura wuta haka wutar son sa take balbala a zuciyar ta so take ma ta yakice
shi amma abu ya ci tura!.

Wajen ƙarfe huɗu na asuba ta ji ta kasa jure yanayin da take ciki, ji take tamkar an ɗakko
dutse an ɗora a ƙarƙashin ƙirjin ta, ƙirjin ya yi mata nauyi sosai. A ƙarshe ta yanke hukuncin
kiran wayar Ya ABDUL ɗin don ko ta rage zafi da raɗaɗin da take ji na kishi fatan ta a zuciyar ta
shi ne Allah sa dai babu wani abu da ya wakana a tsakanin ma'auratan biyu!. Don ko da su
Umma suka ce bokan ya ce akwai aure tsakanin ta da Ya ABDUL sai ta ji ta ƙara ɗora rai a
kansa duk da kasancewar sa miijn ƴar uwar ta kuma da a ce tana da iko da ta dakatar da komai
don a jira lokaci a jira ranar da zai zama nata mallakin bata so ko kaɗan ya kusanci wata ƴa
mace matsawar ba ita ba ce.


Cikin dakiya da rashin gudun abin kunya ta ɗaga wayar ta kamo sunan sa ta shiga doka
masa kiran.

A can gidan amarya kuwa bayan komai ya gama wakana tsakanin su, cikin farin ciki da
annashuwa kowa ya yi murna da kasancewa da abokin rayuwar sa Ya ABDUL sai albarka yake
sanyawa Aunty RABEEYA ita kuma duk kunya ta dabaibaye ta ji take tamkar ƙasa ta tsage ta
shige ciki saboda nauyi da kunyar sa. Ganin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login