Showing 36001 words to 39000 words out of 64514 words

Chapter 13 - BONONO BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MAMAN AFRAH f.pdf

30 Mar 2025

5097

ni!. Tabbas ni kaina tausayin kaina nake' Ta
ƙarasa faɗar hakan a zuciyar ta wani kukan tausayin kanta yana ƙwace mata ta shiga rera shi a
fili ba tare da ta shiryawa hakan ba.


"Waye a nan?" Ta tsinkayi ana tambayar ta wata faɗuwar gaba ce ta ziyarce ta da sauri ta saka
hannu ta damƙe bakin ta da hannu biyu tana zare ido ta cikin ɗan duhun magribar da ya fara yi
wa wajen ƙawanya...


MAMAN AFRAH
09013181851
[2/16, 7:55 PM] MOM MASHKUR & AFRAH:
https://chat.whatsapp.com/F7TUZezpOWLKYnyTNFuy2Y

BONONO


(RUFIN ƘOFA DA ƁARAWO)

NA


MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.


*SADAUKARWA*

Daga farko har ƙarshe sadaukarwa ne ga MARYAM SANI HAFIZ (Merry tah) Alkairin Allah ya
kai gare ki Allah lulluɓe rayuwar ki da tarin ni,imomi da albarkatu Allah raya mana Abdallah
fatan alkairi.

Daga marubuciyar:

Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Jalli joga
Da sauran su.
*09013181851*



PAGE 10



*HUSNA*


Tana nan zaune amma babu alamar HAMEED zai fito daga ɗakin bare har ta saka ran za
ta samu biyan buƙata sai dai bata karaya ba domin kuwa a ranta tana tunanin ko dai maganin
ne bai gama bin jikin sa ba bare har ya fara masa aiki. Hakan ya saka take zaune tana danna
waya wtsapp ta shiga ta buɗe group ɗin nan nasu wanda iya matan aure ne kawai a ciki, duk
wata mace wacce ba matar aure ba ko ta shiga waje ake yi da ita, shi ya sa ma kana shiga
group ɗin za ka ci karo da dokokin group ɗin wanda waɗanda suka san su ƴan mata ne ko

zawarawa ma suna ganin dokokin suke fita daga group ɗin shi ya sa ma yawanci duk sai ta
dalilin wasu ake shigowa ma'ana sai kina da ƙawa a cikin group ɗin sannan idan za a saka ki
sai kin bi ta hannun admin ta tsare ki da tambayoyi kamar ba gobe shi ya sa ma sun fi yin
adding da wuya su fitar da link. MANYAN MATA shi ne sunan group ɗin.
Saƙonnin ta hau duddubawa kamar kullum don bata yarda ta bar saƙonnin group ɗin
MANYAN MATA bata buɗe ba saboda abubuwan da ake gabatarwa a ciki. Hirar da ta ga ana yi
ce ta ƙara mata damuwa a kan wacce take ciki, don dama matan group ɗin basu da aikin da ya
wuce bankaɗa sirrin mazajen su da yadda kowacce take samun tarayraya da kulawa a wajen
mijin ta wannan shi yake ci wa HUSNA tuwo a ƙwarya domin ita a wajen ta babban abu ne tun
da ba samu take yi ba abu ne mai wahala shi ya sa ma ko hira ake sai dai ta ja gefe tana
karantawa tana mamakin dama akwai irin waɗannan mazan a duniya amma mai yasa ita bata yi
dace ko gam da katar na samun irin su ba? Tana alaƙanta hakan da cewa ƙaddarar ta ce haka
sannan ita bata iya ƙarya ba wato ta zauna tana yabawa haɗe da koɗa miji a kan kulawar sa
gare ta tun da ta san ba samu take yi ba.

Ta yi nisa a cikin karanta saƙonnin kafin ta ga kowacce tana yin sallama a kan cewa babyn ta
yana buƙatar kasancewa da ita haka kowa ya watse admin ta kulle gidan ya koma only admin
can send message. Hakan ya sa ta sauka ma daga whatsapp ɗin gabaɗaya ta ajiye watar tare
da sauke nannauyar ajiyar zuciya, tagumi ta yi da hannu biyu tana tuna ita sai yaushe ne za ta
samu waraka daga wannan damuwar gidan auren nata kowacce mace tana jin daɗi da
kasancewa kusa da mijin ta amma ban da ita abu babu marmari koyaushe cikin wannan
matsala shin sai yaushe ne za ta yi ban kwana da damuwar rashin kulawar miji? Ko a haka za
ta ƙare rayuwar ta cikin ƙunci. Tun tana zaune har ta fara gyangyaɗi bacci ya soma awon gaba
da ita a zaunen ba tare da HAMEED ta ji ko da ƙaran buɗe ƙofar ba ne bare har ya zo da haka
ta zame ta kwanta wani ɓarawon bacci ya yi gaba da ita.

HAMEED kuwa tun daya karɓi kayan da ta miƙo masa ya ajiye zaunawa ya yi zai tsiyaya sai
kawai wayar sa ta yi ƙara ganin budurwar sa sai ya washe baki ya koma bakin gado ya zauna,
katse kiran ya yi don ba ya so kuɗin ta ya tafi gwara na shi ya tafi duk da shi yake saka mata
katin. Kiran ta ya yi tana ɗauka ta fashe da wani kukan shagwaɓar da ya sa ya ja filo ya kwanta
yana sauraron muryar ta da take rikita duk wata nutsuwar sa. Lallaɓa ta ya shiga yi ita kuwa ta
shiga kashe murya tana mashe murya ta fara masa hirar don akwai wasu kuɗaɗe da take son
karɓa daga hannun sa.

"Sai in ji duk muryoyin matan duniya amon ta tamkar ƙaran jiniyar ƴan sanda suke idan suna
magana, matsawar kika yi magana to fa taki tamkar busar sarewa ce" Ya ce yana wani koɗata
tare da zuzutata jin haka sai ta ƙara zage dantse ta shiga masa yadda suka saba a ƙarshe suka
koma video call cikin hirar banza da nuna abin da ya haramta, nan suka raba dare suna
haramtacciyar soyayyar da suke ganin more rayuwa ce kuma wayewa ya manta da matarsa ta
sunna da take ta faman bibiyar haƙƙin ta ma ya hana ta bayan wanda yake bi ɗin babu abin da
za su nuna mata tun da babu abin da ta rage sa da shi sai dai ƴan magana suka ce abincin
ƙwalama ya fi daɗi.

Hakan ya sa ya mata alƙawarurruka da dama bayan maƙudan kuɗin da ta tambaya. Yana
kashe wayar ya yi wankan ibada ya yi shame-shame a kan gadon bacci ya yi awon gaba da shi
ba tare da ya bi ta kan shayin da HUSNA ta sha wahala wajen dafa masa ba, tare da amfani da
magani don samun biyan buƙatar ta a matsayin ta na mace mai lafiya kuma wacce bata bibiyar
mazan waje ta tsare kanta.


Ko sallar asuba bai yi ba don sai wajen bakwai ya tashi shi ma kiran SUMY budurwar sa ne
ya tashe shi. Ɗaga wayar ya yi yana kallon sunan ta da yake yawo a saman wayar ya ce.

'Kai sai ni HAMEED mai kala-kala mai buhu -buhun ƴan mata' Ya faɗa a zuciyar sa yana tashi
zaune ya ɗaga kiran.

"Haba baby HAMEED ya haka za ka manta da ni kwana ɗaya tal fa ka ce za ka yi" Ta ƙarasa
faɗa cikin shagwaɓa.

"Haba SUMY yanzu fa ƙarfe bakwai amma kuma har kin fara ƙorafi kin san dai yau ba za ta
wuce ba komin dare a Lagos zan kwana" Wannan furucin ne ya sa ta ji daɗi suka gaisa cikin
soyayya sannan suka yi sallama. Ajiye wayar ya yi tare da tashi ya shiga wanka ya ɗauro
alwala sai da ya shiya sannan ya gabatar da sallar asuba, jakar kayan sa da ya dawo da ita jiya
ya zazzage a kan gado tare da ɗakko wasu kayan a wardrobe ya shirya a jakar tashi da suk
abin da zai buƙata sai kuma ƙarama mai wasu takardu. Ƙasa ya sakko da su. HUSNA da take
kicin tana haɗa break fast sai jin ƙara gara akwati ta yi gabanta ne ya faɗi da sauri ta leƙo daga
kicin ɗin, abin da ta zata ne ta gani wato jakar HAMEED shi kuma yana tsaye tana ɗaura
agogo. Tsabar takaici ma ta rasa bakin magana gas ta koma ta kashe don bata ga dalilin dafa
abincin ba tun da wanda take yi don shi ba ci yake ba ko na jiya da dare ma bai ci ba.


Falon ta fito zuciyar ta babu daɗi lokacin ya zauna yana waya, jim kaɗan direban da ya yi wa
waya ya shigo ya ɗauki jakar ta fita da su.

"Akwai wani abu da kike buƙata a cikin gidan ne ko akwai abin da ya ƙare? Cikin kayan store
mene ne babu?" Ya tambaya haɗe da ɗakko 500k ya ajiye a gabanta. Hawayen da take
maƙalewa ne suka surnano mata ta ɗago ta tsare shi da idanun ta ce


"Bana buƙatar komai, akwai komai da komai, sai dai abin da na fi buƙata shi ne babu akwai shi
amma bani da iko a kan sa" Ta ƙarasa faɗa muryar ta tana fallasa asirin zuciyar ta na raunin da
ta yi.

"Mene ne shi mene ne ya ƙare da har kike so ai babu wani abu da baki da ikon ko nawa ne zan

siya miki...

"Kai ne HAMEED kai nake buƙatata, kai ne bani da iko, sai yaushe za ka zauna da ni a gida?
Kullum kai hankalin ka a bussines babu ruwanka da ni da haƙƙina ka yi wata biyu baka nan
amma ka zo ka yi kwana ɗaya ka ce za ka tafi kuma ba tare da ko makwanci ka haɗa da ni ba,
shin dutse ce ni? Ko ka fi son na fara siyar da mutunci na ga wasu mazan ko kuma in fara
holewa da mazan banza a socila midea...

"Wace irin magana ce wannan HUSNA sau nawa kike so in maimaita miki gida kike so in dawo
in zauna kin sani da cewa kamfanina nake zuwa aiki nake ko zan fasa al'amurana ne saboda ke
shin ni mace ne da zan dawo gida in zauna ai zaman gidan sai mata, ko nusarin namiji zan
mayar da kaina saboda in daɗaɗawa mace? Na zo a jiya saboda da ke na dawo yau an mini
waya da sassafe ana buƙatata a kamfani domin saka hannu a wasu takardu shin sai in bar
komai in zauna a gida in ke soyayya shin soyayyar za mu ci?" Ya katse mata hanzari cikin
hargagi. Gabaɗaya sai ta ji ranta ya ɓaci a nata ganin yana sane amma yake take gaskiya.

"Shikenan bari na shirya kayana mu tafi tun da ai kana da gida a can"

"Babu inda za ki bini wallahi, ke da kika samu ma kina ganina mata nawa ne wata sai ta
shekara da shekaru bata sanya mijin a idanun ta ba kuma take zaune amma ke sai rashin
haƙuri, da kike batun bamu haɗa makwanci ba jiya in ce dai a gajiye nake ko bakya duba nisan
tafiyar da na yi? Ko cewa aka yi soyayya dakusantar juna ne zaman aure? Abu da zamani ma
ya zo ga waya nan sai ka ji muryar mutum" Ya faɗa yana tashi tsaye sai wani muzurai yake
tamkar ta zagi iyayen sa.

"Ni na tafi sai mun yi waya" Ya faɗa tana dosar ƙofar fita.

"Allah tsare" Ta furta tana ƙoƙarin danne kukan da ya taho mata. Da amin ya amsa ko a kwalar
rigar sa ya fice. Da ɗan gudu ta haura sama ta je jikin window tana kallon sa har mai gadi ya
buɗe musu get suka fice tana jin haushi da ciwon abin da HAMEED yake mata da a ce yana
bata kulawa kuma yana karɓar kulawar da take bashi da babu dalilin da zai sa mijin ta zai yi
tafiya amma bata masa rakiya ko da bakin mota ba ne.

Ɗaki ta koma bayan ta gama shan kukan ta, fitowa ta yi ta nufi ɗakin sa saboda tana so ta
tabbatar da ƙaryar da mai maganin nan ta mata tun da dai ga shi bai zo ko inda take ba bare a
yi batun biyan buƙata. Abin mamaki komai a yadda ta bashi a haka ta gani har ta fara tunanin
ko dai HAMEED ya gane abin sa ta saka a ciki shi ya sa bai sha ba sai dai bata da wanda zai
bata amsar wannan tambayar.


*HEEDAYA*

Zaman gidan Aunty ya zame mata tamkar wanda take a kurkuku domin duk abin da tw zo don

ta gabatar amma hakan bai samu ba kullum tana fito da sabbin abubuwa don jan hankalin Ya
ABDUL amma abin ya ci tura saboda shi kwata-kwata ma bai fahimce ta ba kuma ta lura ba ta
gabansa matar sa ce kaɗai a gabansa. Yadda suke sakewa suke nunawa junan su kulawa
tamkar dai basu san an yi ta a wajen ba shi ne abin da ya saka ta kasa ko da zaman falon idan
Ya ABDUL yana gidan, sai dai ta koma ɗaki ta yi ta ƙunsar baƙin ciki daga ƙarshe da ta ga ba ci
satin ta guda ta haɗa kayan ta lokacin suna zaune a falo sai ganin ta suka yi da akwati niƙi-niƙi.

"Sai ina kuma?" Aunty ta tambaya da mamaki.

"Sai gida" Ta faɗa tana ƙoƙarin danne ɓacin ran da yake taso mata domin zaman ta a gidan ba
ƙaramin tsanar Aunty RABEEYA ya ƙara mata ba ta ƙuduri cewar wallahi ba don ya haramta su
auri miji ɗaya ba da ko ta halin ƙaƙa sai ta auri Ya ABDUL kuma ta shigo gidan ta gasa mata
aya a hannu yadda da ƙafafun ta za ta bar gidan kuma da bakin ta za ta nemi saki sai dai kash!
Haramcin auren ne ya sa take ɗaga mata ƙafa.

"Ga kuɗi kya shiga mota" Ya ABDUL ya faɗa cikin halin ko in kula. Kanta ta sunkuyae tana jin
ranta yana suya, ta ɗauka zai ce ta bari ba yau ba ko ma ya nuna kulawarsa cewa ta bari sai da
safe mana amma kamar wanda ta gundure shi kamar wanda dama yake jiran ranar tafiyar ta
wai zai bata kuɗin mota.
"Haba dai ka kai ta mana" Aunty RABEEYA ta faɗa ganin kamar rashin kyautawa ne a ce ta zo
tsawon sati guda amma a bata kuɗin mota.

"Ni ban san ma dalilin da zai sa ki tafi gidan yanzu ba mai ya sa ba za ki bari sai da safe ba?"
Aunty RABEEYA ta faɗa tana kallon ta.

'Wato in zauna baƙin ciki ya kashe ni kina nan maƙale da mijin ki ni ina ɗaki tamkar wata mayya
in dare ya yi ku shiga ku bar ni ni kaɗai dama abin da na zo yi da ban kuma na ga babu haza
dole na san na yi' Ta ce a zuciyar ta a fili kuma sai ta ce

"Babu komai Aunty sai in shiga motar ko ma napep na samu sai in shiga, kawai na yi kewar
Umma ne ina so na gan ta"

"Inyee wato da kika gama boarding school ɗin ba da ina za ki ganta ma " Ta faɗa tana dariya.

"Ya ABDUL ina da kuɗin mota na gode sai da safen ku" Ba tare da ta ba Aunty RABEEYA amsa
ba ta juya ta nufi ƙofar fita, don kallon su liƙe da juna yana neman saka zuciyar ta bugawa. Tana
jin Aunty tana kiran ta amma ta yi kunnen uwar shegu don tana buɗe baki kuka ne zai fito.

"Ka tashi ka je ka miƙa ta plss" Ta ce tana ɗan yawo da idanun ta, da to ya amsa yana cewa sai
dai ta zo su je amma ta ce masa Abba ya hana yawan fita haka ya ɗauki makullin ya fito mai
gadi ya buɗe get masa don lokacin har ta fice daga harabar.

Tsaye ta same ta da alama abin hawan take jira, bata zata ba bata tsammata ba sai ganin
motar sa ta yi ta tsaya a gefen ta wani irin daɗi ya mamaye mata zuciya, ta ɗan juya kai gefe a
ɓoye ta goge hawayen da yake mata sintiri.

Duk tsawon kwanakin nan tana so su ɗan keɓe ma da shi amma abin ya ci tura! Hannu ta
harɗe a ƙirji tana jiran fa fito ta ɗan lallashe ta ko ta ji sawaba a ranta amma sai ta ji yana danna
mata horn. Ɗan taɓe baki ta yi ta sungumi jakar ta saka a baya ita kuna ta buɗe gaba tana
rayawa a ranta cewa w ce dai ta ga Aunty RABEEYA a gaban da kuwa sai ta ce musu su je ta
hau napep. Tana zaunawa ta rufe ƙofar tare sa sakin wata bayyananiyar ajiyar zuciya, don ita
yanzu gani take bata jin kunyar za ta iya bayyana masa son da take masa ko a aikace ne don ta
gaji da dakon son sa tana cutuea da yawa.

"Ya ABDUL ni yanzu ban san laifin da na maka ba duk ka tsane ni sai in ga kana jin haushi na
ban san dalili ba, ko dai ka daina sona ne?" Ta furta cikin wata irin murya mai sanyi tana kafe
fuskar sa mai kyawun gani da ruɗa ta . Ba tare da ya waiwayo ya kalle ta ba ya ce.

"Yaushe Hayatiy ta ce miki bata da lafiya" Wani takaici ne ya turnuƙe ta tamkar ta kai masa
duka ga maganar da take su tattauna kafin su isa gida a ƙalla ya ce mata.

'Haba HEEDAYA nah ina son ki mana' Amma sai ya shigo da wata magana da ban.

"Kawai dai ina son

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login