Showing 45001 words to 48000 words out of 64514 words
Chapter 16 - BONONO BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MAMAN AFRAH f.pdf
Daga farko har ƙarshe sadaukarwa ne ga MARYAM SANI HAFIZ (Merry tah) Alkairin Allah ya
kai gare ki Allah lulluɓe rayuwar ki da tarin ni,imomi da albarkatu Allah raya mana Abdallah
fatan alkairi.
Daga marubuciyar:
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Jalli joga
Da sauran su.
*09013181851*
PAGE 12
*MARYAMA*
Horn ya yi mai gadin da sauri ya wangale musu get tana ta kallon gidan yadda ya tsaru
kuma yake da kyau. Fitowa suka yi tana riƙe da kayan ta sai ɗan noƙewa take irin na rashin
sakin jiki.
"Gidan mu ne nan ba siyar da ke zan yi ba" Ya ce yana kallon ta ɗauke da kurmushi. Bata ce
komai ba fuskar ta ta yi fayau da alama har lokacin damuwa tana nuƙurƙusar zuciyar ta.
Gaba ya yi ta bi bayan sa.
"Kin saka ni a gaba sai ka ce wani ɗan ki" Ya ce lokacin da ya ja ya tsaya yana kallon ta tana
tahowa da sanyin jiki da yake akwai tazara daga get zuwa cikin gidan, ga shi kuma ya ɗan bar
ta a baya sosai.
"Ai da yake ni ban san gidan ba" Ta faɗa cikin sanyin muryar ta.
"Tun da baki sani ba sai ki ɗago ƙafa don in na ɓace miki va samun hanya za ki yi ba"
Da sallama suka shiga gidan wata mata ta amsa musu tana musu marhabin.
"Likita bokan turai" Ta ce cikin zolaya tana dariya.
"Wannan dai bokan ƙauye ne, tun da a can yake aiki" Ya faɗa shi ma yana dariya.
"Duk ɗaya dai" Dariya ya yi suka shige falon bayan MARYAMA ta gaishe da ita.
Zaune take a falon farantin kankana da lemon fata a gabanta tana sha, bayan ta amsa musu
sallamar ta ɗago ta kalle su.
"Zauna MARYAMA ya ce bayan ya samu waje ya zauna kusa da Kaka, tare da ɗaukan kankana
ya kai bakin sa.
"Sai zuwa ba sanarwa" Kaka ta ce tana kallon sa.
"Ni da gidan mu?" Ya ce yana ɗaukan lemon ya sha.
"Barka da rana, ina yini" MARYAMA da ta samu wuri a kan carpet ta zauna ta faɗa cikin
girmamawa.
"Lafiya ƙalau ƴan mata" Kaka ta ce tana bin ta da kallon rashin sani.
"Sunan ta MARYAMA mun haɗu a ƙauyen da nake aiki jiya da dare marainiya ce bata da kowa
ma a taƙaice" Ya kai ƙarshen maganar yana kwashe komai da MARYAMA ta faɗa masa ya faɗa
wa Kakar yana fatan Allah ya sa ta amince da maganar don ya santa wani likacin butsuwa ce.
Kallon ta Kaka take yi tana nazartar ta, MARYAMA kuma ta sunkuyar da kai idanun ta suna
cikowa da ƙwalla, don babu abin da yake saurin karyar mata da zuciya irin ta ji ana batun bata
da kowa musamman da ya ce shekaran jiya mariƙinta ya mutu.
"Daga wane ƙauyan kike?" Kaka ta faɗa tana kallon ta.
"Ƙauyen KANYA" Bayan ta bata amsae ta shiga mata wasu tambayoyin da har sai da ta gamsu
da gaskiyar ta, sannan ta ce ta amince ta zauna da su. Ɗaki aka saka Mero ta raka ta, wacce
aiki take yi kuma dai a gidan take zaune ita da Kakar sai kuma sauran ma'aika maza.
Bayan sun keɓe da Ya HAFEEZ ɗin take ta masa faɗan kar ya ƙara mata kwashe-,kwashe
sannan ma ta ce sai ta saka an binciko mata can ƙauyen KANYA a ɓoye a kan abin da
MARYAMAR ta faɗa duk da ta fahimci iya gaskiyar ta ne ta faɗa.
Bayan kwana biyu, zaune take a gidan Kaka hankali kwance don babu kyara babu
tsangwama ga shi sai suke ta jan ta a jiki ko kuma jan ta da zance, hakan yana rage mata ƙunci
sai yanzu take jin tana rayuwa ta ƴanci tamkar wata mai gata ko mai iyaye a raye ba irin
rayuwar gidan Baffa ba da take yin ta cikin tsangwama da rashin galihu sai ta ɓangaren Baffa
ne ko Goggo kafin ta mutu take samun salama. Ya HAFEEZ ya koma ƙauye tun washe gari
tana jin sa in suna waya da Kaka yana tambayar ta ita. Yanzu Kaka ta ce ma idan ya dawo za a
saka ta a makaranta tun da ta kusa kammalawa tana ss 2 ne.
*BAYAN WATA GUDA*
Kaka zaune take tana kallo sai MARYAMA da take moppin a falon kasancewar bata son
zama sai take aiki ko da an hana ta an ce da masu yi. Kaka ce ta yi tsai tana ƙarewa
MARYAMA kallo mamaki da fargaba cike a zuciyar ta ganin fuskar MARYAMA ta sauya duk ta
ciko hatta jikin ta duk ya sauya tamkar dai mai ciki haka Kaka take mata kallo don dama wani
lokacin tana yi mata kallon hakan sai dai yau abin ya ruɗa ta.
Bata san ya aka yi ba ƙurawa marar MARYAMA ido da ta yi sai kuwa ta yi kiciɓis da ganin
tudu a marar MARYAMA, yawun bakin ta ne ya ƙafe lokaci guda zufa ta wanke mata fuska ta
shiga gangarowa zuwa wuyan ta. Dakyar ta samu kalmomin da ta haɗa haruffan wajen kiran
MARYAMA. MARYAMA jin Kaka ta kira ta, sai ta ajiye mofa ta taho wajen Kaka, sai dai kallon
da ta ga Kaka tana jifanta da shi ya saka mata tsoro da kuma ruɗani.
Saboda gabaɗaya ma ita shagala take da cewa akwai wani ciki a jikin ta, saboda yanzu bata
da damuwa sosai tun da dama ita gorin da ake mata ne yake damunta na cewa ita shagiya ce
tsintacciya yanzu kuwa babu mai mata gori sai kuma damuwar mutuwar Baffa duk da tana
masa addu'a kuma hakan yana sanya salama a ruhin ta.
"Tashi tsaye" Kaka ta faɗa tana kallon ta don tana zuwa gaban Kaka ta durƙusa alamar
girmamawa, ita Kaka ta rasa ma mai yake mata daɗi fatan ta dai zaton ta kar ya zama gaskiya.
Ta san ta aika an binciko mata cewa akwai wata MARYAMA da take ƴar tsintuwa kuma mariƙin
ta ya mutu, mai binciken ya dawo mata da amsar cewa tabbas akwai ta, amma dai matar
mariƙin ta kore ta daga gidan don haka yarinyar bata garin ma. Wannan ne ya sa ta yarda da
gaskiyar MARYAMA amma bayan wannan babu abin da aka binciko mata dangane da ita ashe
dai akwai sauran rina a kaba. MARYAMA tsaye ta tashi ai kuwa Kaka da ita ma ta miƙe tsaye
ganin abin ba na yi ba ne ta saka hannu ta gwale idon MARYAMA gabanta ne ya buga da
mugun ƙarfi. Da sauri ta saka hannu ta ɗan ɗama rigar MARYAMA ai kuwa ta ga marar ta ta yi
tudu kana gani kuma ka san ba timbi bane tun da a mara ne ba a ciki ba. MARYAMA gabanta
ne ta doka da ƙarfi jikin ta ya shiga karkarwa da za a tsaga jikin ta ba za a samu jini ba ko
kaɗan, saboda ruɗewa da kuma fargaba.
"Ciki ne da ke ko?" Kaka ta tambaya muryar ta tana karkarwa. MARYAMA wacce hawaye ya
fara ambaliya a dakalin fuskar ta, cikin sanyin jiki ta shiga gyaɗa kai tamkar ƙadangaruwa don
ta san aikin gama ya gama tun da babu wani abu da za ta ɓoye, tunanin ta ɗaya ma da bata
sanar da Ya HAFEEZ ba tun a ranar da ya buƙaci jin labarin ta, yanzu za su ga ta munafurce
su.
Kaka ganin MARYAMA tana kuka kuma ta gyaɗa kai alamar eh ce amsar tambayar da ta
mata, sai hankalin ta ya ƙara tashi tana ta ambaton innalillahi wa inna ilaihir raji'un a zuciyar ta
don a ganin ta tun da har MARYAMA ta san da cikin to tabbas shi ma wanda ya kawo ta wato
HAFEEZ ya san da hakan nan take zuciyar ta ta shiga saƙa da warwara a kan cewa HAFEEZ
ya yi wa yarinyar ciki ne shi ne ya kawo ta gidan duk da ta yarda da shi a kan tarbiya da tsoron
Allahn sa amma dai ta san shaiɗan shi ne mugun mai yin jagoranci wajen aikata alfasha.
Ko ta kan MARYAMA bata bi ba, don yanzu gabaɗaya ta fi ganin laifin HAFEEZ da ya ɗakko
yarinya ɗauke da cikin shege ya kawo mata gida tun da dai a kaf tarihin yarinya babu inda aka
ce an mata aure. Waya ta ɗauka ta doka masa kira, yana kishingiɗe yana ɗan danna laptop
kiran Kaka ya shigo zaune ta tashi yana sakin murmushi don ko ba komai idan sun yi waya zai
tambayai lafiyar MARYAMAR shi wacce a yanzu yake jin koɓai yake da tunanin ta yake ya san
kuwa babu makawa da son ta zuciyar sa ta kamu.
"Assalamu alaikum Kakata ta kain...
"HAFEEZU ni za ka rainawa wayo ka manta ni na haifi ubanka? Tunanin ka na yi tsufan da za
ka yaudare ni, ka ɗakko yarinyar da ka ɗirkawa ciki kuka raina mini hankali ka kawo mini ita
gida.... Kalaman da ta masa suka daki ƙwaƙwalwar sa, gabansa ya buga da ƙarfi mamaki
al'ajabi suka taru suka cushe masa zuciya, shi kansa bai san lokacin da ya tashi tsaye ba daga
zaunen da yake, tambayoyi barkatai suna cika masa kwanya...
*HEEDAYA*
Da idanun ta ta kafe shi tana jiran amsar sa. Ya ABDUL da bakin sa ya masa nauyi ga wani
irin azababban ciwo da kan nasa yake masa, so yake ya musa wannan maganar sa take
tambayar sa sai dai ji yake ya kasa, ji yake tamkar zuciyar sa za ta kama da wuta idan ya yi
musu saboda wani zafi da yake ji zuciyar tana masa da alama ba zai samu salama ba har sai
ya yi na'am da abin da ta zo masa da shi. Kai ya shiga gyaɗa mata yana kallon ta da rinannun
idanun sa da har yanzu basu washe ba na kukan rashin Aunty RABEEYA da ya yi wanda ya
zame masa jiki. Wani shu'umin murmushin cin nasara HEEDAYA ta yi kafin ta ƙara jefa masa
wata tambayar.
"Kana so na? Za ka aure ni?" Ta tambaya tambaya tana wani haɗe rai don yanzu gyaɗa kan da
ya yi hakan yana mata nuni da ta kama shi a hannu don haka dole ma ta fara yin yadda ta ga
dama.
Kan dai ya ƙara gyaɗa mata a karo na biyu.
"Ba na son auren nan ya ɗauki wani lokaci ina so ka sanar da Abba za ka aure ni domin in
maye maka gurbin Aunty RABEEYA, sunan Aunty RABEEYA kaɗai da ya ji ta ambata sai da ya
ji zuciyar sa ta motsa, sai dai tantamar kalaɓanta yake sai dai ya kasa mata musu, wai aure shi
ABDULHAKEEM ne zai yi aure kuma auren ma HEEDAY?. Waɗannan tambayoyin ne suke
masa kai kawo a birnin zuciyar sa, sai dai babu yadda zai yi ya yi musu.
"To zan samu Abban " Ya faɗa tamkar wani sakarai har lokacin kansa tamkar ana buga masa
guduma. Hannu ta ɗora a haɓar sa ta ce
"I luv you Ya ABDUL na daɗe ina ƙaunar ka, ni na sani na fi kowa son ka tabbas idan ka aure ni
zan saka ka manta da kowace ƴa mace" Tamkar majigi haka yake kallon ta. Ƙofar ta buɗe ta fita
shi kuma ya kifa kansa ya ma rasa wane kalar tunani zai yi.
A guje ta shigo falon Ihsan da Mubashshar da suke zaune Mubashshar yana assignment ita
kuma tana kallo sai gani suka yi ta shigo kamar an jefo ta, ɗakin Umma ta shige ta danna
mukulli Umma ta rungume tana ta tsallen murna, su duka dariya suke tamkar an musu albishir
da kujerar hajji.
"Kar ki kayar da ni" Umma ta faɗa tana dariya.
"Umma wallahi ya amince ko musu bai yi ba kuma ya yarda zai sanar da Abba" Ta faɗa duk ta
wani ruɗe ta zauce.
"Haba yarinya boka fa aka ce kuma kar ki manta laya fa kika haɗiya ai aiki dole ya ci"
"Tabbas Umma ai wallahi ban taɓa zaton zai amince cikin ruwan sanyi ba sai wani dafe kai
yake"
"Ƙyale shi aikin ne ya ci shi ya sa kan yake sara masa ai ko nawa ne sai mun kashe, don sai
kowa ya san ke kike auren sa musamman Hajiya Fati sai na nuna mata gaba da gabanta"
Shiru-shiru suna jiran su ji magana ta kai kunne Abba amma babu amo ba labari sai dai sun
yi ɗif suna jiran tsammani. Tsawon sati uku shiru. A ɓangaren Ya ABDUL kuwa sai ya yi kamar
zai je ya sanar da Abba kawai sai tunanin Aunty RABEEYA ya hana shi sakat sai yake ganin bai
mata adalci ba daga mutuwar ta ya yi aure shi ba ya ma son ya auri HEEDAYA sai dai babu
yadda zai yi don zuciyar sa azalzalar sa take yi. A wani yammacin Litinin ne bayan ya dawo
daga wajen aiki ya yi wanka da yake yanzu gidan su yake ya ƙi zaman gidan sa saboda babu
Aunty RABEEYA a ciki. Da sallama ya shiga falon Abba.
Bayan ya amsa masa ya zauna a ƙasan capet ya gaishe da shi.
"ABDULHAKEEM ka ƙi ka kwantar da hankalin ka ko? Duk ka yi baƙi ka rame kar ka manta fa
Allahn da ya bamu RABEEYA ya fi mu son ta kuma shi ya karɓi abarsa ya kamata ka sawa
ranka dangana kake mata addu'a" Shiru ya yi yana mai sunkuyar da kai sai yake ji tamkar
wanda zai faɗi wani saƙo don a ganin sa tamkar abin kunya ne kuma cin amana sai dai ya kasa
dakatar da kansa shi ma bai san dalili ba.
"Ina mata addu'a Abba"
"To Allah ya ƙara maka haƙuri haƙiƙa da wuya samun irinka a wannan zamanin mai son matar
sa haka saɓanin wasu daga matan sun mutu shikennan sun manta da su"
"Abba dama magana na zo mu yi"
"Ina sauraron ka"
"Am, dama, dama"
"Dama mai?"
"Ina son na auri HEEDAYA" Idanu Abba ya ƙanƙance yana mamakin furucin nasa har sai da ya
ce ya maimaita don shi Abba a iya sanin sa bai taɓa zaton a kwana kusa ABDULHAKEEM zai
nemi yin wani aure, tunanin sa ma sai sun zaɓa masa matar za a masa auren dole don shi da
yake faɗin ya gama aure bare kuma wai HEEDAYA zai aura.
Mamakin sa ya ɓoye ya nuna masa jin daɗin sa amma a zuciyar sa tabbas ya yi mamakin
hakan.
"Ai ta kwana gidan sauƙi HEEDAYA ai ƙanwarka ce sai dai kuma ka same ta ka ji daga bakin ta
ni ma za mu yi magana da Daddyn ka da kuma Hajja"
"Ai mun yi magana da ita ta amince"
"Ikon Allah to, ba damuwa za mu zauna da Daddyn ka sai mu ji yadda za mu ɓullowa lamarin"
Daga haka ya yi wa Abba godiya ya fito sai yake jin tamkar ya sauke wani nauyi don tun da
HEEDAYA ta masa furucin nan bai samu nutsuwa ba sai da ya furzarwa Abba kalaman nan.
Abba kuwa da mamaki ya cika shi sai dai hakan ma abin so ne ko ba komai Ya ABDUL ɗin zai
samu nutsuwa.
Sosai aka sha faɗi tashi da maganar auren aka iyo wa Ya ABDUL caaa musamman Ammie
don a ganin ta yaushe ma matar sa ta mutu har zai nemi ƙara aure auren ma da HEEDAYA. Sai
dai ta san ita bata isa ta hana ba domin sai da Daddyn ABDUL ɗin ya gargaɗe ta don ya san
basa ga miciji da Umma. Hatta Momma sai da ta shiga ta fita ta hanyar kissa da kisisina a kan
ganin ta hana auren amma abin ya ci tura. Saboda Umma da Hajiya Aisha su tashi haiƙan a
kan lamarin auren kullum suna hanyar zuwa wajen bokan su don ganin an yi wa bakin kowa
dabaibayi musamman wanda zai yi yunƙurin hana auren.
Hajja kuwa daɗi ta ji na wannan haɗin don a ganin ta gida bai ƙoshi ba ba a kai daji ba. Aunty
Hafsa kuwa ta san tabbas abin nan ba Ya ABDUL yana hayyacin sa ba ne tun da dama ta san
ƙudurin su Umma tun ba yau ba bare kuma yanzu da suka samu sarari ita dama an daina saka
ta a sabgar an kuma daina shawara da ita tun da sun gane bata tare da su.
Yau ya kama wata uku cif da mutuwar Aunty RABEEYA wanda ya yi daidai da saura kwana
sati ɗaya ɗaurin auren HEEDAYA da Ya ABDUL. Zaune ƴan gidan suke su duka a falon Abba
da ya kira taro, sai dai bai ce komai ba, bayan mintina kaɗan Ya ABDUL da Abba ya kira ya
shigo da sallama gaishe da Abba ya yi sannan ya shiga gaishe da Momma wacce ta amsa
babu yabo babu fallasa don ita yanzu mugun haushin ABDULHAKEEM ɗin take ji, na auren da
zai yi wai ya rasa ma wa