Showing 42001 words to 45000 words out of 64514 words

Chapter 15 - BONONO BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MAMAN AFRAH f.pdf

30 Mar 2025

5136

mai yake nufi. Bata masa musu ba ta koma tana son ganin gudun ruwan
sa duk da ta yi mamaki yadda yake kamili da har ya iya kwana da ita gida ɗaya ba tare da ya
nemi lalata da ita ba.
"Wannan rigar a gidan wata tela da take ɗinka kaya tana siyarwa na siyo miki ki shiga ki yi
wanka ki saka" Ya faɗa bai jira cewar ta ba ya juya zai fita.

"Da baka ba kan ka wahala ba ga kayana a cikin nan" Ta ce cikin sanyin murya bai ma kalle ta

ba bare ta saka ran zai tanka mata illa ficewa da ya yi daga ɗakin. Wankan ta yi tana fitowa ta
tarar da mai haka ta shafa duk da zuciyar ta babu daɗi amma kamar yadda Baffa ne kaɗai a
duniya yake bata kulawa ta ji daɗi da wannan ma ya nuna mata ita ma mutum ce.

Tana zaune ya shigo ya zauna ya haɗe rai kai ta sunkuyar.

"Ki bani labarin ki a taƙaice ko da ba za ki faɗa mini komai ba ina so ina sani" Shiru ta yi tana
nazari sai kuma ta samu kanta da ƙin masa musu ta ce.

"Suna na MARAYAMA ni ƴar tsuntuwa ce ba a san iyayena ba tun ba a yanke mini cibiya ba aka
jefar da ni... Da sauri ya ɗago yana kallon ta sai ya ji ta ɗora da faɗin

"Baffa ne ya riƙe ni da nuna kulawa, ya saka auduga ya toshe kunnuwan sa daga maganganun
mutane, jiya Allah ya masa rasuwa shi ne matar sa ta kore ni daga gidan kuma ni ban san ina
zan je ba ko ina ƙyamata ake an ce mini bani da uba ni shegiya ce...

"Ya isa haka!" Ya furta ransa yana ƙuna sosai ya ji furucin nata ya daki ƙwaƙwalwa da zuciyar
sa. Bai ce mata ƙala ba ya tashi ya dice daga ɗakin, hawaye ta shiga gogewa dama ta san da
wuya wani ya ji wace ce ita a yi maraba da ita don ma bata faɗa masa ɗaya ƙaddarar da ta
same ta ba ta ciki wanda bata san ta ya aka yi ta same shi ba, don ta sani babu wanda ya taɓa
kusantar ta ba sannan har ƙasanta take dubawa ko za ta ga wata alama ta cewa an kusance ta
amma bata ganin komai, ita har yau tana da na sanin wanzuwar ta a wannan duniyar mai cike
da makafin mutane da basu san mece ce ƙaddara ba!.

"Ki ɗauko kayan ki tare za mu wuce Dutse" Shi ne kawai abin da ya furta. Sororo ta bi bayan
sa da kallo sai ƙamshin turaren sa da ya bar mata a ɗakin.

'Kenan bai guje ni ba?' Ta jefawa zuciyarta tambayar. Riƙe da kayanta ta fito tana sanye da
doguwar rigar atamfar da ya kawo mata ta ɗora hijabi a kai.

Tana fitowa ta ga wata haɗaɗliyar mota sai ɗaukan ido take, daga gefe ta samu wuri ta tsaya,
ƙofar gidan ya kulle. Gaban motar ya buɗe mata ya ce ta shiga, tana shiga ya rufe ya koma
mazaunin direba ya shiga ya tada motar maimakon ya bi cikin gari sai ya miƙe ya bi ta can tun
da dama bayan garin ne babu wanda suka haɗu da shi sai wani tsoho da ta ji yana ce masa
likita bokan turai wanda hannu kawai HAFEEZ ɗinya ɗaga masa suka fara tafiya.

Shiru sai karatun qur'ani da yake tashi a motar, kowa da tunanin da yake, ita tana tunanin
yadda za a karɓe ta a inda za su je ba ma wannan ne ba abin jin sai abin da take ɗauke da shi
wanda bata sanar masa tana ɗauke da shi ba. Shi kuma yana tunanin ta ina zai fara? Mai zai
cewa Kaka game da wannan yarinyar shin za ta yarda ta zauna da ita ko kuma yaya shi dai ya ji
yana tausayin yarinyar kuma dai ya yarda da ita bai ga alamar ƙarya a maganganin ta ba.

*YA ABDUL*


Tun da aka yi bakwai sai ya ƙara komawa tamkar ba a wannan duniyar ba, haka yake jin sa
tamkar wanda ya rasa ɓarin jikin sa haka yake ji, bai taɓa zaton haka yake ƙaunar Aunty
RABEEYA ba sai da ta bar duniya!. Ya shaƙu da ita irin shaƙuwar da ko a mafarki bai taɓa kawo
mata mutuwa a kwana kusa ba, kullum tunanin sa sai sun hayayyafa sun aurar kai sai tsufa ya
riske su suna tare da juna, in da san samu ne su mutu a tare amma kash!. Ashe dai ihu yake
bayan hari mai duka ya daɗe da rubuta cewar rayuwar ta gajera ce.

Ya zama tamkar wani mutuntumi, an yi nasihar an yi wa'azin har an gaji, don shi wuyar ta ka
fara masa nasiha a kan ya manta da RABEEYA ya yi lamuran sa sai kawai ya fara maka kuka.
Abu ɗaya ne yake kwantar masa da mikin rashin ta shi ne Little RABEEYA yarinyar da take
kama da uwar ta sak tamkar an tsaga kara, kallon ta ne kawai yake sa ya ji tamkar dai tana
wannan duniyar amma in ba wannan ba komai ya zame masa hoto a wannan duniyar.

Momma ma hakan ne a wajen ta don ta sani RABEEYA mutum ce mai haƙuri da kawar da kai
ga ladabi biyayya ga riƙon ibada da son ƴan uwa hakan ya sa ta kasa jure rashin ta, dakyar ma
Abba ya bar mata Little RABEEYA saboda take rage raɗaɗin mutuwar Aunty RABEEYA don
mutuwa ce da ta riske su babu zato babu tsammani kasancewar ba a taɓa musu mutuwar ba
ma. Gidan Abba nan ne ya zama mazaunin YA ABDUL don shi ko kunyar surukuntaka ba ya ji
ta Momma haka zai shigo ta miƙa masa yarinyar ya zauna ya saka ta a gaba watarana ya ringa
wa yarinyar magana yana kuka in ta ga abin ya yi yawa sai ta karɓe ta.


Madarar da ake bata kuwa har gajiya Momma take da tara su, gasu nan jingim da famfas da
duk wani abu na yarinyar kawai libgowa yake ya kawo. Har kayan wasa yake kawowa sai dai a
kai store na ajiyar kayan wasa a ajiye tun da bata isa wasan ba. A haka har aka yi wa Aunty
RABEEYA arba'in.

*HEEDAYA*

Sun yi jimami na wuni ɗaya ita da Umma, daga ƙarshe kuma sai su shiga ɗaki suna ƙusƙus ita
da Hajiya Aisha da Umma don Hajiya Aisha har sai da aka yi bakwai sannan ta daina zuwa a
cewar ta zaman makoki take zuwa wanda ba haka bane illa shirye-shiryen yadda za su ɓullowa
al'amarin HEEDAYA da ta mutu a kan son Ya ABDUL.

"Umma wai yanzu ya za a yi da wannan sakaran Ya ABDUL ɗin wannan Umma kina gani
ya kafe a kan tunanin mace ɗaya kowa har ya gane shi, ko office ya je babu abin da yake

tsinanawa sai dai sauran ma'aikatan suke yi ko a ina kika gan shi ya yi jugum tamkar shi aka
fara yi wa mutuwa a duniya" HEEDAYA ta ce tana jan wani uban tsaki.

"Haba HEEDAYA kar ma ki fara kishi da kushewa, don ita tata ta ƙare, ai kamar yadda hausawa
suka ce mutuwar wani tashin wani, haka ce za ta kasance, a gaba za ki zo ki murza kambun ki
yadda kike so" Umma ta ce tana dafa kafaɗar ta.


"Na ji Umma amma fa ba ma wai tunanin Aunty RABEEYAR da yake yi ba ne kaɗai abin ji
waccan filillikar jaririyar mai kama da ɗiyar roba duk ya ƙwallafa rai a kanta, ni wallahi haushin ta
nake ji ita ma Ammien da ta bari ɗanta ya zama lusarin namiji duk ya ƙare a kan mace ɗaya da
ƴarta"
"Rabu da sakarkaru da sannu duk za mu damƙa musu kashin su a hannu, ke ni ma diddibtun da
yake a gidan nan ya ishe ni ya zauna yana reno kamar mace"

"Rabu da shi Umma zai daina ne wallahi ni in na shiga gidan sa ba zan ɗauki wannan cin
kashin ba yo ina dalili yarinya uwar ta ta mutu ana ganin kamar an jefar da ƙwallon mangwaro
za a huta da ƙuda ashe dai an kashe miciji ne ba a sare kansa ba wato akwai sauran rina a
kaba" HEEDAYA ta ce tana kama haɓa.

"Bar ni da su ai gobe za mu koma wajen boka kin sa tun ranar kwana ukun mutuwar nan muka
je muka masa godiya a kan binciken da ya mana na cewa akwai aure tsakanin ku da shi, to sai
ya ce idan an yi arba'in mu koma"

"Gwara dai ku je, don na ga sai an zage dantse an hau kan su don wallahi wannan Ya ABDUL
ɗin yadda kika san ƙiyayyta ake dasa masa kullum a rai haka yake nuna mini ko gaishe shi na
yi dakyar yake amsawa sai ka ce ni na kashe masa matar"

" Zai yi bayani ne bari dai ke mu gani sai ya koma bita zai-zai kuma mijin ta ce" Wani murmushi
HEEDAYA ta yi jin furucin nan na Umma don ya daɗaɗa mata sosai, har ta fara hango yadda za
ta gara Ya ABDUL tamkar ƙwallon ƙafa, ba iya shi kaɗai ba hatta Ammie sai ta jogale mata ɗan
matsayin da take ganin tana da shi a wajen ɗan nata.

Washe gari Umma da Hajiya Aisha suka tasamma wajen boka, bayan sun shiga kamar
yadda suka saba suna zaune tamkar wanda suke jiran tsammani sai dai kowa fuskar sa da
annuri.


"Ku daina sarewa akwai aure a tsakani don kamar yadda na faɗa muku a baya to tabbas!.
Auren nan babu fashi sai an yi"

"Boka ka san dai an ce mai zurfin ido da wuri yake fara kuka, to shi yaron ne ko kallo
HEEDAYAR bata ishe shi ba, har yanzu hoton matarsa ne liƙe a zuciyar sa sai kuma ƴar da ta
mutu ta bari, shin ita HEEDAYA ce za ta furta masa kalmar so ko kuwa jira za ta yi ya furta
mata, sannan ka san hatta uwar sa akwai takun saƙa a tsakanina da ita ba lallai ta amince da
auren nan, bare kuma shi mai gayya mai aiki mahaifin ta shi ne abin da yake ci mini tuwo a
ƙwarya"


"Ita ɗin banza ai babu wani shege babu shegiya, kowa sai mun saka shi a taitayin sa,sannan
kuma ina so ki sani sai dai HEEDAYA ta je masa da kalmar so amma shi ba zai faɗa je mata ya
ce yana son ta ba, kuma son matarsa marigayiya ya gama wanzuwa a zuciyar sa mu ba za mu
iya fitar masa ba lokaci guda sai dai a sannu haka ma son ƴarsa fatan mu kawai auren ya shiga
tsakani daga lokacin komai zai zama tarihi don sai na kafa ta a gidan sa"


"Yawwa kamar ka san tana da mugun kishi kuwa bata son kowa ya raɓe shi, shi ma bata son ya
raɓi kowa"

"An gama!" Ya furta yana buga bayan wata ƙwarya wata wuta ta fito bul sai kuma ta ɗauke.Wata
laya ya ɗakko baƙaƙirin ya goga a bayan ƙwaryar inda wutar ta fito sai ya miƙa mata.


"Ta haɗiye wannan da ruwa" Daga Umma har Hajiya Aisha idanu suka zaro.


"Hajiya Fatin wato mahaifiyar ABDULHAKEEM ɗin ce za ta haɗiya?" Umma ta tambaya muryar
ta tana rawa.


"Kar ki zo mana da zancen banza da wofi!. Ita HEEDAYA ce za ta haɗiye layar wannan da
sannu idan ta haɗiya zai fara ganin farin ta a maimakon yanzu da yake ganin baƙin ta da ni ma
ban san dalilin hakan ba"

"To an gama godiya muke za ta haɗiye kuwa" Ta faɗa tana sakawa a jaka suka ɗan kalli juna ita
da Hajiya Aisha kafin suka biya shi kuɗin sa suka kamo hanya.



"Wai kin ji yadda gabana ya faɗi, ya za a yi ta haɗiyi laya ni Zainab?" Umma ta ce tana kallon
Hajiya Aisha da take tuƙi.

"Ni ma na ji hakan amma kar ki manta biyan buƙata muke nema komai ma za mu iya yi kin san

an ce ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba, kuma biyan buƙata ya fi dogon buri" Da
haka suka ƙaraso cikin gari ta ajiye Umma ta wuce gida.


"Gaskiya aikin bokan nan ya fara bani tsoro ya za a yi a ce a haɗiye laya ba ma a ƙona ta ba ko
a binne" Umma ta ce tana kallon HEEDAYA.


"Yanzu Umma haɗiyar layar ne kamar dai wanda ya ce a haɗiyi wuta?!. To ko mai ya ce ai mu
namu to ne tun da biyan buƙata muke nema duk abin da zai faɗa zan zama mai aiwatarwa in
dai a kan Ya ABDUL ne fatana dai idan an yi auren Umma ki saka bokan ya mini asirin mallaka
yadda zai zamana babu shi babu kallon wata mace sa sunan so ya zamana nu kaɗai yake
ƙauna ni kaɗai yake gani"


"Sha kurumin ki ki kwantar da hankalin ki kamar tsumma a randa ai fa za mu buga shi yadda
muke so sai yadda kika ce ko kara kika ajiye bai isa ya tsallaka ba, yanzu dai ki samu ki haɗiyi
layar sai ki je masa goben da maganar soyayyar"


Da safe ta fito daga part ɗin Umma suka yi kiciɓis da Ya ABDUL da ya sanya gaban shi
hanyar part ɗin Momma ta san kuwa zancen gizo ba ya wuce na ƙoƙi wato wurin Little
RABEEYA zai je. Duk da fuskar sa babu walwala amma a hakan ma ya mata kyau ji take
tamkar ta je ta kama hannun sa ta tambaye shi dalilin fushin sa gare ta mai ya sa ya daina son
ta sai dai tunowa da cewa komai ya zo ƙarshe ta marairaice murya ta ce


"Ya ABDUL ina kwana" Kamar ba zai amsa ba har ma ta cire rai zai yi magana ya ce


"Lafiya" A taƙaice ya wuce ta tamkar dai bai ma santa ba. Da harara ta raka bayan shi tare da
yin ƙwafa ta ce


"Duk ranar da ka shigo hannu za ka gane shayi ruwa ne" Ta juya ta tafi. Da yamma ta haɗiyi
layar don ta san dole zai dawo ganin Little da yammar kafin hallaw ya ƙara zuwa da dare. Tana
laɓe tana ganin sa har ya shiga ya fito bayan daɗewar da ya yi. Ganin ya nufi hanyar waje ta fito
daga maɓoyarta ta bi bayansa don zuwa ta aiwatar da abin da bokan ya ce. Yana zaune a mota
ya kifa kansa a kan sitiyarin ta je, sanin a shirye take don ta haɗiyi laya ta san ba zai taka mata
birki ba ko mata shamaki da zuwa wajen sa. Motar ta buɗe ta shiga kujerar mai zaman banza,
hannu ta kai ta shafo fuskar sa ya ɗago da sauri yana kallon ta da idanun sa da suka rine da ja
don tunanin Aunty RABEEYA ne da kewar ta yake addabar zuciyar sa.

Kai ta langaɓar gefe, shi kuma ya sanya hannu ya dafe kansa kamar dai wanda ya sara masa,
baki ta cije tare da yin murmushin gefen baki don ta san tarkon ta ya kusa kama tsuntsu da a ce
maganin bai fara aiki ba da ba yadda za a yi ya ganta cikin motar bai tsawatar mata ba, kuma
har ta kai hannun ta kan fuskar sa bai taka mata birki ba.

Komawa ta yi ta jingina bayanta da jikin kujera, idanu ta lumshe tana hango irin yadda za ta ci
duniyar ta da tsinke idan ta mallaki Ya ABDUL matsayin miji.


"Ya ABDUL tafe nake da wata magana mai girma ina son ka bani amsa ta" Ƙurr ya mata da
idanu tamkar wani dolo ganin bai ce komai ba ta ɗora da cewa.


"Ina son ka Ya ABDUL, ba so na ƴan uwantaka ba so na aure mene ne ra'ayinka kan hakan?"



MAMAN AFRAH
09013181851


*Ina siyar da zannuwan gado, masu filo biyu, masu filo huɗu, akwai masu labuleye masu
bargo da sauran su. Ina siyar da labulaye kala-kala, kayan yara, lesuna atamfofi, abayas
takalma sarƙoƙi, frames na bango, materials. Sayan ɗaya ko sari ina aikawa kowane gari, ga
link nan mai son sari ya shiga ko a mini magana ta no ta 09013181851 idan ba saya zaki yi ba
kar ki mini magana bana son ɓata lkc. Wanda basu da jari za su iya shiga grps su ɗauki kayan
su ɗora ruvar su idan sun samu masu siya su ɗauke ribar su ni kuma zan aikawa duk wanda ya
siya ta hannun su. NGD MAMAN AFRAH*








[2/19, 5:22 PM] MOM MASHKUR & AFRAH:
https://chat.whatsapp.com/F7TUZezpOWLKYnyTNFuy2Y

BONONO

(RUFIN ƘOFA DA ƁARAWO)


NA


MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.


*SADAUKARWA*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login