Showing 33001 words to 36000 words out of 64514 words
Chapter 12 - BONONO BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MAMAN AFRAH f.pdf
Dariya ta yi sosai ta tashi tsaye sai da
ta dubi hanyar bedroom ta ce
"Yanzu ma ai iri ɗaya ne" Tana faɗa ta gudu ya tashi ya bi bayan ta da nasa gudun amma bai
cim mata ba har ta shige ɗakin nata zaune ya same a bakin gado aikuwa ya shiga mata
cakulkuli yana tambayar da na waye bakin nasa yake kama. Cikin dariyar da ta ci ƙarfin ta
saboda cakulkulin ta ce
"Da nawa" Dariyar suke su duka suna jin su tamkar babu wasu masoya kuma makusanta a
duniyar soyayya fiye da su. Fitilar ya kashe musu suka lula duniyar ma'aurata.
*WASHE GARI*
Tsabar farin ciki bacci sai ɓarawo ne ya suri HEEDAYA asubar fari ta cika akwati da kaya da
duk wani abu da za ta buƙata. Umma sosai ta ji daɗin hakan don a ganin ta wannan ce hanya
mafi sauƙi da HEEDAYA za ta hana su RABEEYAR rawar gaban hantsi ta samawa kanta gurbi
a wajen Ya ABDUL ɗin tun da sun tabbatar da boka ya ce akwai rabon aure tsakanin su.
Momma kuwa tun da ta samu labarin zuwan da HEEDAYA za ta je gidan RABEEYA ranta ya
yi mummunan ɓaci ta san duk abin da Abba ya zartar babu mai sauya shi amma dai tabbas ta
san sai dai in wata maƙarƙashiyar ce za a shirya in ba haka ba daga yin aure sai a ɗauki
zabgegiyar budurwa a kai gidan sabbin ma'auratan da ko gama amarci basu yi ba. Tana
dawowa daga falon Abba don a wajen dinner ya sanar da hakan tana shiga ɗakin ta dokawa
Ammie waya ta yi tana ɗauka ko gaisawa basu yi ba ta shiga faɗin.
"Wai kin ji baƙin shirin da baƙar munafukar nan ta yi?"
"Shirin me kuma?" Ta tambaya cikin rashin fahimta. Kwashe komai ta yi ta faɗa mata cikin
hargowa Ammie ta luƙa wata ashariya tana ganin abin ya zo da kissa da rainin hankali don ita
dai ta san ABDUL bai faɗa mata cewa RABEEYA bata da lafiya ba, sai dai in maƙarƙashiya ce
aka shirya ta hana su wali tun da dai su basu san da cewa HEEDAYA tana son Ya ABDUL ɗin
ba sun dai san Umma tana baƙin cikin haɗin wannan shi ne za ta yi wani abu don hana zama
lafiya ko ta hana su sakewa za ta ɗauki ganɗamemiyar budurwa da ta isa a kaita ɗakin miji ta
tura musu ita gida.
"Wallahi ni ma na san sai dai da wata manufa aka yi kuma ta hannun Hajja HEEDAYA ta bi ita
kuma Hajjar ta kira Abban nasu ta sanar masa kin ga kenan wannan tunanin ba na HEEDAYA
ba ne na uwar HEEDAYA ne ita take shirya komai.
"Dama ita ce mana, ga shi kin san dai in Alhaji ya yi magana babu sauyi babu kuma mai sanya
shi ya sauya bare magana da ta biyo daga hannun Hajja kin san kuwa ba zai taɓa janyewa ba.
Ƙwafa Ammie ta yi zuciyar ta na suya ta yi wa Momma sallama tana ta tunanin mafita amma ta
rasa.
"Kin gama naki saura namu, kin aika musu gardiya gida don ki hana su soyewa to da
sannu za ku kwashi kashin ku a hannu, in ma wani abu kike ƙullawa to ta Allah ba taki ba"
Momma da suka yi kiciɓis da Momma a harabar gidan ta furta tana aika mata wani kallo. Wata
dariyar rainin hankali Umma ta saki tana mata kallon uku saura kwata ta ce
"Kar wanda ya fasa duk abin da ya yi niyya, idan kuma akwai wanda zai hana to wanda ya
zartar da maganar yana falon sa za ki iya zuwa ki tsawatar masa" Tana gama faɗar hakan bata
jira cewar Momma ba ta juya ta bar ta a wajen tana jin tamkar ta je ta shaƙo Umma amma ba
hali haka ta juya buguzum-buguzum ta nufi sashen ta.
Lokacin da HEEDAYA ta isa gidan Aunty tana kicin tana haɗa abinci da murna ta fito suka
rungume juna suna ta farin ciki. A falo suka zauna kafin Aunty ta ɗauki jakar ta ce ta zo ta
rakata ɗakin da za ta zauna.
"Aunty ɗakin nan... Sai kuma ta yi shiru.
"Mai ya yi ɗakin ?"
"Kawai sai nake ganin kamar zan ke jin tsoron sa idan dare ya yi" HEEDAYA ta faɗa tana kallon
ɗakin lokacin da suka shiga don a son samun ta suke kwana da Aunty RABEEYA don ba za ta
juri suke shigewa ɗakin su biyu ita suna barin ta ita kaɗai.
"Haba HEEDAYA mai ɗakin kuma ya yi ke da a gida ma ke kaɗai ce a ɗakin ki" Aunty
RABEEYA ta ce tana ƴar dariya.
"Shikena Aunty" Ta ce tana murmushin yaƙe.
"Wai ya aka yi kika cewa Abba bani da lafiya?"
'Don in zo in kasance inuwa ɗaya da masoyina mana, tun da boka ya yi duba ya ce akwai aure
tsakanina da shi na san duk daren daɗewa dole mallakina ne, dole na matso kusa da shi kar in
zauna a nesa da shi ki sa ya manta da ni' Ta faɗa a zuciyar ta a fili kuma ta ce
"Kawai ji na yi ina son zuwa wajen ki Aunty kuma na san in ban ƙirƙiri wani abu ba babu yadda
za a yi in zo"
"Allah sarki HEEDAYA tah ni ma ina cike da kewarki"
"Ina Yayan?"
"Yana asibiti mana" Murmushi ta yi ta ce
"Kuma yaushe yake dawowa Aunty?" Da yamma mana"
"Kamar ƙarfe nawa?" Ta tamabaya don ta yi shirin tarɓar sa na musamman.
"Ƙarfe huɗu" Ta ce tana cewa bari ta duba tukunya a kicin. Gidan ta shiga kallo tana rayawa a
ranta cewa ko sai yaushe ne za ta dawo gabaɗaya da zama ta kasance tare da masoyin ta Ya
ABDUL matsayin ma,aurata don ko a ranta bata jin wani cewa haramun ne su auri miji ɗaya da
ƴar uwar ta, kawai burin ta sanya a gaba da kuma tunanin jiran ranar sakamakon boka tun da ta
san akwai auren bata damu da abin da zai faru har su yi auren ba duk kuwa da ta san ba za su
haɗa miji ɗaya ba.
Ya ABDUL yana zaune a office yana ganin marar lafiya kiran Ammie ya shigo wayar sa
ɗagawa ya yi.
"Ammie barka da wannan lokaci"
"Barka ya aiki, wai wace magana ce nake ji akan cewa HEEDAYA ta ƙaura gidan ka?" Goshi ya
dafe don dama ya san sai an haɗa masa zafi, don ya san a rina wai an saci zanen
mahaukaciya.
"Ba fa ƙaura ta yi ba Ammie zuwa ta yi za take taya RABEEYA aiki kin san bata jin daɗi"
"Yaushe ka koyi ƙarya yaushe ka fara ɓoye mini abu, ko har ka fara zaɓar dangin matarka a
kaina?"
"Haba Ammie ba haka bane"
"To yaya ne ai ga shi nan ni dai da bakina ban taɓa ji ka ce tana rashin lafiya ba" Shiru ya yi don
ya rasa ma mene ne mafita.
'Gaskiya auren zumunci cakwakiya ne' Ya ce a zuciyar sa a fili kuma sai ya ce.
"Ki yi haƙuri Ammie"
"Kawai ka yi takatsan-tsan don na san wannan yarinyar ba yin kanta ba ne zuwa wannan gidan
ka san dai yadda muke da uwar ta, kuma ban da ma rashin hankali HEEDAYA ce mai zuwa
gidan Allah kyauta" Bata jira cewar sa ba ta kashe wayar ajiyar zuciya ya sauke ya cigaba da
aikin sa.
HEEDAYA tun da ta ga ƙarfe uku da wani abu ta shiga ta yi wanka ta ɗauro alwala ta fito ta
shirya cikin silky doguwar rigar da duk ta kama jikin ta sallah la,asar ta yi jin an fara kira, ta
ɗakko turare ta shafa lokaci guda ƙamshi ya haɗe jikin ta. Kallon kanta ta yi a madubi ganin
haɗuwar da ta yi wani murmushi ta yi ta fito ta zauna a falo tana danna waya. Aunty RABEEYA
da ta shiga ɗakin ta yi sallar la'asar ra fito tana sanye da riga da skirt na atamfa sun amshi jikin
ta. Da kallo ta bi HEEDAYA ganin ta sauyo kaya ta yi kwalliya tamkar mai shirin zuwa gidan biki
ga wani ƙamshin turare da ya haɗe falon.
"Wannan gayun fa ko fita za a yi" Ta faɗa cikin tsokana.
"Wanka na yi fa Aunty kuma wannan kwalliyar ai Ya ABDUL na yi wa" Ta faɗa da wasa tana
dariya. Dumm gaban RABEEYA ya buga duk da ta san HEEDAYA da wasa ta yi maganar
amma sai da ta ji faɗuwar gaba tare da jin babu daɗi a ranta. Amma sai ta hau neman tsari da
shaiɗan mai sanya wasi-wasi son ta san sharrin sa ne .
"Ai kuwa yana dab da dawowa" Ta ce ita ma tana dariya tare da wucewa ta je tana jera masa
kayan abinci a dining. Da wani kallo mai cike da harara HEEDAYA ta bi Aunty a fakaice ba tare
da ta bari ta gani ba, don ganin yadda ƙugun Aunty RABEEYAR yake juyawa a cikin skirt ɗin
bare Aunty RABEEYA mai hips sosai saɓanin HEEDAYA da take shafal.
Suna zaune suna ɗan taɓa hira wayar RABEEYA ta yi ƙara a ɗaki tafiya ta yi tana dubawa ta
ga Momma. Bakin gado ta zauna tana amsa kiran bayan sun gaisa.
"Da baki kira kin faɗa mini ba ai na ji"
"Mai Momma?" Ta tambaya cikin sanyi murya.
"Ban sani ba, wai ke mai ya sa RABEEYA kamar wata nusara kike yanzu HEEDAYA ce za ta
ƙaura gidan ki amma kika saki baki shameme kike zaune"
"To ina zan je Momma, kuma HEEDAYA fa ƙanwata ce sannan shi ma Ya ABDUL ai ba bare ba
ne ɗan uwanta ne sannan ma Abba ne fa ya ce ta zo kin...
"Ya isa haka RABEEYA sau nawa zan faɗa miki ƴan uba kuke da HEEDAYA ni kuma kishiyoyi
muke da uwar ta kuma ba zaman lafiya ba ne a tsakanin mu a kan mai za ki yarda ta zo ta tare
miki a gida ai da Abban naku ta kira da kin sanar masa cewa kin ji sauƙi ba sai ta zo ba" Ta faɗa
a harzuƙe.
"To Momma za a kiki gaba"
"Kar ma a koka" Ta ce tana datse kiran. Ajiyar zuciya ta sauke tare da tashi ta saka wayar a caji.
Fitowa ta yi a daidai lokacin kuma Ya ABDUL ya shigo falon ɗauke da sallama a bakin sa. Da
ɗan gudu HEEDAYA ta nufe shi tana masa oyoyo tana zuwa ta kama hannun sa ɗaya da yake
ɗayan yana riƙe da jakar wajen aikin sa. Aunty RABEEYA da ta ƙaraso tsakiyar falon sai suka
zame mata hoto jin shaiɗan yana neman kissima mata jin kishin ƙanwar ta sai ta yi saurin kawar
wa tare da ƙirƙirar murmushin yaƙe wanda iyakar sa leɓanta, ta sani cewa HEEDAYA tana iya
kama hannun Ya ABDUL a baya duk da ba muharramar sa ba ce amma tun sabon yarinta har
yanzu bata daina ba, amma ta ɗauka tun da ya yi aure yanzu ita ma kuma ta mallaki hankalin
kanta za ta daina sai dai kuma ga shi bata daina ba.Yana ƴar dariya yana kallon HEEDAYA don
shi ko kaɗan bai kawo cewa hannun sa da HEEDAYA ta kama zai ƙona ran Aunty RABEEYA
ba.
Ganin ta yi turus a gefe ɗaya sai ya ce
"Yau ba oyoyo Hayati?" Ya ce yana jifanta da wani kallon wanda ya sa fuskar HEEDAYA
sauyawa tamkar dai mijin ta ne ya yi wa kishiyar ta kallon, hatta sunan da ta ji ya kira Aunty
RABEEYA da shi sai da ya sosa ranta ta ji babu wanda ya dace ya kira da sunan sama da ita.
"Oyoyo sannu da zuwa" Ta faɗa da baki tana dariya a maimakon da tana zuwa sai ya rungume
ta amma yau ga shi an samu sauya sai ya fara tunanin ko ganin HEEDAYA ne ya sa ta ƙi masa
hakan.
"Na ƙi wayon" Ya ce yana ƙoƙarin janye hannun sa daga riƙon da HEEDAYA ta masa amma sai
ya ji ta ƙi saki kallon ta ya yi sai kuwa ta saki hannun nasa, wajen Aunty RABEEYA ya nufa
yana sanya hannu ya janyo ta tare da maƙalo ƙugunta ɗaya hannun riƙe da jakarsa.
"Mu je ki haɗa mini ruwan wanka" Ya ce yana kallon fuskar ta. Bata masa musu ba don ta ji
daɗin yadda ya nuna kulawar sa gare ta hakan yana nufin zai iya nuna soyayyar sa gare ta a
gaban kowa tuni ta shagala da cewa HEEDAYA tana wajen. Sama suka haura har lokacin yana
riƙe da ƙugunta ita kuma ta ɗan kwantar da kanta a gefen kafaɗar sa. Tun da suka nufi
matakalar benen take kallon bayan su ranta yana matuƙar suya tana ji tamkar ana watsa mata
ruwan barkono a idanun da take kallon su. Har suka ɓacewa ganin ta tana tsaye a wajen
tamkar an dasa dutse. Hawaye ne suka shiga sintiri a fuskar ta da gudu ta yi hanyar ɗakin da
aka sauke tana zuwa ta faɗa kan gado tare da fashewa da kukan baƙin ciki da kishin da ya cika
mata zuciya. Tana tunanin wataƙila ma yanzu sai sun yi wani abu kafin ya yi wankan, tana ganin
ta zo gidan don samun warakar abin da take ji a zuciyar ta ashe dai ta zo inda za a ke fama
mata ciwon ne...
*MARYAMA*
Tana tafiya gabaɗaya jikin ta ya mata nauyi saboda mutuwar Baffa ga damuwar rashin sanin
takamaiman inda za ta je, sannan ma uwa uba abin da za ta tarar a inda za ta je ɗin. Tana tafiya
tana haɗuwa da mutane waɗanda suke tahowa don zuwa wurin mutuwar wasu a ƙafa wasu
kuwa a mashina. Wasu mata da ta haɗu da su tana ji da za ta gifta su suna cewa an ce ita ce
silar mutuwar mariƙin nata baƙin cikin, abin da take ɗauke da shi ne ya sa ya haɗiyi zuciya ya
mutu!. Wannan furucin nasu ya tabbatar mata da cewa zance har ya fara yawo daman yaɗa
jita-jita ai ba ƙaramin abu ba ne ga mutane bare kuma ƙaramin ƙauye da ko ina dama ba wani
tazara ne da garin nasu ba.
Ta wuce gari uku kenan a ƙafafun ta ga gajiya zuwa yanzu dakyar take ɗaga ƙafafun ta sai
ɓaƙogwaron ta da ya bushe saboda buƙatar ruwa don ita bata ji ko abinci za ta iya sakawa a
bakin ta saboda mutuwar mahaifin ta. Tana dab da shiga ƙauye na huɗu ta ga wasu yara suna
ɗaukan ruwa a famfo ta ruƙi su bata ruwa za ta sha, a marfin bokiti wani yaro ta taro ya miƙa
mata karɓa ta yi sai dai tana kurɓa ta ji ɗaci ruwan kawai Baffa ne a ranta hakan ya ta ji wani
kuka ya taho mata ruwan ta watsar ta miƙa musu marfin ta ce ta gode ta cigaba da tafiya. Tana
dab da fita daga garin can ƙarshen garin ganin wani tsohon gini na asibiti ganin magriba ta yi
kuma babu mutane wajen da yake ƙarshen gari sai wani gida da ta gani daga can gefe shi
kaɗai. Cikin asibitij ta shige duk sai ƙura kasancewar ma duk an ciccire windoji da ƙofofin haka
ta shiga wurin ta ajiye kayanta sai kuma tunanin yin sallah ya faɗo mata don babu sallar da ta yi
ba azhar ba la'asar ga yanzu magriba ta yi. Tsoron kar a ganta duk da bata zaton garin za su
iya sanin wace ce ita tun da akwai tazara sosai da ƙauyen su tun da gari uku ne a tsakani sai
shi ƙauye na huɗu. Tana zaune a kan kayan nata ta dafe fuskarta da hannu biyu kuka take
marae sauti ji take tamkar ta koma ƙauyen su ta yi tozali da kabarin Baffa kewar sa take ji sosai
tana jin ciwo da raɗaɗin rashin sa. Tabbas!. Shi ne gatan ta ga shi yau ɗaya da ba ya raye har
ta fara maraici ta shiga wani hali wanda ko wurin zama ya gagare ta hasali ma bata san ina za
ta je ba haƙiƙa idanun sa ma mashi ne tun da ga shi idanun sa suna kawa har ta yi ban kwana
da gatan da take jin ya rage mata a duniya.
'Mai ya sa? Mai ya sa aka haife ni a haka? Mai ya sa mahaifiyata ta samar da ni ta makauniyar
hanya? Ashe tana tsoron abin kunya amma ta yadda ta same ni ba ta hanyar aure ba, amma
duk wanda ya sayi rariya ya san za ta zubar da ruwa. Shin mene ne laifina? Yanzu ga shi ni ban
san ba ma shin tana raye ko ta mutu? Idan tana raye mai ya sa ta haife ni bayan bata sona shin
ta jefar da ni, ina mahaifin nawa? Su duka basa buƙatata, bani da laifin komai bani na zaɓi
zuwana duniya ta wannan hanyar ba amma mai ya sa nake girbar abin da ba ni na shuka ba?.
Bayan waɗannan abubuwan ga wata ɓoyayyar ƙaddarar da ban san ta yaya ta wanzu a jikina
ba, ya aka yi nake da ciki ba tare da na yi zina ba? Ko wannan yana cikin biyan bashin da
iyayena suka ci na zina? Dama ko baka kusanci namiji ba kana iya samun ciki anya? Ko dai a
kaina ne hakan ta faru ga rashin Baffa wayyo