Showing 54001 words to 57000 words out of 64514 words
Chapter 19 - BONONO BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MAMAN AFRAH f.pdf
ba ya ɗauka
Da sallama ta shigo falon bayan ta yi nocking an mata izini. HEEDAYA ce zaune a kan kujera
ƙafa ɗaya kan ɗaya. Chatting ɗin da ya zame musu jiki suke yi a group nasu na MANYAN MATA
har Ammie ta yi wa kanta masauki a kujera amma HEEDAYA bata ce mata ko ƙala ba.
"HEEDAYA ina wuni ni in gaishe ki" Ta faɗa cikin gatse.
"Lafiya ƙalau mai ziyarar bazata babu neman izini" Baki sake take kallon HEEDAYA. Ya ABDUL
ne ya fito daga kicin ɗauke da plate mai jalof na taliya da ta sha bushashshen kifi da
ruwa-ruwan ta sai turiri take. Falon ya ƙaraso hankalin sa a kan HEEDAYA Ammie kuma baki
sake take kallon sa ganin tamkar bai ganta ba.
"Baby HEEDA na gama dafawa baki ji yadda ta yi daɗi ba" Wani yatsina ta yi don ta ƙara ƙular
da Ammie ta ce
"Sai ka ƙarasa aikin ka wato ka bani a baki"
"Abu mai sauƙi fitar da wando ta ka" Ya ce yana zaunawa kusa da ita.
"ABDULHAKEEM"
"Na'am " Ya amsawa Ammie hankalin sa a kan HEEDAYA.
"Mai ya hana ka zuwa kwwna biyu?"
"Yana tare da iyalansa " HEEDAYA ta ara ta yafa.
"Eh haka ne" Ya faɗa shi ma.
"Ko gaishe ni ba za ka yi ba ina RABEEYA ƙarama?"
"Tana wajen mai renon ta" Ya ce ba tare danya mata maganar gaisuwar ba.
"Ina so ka gaishe da ni" Cewar HEEDAYA zamewa ya yi daga kan kujerar ya durƙusa a kan
gwiwoyin sa ya ce
"Habibty ina wuni" Tsabar mamaki bakin Ammie ya ƙi rufuwa.
*HAFEEZ*
"Wallahi Kaka ban san da wannan maganar ba ki yarda da ni" Ya faɗa cikin ruɗu.
"Waye zai yarda da kai ai tantsuwar ka ba za ta samu shiga a waje na ba, kuma wallahi na baka
mintina ƙalilan ka zo in ba haka ba zan mata korar kare don ni babu mai ɓata mini sunan zuri'a"
Tana gama faɗar haka ta yanke kiran. Gabaɗaya ya haɗa zufa, ga tarin mamakin da ya
dabaibaye masa zuciya, tambayoyi barkatai da ba shi da amsar su, su ne suka taru suka masa
yawa.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ya faɗa yana dafe kai da hannu ɗaya, tare da saka hannun cikin
gashin kansa ya hautsina.
"MARAYAMA ta ciki? Kai impossible" Ya ce a fili tare da jefa wayar aljihun sa, tare da ɗakko
mukullin motar ya fito daga ɗakin ko laptop ɗin bai rufe ba. Ƙofar gidan ya kulle ya shiga motar
ya fige ta a guje. Gudu yake shararawa a kan titin tamkar zai tashi sama fatan sa da burin sa
bai wuce ya isa cikin garin Dutse ya sauka a gida kafin Kaka ta cika abin da ta faɗa na ƙudurta
in bai iso da wuri ba za ta yi wa MARYAMA korar kare.
Ya sani idan ta kore ta babu tabbas ɗin ya sake sanyata a idaniyar ta tun da bai san ina za ta
nufa ba, kazalika ya san Kaka ba za ta yi shaci faɗi ba bata magana a kan abin da bata
tabbatar ba sai dai yana shakku a kan cewa MARYAMA tana ɗauke da ciki. To wa ya mata? Ya
aka yi bata faɗa ba ta yaya ma hakan ta faru wace irin ƙaddara ce wannan da take son shiga
tsakanin sa da ƙaunar MARYAMA bayan ya gama mutuwa a kan son ta, yana tsara ranar da zai
sanar da ita tare da bayyanawa Kaka ƙudurin sa na auren sa ashe dai akwai ƙurar da bai sani
ba.
"Shin mai ya sa kika ƙara yi wa kan ki baƙin fanti bayan wanda kike ɗauke da shi?" Ya tambayi
kansa a fili yana dukan Sitiyarin duk gudun da yake shararawa kan titi sai ya ga kamar ma ko
sauri ba ya yi bare a yi zancen gudu.
MARAYAMA tun daga lokacin da ta ji Kaka ta kira shi a waya tana faɗa masa tana da ciki
kuma za ta mata korar kare. A take ta zube a kan gwiwoyin ta tana faɗin
"Don Allah Kaka ki yi haƙuri kar ki kore ni ban san inda zan je ba, bani da kowa bani da komai
sai ku sai Allah" Ta ce tana miƙa hannu za ta kama ƙafar Kaka. A zuciye Kaka ta saka hannu ta
doke mata hannu, tana nuna ta da yatsa ta ce
"Ai ko ke ce kaf duniya babu wanda ya rage sao mu da ke to na cire ki a kan ma'amala da mu,
ina miki kallon salaha ashe dai lumbu-lumbu ce ke wutar ƙaiƙayi?"
"Mero, mero, mero" Kaka ta shiga ƙwala mata kira amsawa ta yi tare da shigowa da sallama
ganin Kaka tsaye ƙiƙam rai ɓace sai huci take ga MARYAMA zaune tana kuka da magiya sai ta
ji ranta babu daɗi.
"Don Allah ki saka baki kar ta kore ni wallahi ban san inda zan je ba kuma wallahi ni ma ban san
wanda ya mini ciki ba da shi na ganni wallahi ban san ya aka yi ba" Ta faɗa tana kuka tana
kallon Meron da mamaki ya kashe.
"Ciki!!? Wane irin ciki?" Ta tambaya da mamaki.
"Ciki dai na haihuwa ta tashi ki duba ta har idanun ta ki duba ki duba marar ta ma"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ta ce ganin zahirin abin da Kaka ta ce
"Ko a garin mahaukata babu wanda zai ce ya tsinci ciki a jikin sa kuma shi ma munafukin zai zo
ya same ni, da ya ɗauka zai yi wasa da hankali da tunanina a yau sai kun bayyna gaskiya wai
baki san ya aka yi kika samu ba sai ka ce a garin mahaukata in shi ya kitsa miki yadda za ki
faɗa ma asirin ku zai tonu" Kaka ta faɗa rai ɓace Mero tana ta bata baki amma bata sauraron
ta.
HAFEEZ ko da ya shigo garin Dutsen bai rage gudu ba, ana buɗe masa get ko parking bai
gama ba ya fito ba tare da ya rufe ƙofar ba ya shige gidan, mai gadi yana masa sanu da zuwa
ko ta kansa bai bi ba. Yana shigowa ya tsinkayi muryar MARYAMA tana kuka tana faɗin ita ma
bata san wanda ya mata ciki ba. Jingina ya yi da bango yana dafe kai da hannu biyu ya shiga
jero sunayen Allah a zuciyar sa.
'Ko mai zai faru dole na kare MARYAMA dole ni na ɗauki lafin ba zan juri ganin ta a damuwa ba,
ba zan yarda a raba ni da ita ba wato a kore ta don muddin Kaka ta ji ni ma ban san da cikin ba
to tabbas!. Sai ta kori MARYAMA' Ya ce w zuciyar sa, tare da yin ƙundunbala ya shige falon
Kaka murya na rawa ya ce
"Cikina ne Kaka!. Ni na mata cikib kuma ba a son ranta ba fyaɗe na mata" Ya faɗa hawaye
yana cika masa idanu, don shi ciwo yake ji a ransa in ya tuna wani namijin ya san MARYAMA a
mace kuma har da ciki alhalin babu aure. MARYAMA da ta tsinkayi muryar sa jin abin da ya ce
ta shiga tashin hankali jin zai yi wata sadaukarwa saboda ita bayan ta san ba shi ya yi cikin ba
kuma ita kanta bata san cikin na waye ba.
Kaka da Mero daskarewa suka yi a wajen jin furucin sa.
Ban yi editing ba a yi hƙr da typin errors
*MUNA DAF DA GAMA FREE PAGES MAI BUƘATAR SHIGA GROUP DON KARANTAWA
HAR ƘARSHE YA BIYA 500 TA ASUSUN FAIZA ABUBAKAR 9030282375 OPAY*
[2/19, 5:22 PM] MOM MASHKUR & AFRAH: BONONO
(RUFIN ƘOFA DA ƁARAWO)
NA
MAMAN AFRAH
First Class Writer's Asso.
*SADAUKARWA*
Daga farko har ƙarshe sadaukarwa ne ga MARYAM SANI HAFIZ (Merry tah) Alkairin Allah ya
kai gare ki Allah lulluɓe rayuwar ki da tarin ni,imomi da albarkatu Allah raya mana Abdallah
fatan alkairi.
Daga marubuciyar:
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Jalli joga
Da sauran su.
*09013181851*
PAGE 14
*AMMIE*
Da mamakin HEEDAYA da ABDULHAKEEM ta bar gidan don ko Little RABEE ɗin babu
wanda ya kawo mata ita sai dai ta san cewa tabbas!. Wannan ba ABDULHAKEEM ɗinta ba ne
domin shi wancan mai tsananin biyayya ne da girmama ta, amma ta san yanzu an sauya mata
shi wannan ta guda shi ya sa bata so auren sa da HEEDAYA ba don ta san babu mutunci a
lamarin HEEDAYA da uwar ta. Sai dai babu wanda ta sanar ta je ta kama addu'a a kan Allah ya
dawo mata da hankalun ɗanta jikinsa kuma ta san Allah maji roƙo ne sai dai a samu jinkiri.
HEEDAYA da Ummar ta duniya ta musu daɗi suna cin kare su babu babbaka, musamman
HEEDAYA da ta kasa ta tsare a gidan mijin ta kambunta kawai take murzawa shi kuwa
ABDULHAKEEM ya gama mutuwa a kan son da aka sanya masa na ƙarfi da yaji wato ta bin
bokaye da malamai da kuma mallake -mallake na magungunan mata waɗanda basu da alƙibla.
Domin yanzu HEEDAYA ta yi ƙaurin suna a wajen zuwa malamai daman an ce barewa ba za ta
yi gudu ɗanta ya yi rarrafe ba
Alaƙa ta yi ƙarfi tsakanin ta da HUSNA yanzu kaf online bata da aminiya kamar HUSNA kuma
nan ne wajen baje kolin gabaɗaya katafanin sirrin gidan auren ta. Duk da suna baje hajar
sirrikan gidan auren su a group a nasu ganin ai ba sanin juna suka yi ba don haka don wani ya
san sirrin wani ba wani abu bane duk da cewa gabaɗaya sirrin da suke faɗa a group ɗin abu ne
na daɗin da suke fuskanta a gidan aure. Kaf group ɗin MANYAN MATA yanzu sun yarda cewa
HEEDAYA ta fi kowa yin yadda take so a gidan mijin ta kowa tana bashi sha,awa don nata
samun ya zarta hankali gabaɗaya ta mayar sa mijin ta sauna ko kuma shashasha bashi da
burin da ya wuce faranta mata don ita kaɗai yake kallo, ya manta da mahaifiyar sa da sauran
duk wasu abubuwa komai nasa HEEDAYA sai dai duk abin nan da ake abin bai yi tasirin
rabuwa da ƴarsa ba yana bata kulawa duk da hakan ma HEEDAYA ta saka a ranta sai ta saka
Little RABEE ta zama tarihi a zuciyar sa don da ita take kishi a yanzu ita kuma ta fi so ya
zamana daga ita sai ƴaƴan da za ta haifa nan gaba ne take so su kasance a zuciyar sa, tun da
a halin da ake ciki yanzu babu haihuwa a tsarin ta a cewar ta sai ta gama cin duniyar ta da
tsinken tsire don haka ma take yin tsarin haihuwa wato planning.
Umma yanzu babu abin da take sai turawa Momma haushi saboda ta san Momma ta ɗauki
son duniya ta ɗora a kan Little RABEE amma kuma an ƙwace ta a hannun ta yanzu tana
hannun su tun da HEEDAYA ce a gidan ita kuma wannan abun yana ci mata tuwo a ƙwarya.
"Aminiyata Husna wallahi shaƙuwata da ke na ɗauke ki tamkar ƴar uwata shi ya sa nake
kwashe duk wani abu da ya shafe ni nake faɗa miki, yanzu ina so ma in saka rana in zo har
garin kano domin in ganki a zahiri ba kamar yadda muka san juna a hoto ba" HEEDAYA ta tura
mata saƙon lokacin suna chatting.
"Allah sarki ai ni ma na matsu mu haɗu yadda muke ɗin nan babu abin da bamu sani ba da ya
shafi rayuwar mu ya kamata wani ya ziyarci wani"
"Kar ki damu tun da shi HAMEED ba zai kawo ki ba tun da ba shi da lokacin ki ni zan saka
ABDULHAKEEM ya kawo ni"
"Ka ji matar so wallahi aminiyata soyayyar ku tana birge ni kin tsinci dami a kale a yanzu ba
duka maza ba ne suke ba mace kulawa da soyayya ta zama tana cikin jin daɗin rayuwa kamar
yadda kike ji, kina gani dai hatta uku bala'in da kika aiko mini na yi amfani da shi a banza duk
da dai an samu sauyi amma dai ke kam ta dabance ina fatan Allah ya ƙara ɗora ki a kan mijin ki
har ƙarshen rayuwar ku"
"To amin amma dai ni kin san ba zan taɓa yarda na zauna namiji ya ci abinci a kaina ba duk
wani cin kashi ya mini ba"
"To ai ba daga macen ba ne kowace mace za ta so ta samu komai na rayuwar aure da
kwanciyar hankali da kulawa da soyayya sai dai idan bata samu ba ya za ta yi?" HUSNA ta jefa
mata tambayar.
"Ni ai kin san bana zama kullum kuɗina suna wajen malamai da bokaye ai kuwa ina ganin biyan
buƙata don ga shi da ƙorafin gidan aure sai dai in ji ana yi"
"Haka ne amma ni ba zan iya bin malamai da bokaye ba a kan namiji in ɓata lahirar ta don
hakan shirka ne"
"Yo ai sai ka nemi gafara ni kam gwara in gwara kan namiji yanzu fa Ya ABDUL ko uwar da ta
haife shi sai na ga dama nake barin sa ya je gaishe ta in ma ya je sai dai in ni na masa umarni
in bam bashi ba kuwa wallahi ko za a ɗauki watanni ko gidan su ba zai je ba ke ko kallon gidan
ba zai yi ba ga shi dai zai je gidan mu gaishe da uwata amma ba zai shiga gidan su ba sai in ni
na ce kin ga kuwa ai kwalliya tana biyan kuɗin sabulu don in ba haka ba da yanzu na zama
sorry a gidan nan"
"Kina yadda kike so aminiyata"
"To ke ya kika gani, ai shi ya sa daga ni babu ƙari ke ni fa na saka a raina dama a duniya dai
babu wata mace da Ya ABDUL zai mata kallo na so ke har jaddada masa nake cewa ko fita ya
yi kar ya yi wa kowace ƴa mace kallo sau biyu, ya kan ce mini ai in ma daina tunanin zai ga
wata mace da sunan so don daga ni ya rufe ƙofa har gaban abadah"
"Kin ciri tuta ai nake faɗa miki matsalar mata kishiya ce don baka ƙara sanin mene ne zaman
aure sai kana da abokiyar zama"
"Hahaha! Ai ni dama don ma na san babu ita a tsarina ba zan taɓa ma yarda ba Ya ABDUL
nawa ne na ni kaɗai!. Don ni aka halicce shi, wallahi duk ranar da na buɗi ido na ga an mini
kashiya ko ta ɗiyar kara ce na tabbata mutuwa zan yi"
"Ai shi ma ba zai ma fara ba kawai ki cigaba da gashi kuma ki saka a ranki baki da kaishiya a
gidan auren ki don kin kasa kin tsare aminiyata"
Waɗannan kalaman ne suke sanya HEEDAYA ta ji kanta ya fashe a duk lokacin da HUSNA ta
mata su ƙawa ɗaya tamkar da miliyan a cewar ta kenan yanzu yadda take baje sirrin ta na
gidan aure hatta magungunan mata da yadda suke mu'amalar aure da mijin ta babu wanda take
ragewa sai ta faɗawa HUSNA ko MEEMA bata sanin wasu abubuwan kamar yadda take
kwashewa take faɗa mata, hatta magani in ta yi amfani da shi da yadda mijin ta ya yaba a kan
yadda ya same ta sai ta faɗawa HUSNA. Ita kuma HUSNA baiwar Allah babu wani abu da take
ɗauka a gidan HAMEED sai takaici kamar dai yadda aka saba don shi har yanzu bai damu
danita ba ita kuma da a ce zai nuna mata kulawa ko yaya ne da sai ta ji babu ya ita a duniya kai
ita ko dai zai auro mata uku ne babu ruwan ta amma dai ga shi ita bata samu komai ba daga
gare shi na haƙƙin auratayyar shi ya sa ko a group ɗin idan ana hirar mazaje take jan bakin ta ta
yi shiru saboda ita ko gutsuren abin da suke samu ba samu za ta yi ba haƙurin man dai shi take
yi tana neman zaɓi da mafita daga ubangiji.
*BAYAN WATA BIYU*
Yau ne HEEDAYA ta shirya domin zuwa garin Kano ta kaiwa HUSNA aminiyar ta ta online
ziyara kowa cike yake da ɗoki da murnar haɗuwar sa da wacce ya saba. HEEDAYA tana ta
Alla-alla su isa Kano kawai so take ta ga HUSNA. HUSNA ma a nata ɓangaren haka ne ta
shirya musu tarɓa ta musamman suna waya da HEEDAYA har suka iso ƙofar tangameman get
ɗin gidan in da mai gadi ya wangale musu get ɗin Ya ABDUL ya kutsa hancin motar ciki.
HUSNA da ta kasa zaune ta kasa tsaye saboda farin ciki tana tsaye a harabar get ɗin, motar
tana