Showing 57001 words to 60000 words out of 64514 words
Chapter 20 - BONONO BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MAMAN AFRAH f.pdf
tsayawa ta taho wajen da sauri, Ya ABDUL ne ya fito ya zagaya ya buɗewa HEEDAYA
ƙofa hannu ta miƙo masa ya kamo ta ta fito da sauri suka rungume juna ita da HUSNA cike da
tsananin murnar haɗuwa. Shi kuwa yana ta musu dariya a haka suka saki juna HEEDAYA da
HUSNA suna riƙe da hannun juna suka shige cikin gidan Ya ABDULA yana biye da su tana
faɗin an nuna masa wariya. Bayan an gaisa ta gabatar musu da abinci suka ci sai Ya ABDUL
ɗin ya ce zai je wajen wani abokin sa ya dawo nan HEEDAYA ta ringa faɗa masa ya kiyaye ban
da kallon mace sau biyu don hakan ganganci ne da wasa da ranta sumbatar ta ya dawo ya yi a
gaban HUSNA yana faɗin ai shi nata ne babu wata mace da zai iya kalla da sunan so don
sauran mata ma kallon muciya da zani yake musu ita kaɗai yake wa kallon mace.
HUSNA dariya take ra musu bayan fitar sa ta ringa cewa gaskiya sun dace da juna mijin ta
rana ƙaunar ta. Hira suka cigaba da yi har sai da ta dawo kafin ya fito da tsarabar da suka kawo
mata tana ta godiya bayan kayan matan da HEEDAYA ta jibgo mata. Tata tsarabar ta bayar
wanda kayan yara ne masu kyau ta tsada ta ce su kai wa Little RABEE da kewar juna suka
rabu HEEDAYA da HUSNA suna ta ɗagawa juna hannu.
Haɗuwar da suka yi a zahiri ya ƙara danƙon zumuncin su tare da shaƙuwar su. HEEDAYA da
take ɗaga kai da hanci a group tana nuna ta fi kowa shawo kan mijin ta musamman da wasu
daga cikin matan group ɗin suke fasa mata kai. Yanzu tsabar jijji da kai ma har ta fara share
MEEMA idan ta mata magana sai ta ga dama za ta amsa.
"Wai HEEDAYA mai na miki ne kwana biyun nan na ga ko a group na MANYAN MATA in kika yi
magana na yi magana sai ki wa kowa replay ki share magana ta anya hakan daidai ne kuwa
amma in wani abu na miki ki yi hakuri" Haka MEEMA ta rubuta ta tura mata amma sai bayan
kwana biyu ta mata replay da cewa
"Babu abin da kika mini ra'ayi ne kawai kin san kuma hausawa sun ce ra'ayi kukan jaki"
"Ban gane ba, ai na ce ki yi haƙuri ko na miki wani laifin cikin rashin sani"
"Ni fa babu abin da kika mini"
"Wai yanzu don a kan HUSNA na ne kike share ni kar ki manta ni fa ƙawar ki ce ta kusa tare
muka yi karatu kuma duk wani mataki da kika taka a gidan ABDULHAKEEM ni ce sila ko kin
manta a daren ki na farko ma ko inda kike bai kalla ba? In kin manta in tuna miki hatta malamai
ni na kai ki kika san wajen su suje miki aiki amma ya dace ki watsa mini ƙasa a ido, saboda
wata ita fa online kuka haɗu ni kuwa tun bamu san kanmu ba muje tare...
"Dakata! MEEMA baki da hurumin da za ki faɗa mini mai zan yi a rayuwtaa, kuma HUSNA ta fiki
sau miliyan a wajena an faɗa miki shi zumuncin online ɗin ba ya fin na zahiri? Sannan da kike
wani yanyanyayan ɗin kin zama silar zamana wani abu a gidan miji mene ne yanzu kuma ina ne
ban sani ba ni kawai ji na yi na daina ra'ayin ƙawancen da ke " Tana gama faɗar hakan ta daina
buɗe saƙon na MEEMA ma. Wannan abin ya yi wa MEEMA ciwo sai dai duba da butulci irin na
ɗan adam sai ta janye jikin ta daga wajen HEEDAYA ita kuwa HEEDAYA ko a kwalar rigar ta,
yanzu wasu ƙawayen ma ta sake a wasu groups ɗin amma dai babu kamar HUSNA.
*BAYAN SHEKARA ƊAYA*
Yanzu Little RABEE tana tafiya ga kuma tana cin abinci sanna yarinyar sai kyawun ta haɗe
da kamamnin ta da mahaifiyar ta suka ƙara bayyana in da yarinta ba sai ka ce Aunty RABEEYA
ce idan ka ganta. Sai dai wani abu da ya fara ci wa HEEDAYA tuwo a ƙwarya yadda Ya ABDUL
ya damu da yarinyar sosai yanzu ko gidan ya shigo sai ya ce mai renon ta ta kawo masa ita
haka zai zauna ya yi ta mata wasa ko ma ya ɗauke ta su fita. Sawun ta wajen manyan
malaman ta da take ji da su uku a kan a yi farraƙu tsakanin Ya ABDUL da Little RABEE amma
abin ya ci tura!. Kowa sai ya ce ba zai iyu a farraƙa su ba don a nata rashin imanin so take a
saka masa tsanar yarinyar a ransa yake mantawa ma da ita amma sai take ganin tamkar wutar
soyayyar ake rurawa a tsakanin su ba ta ƙiyayya ba. Ta kashe kuɗi don cim ma wannan burin
amma abin ya ƙi ci ya ƙi cinyewa hakan ya sa ita ta ɗauki tsana da kishin yarinyar ta saka a
ranta tamkar dai ta manta da karamci da halaccin mahaifiyar ta lokacin tana raye ita kawai sai
ita da ƴaƴanta ƴaƴa da babu rana bare watan haihuwar su don babu haihuwa ma a ranta yanzu.
Wani abu da ya fara kutso kai cikin lamarin zamanta da Ya ABDUL shi ne ƙaurace mata, ya fi
son kasancewa shi kaɗai bayan ra san koyaushe muradin sa bai wuce ya gan shi tare da ita ba.
Amma yanzu sai ya haura sama ya kulle ƙofa ta rasa mai yake idan ta tambaye shi sai ya ce
hanyaniya ce ba ya so. Ta faɗawa HUSNA wannan ƙorafin amma sun kasa samo bakin zaren.
Don haka sai ta ɗauki aniyar bin ƙwaƙƙwafin sa ko za ta gano dalilin sa don bata yarda da hujjar
da ya bata ba ta cewa hayaniya ce ba ya so.
Da dare misalin ƙarfe sha ɗaya na dare ta gaji da zama ita kaɗai a ɗakin ta tana ta juyi so
take bacci ya ɗauke ta amma ta kasa sai tunane-tunane take tana saƙa da warwara. Ƙafafun ta
ta sako daga kan gadon tana hamma, sanye take da riga da wando na bacci kanta da hula mai
net. Saman ta haura cikin sanɗa ta je ƙofar ɗakin nasa ta tsaya. Kunnen ta ta kara sai ta ji dirin
magana. Mamaki ya kamata ta rasa da wa yake magana . Kunne ta kasa a nan ta gane waya
yake.
"Ina son ki mana, ai ko duniya zan iya ɗaga babbar murya na faɗawa ina ƙaunar ki" Wani irin
bugu ƙirjin HEEDAYA ya yi lokaci guda zufa ta jiƙata jikinnta ya ɗauki karkarwa ji da ganin ta ya
ɗauke na sakanni. Ta kasa gaskata kunnuwan ta abin da suka jiye mata.
'Mace?' Ta jefawa kanta tambayar zuciyar ta tamkar ta huda ƙirjin ta ta fito.
"Yaushe na yi wannan sakacin Ya ABDUL yake wayar soyayya da mace na shiga uku ni kam"
Ta faɗa a fili tana kama handle ɗin ƙofar ta murɗa amma sai ta ji a rufe. Ya ABDUL da yake
waya da masoyiyar sa jin an taɓa ƙofa alamar za a shigo sai ya ce mata yana zuwa zai kira.
Tasowa ya yi ya buɗe ƙofar maimakon ya girmama ta ko dai ya matsa ta shiga ɗakin sai ya
kasa ya tsare. Mamaki al'ajabi suka cika mata zuciya.
"Kina buƙatar wani abu ne?" Ya tambaya a dake. Kallon sa take da idanun ta da suka kawo
ruwa ta danne abin da take ji ta ce
"Na ji shiru ne kuma na kasa bacci shi ne na ce bari na taho nan"
"Ina buƙatar kasancewa ni kaɗai ba na buƙatar takura" Yana gama faɗar hakan ya rufe ƙofar.
Idanun ta kamar za su faɗo a take ta ji komai ya sare mata lokaci guda ta tuna cewa Umma
shekaran jiya ta ce mata ta ga ya shiga gidan su bayan ta san sai ta masa umarni yake zuwa
gidan nasu to mai hakan ke nufi.
Ba wannan ne damuwar ta, soyayya yake da wata a waya? Da bibiyu take taka matakalar
ƙasa ta dawo ta nufi ɗakin ta tana zuwa ta ɗauki wayar ta hannun ta har rawa yake ta kira
HUSNA don ta san ita kaɗai za ta tattauna da matsalolin ta. Sau uku tana kira amma babu
amsa.
'Haba HUSNA ki ɗauka mana ki ji danuwar da ta kutso kai cikin gidana' Ta faɗa a zuciyar ta
tana jin wani tashin hankalin yana baibaye zuciyar ta.
A karo na huɗu HUSNA ta ɗauka muryar ta cike da bacci ta ce
"HEEDAYA lafiya" Kuka HEEDAYA ta fashe da shi don ta kaaa furta komai.
"Haba aminiyata ya da kuka kuma ko mutuwa aka miki?"
"Yo ba gwara a mini mutuwa ba da bala'in da yake tunkaro ni"
"Subhanallahi mene ne damuwar"
"HUSNA Ya ABDUL ne na kama shi yana waya da mace, kin san ai na fala miki sauyin da ya
fata shigo minj da shi cikin rayuwar auren mu to wallahi ɗazu cikin kunnuwana na ji yana furta
kalmar so ga wata mace
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un wannan wace irin baƙar rana ce?" Ta faɗa hankali tashe tana
tashi zaune daga kwanciyar da take.
"Shi ne da ya buɗe ƙofar ma wai ni HEEDAYA yake tambaya ina da buƙatar wani abu, sannan
na taho ke ma na zo ina kiran ki kika ƙi ɗauka"
"Ayya!. Ki yi haƙuri bacci nake kin san gwauruwa da bata da miji a kusa da na yi isha'i sai na
kwanta bacci baki ga yau ko chatting ba mu yi sosai ba tun wuri na sauk...
"Bar wannan labarin ƙanzon kuregen mene ne mafita wallahi kaina ya kulle na kasa kowane
tunani ban taɓa tunanin ko hasashen akwai irin wannan ranar za ta riske ni ba"
"Ki bar wannan tada hankalin ƙaryar sa ya ce zai aure ta ai"
"Yo ko ba auren ta zai yi ba ni yin kalmar sa ta so ga wata mace ai bala'i ne me lasisi a wajena
vana ƙaunar komai ya haɗa shi da kowace mace ki hatta ƴarsa ta cikin sa Little ɗin nan na
tsane ta kishin ta nake wallahi dama ɓarin ta aka yi ko kuma a take da aka haife ta ta bi uwar
ta...
"Ya isa haka HEEDAYA ƴar zumun naki, yarinyar da mahaifiyar ta ta so ki kamar mai to ko ba
don mahaifiyar ta ba albarkacin uban ta bai kama ta kike faɗar wannan ba ai ba a kishi da ƴaƴa"
"Ke kike ganin haka ke ni kishina hatta uwar sa bai tsallake ba sai da na musu farraƙu ko yanzu
ma ina da niyyar ƙara farraƙa su don na ji ƙishin-ƙishin yana zuwa gaishe ta" Kai HUSNA ta
gyara tana mamakin irin baƙin kishin HEEDAYA bayan maza kuma ba tabbas gare su a kan
mace ba tun da har ta ji yana furucin so ga wata to tabbas sai dai addu'a dama da wuya namiji
ya ƙaunaci mace ita kaɗai.
Sosai HEEDAYA take kukan baƙin ciki a cewar ta yau ba za ta iya bacci ba ita dai HUSNA ta
bata baki daga ƙarshe suka yi sallama ranta yana suya idan ta tuna furucin da ta ji Ya ABDUL
ya yi wa wata sai ta ji tamkar ta yi ƙaramar hauka.
Washe gari da safe da ta tashi ko kicin bata kalla ba dama duk saboda baƙin kishin ta ko
masu taya ta aiki babu ta gwammace ta yi girkin ta da sauran ayyuka sai dai sauran na harabar
gidan da ba fulawoyi ruwa maza su yi, sai sai renon Little RABEE ita kuwa ta haife ta ma ko yin
jika da ita.
Ko da ya fito ko kallon arziƙi bai samu ba, shi ma kuma sai ya ɗaure fuska ko sallama bai
mata ba tana jin lokacin da ya tafi ganin Little RABBE. Tana jin fitar motar sa ta fito ta saka
direba ya ɗauke ta sai suka keta hazon shiga daji suna karo da ciyayi. Wurin bokan da MEEMA
ta haɗa ta da shi ta je bayan ta kora masa jawabin abin da yake tafe da ita sai ya ce ta kwantar
da hankalin ta ko da ya yi soyayya ba zai taɓa auren macen ba ai sun gama kama mata shi a
hannu babu shi babu sha'awar wata ƴa mace sai ita!. Kalaman sun mata daɗi inda ya bata wani
garin magani ya ce ta saka masa a miya. Kuɗi ta biya shi ta shiga mota direban ya ɗakko ta don
har ya saba kawo ta wajen.
Daga nan gidan su ta wuce ta je ta korawa Umma jawabi. Zare idanu Umma ta yi tana ta
ambaton bai isa ya buɗaɗa musu ƙasa a ido ba don HEEDAYA bata da kishiya a duniya!. Ita ma
wurin nata bokan ta ce za ta nufa ya juyarwa da ABDULHAKEEM ɗin hankali a kan mace don
ba za ta iya ganin wannan abin kunyar ba a jawo mata gori a wajen kishiya don har yau takun
saƙa suke ita da Momma har ma Ammien don suna ganin sun mallake ABDULHAKEEM.
Kaf sai da HEEDAYA ta faɗawa HUSNA labarin zuwa wajen boka da kuma yadda ya faɗa
mata, sannan ta ƙara faɗa mata maganin da ya bata da inda ya ce ta sakawa mijin nata a miyar
abinci. Kwana biyu dai ta ga daidaituwar al'amura har ma wurin su Ammien ya daina zuwa
wanna lamari ya mata daɗi hankalin ra ya kwanta tana ganin amfanin zuwa wajen bokaye da
malamai.
Kwanci tashi asarar mai rai wata uku da yin haka a lokacin da duniya ta yi wa HEEDAYA da
Umma daɗi suna ganin sun samu kan ABDULHAKEEM ashe dai basu sani ba lumbu-lumbu ya
musu babu zato babu tsammani wani labarin mai kama da ya fi faɗar mutuwa ya riski Umma da
HEEDAYA lamarin da ya sanya suka shiga mummunan tashin hankalin da suka kusa zaucewa
musamman HEEDAYA da jin labarin ya sa ta zama kamar mahaukaciya. A ranar wata labara ne
tana kwance tana danna waya ga yankaken apple mai sanyi a plate tana ɗauka tana ci
Shigowar Ya ABDUL da sallama da wasu samari guda biyu suna biye da shi ɗauke da set guda
na akwati. Zaune ta tashi tana murmusawa tana jin daɗin yau kuma kyautar da za a mata kenan
kasancewar ta saba da kyaututtukan da yake mata don ita ko lefen aure ma ba wani damuwa ta
yi da shi ba amma wannan ya faranta ranta. Suna ajiyewa suka gaishe ta tare da fita fuskar ta
cike da murmushi take musu sannu har da ɗaukan 5k ta basu wai sa sha lemo. Bayan sun mata
godiya sun fita ta tashi tana wani fari da ido ta ƙarasa wajen sa gani ya zauna dafa kafaɗar sa
ta yi tana aika masa wani sihirtaccen kallo mai cike da ma'anoni da dama na so da ƙauna.
"Yanzu wannan duk ni kaɗai?. Ina godiya a gare ka ba zan gushe ba ina ambaton na yi dacen
miji ba har sai numfashina ya bar gangar jikina, ina ƙaunar ka Ya ABDUL ina faran har abada
mu zauna mu kaɗai don ba na fatan ko a mafarki wata mace ta raɓar mini ko da takalmin
sawarka ne bare kuma kai ɗin da kan ka...
"Wannan kayan faɗar kishiya ne, yau saura sati guda za a ɗaura mini aure" Kalaman sa suka yi
gaggawar katse wa nata kalaman hanzari. Duhu ne dimm ya wulgawa ganin ta, cikin sakanni
ganin nata ya dawo sai kuma falon ya shiga juyawa mata tamkar famka, kunnuwan ta suka yi
dummm basa jin kowane sauti. Sororo take kallon sa da idanun ta da suka ƙanƙance saboda
mamaki. Lokaci guda komai ya kwance a zabure ta tashi tsaye tana kallon akwatinan masu
kalar ruwan goro da suke ta faman sheƙin sabunta, sannan ta waiwaya ta kalli Ya ABDUL da ya
koma ya jingina bayan sa da jikin kujera yana kallon ta hankalin sa kwance kamar tsumma a
randa!.
[2/19, 5:22 PM] MOM MASHKUR & AFRAH: BONONO
(RUFIN ƘOFA DA ƁARAWO)
NA
MAMAN AFRAH
First Class Writer's Asso.
*SADAUKARWA*
Daga farko har ƙarshe sadaukarwa ne ga MARYAM SANI HAFIZ (Merry tah) Alkairin Allah ya
kai gare ki Allah lulluɓe rayuwar ki da tarin ni,imomi da albarkatu Allah raya mana Abdallah
fatan alkairi.
Daga marubuciyar:
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Jalli joga
Da sauran su.
*09013181851*
PAGE 15
*MARYAMA*
Ta shiga tashin hankali sosai na jin furucin Ya HAFEEZ zai ɗauki abin da bai san nashi ba
ne ya ce cikin sa bayan ko ita da cikin yake jikin ta bata san mai shi ba. Kaka sosai ta sha masa
faɗa tana cewa ya bata mamaki ya yi abin da bata taɓa zato ba duk da dai tana kokwanton
hakan amma ba