Showing 30001 words to 33000 words out of 64514 words

Chapter 11 - BONONO BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MAMAN AFRAH f.pdf

30 Mar 2025

5104

dosowar asuba sai ya ce su je su yi wanka, da to
ta amsa masa tana shirin sakkowa daga gadon sai ji ta yi an yi sama da ita, hannu ta sanya ta
rufe idanun ta gabaɗaya kunyar sa take ji bata san dai ko don ranar farko ba ce kuma a daren
farko amma dai ji take tabbas za ta dawwama da kunyar sa. Ruwan ɗumi ya haɗa ya saka ta a
ciki ta gasa jikin ta. Sannan suka gabatar da wankan tare kamar yadda annabi S.A .W ya ce
yana da kyau ma'aurata su yi wanka a tare hannayen su suna gwauraya a ruwan. Kasancewar
tana ta jin kunya ta ƙi sakin jiki da shi, sai ta riga shi gana alwala ta fito daga bayin ta bar shi zai
yi alwalar.


Towel ne ɗaure a jikin ta sai wani ƙarami da ta naɗa a kan nata tana tsane ruwan. Wayar Ya
ABDUL da take ajiye a gefen bed side drower ta hanga tana kawo haske tana ɗaukewa har ta
banzantar da wayar ganin ba hurumin ta ba ne, kuma dai ta san an ce duba wayar miji tamkar
mace tana yankan albasa ne wato tana gani idanun ta yana hawaye don ba lallai abin da za ta
gani ya zama mai farantawa ba ita kuwa ta daɗe da sanyawa ranta cewa babu ita babu binciken
wayar miji kamar yadda ta ji ana labarin wasu suna yi har a yi faɗa a kan hakan wasu har igiyar
auren su ake tsinkewa ta sanadiyyar hakan shi ya sa ta ga maganin kar a yi to kar a fara.

Har hasken wayar ya ɗauke sannan ta juya wardrobe tana son samu kayan da za ta sanya a
jikin ta, amma sai ta ƙara ganin wayar ta kawo haske a karo na biyu, a wannan karon sai ta
kasa haƙuri ta nufi wayar ba don binciken wanda yake kiran ba sai don son ta ga mai kiran
sabon ango a wannan lokaci.

'Ko dai Ya ABDUL yana da wasu ƴan matan ne shi ne suke kiran sa wataƙila bai sanar da su ya
yi aure ba' Wani sashen na zuciyar ta ya kissima mata hakan.


"HEEDAYA" Shi ne abin sa ta gani yana yawo akan screen ɗin wayar, gabanta ne ya yi
mummunar faɗuwa tana ji a ranta anya lafiya kuwa? Sannan dama zuciyar ta tun jiya take cike
da zulumin rashin samun wayar HEEDAYA kasancewar a kashe, sannan tana ta mamakin
yadda ba ta zo kawo amarya ba, ta yi kewar ta, tabbas za ta so a ce ita HEEDAYA ta kira
saboda ta san ta fi Ya ABDUL kewar ta sai dai zulumin kiran na lafiya ne kuwa shi ne abin da ya
fi ɗaga mata hankali.

"Mene ne" Ta tsinkayi muryar Ya ABDUL ashe har ya fito daga bayin ya zo bata sani ba.

"HEEDAYA ce fa take kiran ka"

"Kuma mene ne na ruɗewar?"

"Kar fa ko ba lafiya ba"

"Sai ka ce baki san rigimar HEEDAYA ba wataƙila saboda ke bata yi bacci ba yau"

"Amma a wayar ka ta kira fa"

"Kuma ke take nema ba" Ya bata amsa tare da juyawa ya haura sama ɗakin sa domin shiryawa.
Shiru ta yi dai tana zulumi a zuciyar ta har wani kiran ya shigo, wayar ta ɗauka ta zauna a bakin
gado tare da manna wayar a kunnen ta.

HEEDAYA wacce take jin bugun zuciyar ta yana sama da ƙasa jin duk kiran da take ba a
ɗauka ba, ta fara tunanin suna can suna soyewa wanda tunanin hakan da ya faɗo mata ba
ƙaramin baƙin ciki ta ƙunsa a ranta ba. Sai dai jin wannan karon an ɗaga kiran sai da ta ƙara
dubawa ta tabbatar an ɗaga ɗin kafin ta kai wayar kunnen ra bayan ta sauke ɓoyayyar ajiyar
zuciya. Ji take tana kewar sa sosai ji take tamkar ta shekara bata ji muryar sa ba. Idanu ta
lumshe bayan ta gyara kwanciyar ta, tana jin damuwa da ƙuncin zuciyar ta yana wankewa cikin
wata muryar da bata san tana da ita ba ta ce.

"Hlo Yayanah!" Aunty RABEEYA da sauri ta janye wayar a kunnen ta don yanayin yadda
HEEDAYA ta yi furucin sai da ta ji wani iri da a ce ba HEEDAYA ba ce wata macen ce da ban da
babu makawa za ta ce budurwar sa ce don yanayin yadda ta yi furucin ya nuna tamkar akwai
wani abu a ƙasan zuciyar ta. Amma sanin HEEDAYAR ta ce sai wani murmushi ya suɓuce mata
ta ce

"HEEDAYA tah" Da mugun sauri HEEDAYA ta cire wayar daga kunne ta, tare da tashi zaune
gabanta yana faɗuwa don bata taɓa zaton za ta ji muryar Aunty RABEEYA ba duk da ta san za

su iya zama waje ɗaya a yanzun amma bata kawo cewa har an kai lokacin da za ta iya ɗaga
kiran ba sai dai wani ɓari na zuciyar ta ya tunasar da ita cewa yanzu fa matsayin matarsa take.
Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokare mata zuciya tabbas bata ƙara tabbatar tana da mugun kishi
ba sai yanzu da ta ji Aunty RABEEYA ta ɗaga wayar Ya ABDUL a take zuciyar ta ta shiga hasko
mata huton su na wataƙila ma kan Aunty RABEEYAR ma yana kafaɗar Ya ABDUL ɗin.

Wani kuka ne ya ƙwace mata wanda ta kasa iya riƙe shi.

"Auntyyyy" Ta faɗa cikin kukan, wanda a zahiri HEEDAYA ta nuna wa Aunty RABEEYA tana
kukan rashin ta ne da kewar ta a baɗini kuma tana kukan kishin Aunty RABEEYAR ne.


"HEEDAYA tah mene ne wa ya taɓa mini ke?" Ta tambaya hankali tashe.

"Ba ke ba ce"

"Mai na yi kuma?"

"Tun jiya ba na samun wayar ki kwana na yi ina tunanin ki na yi kewar ki Aunty shi ne yanzu da
na ga asuba ta yi sai na ce bari na kira Ya ABDUL ya haɗa ni da ke" Akiyar zuciya Aunty
RABEEYA ta sauke sai yanzu ta tabbatar da cewa lafiya sannan ta ƙara tabbatar da ƙaunar ƴar
uwar ta gare ta tamkar dai ba ƴan uba suke da HEEDAYA ba suna ƙaunar junan su.

",Tuba nake HEEDAYA ni ma na yi cigiyar ki har na gaji kuma bana samun wayar ki"

"Matsalar network ne ina Ya ABDUL?" Ta tambaya don ta matsu ta ji ina yake har ta ɗauki
wayar kafin ya ɗauka.

"Ya fito wanka ne yana shiryawa ne da na ce masa kina kiran wayar sai ya ce ni kike nema"

'Dole sai na tashi tsaye na zage dantse kenan dai har wayar ma ta koma hannun ta? Kuma da
ta ce yana shiryawa da alama wanka ya fito to ma in ba wanka na ibadah ba wankan mai za a
yi da asubar farin nan?' Ta jefawa kanta tambayar a zuciyar ta.

"To Aunty ki gaishe da shi tun da na ni lafiyar ki hankali na ya kwanta" Tana gama faɗar hakan
ta datse kiran ba tare sa ta jira cewar Aunty RABEEYA ba, don ba za ta iya jure cigaba da
magana da ita ba wataƙila ma in aka jima tana iya jin abin da zai fi wannan ƙona mata rai. Aunty
RABEEYA kuwa murmushi ne kwance a saman fuskar ta tana jinjina ƙaunar sa HEEDAYA take
mata kuma ita ma haka ne a nata ɓangaren.

*BAYAN SATI UKU*


Kwance take a ɗakin ta tana ta tunanin mafita don yanzu sai ta yi kwana da kwanaki bata
sanya Ya ABDUL a idanun ta ba wanda ta kasa jure hakan. So take a kullum a ce tana tozali da
kyakkyawar fuskar sa mai haifar mata da nutsuwa da kwanciyar hankali. Yau kwana uku kenan
rabon da ta saka shi a idanun ta tun ranar da suka zo gaishe da su Abba da daddare shi da
Aunty RABEEYA yadda suka murmure suka yi wani kyai daga shi har Aunty RABEEYAR shi
zau nuna maka tare da tabbatar maka suna ba juba kulawa kuma suna cikin kwanciyar hankali.
Wannan abin da ta gani ya daɗa rura soyayyar Ya ABDUL a zuciyar ta, kullum abin cigaba yake
a maimakon ci baya ga kishin Aunty RABEEYA da take ji yana ƙaruwa tare da nuƙurɗusar
zuciyar ta. Babban abin da yake damun ta ma bai wuce yadda ta ga Ya ABDUL tun da ta yi aure
shaƙuwa ta ragu a tsakanin su idan ba ƙarya idanu da zuciyar ta suka mata ba sai take ganin
ma yanzu kamar ya daina son ta da tarairayar ta kawai daga asibitin sa sai matar sa ne kaɗai
yake ba kulawa sai kuma iyaye.


Zuwan ta gidan sa ɗaya wansa sai da ta yi da na sanin zuwa domun mummunan angamon
da idanun ta suka mata a tsakanin masoyan biyu. Amma dai yanzu so take ta samarwa kanra
mafita.

"Hajja ta furta a fili tare da tashi ta ɗauki jakar ta ta saka wayar ta a ciki Umma ta sanar wa za ta
je gidan Hajji baki Umma ta taɓe ta ce sai ta dawo. Abba kuwa tana faɗa masa ya yi murna da
hakan jin za ta je gaishe da mahaifiyar sa. Direba ya sauke ta a ƙofar gidan na Hajja ta shiga da
sallama.
"Lale marhabin da ƙawata" Hajja ta faɗa tana tafa hannu tare da yin dariya a lokaci guda.
HEEDAYA ma dariyar ta yi ra samu waje ta zauna suka dasa hira bayan ta bata lemo da
bakilawa da alkaki tana ci suna taɓa hira.

"Hajja wata magana nake son faɗa miki ki faɗawa Abba ni tsoron faɗa masa nake"

"Kin samu mijin ne?" Hajja ta tambaya baki washe.

"Ba wannan ba ne mijin ma yana nan zuwa in sha Allah lokaci kawai ake jira"

"Allah kawo shi amma mene ne"

"Amin Aunty RABEEYA ce ta ce mini bata jin daɗi in je gidan ta in mata kwana biyu to ina tsoron
tunkarae Abba da maganar kin san halin sa"

"Ayyiri-yiri" Hajja ta carara guɗa.

"Kai na fi kowa farin ciki yo ki ce an samu ɗan baba, ai rashin lafiyar mai dalili ce kuma dole a je
a taimaka mata da wasu ayyukan kafin cikin ya yi ƙwari "

"Wallahi kuwa Hajja kin san ta bata son ƴan aiki suke mata komai" HEEDAYA da maganar cikin
ta doke ta duk da ta san maganar ba haka ba ce Hajja ce ta faɗa amma sai da ta ji wani iri,
sannan ta san wani ƙudurin ta ne zai kai ta gidan don ita Aunty RABEEYA ma bata san da
maganar ba.
"Ai Abban naku zan kira in masa jawabi"

"Barka da yamma Hajja" Abba ya faɗa bayan ya ɗaga kiran Hajja.

"Barka Bashir ya gida da iyalin"

"Kowa lafiya"

"Ma sha Allah, Allah yi albarka"

"Amin Hajja"

"Wannan yarinya RABEEYA ce bata jin daɗi shi ne ta kira ni a waya rake so HEEDAYA ta je
gidan nata ta yi kwana biyu kafin ta ji ƙarfin jikin ta ka san ƙaramin ciki akwai laulayi" Shiru ya yi
yana ɗan nazari ya yi mamakin da RABEEYA ta faɗi maganar nan kasancewar ta santa da
alkunya amma in ya duba cewa Hajja kakar ta ce sai ya ga hakan ba komai ba ne.

Amsa mata ya yi da cewa HEEDAYA za ta je. HEEDAYA kuwa ta ji daɗi sosai don za ta cim
ma ƙudurin ta ga kuma komawa kusa da masoyin ta take sanya shi a idanun ta a kullum.


Sai magriba ta baro gidan Hajja, bayan isha'i Abba ya kira ta a waya part ɗin sa ta nufa ta
same shi a falo yana duba news.

"HEEDAYA mai ya samu Aunty naki?" Dumm gabanta ya buga sai dai ta yj gaggawar saita
nutsuwar ta ta ce

"Abba bata faɗa mini ba sai dai ta ce mini kawai in je bata da lafiya" Bai yi magana ba ya shiya
latsa waya gabanta sai faɗuwa yake bata ankara ba sai jin muryar Aunty RABBEYA ta yi tana
cewa

"Ina yini Abba" Ta faɗa bayan ta yi sallama. Idanu HEEDAYA ta shiga zarawa tana jin faɗuwar
gabanta yana tsananta muddin aka tabbatarwa da Abba gaskiyar magana ta san kashin ta ya

bushe.

"Lafiya ƙalau ina ABDULHAKEEM ɗin?"

"Yan lafiya Abba"

"Madalla!. Ya jikin naki?" Aunty RABEEYA da take kwance kanta a cinyar Ya ABDUL ta ma rasa
abin cewa tun da ita dai ta san lafiyar ta ƙalau kuma babu wanda ta cewa bata da lafiya.

"Alhamdulillah!." Ta samu kanta da faɗa saboda bata son tambayar Abba wanda ya ce bata da
lafiya kuma hakan tamkar tuhuma ce. HEEDAYA wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauke jin ba a
ƙaryata ta ba.

"Gobe za ta dawo nan ɗin ai HEEDAYAR har zuwa ki samu ki warware Hajja ai ta kira ni a waya
ta bani umarnin in bar HEEDAYA ta je ta taya ki zama kamar yadda kika buƙata baka jin daɗin
jikin ki" Shiru ta yi don zuwa yanzu ta kasa magana ma mamaki ya kashe mata jiki.

"To Abba" Ta ce don bata san mai za ta ce ba. Sallama suka yi ya kashe wayar tare da cewa
HEEDAYA gobe sai ta je. Da farin ciki ta koma ɗakin ta.


Aunty RABEEYA kuwa dakyar ta ƙirƙiri murmushin yaƙe wanda iyakar sa fatar baki, duk da ta
san HEEDAYA ƙanwar ta ce amma ta yi girma ta zo suna da sati uku da tarewa ba za su sake
ba idan tana nan amma sai ta danganta hakan da cewa HEEDAYA ce ta kasa jure rashin ta a
gidan shi ya sa har ta ɓullo da wannan batun.

MAMAN AFRAH
09013181851







[2/16, 7:55 PM] MOM MASHKUR & AFRAH:
https://chat.whatsapp.com/F7TUZezpOWLKYnyTNFuy2Y




BONONO

(RUFIN ƘOFA DA ƁARAWO)


NA


MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.


*SADAUKARWA*

Daga farko har ƙarshe sadaukarwa ne ga MARYAM SANI HAFIZ (Merry tah) Alkairin Allah ya
kai gare ki Allah lulluɓe rayuwar ki da tarin ni,imomi da albarkatu Allah raya mana Abdallah
fatan alkairi.

Daga marubuciyar:

Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Jalli joga
Da sauran su.
*09013181851*



PAGE 9


"Hayati mene ne?" Ya tambaya yana ranƙwafowa yana leƙen fuskarta da ya ga ta lunshe
ido da alamar kamar an faɗa mata wani abu da bai mata daɗi ba sai dai ya san ta da zurfin ciki
ba lallai ta bari ma ya fuskanci damuwar ta ba.

"HEEDAYA ce ta kasa jure rashi na shi ne ta cewa Abba za ta zo ta mana kwana biyu" Fuska
ya yamutsa cike da mamaki yana kallon idanun ta da har lokacin suke a rufe sai gashin idanun
da suke zare-zare sun rufe saman idanun.

"HEEDAYA ce za ta zo nan ta yi kwana biyu?"

"Eh" Ta faɗa cikin sanyin murya tare da tattaro jarumta a jikin ta ta tashi zaune tana ɗan kallon
cikin ƙwayar idanun sa ta sakar masa murmushin nan da yake tafiya da shi.

"Ko baka so ta zo?" Ta faɗa tana rausayar da kai tare da ɗan jujjuya idanun ta. Dimm ya ɗan yi
shi dai ya san RABEEYA da kunya iya su ma sai yana ɗan dagewa wajen ganin ta sake jiki da
shi saboda matsananciyar kunyar da take da ita duk da kunyar tata tana birge, shi amma kuma
dai ya san matsawar HEEDAYA za ta dawo ba lallai take iya nuna masa so da ƙauna haɗe da
kulawa ba saboda alkunya ga shi a iya ɗan zaman nan ya fara sabawa da kulawar ta ba ya iya
komai cikin nutsuwa matsawar bata kusa da shi sai yanzu ne ya gane rayuwar sa tana damfare
da tata ne sosai yake ƙaunar ta ita ma ya fahimci hakan a tattare da ita.

"Ina son ƴar uwata" Ta furta tana kallon sa, duk da ta ji babu daɗi a ranta ganin HEEDAYA idan
ta zo za ta ɗan kasa sakewa amma girman gidan ya isa su sake matsayin su na sabbin
ma'aurata sannan duk da Ya ABDUL ɗan uwa yake wajen ta kuma ta san ba zai hana
HEEDAYA zuwa ba amma ya zama wajibi a wajen ta ta nuna masa muhimmancin ƴan uwanta a
wajen ta don namiji ba a masa haka daga lokacin da ka nuna masa ƴan uwan ka basu da
muhimmanci daga lokacin zai fara tunanin wofintar da su gwara tun farko ka nuna masa kana
son ƴan uwanka.

"Ni ma ai ina son ta" Ya ce yana sakar mata murmushi haɗe da lakato dogon hancin ta. Sosai ta
faɗaɗa murmushin ta.

"Gadkiya na iya kiwo dubi hatta hancin ki ya ƙara tsawo" Ya faɗa yana ƴar dariyar zolaya. Ita ma
dariyar ta saki ta ce

"Kai kuma hatta bakin ka ya ƙara tsawo" Fuska ya cukuni cikin sigar wasa ya ce

"Wato ya yi tsawo kenan nan gaba irin na jaɓa zai zama"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login