Showing 39001 words to 42000 words out of 64514 words
Chapter 14 - BONONO BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MAMAN AFRAH f.pdf
zuwa wajen ku ne" Ta faɗa kamar za ta yi kuka. Kuma ta ce wajen su ne don
ita saboda shi ma ta je. Bai ƙara cewa uffan ba, ya kunna karatub qur'ani ya shiga bin karatun.
Sosai ta ji haushi har tana mamaki ta rasa gane kan Ya ABDUL a auren wata ɗayan da ya yi
gabaɗaya ya sauya matar sa kaɗai yake nunawa so da kulawa.
Yana tsayawa a ta buɗe ƙofar tare da buɗe bayan ta ɗauki jakar ta ko ta kansa bata bi ba ta
shige gidan. Shi ma bayan ta ya bi ya je ya gaishe da su Abba ya shiga gidan su ya fito ya
koma gidan sa don ba ya son yin nisa da matar sa ko kaɗan.
*BAYAN WATA BIYAR*
Yanzu gabaɗaya jikin Umma da na HEEDAYA kai har ma da na Hajiya Aisha ya yi sanyi, sun
sare da lamarin da boka ya ce HEEDAYA za ta auri Ya ABDUL domin kuwa sun ga babu niyya
wai ango ya kwana da wando. Saboda yanzu Aunty RABEEYA ciki ne da ita na tsawon wata
shida ga ta ƙara yin wani kyau ta yi ƙiba fatar ra tamkar ba a Nigeri'a suke rayuwa ba gabaɗaya
ta sauya kowa sai murma yake mata da aamun nagartaccen miji mai ƙaunar ta da nuna mata
kulawa. Umma da Hajiya Aisha har sum gaji da zuwa wajen boka amma sai ya ce musu akwai
dai lokaci su jira shi ba ya taɓa gano abin da ba zai faru ba. Ba ma wannan ne damuwar
HEEDAYA ba yadda Abba yake yawan tambayar ta wanda za ta fitar matsayin miji shi ne tashin
hankalin ta wannan ya sa take kula samari don kar a ga kamar ta rasa ne. Ga shi aminiyar ta
MEEMA har an yi bikin ta ita RAUDA duka ƙawayen ta ne da take ganin sai ta riga su aure
amma ga shi dai ta tsaya kallon ruwa kwaɗo ya mata ƙafa. Yanzu daga ita sai Ifteehal su ne dai
suka rage a cikin makusantan ƙawayen nata.
Ta gaji da jiran gawon shanu don ko gida Aunty RABEEYA ta zo ta tsani ta ga cikin jikin nan
nata tana jin baƙin ciki a ce ɗan jinin Ya ABDUL ne a jikin ta hakan ya sa ko ta zo gidan sai ta yi
wunin ɗaki ko dai ta kaucewa duk hanyar da za su haɗu watarana kuma ta tsiri fita unguwa,
bare ita dama yanzu bata ma sha'awar zuwa gidan ta tun da yanzu wanda take yi domin shi
hatta wayar ta sai ya ga dama yake ɗauka kwata-kwata ya sauya tamkar daj ya san abin da
yake zuciyar ta.
Kwanci tashi asarar mai rai Aunty RABEEYA ta shiga watan haihuwa, cikin ya tsufa ya mata
nauyi duk ta sauya kama ga wani kumburi da har an yi ta maganin an gaji sai aka ce ba zai
ware ba har sai da haihu. Gata sosai Ya ABDUL yake nuna mata tamkar dai ya ɗauke mata
cikin ya mayar jikin ta ga kaya sun saya kamar za a buɗe shago da yake shi da kansa ya mata
scanning a asibitin saya ga ƴa mace kwance a marar ta hakan ya sa siyayyar ta zo da sauƙi
don yana ganin sun san mai za a haifa. A wata ranar alhamis da safe naƙuda mai ƙarfi ta sarƙe
Aunty RABEEYA a kiɗime sula tafi asibitin Ya ABDUL duk ya bi ta ruɗe tamkar ya mayar da
ciwon jikin sa haka yake ji. Sai dai haihuwa ta ƙi daɗi gabaɗaya sai wuya take sha, ga shi ƴan
uwa da iyaye duk sun tare a asibitin. Dab da magriba ta samu ta haihu bayan ta sha baƙar
azaba, ana ta murna Ya ABDUL tamkar ya yi tsalle saboda farin ciki ji yake bai taɓa shiga farin
ciki mai tarin yawa ba kamar na yau musamman da ya ga babyn kamar ta ɗaya da maman ta.
Sai dai ana cikin murna da farin ciki sai murna ta koma ciki domin kuwa jini ne ya ɓallewa Aunty
RABEEYA an yj ta ƙoƙarin tsayar da shi sai dai abu ya ci tura don ana ƙara wani, wani yana fita.
Tuni hankalin kowa ya tashi musamman Ya ABDUL da ya fi kowa shiga tashin hankali
musamman da ya ga Aunty RABEEYA ta riƙe hannun sa cikin galabaita tana faɗin ya yafe mata
tare da bar masa wasiyyar kulawa da jaririyar da ta bari don gabaɗaya ta sare da mutuwa za ta
yi!.
Kuka kawai yake tamkar mace tamkar ba likita ba gabaɗaya ya fita hayyacin sa ganin hatta
magana ta gagare ta shi kuma ji yake tamkar dai idan har ajalin ne zai saukar mata gwara
mutuwa ta ɗauke su tare son har ya fara tunanin yadda zai rayu ba tare da RABEEYA ba a
wannan duniyar!.
HEEDAYA wacce da take jin tamkar ta yi wa Aunty RABEEYA addu'ar mutuwa wajen
haihuwa amma ganin halin da take ciki sai ta ji zuciyarta ta yi rauni ta ji tana tausaya mata kai
har ma ta ji da za ta warke da ta haƙura da aure mata miji sai dai kash! Abin da Allah ya rubutu
babu mai gogewa a wannan lokacin ne rai ya yi halin sa Aunty RABEEYA ta amsa kiran
mahalicci tana mai ambaton kalmar shahada dakyar don sai dai ka gane furucin bakin ta amma
ba a jin sauti ko kaɗan. Allahu akbar! Rai baƙon duniya.
Ya ABDUL sai da aka rirriƙe shi Abba da Daddy suna ta bashi baki amma ina!. Sunan ta
kawai yake ambato hatta su Abba sai da suka zubar masa da hawaye riƙe yake da jaririyar
yana ta kuka tamkar ƙaramin yaro, HEEDAYA ma tausayin masoyin ta da kuma rabuwa da
Auntyn ta mai ƙaunar ta tsakani da Allah ya sa ta fashe da kuka tare da rungume Ya ABDUL da
babyn suna kukan tare.
Kwanan keso ta yi ana ta nema mata gafara ga mahalicci kamar yadda annbin rahma S.A.W
ya ce a nemawa mamaci gafara. Da yake dama gidan Abba aka kai ta, bayan an shirya ta aka
sallace ta tare da tafiya da ita makwancin ta!. Ya ABDUL wanda Allah ya dasawa haƙurin danne
zuciyar sa bisa ga wannan babban rashin da ya yi shi ne wanda ya sanyata a kabarin ta.
*A gafarce ni da mutuwar Aunty RABEEYA haka labarin namu ya zo ne, sannan ita dama
mutuwa a har kullum tana zuwa ne ba tare da an shirya ba. Sai dai ftn Allah sa mu cika sa imani
ya mana kyakkyawan ƙarshe.*
MAMAN AFRAH
09013181851
[2/16, 7:55 PM] MOM MASHKUR & AFRAH:
https://chat.whatsapp.com/F7TUZezpOWLKYnyTNFuy2Y
BONONO
(RUFIN ƘOFA DA ƁARAWO)
NA
MAMAN AFRAH
First Class Writer's Asso.
*SADAUKARWA*
Daga farko har ƙarshe sadaukarwa ne ga MARYAM SANI HAFIZ (Merry tah) Alkairin Allah ya
kai gare ki Allah lulluɓe rayuwar ki da tarin ni,imomi da albarkatu Allah raya mana Abdallah
fatan alkairi.
Daga marubuciyar:
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Jalli joga
Da sauran su.
*09013181851*
PAGE 11
*MARYAMA*
Tunanin inda za ta nufa ta gujewa haɗuwa da mai muryar da ta ji yana jefo tambayar waye
a nan. Don a halin da take ciki yanzu kowa ma tsoron sa take tun da ita bata da kowa, amma
ina! Babu wata hanya da za ta bi ta fita sai inda ta shigo kuma ta nan ne take jin muryar mai
maganar yana nufowa, sannan matsawar ta motsa ta ce za ta koma wani ɗakin ta ɓuya to
tabbas zai iya cim mata don ya riga da ya zo dab.
Hasken fitilar da ya dalle mata idanu ne ya sa ta yi tsuru-tsuru tamkar an tsamo ɓera daga
ruwa.
"Wace ce ke? Kuma kukan mai kike?" Tambayar da ya guntso ya fesar mata ya sa gudun
numfashin ta ƙaruwa gabaɗaya ta ruɗe ta rasa bakin magana sai wani kukan da yake taso
mata, a ganin ta ta samu maɓoya amma ashe asirin ta zai tonu.
"Na ce wace ce ke?" Ko aljana ce ke?" Ya ƙara jefo mini tambayar a zafafe. Da sauri na shiga
girgiza kai ina cewa.
"Mutum ce ni wallahi ba aljana ba ce"
"Me kike a nan?"
"Tafiya nake dare ya mini shi ne na zauna kafin gari ya waye in cigaba da tafiya"
Bai ce komai ba ya shiga zagaya ta yana ƙara haske ta, tare da haske kayan nata.
"Shi ne baki zauna a cikin gari ba, ko kin shiga wani gida kin nemi alfarma kika zo dokar daji
cikin tsohon ginin nan da bashi da tsaro kika zauna bakya tsoron wani abu ya cutar da ke? Ko
bakya tsoron matsayin ki na mace wasu mazan su far miki?" Kai ta sunkuyar hawaye suna
zuba tun da ta tabbata maganar da yake yi ita babu wannan abin a ranta tun da ga shi ni cikin
wata baiwa ta samu ciki a jikin ta ba tare da namiji ya kusance ta ba to gudun mai za ta yi?.
"Daga ina kike?" Shiru ta yi tana tunanin faɗa masa daga inda nake a ganin ta ba abin da ya
shafe shi ba ne sannan daga ganin sa bai yi kama da mutumin ƙauye ba don sai yanzu ta lura
ma ashe ba fitila ba ce a hannun sa waya ce.
"Suna na HAFEEZ ni mutumin garin Dutse ne ina zaune da Kakata a can sannan ni ma'aikaci
ne a wannan asibitin na ƙauyan nan, wannan gidan shi ne wanda nake zaune a ciki, tun da kin
baro cikin gari ki zo ki shiga akwai ɗaki ki yarda da ni ba zan cutar da ke ba kuma ki saka a
ranki cewa Allah zai kare ki ko da na yi niyyar cutar da ke da safe sai ki tafi inda kika nufa"
Cewar HAFEEZ mutum mai tausayi haɗe da riƙo da addini mutum ne da ya tsani zina da kuma
duk wani aikin alfasha duk da kuwa bashi da aure. Idanu ta ɗaga ta shiga kallon fuskar sa ganin
ya haske mata fuskar tashi alamun ta gan shi. Baƙi ne ba sosai ba irin baƙin kyau nan, dogo ne
sosai yana da ɗan jiki don ba za a kira shi rammamme ba yana da faɗin ƙirji duguwar fuska da
dogon hanci haɗe da kwantaccen gashin kansa da yake kwance luf kamar na mutanen ƙasar
indiya, sajen sa da ake kira da kwata million ya ƙara ƙawata fuskar. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta
sauke amma har cikin ranta sai ta ji hankalin ta ya kwanta da shi har zuciyar ta take ji ba zai
cutar da ita ba!.
Ba tare da ta yi magana ba ta ɗauki kayan nata ta rungume, murmushi ya saki ganin kamar
dai bata saki jiki da shi ba ya rasa ma daga ina take yanayin ta ya nuna masa tamkar tana cikin
matsananciyar damuwa amma bata son ta faɗa. A gaba yake tana bin sa a baya har suka
ƙarasa gidan ya buɗe ƙofar ya shiga hasken sola da ya haske gidan sannan gidan share ƙal
kamar akwai mace a ciki ginin siminti ne tamkar ba a ƙauye da dama haka ake idan an gina
asibiti sai a gina gidan ma'aikatan a gidan. Ciki da falo ne sai wasu ɗakunan guda uku a jere sai
bayi da kuma kicin.
Ɗakin da ya nuna mata ta shiga ta zauna babu komai sai ƙaramar katifa. Da sallama ya shiga
ɗakin.
"Akwai abin da kike buƙata?"
"Ina so zan yi sallah" Shiru ya yi yana bin ta da kallo yanayin ta babu nutsuwa akwai alamar
damuwa, sannan kana ganinta ka san tana jin yunwa amma kuma sai ta ce sallah, ta birge shi
sosai kasancewar yana lura da wasu matan ƙauye basu damu da sallah ba sannan ma ya lura
ita kamar ba ƴar ƙauye ba amma suturar jikin ta ta yamushe da yawa.
"Ga banɗaki can a waje akwai ruwa" Yana faɗar hakan ya juya ya fita. Fitowa ta yi ta shiga
banɗakin wanke yake ƙal sai ƙamshi ma yake tsarki ta yi ta yi alwala ta fito tana komawa ta ga
sallaya a ajiye da alama shi ya kai mata sallolin ta jero ta gama ta zauna tana ta jerowa Baffan
ta addu'ar samun gafara ta gama ta shafa sai bata cire hannuwan daga fuskarta ba ta bari a
haka hawayen tunanin Baffan ta yana zubowa tana ji a ranta bata san ranar da za ta daina
kukan rashin sa ba gaskiya mutuwar Baffa tabo ne a zuciyar ta wanda ba zai taɓa kankaruwa
ba har abada!.
Da sallama ya shiga bayan ta amsa, plate ya shigo da shi a rufe ya ajiye da cibi (Fork) A kan
plate ɗin ya ce
"Ki ci abinci"
"Na ƙoshi" Da kallo ya bi ta sai lokacin ya lura da lema a fuskar ta kuma idanun jawur da alama
kuka ta sake yi. Shiru ya yi yana nazarin ta sai ya ce
"Amma akwai yunwa a tare da ke ba zan cutar da ke ba, wallahi ban zuba komai a ciki ba,
indomie ne na dafa miki"
"Ba zan iya ci ba"
"Baki isa ba ni babu wanda ya isa in ɓata lokaci na in girka abu saboda shi ya ce ba zai ci ba"
Ya faɗa cikin faɗa-faɗa don ya lura akwai yunwar a jikin ta cin ne kawai ba za ta yi ba. Yana
gama faɗar haka ya zauna tare da buɗe plate ɗin ya ɗora fork ɗin a kan indomien da take ta
turiri ta sha attaruhu da albasa.
"Ɗauki ki ci" Ya ce cikin bada umarni muryar sa babu alamun wasa. Gabaɗaya yadda ya yi
maganar sai ya bata tsoro duk sai ta ruɗe ta ma rasa mai za ta yi.
"Ki ɗauka ki ci na ce" Hannun ta har karkarwa yake ta ɗau fork ɗin ta ɗauki indomie ɗin ta nufi
bakin ta sai dai tuno da Baffan ta sai kawai ta rushe da kuka. Jikin sa ne ya yi sanyi ganin tana
kuka ko abincin bata kai baki ba.
"Mene ne damuwar ki?"
"Baffana ne ya mutu jiya da dare" Da mamaki yake kallon ta.
"Yanzu ina Baffan naki?"
"An binne shi da safe"
Shiru ne ya ratsa ɗakin sai shashshekar kukan ta ne kawai don tambayar ta da ya yi ina Baffan
sai ta ji an tada mata mikin mutuwar.
"Ki yi haƙuri Allah ya jiƙan sa mu ma zaman jiranta muke yi" Ya faɗi hakan amma zuciyar sa
cike take da tarin tambayoyi sai dai ya ja bakin sa saboda ya ga bata da aiki sai kuka sai yanzu
ya san mene ne damuwar ta, kuma ba zai matsa mata da cewa sai ta ci ba don ya san ciwon
mutuwa tun da shi daga uwa har uban nasa basa raye duk da ba shi da wayo sosai suka mutu
amma tabbas!. Ya san mutuwa tana da ciwo.
Fita ya yi jim kaɗan sai ga shi da shayi mai kauri a kofi, matsa mata ya yi sai da ta shanye tas.
Bai ƙara bi ta kanta ba ko da ya je masallaci sallar isha ya dawo rufe gidan ya yi ya wuce ɗakin
sa ya kwanta. MARAYAMA kuwa haka ta kwana ido biyu ga damuwar rashin Baffa ga damuwar
inda za ta dosa daga nan goben sai kawai ta kwana tana nafila da addu'o,i a kan Allah kawo
mata ɗauki cikin lamuran ta.
Da safe ma shayin ya haɗa ya kai mata duk da yana jin motsin ta da asuba da alama alwala
ta yi, ya yaba da riƙon addinin yarinyar sosai. Ko da ya shiga ɗakin ma samun ta ya yi tana
zaune ta yi nisa a tunani ganin sa cikin sanyin murya ta ce
"Yaya HAFEEZ ina kwana" Sai da ya lumshe idanun sa kafin ya amsa ya ji daɗin kiran sa da
Yaya da ta yi, saboda shi bashi da ƙanwa bashi da Yaya shi kaɗai iyayen sa suka haifa.
"Lafiya lau" Ya amsa cike da murmushi.
Bayan ya fita ta shanye ganin gari ya yi haske jim kaɗan sai ta fito da kayanta a riƙe ta tsaya
daga bakin barandar tana cewa.
"Zan tafi" Amma ta ji shiru ta maimaita ya fi sau biyar amma babu amsa da niyyar ta ta masa
godiya amma ganin shirun ya yi yawa sai ta juya ta tafi, a bakin ƙofa suka yi kiciɓis da shi riƙe
da leda a hannun sa. Da mamaki yake kallon ta.
"Ina za ki je?"
"Zan cigaba da tafiya"
"Zuwa ina?"
"Ni ma ban sani ba"
"Juya ki koma ciki" Sororo ta yi tana kallon sa ta san dai wajen kwana ya bata amma kuma yana
mata umarnin ta koma