Showing 63001 words to 64514 words out of 64514 words

Chapter 22 - BONONO BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MAMAN AFRAH f.pdf

30 Mar 2025

5107

mara rashin kunya
wai ai da ita Ya ABDUL yake shawara amma saboda ta tsane ta bata bashi shawarar kar ya
mata kishiya ba ita kuwa ta ɗauki ƴar ta Ikram da Little RABEE suka koma gida.

Zuwan Ihsan da Mubashshar tare da Na'eema ya yi daidai da shigowar motocin kawo
amarya. Guɗa ce take tashi haɗe da bugun ƙirjin HEEDAYA. An wuce da amarta part ɗin ta da
take a lulluɓe.

"Aunty HEEDAYA wallahi duk ƴan gayu ne baki gan su ba farare da su, amaryar tana lulluɓe da
mayafi baki ga yadda aka mata ƙunshi mai bala'in k...

"Ya ishe ki Ihsan in zuzuta kyan kishiyata ne ya kawo ki ki ɗauki ƙafafun ki ki tafi" HEEDAYA ta
faɗa a harzuƙe don kuwa ta cika fam. Sai wajen takwas da wani abu RAUDA ta tafj su kuma su
Ihsan sai da tara ma ta gota.

Zaune take dirshan a ƙasan ɗakin tarasa mai yake mata daɗi. Ƙofar aka turo jikin ta ya bata
shi ne. A fusace ta ɗago jin ƙamshin turaren sa ya gama haɗe ɗakin. Farar shadda ce a jikin sa
an mata aikin baƙi sai farar hula mai ratsin baƙi. Fuskar sa a washe kamar gonar auduga.

"Uwar gida ran gida, uwar gida sarautar mata" Ya faɗa cike da daɗin baki bata tamka masa ba
don tana buɗe bakin ta wataƙila zagi ne zai fito.

"Ni zan tafi sai da safe" Ya ce yana ajiye mata leda ɗaya da yake ledoji biyu ne a hannun nasa.
Yana fita ta yi cilli da ledar kaza da lemukan, takaici yana cika ta ganin ita a nata ranar amarcin
ko tattabara bai kawo ba amma yau za ta ci albarkacin kishiya!?.

Yadda ta ga safiya haka ta ga dare kuka kuwa har ta yi ta ƙoshi sai dai tana ta ƙudurtar sabon
shiri don kuwa sai amaryar nan ta fita da ƙafafun ta don Ya ABDUL nata ne ita kaɗai.


Amarya da ango an yi kwanan farin ciki cike da farantawa juna, sun yi matuƙar murnar
kasancewa da juna. Misalin ƙarfe tara suka sakko daga saman benen hannun su sarƙe da juna
sanye suke da shadda baƙa sun yi anko kasancewar su farare sai ta mugun karɓi kikin su.
Amarya kyakkyawa mai zubi da tsari na halitta ta sha ɗaurin ɗankwali gashin kanta da ta tufke
jelar har har gadon bayan ta. Riƙe yake da ƙungunta bayan hannun nasa ɗaya yana sarƙe cikin
nasa ji suke ba ya su a fagen masoya. HEEDAYA wacce baƙin kishi ya hana ta sakat ta baro
part ɗin ta ta nufi part ɗin Ya ABDUL tun da yanzu ya koma nasa ya bar saman da yake a part
ɗin ta. Zuciya da take ta mata saƙe saƙe ce a kan wai har tare bai fito ba sun raina mata
hankali. Babu zato suka ga an banko ƙofar wacce Ya ABDUL da ya dawo daga masallacin
asuba bai kulle ba. Da yake sun bata baya da ta shigo sai ta yi mutuwar rsaye ganin su sarƙe
da hannu sannan yana maƙale da ƙugunta sai wani ƙamshin turarukan su mai sanyin ƙamshi da
ya cika falon.


Wayar ta da take hannun ta wacce take ta faman kiran HUSNA tun jiya bata shiga, tana dab
da shiga falon ta danna kiran HUSNA ashe dai kiran ya tafi kuma wayar tana ringin. Hakan ya yi
daidai da fara ƙaran wata waya da take kan kujera can wajen da suke tsaye. Ya ABDUL ɗin ne
kaɗai ya juyo fuskar sa ɗauke da murmushi. Ita kuma amarya bata juyo ba sai ta ƙarasa gaban
kujera ta ɗauko wayar da take ƙara, lokacin kiran ya katse sannan da ta juyo ta taho bayan
angon ya mata shamaki da ganin uwar gidan nata wacce bata taɓa gani ido da ido a sai a yau
take sa ran ganin ta. Tana dab da ƙarasowa Ya ABDUL ya ɗan kauce sai kuwa amarya da
idanun ta suke kan fuskar HEEDAYA da ta yi mutuwar tsaye riƙe da waya idanun ta suna kallon
ƙasa da alama dai ganin su ya daki zuciyar ta kishi ya motsa. Taku ɗaya biyu amarya ta yi ta
ɗaga hannunta ta ɗora a kafaɗar HEEDAYA da sauri HEEDAYA ta ɗago tana son ganin shin Ya
ABDUL dafa ta ɗin da ya yi mai zai ce mata har yana da bakin magana? Amma sai ta samu
saɓanin tunanin ta a kan fuskar da idanun ta ya sauka ta kusa samun taɓin hankali tsabar ruɗun
da ya ziyarci ƙwƙwalwar ta. Sai dai tunanin ta ya ƙi tsayuwa wuri ɗaya saboda ta lura akwai

bambanci da fuskar da take zato sai dai kama ɗaya tamkar an tsaga kara wannan ta fi waccan
haske kuma waccan tana da faɗin fuska sannan wannan fuskar ta doguwa ce.

"HEEDAYA!!!. Ki daina wahalar da kan ki wajen kirana a waya domin kuwa ga ni na dawo kusa
da ke, kin ga wayar da kike kira a hannuna suna na HUSNA aminiyar ki ta online, ina so ki sani
mu biyu iyayen mu suka haifa wato ƴan biyu kuma, ni ce Hassana ake kirana da HUSNA ita
kuma Husaina. Da ni kike chatting da ni kike waya da ni kike komai amma ba ni kika gani ba
ranar da kika ziyarce ni gidan ƙanwata Husaina kika je kuma da ita kuka haɗu ba da ni ba"
Bakin HEEDAYA tamkar ƙofar gari haka yake a buɗe saboda mamakin da aka kashe ta da shi
wanda tana tunanin tun da ta zo duniya ba a taɓa bata mamaki irin na yau ba.

Amarya taku ɗaya biyu ta yi ta ce

"Na kamu da son mijin ki ne tun lokacin da kike baje sirrin ki a faranti, kike kwashe komai kina
faɗa mini, kin san zuciya bata da ƙashi sai na ji ina ma ni ce Allah ya ba ni'imar nan kullum cikin
faɗa mini sirrin ki kike wanda ya dace da wanda bai kamata a ce kina faɗa ba har son da nake
yi wa mijin ki ya linku bila adadin sai dai kash auren wani a kaina ya hana ni aiwatar da komai.
Kwatsam wata rana na kama HAMEED ya kawo mini mace gida lokacin na tafi Kano ganin gida
da yake mu ƴan asalin Kano ne to Husaina ta a Kano take aure ni kuma a Abuja. Ban sanar da
shi dawowata ba da yake sai bayan na tafi ya zo Abujar sai a ranar na gane ashe manemin
mata ne buƙatar sa yake biya a waje da matan banza shi ya sa yake hana ni nawa haƙƙin. A
ranar na nemi saki da yake ba damuwa ya yi da ni ba a take ya sawwaƙe mini. A haka har na
gama idda ke kuma kina nan kina baje mini sirrin ki wanda yake ƙara mini kwaɗayin son auren
miji mai nagarta kamar ABDULHAKEEM. Kwasam kika ga na ɗora tallar wasu takalma na wata
ƙawata a status kika ce kina so kika yi oder lambar da za ta karɓi kayan naki sai kika turo mini
lambar mijin ki a nan na samu tsuntsu daga sama gasasshe.



Husaina ta da ita muke shirya komai don ganin na cika burina. Ashe dai faɗuwa ce ta zo
daidai da zama shi ma kina bashi labarina ta haka ya kamu da sona ba tare da ya sanar miki
ba. Ko da na kira shi na sanar da shi wace ce ni da ƙudurina na sanar da shi labarina sai ya
amince da ni tare da nuna mini dama yana jin labarina a wajen ki daga nan muka ƙulla soyayya
wacce ta kai mu ga aure kin ga yanzu sai mu ƙara ɗamarar zama aminan juna tun da gamu a
ƙarƙashin inuwa ɗaya " Ta kai ƙarshen maganar tana kallon HEEDAYA da ta yi mutuwar tsaye
hawayen nadama da da na sani suna zirya a kumatun ta.


'HUSNA, HUSNA, HUSNA kenan shuka nake a idon makwarwa? Ina kiwon ɗan damisa a
matsayin mage? Ina ta famkamar kishi ina hangen kar wasu su shigo ashe dai na yi BONONO
RUFIN ƘOFA DA ƁARAWO? ' HEEDAYA ta faɗi hakan a zuciyar ta ta ma kasa haɗa kalmomin
da za ta yi magana da su wajen wannan gagarumar cin amanar da mijin ta da kuma wacce ta
ɗauka aminiya suka mata!!!.

*LAST FREE PAGES MAI SON JIN YADDA ZA TA KAYA ZAI BIYA 500 A SAKA SHI A
GROUP DON YA ƘARANTA HAR ƘARSHE IDAN NA KAMMALA CMPLT DOCMENT 700. ZA A
BIYA TA ASUSUN FAIZA ABUBAKAR 9030283375 Opay ko FAIZA ABUBAKAR 9013181851
Palmpay shaidar biya ta 09013181851* K *ULLUM PAGE 2 IN SHA ALLAH KAFIN AZUMI ZA
MU KAMMALA*


*SHIN MENE NE A CIKIN MARYAMA? SANNAN KUMA YA ZAMA ZAI KASANCE TSAKANIN
UWAR GIDA HEEDAYA DA AMARYA HUSNA? KI BIYA KI KARANTA HANKALI KWANCE*

MAMAN AFRAH
09013181851

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login