Showing 48001 words to 51000 words out of 64514 words

Chapter 17 - BONONO BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MAMAN AFRAH f.pdf

30 Mar 2025

5101

zai aura sai HEEDAYA , sosai take jin takaicin hakan don har
maganganu Umma take yada mata, shi ya sa yanzu ko ganin Little RABEEYA ya zo sai ta ga
dama take barin sa ya ganta wataran ma sai ta ce maaa bacci take ta hana shi ganin ta haka
zai gaji ya tafi.

Ko da ya gaishe da Umma faram-faram ta amsa daɗi duk ya cika mata zuciya ganin Momma
tana ta muzurai. Yaran ne suka shiga gaishe da shi ya amsa ya samu waje ya zauna.


Gyaran murya Abba ya yi ya fara magana.


"Abin da ya sa na tara ku a nan ba komai ba ne sai magana a kan RABEEYA ƙarama, wato
ABDULHAKEEM ya same ni a kan cewa idan ya yi aure za ta koma hannun sa da zama"
Ƙirajen mutum uku ne suka buga da sautin diririmdimmmmm. Ƙirjin Momma wacce ta ci
alwashin azabtar da Ya ABDUL ta dalilin yarinyar don yanzu ta saka a ranta sai ta ringa zuwar
masa da buƙatun kuɗi don take tatiƙe shi sannan take azabtar da shi ta hanyar hana shi ganin
yarinyar don ta ɗaga mas hankali ta hana shi kwanciyar hankali don kishi take taya ƴarta duk da
bata raye. Sai kuma ƙirjin Umma uwar amarya jin wai za a ɗauki yarinya a kai gidan ƴarta kenan
waye zai reni yarinyar da ko zama bata yi? HEEDAYA za a kaiwa wahalar ko wa?. Sai kuma
ƙirjin mai gayya mai aiki HEEDAYA da ta ji tamkar ana dakan sakwara a ƙirjin nata jin wai za a
mayar da ita ƴar raino ita da ta ci burin zuwa ta miƙe ƙafa ta huta amma ake wani batu.


"Haba Alhaji yarinyar da bata gama warewa ba, a barta mana a nan in ma zuwa gidan uban
nata ne sai take zuwa bayan ta girma take zuwa da yawo" Momma ta faɗa.

"Kin san dai in na yi magana babu mai warware mini, ko ƴarki ce? To mai ƴar ne ya buƙaci haka
kuma babu sauyi duk ranar da ya buƙaci karɓar ƴarsa bayan ya yi auren zai iya zuwa ya ɗauke
ta ni dai na sanar da ku na fita haƙƙi shi ya sa na kirawo shi don ku ji daga bakin sa" Abba ya
faɗa cikin faɗa.

"ABDULHAKEEM idan ka yi aure duk ranar da ka ji ta raya maka ka zo ka ɗauki ƴarka ka tafi da
ita" Abba ya ce yana masa umarnin ya tashi ya tafi. Fita ya yi ya tafi.


"Bayan shekara biyar amma?" Umma ma da ta kasa haƙuri ta tambaya.


"In ma bayan shekara ɗaya ne ruwan sa ne wannan, ni dai na sanar ne don ku kwana da sanin
hakan watarana ku tashi na sallami kowa" Da wannan aka watse ran kowa yana suya.


"Umma kin ji wani sabon tashin hankalin kuma ko? Wai mai ya sa komai idan za a yi sai an
samu gargada ne ?" HEEDAYA ta tambaya ranta a ɓace don bata taɓa kawowa haka za ta faru

ba.


"Kayya HEEDAYA ni ma abin ya ɗaure mini kai amma ai tun da bayan shekaru ne ba ma nuna
zalamar mu a fili ba kin ga sannan ma yarinyar ra zama ta dara moruwa ba sai ta zama ƴar aike
da aikin ki ba" Umma ta ce tana dafa ta. Shiru ta yi sai kuma ta murmusa amma dai duk da
haka ba hakan aka so ba ƙanin miji ya fi miji kyau!.

Duk da haka sai da su Umma suka ziyarci boka amma ya tabbatar musu da cewa babu ruwan
su game da ƴarsa don son ƴar a cikin jini da tsokarsa yake ba za a iya raba shi da son ba haka
ma matarsa da ta mutu ba za a iya hana shi tunanin ta ba tun da dai auren ne muradin su kuma
an yi to su yi haƙuri da wannan. Haka dai suka dawo jiki babu ƙwari sai dai sun lallashi
HEEDAYA a kan cewa ta haƙuran tun da kafin ma yarinyar ta koma wataƙila ita ma ta haifi nata
yaran tun da ba sanin ranar komawar aka yi ba, tun da sai an ɗauki shekaru an dai sanar ne
don su sani ko ba daɗe riƙo ƴa zai koma gidan ubanta.



Hanzari ba gudu ba Abba ya taka birkin duk wani shirye-shirye na auren domin kuwa ya ce
ko walima ba za a yi ba aure za a ɗaura a samu mutum biyu zuwa uku su rakara ɗakin ta!. Abin
nan ya ƙonawa HEEDAYA da Umma rai sun so su raƙashe amma babu hali.

Hanya HEEDAYA ta sata ta tafi ƙunshi na gani na faɗa, aka mata saloon tare da ƙananan kitso
aka yaryara mata. Maganin mata tamkar zai yi magana haka aa dirka mata ban da maganin
matsi duk da tana budurwa amma wai gwara ya jita zam-zam ya san da bambanci da tsakanin
ta da matar sa marigayiya, don Umma ta faɗa mata cewa matsawar namiji ya taɓa aure to sai
mace ta zage dantse wajen gyara don kar ya ji matarsa ta fi ta komai.


A yau aka ɗaura aure tsakanin HEEDAYA Bashir da ABDULHAKEEM Mukhtar, Umma an ci
leshi wanda suka yi anko ita da Hajiya Aisha da Ihsan da kuma amarya amma ban da Aunty
Hafsa don basu ma faɗa mata ba bare ta saya. Da daddare amarya ta ci gayun ta bayan ta yi
wanka, ranta fari ƙal yau za su angwance da ango. Momma, da wasu mata biyu su ne masu
rakiyar amarya, su Abba da Daddy suka umarta a ka ɗauki mota biyu suka tafi kai amarya Hajja
tana ta sanya albarka. Ran Ammie da Momma baƙiƙƙirin don komai an kwashe na Aunty
RABEEYA an jera sabo na HEEDAYA.



Zaune take a tsakiyar gadon ta, tana ta murmusawa ita kaɗai ta daɗe a rayuwar ta bata
shiga farin ciki makamancin wannan ba, ji take tamkar an mara albishir da aljanna. Tabbas ta ci
alwashin yau za ta mantar da Ya ABDUL tunanin tsohuwar matarsa da ta daɗe a kushewa!.

Wacce ya kasa daina tunanin ta, yau za ta nuna masa tsantsar so da wayewa a yau take so ta
tanadi filin da za ta fara ginin tubalin soyayyar ta a zuciyar sa.


Lulluɓe take da mayafin ta da yake ta fitar da sassanyan ƙamshin turaruka masu tsada da daɗin
ƙamshi. Ƙaran buɗewar get ta ji wanda ya sa ta ji wani sanyi a ruhinta don ta tabbatar masoyin
ta ya ƙaraso. Jim kaɗan ta ji ƙaran buɗe ƙofar babban falon, sai kuma ta ji an turo ƙofar ɗakin
da take ciki, bakinsa ɗauke da sallama cikin muryar sa da take mata daɗin sauraro, idanu ta
lumshe tare da saisaita muryar ta ta mata lanƙwasa ta amsa sallamar tana jin wata ƙaunarsa na
fisgarta. Babu zato babu tsammani ta ji wani abu da ya so hargitsa ƙwaƙwalwar ta, wato kukan
yarinya ƙarama. Da sauri ta yaye mayafin da ya mata shamaki da ganin komai duk da bashi da
wani kauri amma ta fi so ta ga wannan abin mamakin da yake shirin faruwa.


Zaton da ta yi ne ya zama gaskiya domin kuwa tabbas Little RABEEYA ce shimfiɗe a kafaɗar
Ya ABDUL yana jijjigata.


"Yi shiru kin ji my Little RABEE " Ya ce yana ajiye wata ƙaramar akwati wacce ba sai an
tambaya ba kayan yarinyar ne a ciki don da ɗaya hannun yake jijjigata ɗaya kuma yana riƙe da
akwatin. Haushi, baƙin ciki haɗe da mummunan takaici ne lokaci guda suka daki zuciyar
HEEDAYA.


Ranar da ta ci buri iya rayuwar ta? Rana ɗaya tamkar da dubu a wajen ta? Ranar amarcin ta?
Ranar da ta so shayar da mijin ta ruwan ƙauna? Ranar da take so ta bayyana masa irin nisa da
nutson da ta yi a bege da ƙaunar sa. Amma ya taho mata da yarinya, dama dawowar yarinyar
ba sai bayan shekaru ba ne? Dama a ranar yau ne ranar tariyar ta za su tare tare da yarinyar,
yarinyar nan mai shegen kukan dare zai ɗakko ya kawo mata mai za ta yi a yau ɗin raino ko
amarci?


Ango kuwa ko a kwalar rigar sa bai ma lura da yanayin firgicin da amarya HEEDAYA take ciki
ba, gadon ya ƙarasa ya kwanta tare da ɗora Little ɗin a saman ƙirjinsa yana jijjigata yana
lallashin ta. Baki sake HEEDAYA take kallon sa wato bai ma san abin da ya mata ba bai gane
ya ci mutuncin ranar amarcin ta ba shi ta ƴarsa ma yake wato tana ganin Aunty RABEEYA ta
mutu ashe dai ga wata RABEEYAR za ta hana ta rawar hantsi tana ganin ta kashe miciji ashe
dai bata sare kansa ba lallai akwai badaƙala!!!.



*SAURAN SHAFUKA KAƊAN NA GAMA FREE PAGES DUK MAI SON KARANTA BONONO

HAR ƘARSHE ZAI BIYA 500 DON IN SAKA SHI A GROUP IDAN KUMA NA GAMA CMPLT
DOCMENT 700 ne. WANDA YAKE BUƘATA ZAI IYA BIYA TUN YANZU KO SAI AN KAMMALA
FREE NE MA TO GA DAI ACC ƊIN DA ZA A TURA FAIZA ABUBAKAR 9030283375 OPAY SAI
A TURA MINI SHAIDAR BIYA TA 09013181851*
MAMAN AFRAH
09013181851
[2/19, 5:22 PM] MOM MASHKUR & AFRAH:
https://chat.whatsapp.com/BxScHoTf7PzDHEWZgZCnnf

BONONO


(RUFIN ƘOFA DA ƁARAWO)


NA


MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.


*SADAUKARWA*

Daga farko har ƙarshe sadaukarwa ne ga MARYAM SANI HAFIZ (Merry tah) Alkairin Allah ya
kai gare ki Allah lulluɓe rayuwar ki da tarin ni,imomi da albarkatu Allah raya mana Abdallah
fatan alkairi.

Daga marubuciyar:

Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Jalli joga
Da sauran su.
*09013181851*

PAGE 13


*HEEDAYA*

"Ya ABDUL ya na ganka da Little RABEEYA?" HEEDAYA da ta sha yaƙi da zuciyar ta ganin ta
danne zugin da zuciyar ta take mata da azalzalar ta ta faɗa tamkar ta sake kuka don a halin
yanzu marar ta ma ciwo take mata saboda ɗimbin magungunan da ta bankama tsabar son ta
burge shi kowanne magani over dose ta yi.
"Na kasa haƙuri in taho in bar ta ne, kin san a cikin gidan nan da Hayatiy na fara rayuwa sannan
daga lokacin da ta bar duniya ban ƙara sha'awar zaman gidan ba shi ya sa yanzu ma da zan
dawo na taho da Little hakan zai rage mini kewar mahaifiyar ta, kin san komai nake yi a
rayuwata da tunanin Hayatiy nake yi haƙiƙa a zahiri ta mutu amma a baɗini ina jin ta tamkar
bata mutu ba don ni da so da ƙaunar ta nake rayuwa kuma da shi zan mutu" Ya kai ƙarshen
maganar hannunsa biyu suna dafe da bayan Little idanun sa kuma suna kafe da silin. Sororo ta
yi tana kallon sa tare da mamakin kalaman sa sai da ya yi maganar nan ne ta gane kenan ita
bosho ce kenan bata ma da wani amfani tun da da son marigayiyar mayar sa yake rayuwa sai
dai ya maje bata bari ya gane ba don dole sai ta fara koyawa kanta kissa wajen zaman gidan
nan don ta lura abin na Ya ABDUL ba na ƙare ba ne.


"Allah jiƙan Aunty RABEEYA ya sa ta huta" Ta ce cikin sanyin murya don ta san vata da mafita
sai faɗar hakan tun da hatta boka ma ya ce ba za a iya cirr masa so da tunanin su ba kuma
dama bokan ne ƙarfin dum wani sheɗanci nasu.

Har ƙarfe sha biyu idanun su biyu ana fama da Little ta ƙi kwanciya daga ya tarki ajiye ta sai ta
tsanyara kuka. HEEDAYA kamar ta kwaɗawa yarinyar mari haka take ji amma ta ba kanta
haƙuri.

"Buɗe jakar ta akwai madarar ta ki je kicin ki ɗora ruwan ɗumi ki haɗa mata" Ya faɗa ba tare da
ya kalli inda take ba abin takaicin a matsayin ta na sabuwar amarya ko kallon soyayya bata
samu daga ango ba kai idan ba ƙarya idanun ta suka mata ba sai ta ga tun da ya shigo ma bai
kalle ta ba. Jin aikin da ya saka ta, tamkar ta rusa ihu ita da take amarya za a lallaɓa ta a buɗe
mata mayafi ya lallashe ta ta yi shagwaɓar ta son ranta amma ta ƙare a shiga kicin ango ya
ƙare a reno? Da to ta amsa ta ɗauki madarar har da fida a ciki ta fita bayan ta ɗauki wayar ta da
yake gidan ba baƙon ta ba ne haka ta nufi kicin ɗin cike da takaici.

"Umma" Ta ce tare da rushewa da kuka bayan Umma ta ɗaga wayar.

"Haba HEEDAYA na kira ki ya fi sau goma amma baki ɗauka ba" Umma ta faɗa tana sauraron
ta.

"Wayar ce a silent kin san ina zaune kan gado a lulluɓe ina jiran dawowar sa ya buɗe ni irin na
amare masu gata amma shi ne...

"Wai gidan uban wa ya kai wannnan marainiyar ƴar tasa?" Umma ta katse ta don ba ita ce
maganar da take son ji ba.

"Gidan nan mana Umma har yanzu ko yarda bata yi ya ajiye ta ba, yanzu ma kin ganni a kicin
wai in dafa ruwan zafi in haɗa mata madara"

"Sha biyun daren ne kike a kicin? Ni ma ina nan na fara jiyo hayaniya ashe wai ɗaukan ƴar ya
zo ita kuma Hajiya Baturiya ta hana shi ita wai sai ta girma shi ne fa Alhaji ya ce ko ta haɗo
kayan da yarinyar ta ba ABDULHAKEEM ɗin ko kuma ta fuskanci tsatstsauran hukunci daga
gare sh, babu shiri ta ɗauko ta bashi tana kukan rabuwa danyarinyar, ai wallahi
ABDULHAKEEM ɗin na an yi shegen yaro ni na fi tunanin ma uwar sa ce ta zuga shi don a kai
miki reno a hana ki sakat'

"Cewa ya yi wai saboda ba zai iya zama a gidan da babi Aunty RABEEYA ba shi ne ya taho da
it...

"Rabu fa shege gulmamme in ma uwar tasa ce ta saka shi ai ba zai faɗi gaskiya ba raba kan ki
da na miji wani munafuki ne ya fi wasu matan ma munfurci"

"HEEDAYA, HEEDAYA" Ta jiyo yana rafka mata kira, ga daga kicin ɗin ma tana jiyo kukan
yarinyar haushin kiran sunan ta da ya yi ya tokare mata zuciya wato ita ɗan sunan soyayyar ma
ba za ta samu a kira ta ba.

"Umma sai da safe yana kira na"

"To HEEDAYA Allah ɗora ki a kan yarinyar nan ta yarda ya ajiye ta in ba haka ba ɗan amarcin
nan ma na daren farko sai dai kike jin labari wajen ƙawaye" Umma ta ce tana yanke kiran dama
takaicin ɗaukan yarinyar da ABDUL ɗin ya yi shi ya hana ta bacci take zaune tana tunani.

Jin abin da Umma ta ce ya ƙara ɓatawa HEEDAYA rai don ta faɗawa su MEEMA ita yau sai
kwanan amarci ita da yake MEEMA ta yi auren ita da RAUDA sai suke ta mata dariya suna
cewa za ta sha amarci ashe dai ita raino za ta sha don babu alamar za ta adar da wani abin
arziƙi, wannan shi ne karin maganar da bahaushe yake cewa babu niyya ango ya kwana da
wando.


Madarar ta kai masa ta tarar shi tsaye yana zagaya ɗakin tana kafaɗar sa sai lallashin ta yake
har da ƴat waƙa yake mata, shi da alama ma cikin nishaɗi yake wannan ya ƙara ƙona mata rai.

"Yawwa my Little RABEE za ki sha madara ai ko uhm yarinyar kirki mai kama da maman ta" Ya
ce yana zaunawa bakin gado ya ɗora ta cinya tare da karɓar fidar sai da ya kara a gefen
fuskarsa don ya ji ko da zafi sai ya ji za ta iya sha, wannan ya ƙara ɓatawa HEEDAYA rai wato
yana ganin ma za ta iya kawo mai zafin da zai ƙonawa yarinyar baki.
"Za ta sha mana yarinyar kirki ce ai" HEEDAYA ta ce tana ƴar dariyar yaƙe a fakaice kuma tana
aika musu harara. Yarinya ta zuƙe madara tas ta saki gyatsa amma ta daina kuka sai wasa da
take tana ta ɓangalawa uban dariya shi kuma sai farin ciki yake yana dariya tamkar yana
magana da sa'an sa haka yake mata magana ita HEEDAYA rabon ma ta ga yana dariya haka
tun kan Aunty RABEEYA ta rasu.



Haka nan suke zaune HEEDAYA tun tana doguwar hamma har ta gyanyaɗi ya fara ɗiban ta
bata san ta ɓingire bacci ba sai wajen ƙarfe huɗu saura ta tashi ta gan shi rungume da ƴarsa
suna bacci. Takaici duk ya ishe ta wato ƴar ta yi bacci maimakon ya tashe ta matsayin ta na
amarya shi ya kwanta bacci abin sa ita sai yanzu ma ta tuna cewa ana kawowa amarya kaza da
kayan maƙulashe amma shi daga jakar ƴarsa sai ƴar tasa ya shigo ƙwafa ta yi ta juya musu
baya ta koma bacci.

Ko da asuba da ya tashi ya tashe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login